Bissalam
Da haka za mu yi bankwana da ku sai kuma gobe Litinin. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
A wannan shafin za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a duk fadin Najeriya da sauran lungu da saƙo na duniya.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin
Da haka za mu yi bankwana da ku sai kuma gobe Litinin. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani kasurgumin ɗan fashin daji Albdulkarim Boss da mutanansa 27 a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaƙi ya yi a kan maboyarsu.
Abdulkareem Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareem Boss, an jima ana farautarsa kafin a hallaka shi a wannan lokaci.
Hare-haren sama da sojojin suka kaddamar na zuwa ne kasa da mako guda da shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da su ka yi alkawarin kawo ƙarshen matsalolin tsaron Najeriya.
An hallaka ɗan fashin ne a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana ta Katsina.
Abdulkareem ne ya jagoranci muggan hare-haren ta'addanci da dama a yankunan arewacin Najeriya da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Sannan shi ya jagoranci kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa a Daura da kuma mutuwar shugaban 'yan sanda yankin Dustinma a cikin watan Yuli.
An kuma kai irin wadannan hare-haren sama a maboyar 'yan bindiga a kauyukan Abuja a cewar jaridar PRNigeria.
A cewar rahotanni 'yan bindiga da ke maboya a dazukan Kaduna da Neja da Zamfara ke haifar da barazanar tsaro a babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.
Dan takarar jam’iyyar ADC, Sani Muhammad Gumel ya ce kayar da sauran manyan jam'iyyu gare shi ba abu ne mai wahala, la'akari da gaza tabuka abun azo a gani da suka yi yayin da talakawa suka basu dama a baya.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya ce ya yi afuwa ga tsohon abokin hamayyarsa Lauren Gbagbo.
Tsohon Shugaban na fuskantar zaman gidan yari na tsawon shekaru 20, bisa kama shi da laifin kawo rikicin siyasa a 2010 zuwa 2011.
A wani jawabi yayin cikar kasar shekaru 62 da samun yancin kai, Shugaba Ouattara ya ce ya yi hakan ne da nufin hada kan 'yan kasar.
A baya kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke Mr Gbagbo da zargin tada husuma, bayan kin amsa shan kaye a zaben 2010, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma'aurata bayan kashe jami'an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.
A cewar mazauna unguwar 'yan bindigar sun far mu su ne da misalin ɗaya da minti ashirin da biyar na dare, kuma sun shafe sa'a guda su na harbe-harbe.
Sun shaida cewa 'yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma'auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.
Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa 'yan bindigar sun fi karfinsu.
Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura jiya dauke da bindigogi suna harbe-harbe.
Mutumin yace ‘yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata.
Ya kuma ce baya ga ma'auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ‘yan bindiga sun shiga yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.
Bugu-da-kari SP Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.
Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.
Ƙungiyar dattawan arewacin kasar ta yi tir da harin da wasu 'yan bindiga ke kaiwa kan al'ummar arewa mazauna kudu, tana gargadi cewa lamarin zai iya rikita kasa baki daya.
Kungiyar ta bukaci masu neman takara a 2023 da su fito su la'anci masu wannan aika-aikar.
Ko a makon da wuce an kashe wasu 'yan asalin jumhuriyar Nijar a yankin kudu maso gabashin Najeriyar, wadanda ake zargin sun zaci 'yan arewacin Najeriya ne.
A saurari karin bayyanin da Dr Hakeem Baba Ahmed kakakin kungiyar, ya yi wa BBC.

Asalin hoton, Horniman Museum
Wani gidan ajiye kayan tarihi a birnin Landan ya amince zai mayar wa Najeriya kayayyakin da aka sata daga ƙasar a ƙarni na 19 daga Masarautar Benin.
Gidan kayan tarihi na Horniman Museum ya ce zai miƙa kayan 72 ga gwamnatin Najeriya.
Kayayyakin sun ƙunshi tagullar Benin 12, da kuma makullin shiga fadar sarki.
Gidan tarihin da ke kudancin Landan ya ce ya shawarci mazauna unguwar da masu ziyara da yara 'yan makaranta da malaman jami'a da ƙwararru kan al'adu da masu zane-zane da ke Birtaniya da Najeriya kafin ɗaukar matakin.
Hukumar kula da wuraren ajiye kayan tarihi ta Najeriya ce ta miƙa buƙatar mayar mata kayayyakin.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani tsohon soja mai shekara 90 da zargin yi wa 'yan fashin daji safarar ƙwayoyi a Jihar Sokoto.
Wata sanarwa ta ce an kama Usman Adamu ne ranar Laraba, 3 ga watan Agusta a garin Mailalle na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.
"An kama shi da tabar wiwi mai nauyin 5.1kg," a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.
Kazalika a ranar Alhamis, hukumar ta kama wata mota a JIhar Zamfara maƙare da ƙwayar Diazepam 50,000 a kan hanyarta ta zuwa Sokoto daga birnin Benin na Jihar Edo, wanda ta ce mallakar wani ne mai suna Umaru Attahiru.
A wani binciken na daban, NDLEA ta damƙe wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong da duro uku na ƙwayar crystal methampetamine - wadda ake kira Mkpuru Mmiri a Najeriya.
Kayan da NDLEA ke zargin an shiga da su ne daga Indiya, an kama su yayin da ake shirin kai su wani wuri a birnin Legas lokacin da aka tare motar da ke ɗauke da su.

Asalin hoton, NDLEA

Asalin hoton, @KatsinaPoliceNG
Mutum aƙalla shida ne dakarun 'yan sandan Najeriya suka kuɓutar bayan sun kai samame kan sansanin 'yan fashin daji a Ƙaramar Hukumar Danja ta Jihar Katsina, a cewar rundunar.
Kakakin 'yan sandan a Katsina, SP Gambo Isah, ya ce sun samu nasarar ce a ƙauyen Tandama ranar Asabar bayan jami'an tsaro sun samu bayanan sirri.
Mutanen da aka ceto su ne: Alhaji Garba Dan Mallam mai shekara 52, Rabiu Idris mai 45, Abba Sama’ila mai 38, Yunusa Sani mai 54, Ishaq Yakub mai 40, Danjuma Sama’ila mai 45.
Wasu rahotanni sun ce rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya ta yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan fashi Abdulkarim Faka-Faka a yankin na Tandama tare da raunata yaransa da dama.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar tsere ta matan Najeriya ta sake yin nasarar lashe zinare a tseren mita 400 da ke gudana tsakanin ƙasashe rainon Ingila a birnin Birmingham na Birtaniya.
Tawagar ta 'yan wasa huɗu ta ƙunshi Tobi Amusan, da Rosemary Chukwuma, da Grace Nwokocha da kuma Favour Ofili.
Kafin yanzu, Tobi Amusan ta ci zinare a tseren mita 100, har ma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya ta murna.
'Yan tseren sun kafa tarihin kammala gudun cikin daƙiƙa 42.10, wanda babu wata tawaga daga Afirka da taɓa yi.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar Lafiya ta Zirin Gaza ta yi gargaɗin cewa awa 48 kacal suka rage kafin dukkan kayayyakin aikin lafiyar da take da su su ƙare a yankin sakamakon datse hanyoyin shiga da fita da Isra'ila ta yi.
Sanarwar da ta fitar na cewa ba za ta iya ci gaba da ayyuka a asibitoci ba saboda tashar lantarki tilo da take bai wa Gaza wuta ta rufe saboda rashin man fetur da take fama da shi.
Yanzu haka asibitocin na aiki ne da ƙananan injinan lantarki, waɗanda ke fama da ƙarancin man su ma.
Ya zuwa yanzu, ma'aikatar lafiyar ta ce an jikkata Falasɗinawa 215, yayin da jiragen Isra'ilar ke ci gaba da ruwan wuta a kan unguwannin Gaza.
Isra'ila ta ce tana harar mayaƙan ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad ne, amma hare-haren sun kashe fararen hula 32 zuwa yanzu.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi shugabanni da mazauna yankin kudu maso gabashin ƙasar da su bayyana waɗanda ke kashe baƙi da jami'an tsaro a yankin "idan sun san inda suke".
Kiran shugaban na zuwa ne kwana ɗaya bayan wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda huɗu ranar Asabar da kuma kisan fararen hula shida a farkon mako a Jihar Imo.
Rundunar 'yan sandan ƙasar ta ce mayaƙan ƙungiyar IPOB ne suka kai harin kan jami'anta a ofishinsu da ke Agwa na Jihar ta Imo.
Buhari ya kira kisan a matsayin "na ta'addanci" sannan ya nemi shugabannin yankin da "su dinga nuna ƙyamar kashe-kashen a fili don tsare al'adu da addinin mutane".
"Waɗanda suka san mutanen da suka aikata hakan su bayyana su," in ji shi cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu ya fitar ranar Asabar.
Shugaban ya kuma yi alƙwarin gudanar da bincike "na gaggawa" don gano "waɗanda suka aikata ta'addanci".

Asalin hoton, Getty Images
Makaman kariya na Isra'ila da ake kira Iron Dome sun harbe kashi 97 cikin 100 na makaman roka da Falasɗinawa ke harba mata tun ranar Juma'a, a cewar rundunar sojan ƙasar.
Tun a shekarar 2011 aka kafa na'urorin da ke harba makami mai linzami don kakkaɓe makamin da aka harbo kuma ƙwararru daga Amurka da Isra'ila suka ce suna aiki da kashi 85 cikin 100.
"Muna ta ƙara inganta tsaronmu a kodayaushe," in ji mai magana da yawun rundunar sojan ta Isra'ila.
Jami'an Isra'ila sun ce mayaƙn PIJ sun harba rokoki kusan 600 cikin ƙasar tun daga ranar Juma'a.
A karon farko tun yaƙin da suka gwabza a 2011, makamin roka ya isa Birnin Ƙudus ɓangaren Isra'ila da 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa ke harbawa.
Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu na wannan makon ya karɓi baƙuncin ma'aikatanmu Awwal Janyau da Imam Saleh, waɗanda suka isa birnin Landan a farkon mako.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Jihar New Mexico da ke Amurka sun sanar cewa suna bincike kan ko kisan wasu Musulmai 14 na da alaƙa da juna.
A jiya Asabar 'yan sanda suka ce an kashe wani Musulmi kuma "kisan zai iya kasancewa yana da alaƙa da kisan wasu Musulmai huɗu 'yan asalin kudancin Asiya".
Gwamnan New Mexico Michelle Lohan Grisham ya bayyana ɓacin ransa game da kashe-kashen kuma ya bayyana goyon bayansa ga al'ummar Musulmi da ke jihar.
"Wannan tashin hankali ba Musulmi kaɗai yake shafa ba, har da Amurkawa baki ɗaya," kamar yadda ya faɗa wa majalisar tuntuɓa ta Musulman Amurka.
Daga ranar Juma'a zuwa yanzu, Isra'ila ta kashe mutum aƙalla 32.
Daga cikin waɗanda hare-haren suka kashe akwai yara shida da kwamandojin gwagwarmaya na Falasɗinawa biyu.
Ta ce ta ƙaddamar da hare-haren ne sakamakon "barazanar gaggawa" da ta fuskantar daga mayaƙan ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad (PIJ).
Su ma Falasɗinawa sun harba makaman roka kusan 600 tun daga Juma'a zuwa cikin Isra'ila, inda suka kai Birnin Ƙudus a karon farko tun Mayun 2021.

Isra'ila ta sake kashe wani kwamandan gwagwarmya na Falasɗinawa daga ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad (PIJ), yayin da adadin waɗanda ta kashe a hare-haren Zirin Gaza ke ƙaruwa.
Yara ƙananana shida da mayaƙan PIJ da dama - ciki har da jagorori Khalid Mansour da Tayseer Jabari - na cikin Falasɗinawa 32 da aka kashe zuwa yanzu.
Makaman roka da mortar kusan 600 'yan gwagwarmaya suka harba kan Isra'ila daga Gaza tun daga Juma'a, a cewar wani jami'in gwamnatin yankin.
Wannan ne tashin hankali mafi girma tsakanin ɓangarorin biyu tun wanda aka yi na kwana 11 a watan Mayun 2021, wanda ya yi sanadiyyar kashe Falasɗinawa fiye da 200 da kuma Isra'ilawa kusan 12.
Jami'an Isra'ilar na gargaɗin cewa hare-haren da take kaiwa za su ɗauki tsawon mako ɗaya.
A ranar Lahadi, makamin roka da Falasɗinawa ke harbawa sun kai Birnin Ƙudus a karon farko tun yaƙin 2021.
Maraba da sake haɗuwa a shafin rahotanni kai-tsaye tare da ni Umar Mikail.
Za mu kawo labarai na abubuwan da suke faruwa a sassan duniya, amma za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.
Barkanmu da hantsin Lahadi.