Shugaba Buhari ya taya William Ruto murnar cin zaben shugaban Kenya

Asalin hoton, BUHARI SALLAU
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya mutumin da ya ci zaben shugaban kasar Kenya, William Ruto, murna.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Buharin a harkokin yada labarai Femi Adesina, ya fitar a yau Litinin, ya ce, shugaban ya yaba wa al'ummar kasar ta Kenya kan yadda aka fitar da sakamakon zaben na ranar 9 ga Agustan nan a fayyace kuma lami lafiya.
Shugaban ya kara da cewa zaben ya nuna yadda tsarin na dumukuradiyya da manufofi da kuma hanyoyinsa shi ne har yanzu hanyar da ta fi dacewa wajen zabar shugabanni da kuma bincikensu.
Shugaba Buhari ya ce Najeriya na martaba Kenya a matsayin muhimmiyar kawa a yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi na tayar da hankali.
Alakar da ta danfaru a dadadden tarihi na abokantaka da tattalin arziki da kasuwanci da kuma kyakkyawar mu'amulla ta aiki tare a kungiyoyin kasa da kasa kamar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashe renon Ingila (Commonwealth).
Bayan fata da Shugaban na Najeriya ya yi wa Mista Ruto na rantsar da shi da kama aiki cikin nasara, ya ce yana fatan ci gaba da samun kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu a kan muhimman abubuwa na hadin gwiwa da suka fi ba fifiko kamar zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka da dumukuradiyya da kuma bunkasar tattalin arziki da kyautatuwar rayuwar jama'a.
Haka kuma Buharin ya yaba wa Shugaba Uhuru Kenyatta a kan dattijantaka da shugabanci na-gari da ya ce ya nuna ga al'ummar Kenya a shekara tara da ta gabata.
Da kuma irin muhimman ababan tarihi da gwamnatinsa ta samar a fannin kayan jin dadin jama'a da ilimi da sauye-sauye a harkar kula da lafiya da yawon bude idanu tare da kwakkwaran tasiri da tallafi ga tsaron nahiyar.
















