An dakatar da daukar sabbin 'yan sanda aiki a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a fadin Najeriya da sauran lungu da saƙo na duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa and Sani Aliyu

  1. Ban kwana 🤩

    Planet Jupiter

    Asalin hoton, NASA

    Masu iya magana na cewa "laifin dadi karewa", kuma mun kawo karshen wannan yini na kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke aukuwa a ciki da wajen Najeriya da Nijar da Ghana da Chadi da kuma Kamaru.

    A madadin sauran abokan aikina kamar Aisha Shariff Baffa wadda ta bude wannan shafin tun da sanyin safiya, ni Sani Aliyu ke muku fatan alheri, da kuma fatan mai duka ya kare mu daga dukkan abin da zai cutar da mu.

    Bari in bar ku da wannan hoton na duniyar Jupiter wadda na'ura mai hangen nesa ta James Webb da hukumar binciken sarari samaniya ta Amurka wato NASA ta aika ta dauko.

    Sai da safe!

  2. Ukraine na tsammanin karin dala biliyan 16 daga wajen kawayenta

    Firaiministan Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaiministan Ukraine

    Firaiministan Ukraine ya ce suna tsammanin za su samu karin taimako na dala biliyan 16 daga wajen kawayensu a cikin shekarar nan.

    Denys Shmyhal, ya ce a yanzu kasarsu ta dawo daidai, kuma mai yiwu ne da taimakon kasashen yamma, a don haka suna masu matukar godiya.

    To amma ya ce fiye da kaso 40 cikin 100 na kudaden da gwamnatinsu ta kashe sun tafi ne a bangaren sojoji.

    Ya ce an kara wa sojojin albashi, sannan an sayi makamai da sauran kayan aiki.

  3. Tilas a hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Goni Aisami – JNI

    Marigayi Sheikh Goni Aisami

    Asalin hoton, Family Goni Aisami

    Bayanan hoto, Marigayi Sheikh Goni Aisami

    Jama’atu Nasiril Islam (JNI) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da kuma hukumomin sojin kasar da su yi adalci, su hukunta wadanda suka kashe Sheikh Muhammad Goni Aisami cikin hanzari.

    Cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ta JNI Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu, kungiyar ta jaddada cewa tilas a dauki matakin ladabtarwa kan masu hannu a wannan kisan.

    Sai dai ya kara da cewa hukumomin Najeriya su daina kawar da kai kan wadannan jerin kashe-kashen da a yanzu suka zama ruwan dare, "Muna da karfin gwuiwa cewa ana kitsa wadannan kashe-kashen ne da gangar."

    JNI ta kuma ce "duk da cewa sojoji biyun da aka kama, wato John Gabriel da Adamu Gideon, sun hada baki domin sace motar malamin addinin Islaman, al'ummar Musulmi ba su fito sun tuhumi 'yan ta'adda Kirista da kai wa Musulmi hari ba, wanda da Kirista aka kai wa irin wannan harin, da tuni kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta fara kururuwa cewa Musulmi sun halaka wani fasto ko rabaran, sannan da tuni kafofin yada labarai sun cika shafukansu da labarin."

    Sanarwar ta kuma ce kisan da aka yi wa Sheikh Aisami alama ce ta yadda aikata manyan laifuka ya kai ga dukkan sassa na kasar nan, har ma ya kai ga jami'an tsaro, wadanda aikinsu ne su kare rayukan al'umma.

  4. Shugaba Buhari ya umarci a hukunta sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

    Shugaba Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar yi Allah-wadai da abin da ya kira "kisan babu gaira-babu-dalili da aka yi wa Sheikh Goni Aisami" wanda ake tuhumar wani sojan Najeriya da kashe shi bayan da shaihin malamin ya ya rage masa hanya a motarsa, kamar yadda ƴan sanda suka tabbatar.

    Yayin da yake mayar da martani kan lamarin, cikin wata sanarwa da kakakinsa Mallam Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce "wannan mummunan kisan da sojan Najeriya yayi wa wannan mutumin kirkin da ya taimake shi ba hali ne da aka san sojojin kasar nan da shi ba, kuma ya yi hannun riga da horon da ak ba sojoji na nuna da'a da girmamawa da kare rayukan wadanda ba su aikata wani laifi ba."

    Shugaba Buhari ya kara da cewa, "a matsayi na na babban kwamandan sojojin Najeriya, na fusata matuka kan wannan mummunan aikin da jami'in tsaro da aka horas domin ya kare rayuka ya aikata."

    Ya kuma yi kira ga hukumomin sojin kasar "da su hukunta wadanda suka aikata wannan kazamin laifin ba tare da bata lokaci ba, sannan su yi waje da ire-iren wadannan sojojin masu mummunan hali."

    A karshe ya mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Jihar Yobe da jama'ar jihar da kuma iyalan Sheikh Goni Aisami.

  5. An dakatar da ɗaukar sababbin ƴan sandan Najeriya bayan Sufeton-Janar na Ƴan sanda ya koka

    Nigeria Policemen

    Asalin hoton, NPF.GOV.NG

    Hukumar da ke kula da batutuwan da suka shafi aikin dan sanda a Najeriya (PSC) ta dakatar da aikin daukar sababbin kuratan ƴan sanda.

    Hukumar ta dauki wannan matakin ne kasa da sa'a 24 bayan da sufeto-janar na ƴan sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana bacin ransa kan wani talla da aka wallafa kan daukan masu sha'awar aikin dan sandan.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar, sufeto-janar din ya bukaci ƴan Najeriya su yi watsi da tallan da aka wallafa a wsu manyan jaridun kasar.

    A nata bangaren, hukumar ta PSC ta ce akwai wani rashin fahimta tsakaninta da rundunar ƴan sandan Najeriya.

    Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya ce nan ba da dadewa ba za a sasanta kan wannan batun. Ya kuma ba masu sha'awar aikin da su jinkirta zuwa wani lokaci nan gaba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta PSC ta taba kai karar rundunar ƴan sandan Najeriyar da tsoho sufeto-janar Mohammed Adamu kan gudanar da aikin daukan kuratan ƴan sanda 10,000 a 2019, sai dai daga baya sun sasanta.

  6. Wayar salula ta yi sanadin ƙonewar gidan mai ƙurmus a garin Badagry na Jihar Legas

    Petrol station on fire

    Asalin hoton, Other

    Hukumar ƴan kwana-kwana ta Jihar Legas ta ce a ranar Litinin, wani mutum ya sami raunuka bayan da wani abu ya fashe a wani gidan mai mai zaman kansa da ke garin Badagry na jihar.

    Babban jami'i da ke kula da reashen hukumar ta Badagry Abel Husu ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar wannan iftila'in.

    ya ce hukumar tasu ta sami labarin abin da ke aukuwa ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin karfe 8:55 na ranar ta Litinin.

    Ya ce jami'ansa sun isa gidan man bayan minti 10 da sami rahoton, kuma nan take suka fara kokarin kashe gobarar.

    "Bincikenmu ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya haddasa gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa".

    Ya kuma ce "bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take".

    Sai dai ma'aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba ma sa fetur cikin wata jarka.

  7. Najeriya ta hana kafofin yada labarai amfani da ƴan kasar waje cikin tallace-tallacen da suke haskawa

    Dakta Olalekan Fadolapo

    Asalin hoton, Dakta Olalekan Fadolapo

    Bayanan hoto, Dakta Olalekan Fadolapo na hukumar ARCON

    Hukumar da ke kula da tallace-tallacen da ake yadawa a kafofin yada labarai ta Najeriya (ARCON) ta sanar cewa ta hana kafofin yada labaran kasar yin amfani da ƴan kasashen waje har da muryoyinsu cikin tallace-tallacen da da ake yada wa cikin kasar.

    Hukumar ta sanar da haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar wadda babban daraktan hukumar, Dakta Olalekan Fadolapo ya sanya wa hannu, inda ta ce hanin zai fara aiki ne daga 1 ga watan Oktoban wannan shekarar.

    Dakta Fadolapo ya kuma ce tilas a far amfani da ƴan Najeriya ko muryoyin ƴan najeriya cikin dukkan tallace-tallacen da za a rika haskawa da yadawa a kafofin yada labarai na fadin kasar.

    Sai dai ya kara bayani, inda ya ce talace-tallacen da ake haskawa a halin yanzu na ya ci gaba har zuwa lokacin da kwangilar da aka cimma tsakani masu tallan da kafofin yada labaran ta kawo krshe.

    Daga wannan lokacin ya ce tilas masu tallace-tallacen su nemi izini daga hukumar.

  8. An daure ɗan Birtaniya tsawon shekara 21 saboda kisan wata ƴar gudu hijira

    Yordanos Brhane had just started to build a life for herself in Birmingham when she was stabbed to death

    Asalin hoton, FAMILY

    Bayanan hoto, Yordanos Brhane ta fara natsuwa a rayuwarta a garin Birmingham sai kwatsam aka hallaka ta

    Wani mutum zai shafe akalla shekara 21 a kurkuku bayan da ya yarda cewa shi ne ya kashe wata ƴar gudun hijira da ta ki amincewa da soyayyar da ya bayyana ma ta.

    An gano gawar Yordanos Brhane, mai shekara 19 da haihuwa da alamun an daba ma ta wuka a cikin gidanta da ke layin Unett a Hockley cikin Birmingham a ranar 31 ga watan Yulin 2021.

    Halefom Weldeyohannes, mazaunin titin London a garin Sheffield ya fusata bayan da Miss Brhane ta sanar da shi cewa ba ta sha'awar su yi soyayya, kamar yadda aka shaida wa wata kotu.

    yayin da yake yanke ma sa hukunci, alkalin kotun Birmingham Crown Court ya bayyana Halefom mai shekara 26 a matsayin wanda ya ke "haukar son Yordanos".

    Ya ce, "saboda ta ki amince ma ka, sai ka fusata kuma ka kai ma ta hari har ka kashe ta."

  9. An kama jami'an ƴan sandan Colombia bisa laifin kisan wasu matasa uku

    Dan sanda

    Asalin hoton, COLOMBIAN POLICE

    Bayanan hoto, Dan sanda

    An kama jami'an ƴan sanda goma a kasar Colombia bisa tuhumar suna da hannu a kisan wasu matasa uku.

    An harbe matasan uku ne a lokacin da suke hannun ƴan sanda a lardin Sucre na arewacin kasar a ranar 25 ga watan Yuli.

    Wan jami'in ɗan sanda mai mukain kanar, na cikin wadanda ake tuhuma sai dai ya tsere kuma ana tunanin ba ya ƙasar.

    Colombia na da mummunan tarihi na "ɓoye gaskiya" inda sojoji ke kashe fararen hula kuma su ce ƴan tawaye ne domin kawai su kara yawan masu laifin da suka kashe.

    Wani bincike ya gano cewa a bara sojojin Colombia sun kashe mutane sama da 6,400 tsakanin shekarar 2002 zuwa ta 2008 tare da yi musu sharri cewa abokan gaba mayaƙa ne.

  10. 'Yan sanda na bincike kan kisan jami'in zaɓe a Kenya

    'Yan sanda a Kenya na bincike kan kisan wani jami'in hukumar zaɓe lokacin zaɓen da aka yi, lamari irin haka cikin mako guda.

    Rahotanni sun bayyana cewa, Geoffrey Gitobu ya fadi ne kuma ba da jimawa ba rai ya yi halin shi a wani asibiti da tsakiyar garin Nanyuki.

    A makon da ya wuce ma an gano gawar wani jami'in hukumar mai suna Daniel Musyoka, mai kula da mazabar birnin Nairobi, bayan shafe kwanaki ana nemansa.

    Gawar ta nuna an azabtar da shi kafin ya mutu.

    Shugaban hukumar zaben Kenya, Wafula Chebukati, ya ce an yi aikewa jami'ansu sakonnin barazana a lokacin zaben shugaban kasa a farkon watan nan.

    Mataimakin shugaban kasa Willian Ruto ne ya yi nasara, yayin da madugun 'yan adawa Raila Odinga ya sha kaye tare da watsi da sakamakon.

  11. Yarinya 'yar shekara tara ta mutu bayan an harbe ta a kirji

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, 'Yan sanda

    Wata yarinya 'yar kimanin shekara tara da haihuwa ta mutu bayan an harbe a Liverpool.

    Rahotanni sun ce wani mutum ne ya harba bindiga cikin wani gida da ke layin Kingsheath a Dovecot a ranar Litinin din da ta wuce.

    An harbi yarinyar ne a kirji kuma ta mutu bayan an kai ta asibiti, sannan akwai wani mutum da wata mata da suma suka samu raunuka sakamakon harbin da aka yi musu.

    Tuni 'yan sanda suka rufe hanyar wajen a yayin da suka bazama don gano mutumin da ya yi harbin.

    Jami'an 'yan sandan da suka je wajen sun ce suna neman hadin kai da goyon bayan mazauna unguwar da lamarin ya afku don gano mutumin.

  12. Masu zanga-zanga na zaman dirshan a Iraqi

    Firaiministan Iraqi, Mustafa al-Kadhimi, ya katse ziyarar da ya ke yi a Masar saboda zaman dirshan din da masu zanga-zanga suka yi a harabar shalkwatar shari'a da ke birnin Bagadaza.

    Hukumar shari'a a kasar dai ta dakatar da dukkan zaman shari'un da kotuna ke yi a birnin saboda zanga-zangar da mabiya fitaccen malamin mabiya mazhabar shi'a Moqtada al-Sadr suka shirya.

    Masu boren sun rika ihu da rera wakar kalaman batanci ga gwamnati.

    Tun makwanni uku da suka gabata ne magoya bayan malamin ke ta zanga-zanga da zaman dirshan a majalisar kasar in da suke kiran dukkan 'yan majalisar su sauka daga mukaminsu, a kuma gudanar da sabon zabe.

  13. Manoma sun koka da karancin takin zamani a Kano

    Takin zamani

    Asalin hoton, OTHER

    Bayanan hoto, Takin zamani

    Wasu manoma a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, sun koka da gazawar gwamnatin jihar na wadata su da takin zamani.

    Manoman sun ce duk da an raba musu takin ta hanyar kungiyoyinsu da ke kauyuka, wadda aka raban bata kai ta kawo ba.

    Wasu manoma da BBC ta tattauna da su sun ce baya ga karancinta ga kuma tsadar da ta yi in da har wadanda ke siyan buhu a da a yanzu sun koma siyan rabin buhu, yayin da wadanda ke siyan rabin buhu a da kuma, sun koma siyan kwano-kwano.

    A don haka suka ce a yanzu yawancinsu sun koma amfani da kashin dabbobi, shi dinma sai wanda ke da farcen susa ne ke samunsa in ji su.

    Karancin takin ya afku ne bayan da ma'aikatar kula aikin noma da bunkasa karkara ta tarayya ta rufe wasu kamfanoni da ke yin takin hudu da aka zarga na aiki ba bisa ka'ida ba.

    Tun a farkon damunar bana ne dai manoma a Najeirya suka fara koka wa kan yadda farashin takin zamanin yayi tashin gauron zabi, wani dalili da masu lura da al’amuran yau da kullum ke masa kallon akwai bukatar a sake duba wannan matsala.

  14. Tsohon firaiministan Malaysia zai fara zaman gidan kason shekara 12

    Najib Razak

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Najib Razak

    An yanke wa tsohon firaiministan Malaysia Najib Razak, hukuncin zaman kaso na shekara 12, bayan babbar kotun kasar ta yi watsi da karar da ya daukaka.

    Tsohon firaiministan mai shekara 69 da haihuwa, ana tuhumarsa da hannu a badakalar cin hanci ta gidauniyar kasar.

    An tabbatar da laifin na sa ne a watan Yulin 2020, to amma an bayar da belinsa a yayin da ya daukaka kara.

    Kotun ta kuma ki amincewa da jan kafa wajen yanke masa hukuncin kamar yadda ya nema..

    Najib Razak, dai ya musanta aikata bai daidai ba.

    An yanke masa hukuncin da kuma biyan tarar dala miliyan 46 da dubu dari takwas.

    Masu kare shi sun ce Najib, ya yi tsammanin kudin da ya gani a asusunsa na banki kyauta ce daga masarautar Saudi Arabiya.

    Suka ce masu bashi shawara kan harkokin kudi ne suka yaudareshi da har ake tuhumarsa.

  15. Matashiyar da ke ceto yara daga gobarar dajin Aljeriya ta mutu

    Gobarar daji

    Asalin hoton, ALGERIAN CIVIL DEFENCE

    Bayanan hoto, Gobarar daji

    An bayyana wata matashiya Dounia Bouhelassa, mai shekaru 18 a matsayin gwarzuwa a Algeria, bayan ta mutu sakamakon raunukan da ta samu a yayin ceton yara daga gobarar dajin kasar.

    An rinka sanya hotunan matashiyar a kafafan sada zumunta in da ake jin-jina mata a kan rawar da ta taka na ceto yara da dama.

    Rahotanni daga kafar yada labaran kasar sun ce matashiyar ta ceci gwamman yara a wani wajen wasa da ke birnin El Kala a gabashin kasar.

    Matashiyar wadda 'yar kungiyar 'yan sikawut ce ta fada cikin wutar ne a yayin da ta ke tafiya a kan wasu katakwaye a makon jiya.

    Abokan aikinta takwas sun samu raunuka a yayin da suke aikin ceton tare.

    Fiye da mutum 40 sun mutu, yayin da wasu 200 kuma suka samu rauni a sakamakon gobarar dajin da ta afka wa arewa maso gabashin kasar ta Aljeriya.

    .

  16. Ukraine ta ce an kashe sojojin Rasha dubu 45

    Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rasha

    Rundunar sojin Ukraine ta ce an kashe sojojin Rasha fiye da dubu 45 tun bayan da shugaba Putin ya fara mamaye kasar a watan Fabrairun da ya wuce.

    A shafinta na Facebook, rundunar ta ce ya zuwa yanzu an kashe sojojin Rasha dubu 45,500, adadin da BBC ba ta tabbatar da su ba.

    Tun daga watan Maris Rasha ba ta kara fitar da wani adadi na sojojinta da aka kashe a yakin da take a Ukraine ba.

    A watan Maris ne Rasha ta ce an kashe mata sojjoji dubu daya da dari uku da hamsin da daya, adadin da kasashen yamma suka musanta tare da cewa yafi haka.

    Binciken da BBC ta yi ya gano cewa an kashe sojoji dubu biyar da dari hudu da goma sha shida a yakin da ake a Ukraine din.

    An dai samu wannan adadi ne daga sanarwar da jami'an gwamnati da na jami'oi da kuma kafafan yada labarai ke yi.

  17. An sake samun bullar Ebola a Congo

    Jami'an lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce an samu wata mata da ta kamu da cutar Ebola a lardin arewacin Kivu da ke kasar.

    Matar mai shekara 46, ta mutu ne a ranar 15 ga watan Augustan da ya wuce a wani asibiti da ke Benni.

    Jami'an sun ce matar ta fara rashin lafiya a hankali daga nan kuma sai ta fara nuna alamomi na cutar Ebola a tare da ita.

    Ana dai samun sake bullar cutar akai- akai a kasar abin da mahukunta suka ce abin damuwa ne.

    A yanzu haka an tattara wadanda matar ta yi mu'amala da su don yi musu gwaji a kan cutar.

    Jami'an lafiyar sun ce a yanzu haka akwai rigakafin cutar Ebola dubu guda a kasar, a in da a yanzu za a aika 200 zuwa Beni don dakile yaduwarta a garin.

  18. Za a kafa wuraren fake wa hare-haren bam a Ukraine

    Mafaka

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Mafaka

    Shugaban Zelensky, na Ukraine, ya sanya hannu kan wata sabuwar doka ta kafa wuraren fake wa hare-haren bama bamai a sabbin gine-ginen kasar.

    A watan Yuli bangaren majalisar dokokin kasar ya kafa wata doka wadda Zelensky, ya sanya hannu a daren jiya Litinin.

    Kazalika cikin dokar za a samar da abubuwa da kuma na'urori daban-daban a wuraren fakewar.

  19. 'Yan sanda sun kama mutum 18 da ake zargi da satar mutane a Benue

    'Yan sanda
    Bayanan hoto, 'Yan sanda

    Rundunar 'yan sanda a jihar Benue da ke Najeriya ta ce jami'anta sun kama wasu mutum 18 da ake zargi da satar mutane tare da kwace makamai daga wajensu.

    Mai magana da yawun rundunar, Catherine Anene Sewuese, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce mutanen da ake zargin sun yi kokarin tserewa jami'an 'yan sanda a wani wajen binciken ababen hawa a kan hanyar karamar hukumar Utonkon inda aka kama su.

    Ta ce an samu makamai a wajen mutanen ciki har da bindiga daya samfurin AK-47, da kananan bindigogi biyu da kuma alburusai da dama da aka nade a jarida.

    Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce tuni aka kaddamar da bincike a kan mutanen wadanda yanzu haka ke hannun 'yan sanda a tsare.

    A bangare guda kuma, rundunar 'yan sandan jihar Gombe ma ta ce ta kama wasu mutum biyu da take zargi da satar mutane da kuma mallakar makamai.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP, Mahid Mu'azu, ya raba wa manema labarai, ya ce mutanen dukkansu daga karamar hukumar Dukku, an kama su ne a kan hanyarsu ta zuwa maboyar da suke taruwa a dajin Yankari da ke Bauchi.

    Ya ce, an kama su ne a ranar 19 ga watan Augusta a kauyen Tudun Kwaya da ke karamar hukumar Biiliri tare da hadin gwiwar jami'an sintiri da mafarauta a yankin.

    Ya ce koda aka tambayesu sun bayyana cewa suna daga cikin masu satar mutanen da ke addabar mutane a Pindiga.

  20. Jami'in zaben Kenya ya mutu a wani yanayi mai daure kai

    Zabe

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Zabe

    Wani jami'in zabe a Kenya wanda ke kula da mazaba guda a zaben da aka kammala a kasar ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a ranar Litinin.

    Geoffrey Gitobu, na cikin ofishin hukumar zabe da ke garin Nanyuki, a tsakiyar Kenya, a nan ne kawai aka ga ya yanke jiki ya fadi aka kwasheshi sai asibitin da ke kusa da ofishin kafin aje ma ya mutu.

    Jami'in shi ne wanda aka tura daga hukumar zaben kasar don kula da zabukan mazabun Gichugu da kuma Kirinyaga da ke tsakiyar Kenya.

    Rahotanni sun ce mr Gitobu, bai bayyana cewa bashi da lafiya ko kuma wani abu na damunsa ba, kuma sai da ya ziyarci wasu 'yan uwansa a karshen mako kafin ya je ofishin zaben da ya yanke jiki ya fadi a can.

    Wata jam'ar zabe da suke aiki tare Jane Gitonga, ta ce mutuwar abokin aikin na su ta girgiza su, kuma ya mutu ne kwanaki bayan kisan wani jami'insu a Nairobi.

    Wata kwamishinar zabe a hukumar zaben kasar, ta ce jami'ansu na fuskantar barazana kala-kala tun bayan kammala zaben kasar a ranar 9 ga watan da muke ciki.