Gwamnatin jihar Benue ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran da ke faruwa a Najeriya da yammacin Afirka har ma da sauran sassan duniya baki daya.

Rahoto kai-tsaye

Bello Habeeb Galadanchi

  1. To jama'a a nan Muhammad Annur Muhammad ke muku sallama daga wannan shafi da muke kawo muku labaran kai tsaye. Sai kuma gobe Juma'a da safe idan Allah Ya kai mu. Kafin sannan mu kwan lafiya. Kamar yadda 'yan-magana kan ce Rai Dangin Goro....

  2. Tsohon Babban Sufeton 'Yan-sandan Najeriya Tafa Balogun ya rasu

    Tafa Balogun

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Shari'ar da EFFC ta gurfanar da shi a 2005 ta dauki hankalin duniya

    Tsohon Babban Sufeton 'Yan-sandan Najeriya, Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu bayan wata gajeruwar jinya a Lagos, yana da shekara 74.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata kafa daga iyalansa ta tabbatar mata cewa ya rasu ne a yau Alhamis da misalin karfe 8:30 na daren nan a wani asibiti da ke Lekki a Jihar Lagos bayan wata gajeruwar jinya.

    Balogun wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Agusta na 1947 a garin Ila-Orangun da ke jihar Osun, shi ne Shugaban Rundunar 'Yan-sandan Najeriya na 21 a tarihi, bayan da aka nada shi a makumin a watan Maris na 2002.

    Kafin ya kai wannan matsayi ya rike mukamai da dama da suka hada da mukaddashin kwamishinan 'yan-sanda a JIhar Edo.

    Ya kasance da Kwamishinan 'yan-sanda na farko na Jihar Delta. Ya kasance Kwamishinan 'yan-sanda na jihar Ribas da kuma Jihar Abia.

    Bayan da ya samu karamin mukami zuwa mataimakin babban sufeton 'yan-sanda mai kula da shiyya ta daya a Kano, daga nan ne likkafarsa ta yi gaba inda aka nada shi Sufeto Janar din a ranar 6 ga watan Maris na 2002.

    A ranar 4 ga watan Afrilu na 2005 hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati EFCC ta gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kan zargin sata da halatta kudaden haram sama da dala miliyan 100 a tsawon shekara uku da ya yi a mukamin Sufeto-Janar.

    Hukumar ta EFCC karkashin jagorancin Nuhu Ribadu ta tuhume shi da laifuka 70, inda daga bisani ya yi yarjejeniya ta bayar da wasu daga cikin kudade da abuibuwan da ake zarginsa da sace wa domin a sassauta masa, inda aka yanke masa hukuncin wata shida a gidan yari.

    Mai shari'a Binta Nyako ta zartar da cewa kasancewar ya nuna nadama kuma wannan shi ne lokaci na farko da ya aikata laifi ta sassauta masa hukunci.

    Ta umarci da ya biya Naira dubu 500 a kan kowanne daga cikin laifuka takwas da ya amince ya aikata daga cikin 56 da suka shafe shi kai tsaye, tarar da ta kama jumulla Naira miliyan 4.

    Mai shariar ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata shida a kan kowanne daga cikin laifukan 8, wadanda zai yi su tare.

    Shariar tasa ta dauki hankali inda a wani lokaci ya fadi a kujerar da ya ke a ranar 29 ga watan Yuni na 2005 a kotun.

    An sake shi a ranar 9 ga watan fabrairu na 2006 bayan da ya kammala wa'adin, wani daga ciki a babban asibitin kasa na Abuja.

  3. An tuhumi 'yan-sandan Amurka da laifin kashe bakar-fata

    Breonna Taylor

    Asalin hoton, Facebook

    Bayanan hoto, Breonna Taylor, mai shekara 26 ma'aikaciyar lafiya ce

    Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ta samu wasu jami'an ‘yan sanda 4 da kuma wasu tsoffin 'yan sanda a birnin Louisville kan kisan da aka yi wa wata mata bakar-fata.

    Mutuwar Breonna Taylor a shekarar 2020 na cikin abubuwan da suka janyo zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda 'yan-sanda ke wuce gona da iri a kan bakaken-fata wato Black Lives Matter a fadin Amurka.

    Babban lauyan gwamnatin jihar Kentucky Merrick Garland ya ce laifukan da ake zarginsu da aikatawa sun hada da keta hakkin bil-adama da amfani da karfi ba kan ka'ida ba.

    Ya ce ana kuma tuhumarsu da amfani da bayanan karya wajen samun sammacin shiga cikin gidan Ms Taylor mai shekara 26.

    A wancan lokaci masu gabatar da kara a jihar ta Kentucky sun yanke shawarar cewa ba za su tuhumi kowane jami'in dan-sanda ba.

  4. Burtaniya na fuskantar koma bayan tattalin arziƙi

    Bank of England

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta haifar da tsadar rayuwa a duniya

    Bankin Ingila yayi hasashen cewa Burtaniya za ta fada matsalar tattalin arziki a wannan shekara.

    Hakan yana nufin tattalin arzikin kasar zai ragu wanda zai haddasa rashin aikin yi da kuma raguwar saye da sayarwa.

    An yi hasashen tattalin arzikin zai ragu a cikin wata uku na karshen wannan shekara inda zai ci gaba da raguwa har zuwa karshen shekara mai zuwa 2023.

    Babban dalilin karuwar tsadar rayuwa da ake fama da ita yanzu da kuma raguwar bunkasar tattalin arzikin kasar shi ne tsadar makamashi da farashinsa ke ta karuwa, sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    A mafi yawancin ƙasashen duniya, ciki har da Burtaniya, tilas tattalin arziƙin kasa ya ragu tsawon wata shida kafin a tabbatar cewa kasa ta shiga koma bayan tattalin arziki.

  5. Sudan ta Kudu mai fama da rikicin kabilanci ta jinkirta zaɓe

    Salva Kiir da Riek Machar

    Asalin hoton, AFP

    Shugabannin Sudan ta Kudu sun sanya hannu a kan wani shiri, da zai kara wa'adin mulkin gwamnatin rikon kwarya da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiya ta wata 24

    Karin zai fara ne daga ranar 22 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa, 2023.

    Shugaba Salva Kiir da tsohon abokin hamayyarsa, Riek Machar, wanda yanzu shi ne mataimakin shugaba da wasu manyan ƙusoshi sun rattaba hannu a kan shirin a babban birnin Kasar, Juba yau Alhamis.

    Wannan karin wa'adi na nufin Sudan ta Kudu ba za ta yi zaben da aka dade ana jira ba a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

    Sabuwar yarjejeniyar ta tanadi yin zaben a watan Disambar shekara ta 2024.

  6. Gwamnatin jihar Benue ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaro

    Jami'an tsaro

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Masana na ganin jihohi sun dawo daga rakiyar hukumomin tsaro na kasar ne

    Gwamnatin jihar Benue a Najeriya ta ƙaddamar da wata rundunar tsaro ta 'yan sa-kai mai suna Volunteer Guards.

    Benue na daya daga cikin jihohin da ake samun rikicin manoma da makiyaya, abin da kan kai ga kashe-kashe.

    Daga cikin ayyukan 'yan rundunar wadanda aka danka wa makamai, za su haɗu da ƴan sandan Najeriya da wasu hukumomin tsaro don mayar da martani kan hare-haren.

    Saboda ƙaruwar hare-hare da garkuwa da mutane a ƙasar, kananan hukumomi na tashi tsaye domin kare kansu da al'ummarsu.

    Ko a baya ma gwamnatin jihar Zamfara ta arewa maso yamma ta bukaci al'ummarta da su mallaki makamai domin kare kansu daga ƴan ta'adda da barayin daji.

    Wadanda suka addabe su da miyagun hare-hare da rashin kwanciyar hankali na gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

    Jihohin yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso gabashin Najeriya suma sun haɗa irin wannan rundunar tsaro mai suna

    Amotekun da Ebube-Agu don taimakawa wajen tsaro.

    Masana na ganin jihohi sun dawo daga rakiyar hukumomin tsaro na kasar ne shi ya sa suke samar da rundunonin tsaro na kansu.

    Domin maganin matsalar tsaro ta masu garkuwa da mutane da masu tsattsauran ra'ayi da ke ta kara habaka.

  7. Ana huce fushin fyaɗen taron-dangi a kan baƙin-haure a Afirka ta Kudu

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    Mazauna wani gari da ke kusa da Johannesburg a Afirka ta Kudu suna kona gidajen baƙin haure, wadanda suke ganin suna iki ne ba bisa ka'ida ba a wata mahakar ma'adanan da aka daina aiki da su.

    Jama'a a yankuna da yawa sun fusata saboda fyaden taron-dangi da wani gungun mahaƙa suka yi wa mata 8 a makon da ya wuce.

    Gomman mutane ne wadanda ke da alaka da harin, suke hannun jami'an tsaro amma babu wanda aka tuhuma da aikata fyade tukuna.

    A shekarun da suka gabata, talauci na daya daga cikin dalilan hare-haren ƙin baƙi.

    Wasu sun yi amanna cewa - ko da gaske ne, ko ba da gaske ba ne - baƙin haure ne tushen matsalolinsu masu yawa.

  8. Gwamnatin Plateau ta kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar

    DALIBAI

    Asalin hoton, OTHERS

    Gwamnatin jihar Filato ta kwace lasisin dukkan makarantun firamare da kuma na sakandari masu zaman kansu a fadin jihar.

    Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Elizabeth Wampum, ita ce ta bayyana hakan a yau alhamis.

    A cewarta, an dauki matakin ne bayan gano cewa sama da makarantu 5000 na koyarwa ba tare da lasisi ba.

    Kwamishiniyar ta ce kashi 90 cikin dari na makarantu masu zaman kansu a Filato ba sa bin ka'idoji da tsare-tsaren gwamnati.

    Inda ta kara da cewa kashi 85 na makarantu 495 masu zaman kansu da aka bai wa lasisi tun da farko ba su bi ka'ida ba.

    Elizabeth ta ce ana kuma sanar da al'umma cewa dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar za su sake sabunta lasisinsu.

    Gwamnatin ta ce za a yi hakan ne domin gano makarantun da ke koyarwa ba bisa ka'ida ba da kuma taimakawa wadanda doka ta san da zamansu, domin samar da ilimi mai inganci ga kowa.

  9. Ana binciken wani ma'aikacin jinya saboda hoton gawar wata da aka kashe

    Nayera Ashraf

    Asalin hoton, twitter

    An kaddamar da bincike a Masar dangane da wani hoto da ya fito da ke nuna gawar wata matashiya da ta rasa ranta a hannun wani mutum da ta ce ba ta son sa.

    Ana binciken ma'aikacin kiwon lafiyar ne a asibitin da aka kai Nayera Ashraf bayan an caccaka mata wuƙa a wajen jami'ar da take karatu a birnin Mansoura.

    Fitowar hoton ta ƙara fusata Misrawa a kan wata shari'a da ta jawo muhawara mai zafi dangane da lalatar da maza ke yi wa mata.

    An yanke wa mutumin da aka samu da laifin kisan, Mohamed Adel, hukuncin kisa.

  10. Makamai masu linzami biyar da China ta harba sun fada yankin Japan

    Japan PM

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Japan ya ce wasu makamai masu linzami biyar na kasar China da aka harba a wani bangare na atisayen soji a kusa da Taiwan sun fada cikin ruwan wani yankin tattalin arzikinta.

    Nubuo Kishi ya ce, wannan shi ne karo na farko da makamai masu linzami na kasar Sin suka fada cikin yankinta, inda Japan ta ce tana da hakkin gudanar da wasu ayyuka kamar kamun kifi.

    Chinar ta harba makaman roka da makamai masu linzami a cikin ruwan da ke kewayen Taiwan, a yayin atisayen soji da ba a taɓa ganin irinsa ba, a matsayin martani ga ziyarar da 'yar siyasar Amurka Nancy Pelosi ta kai wa yankin.

  11. An bai wa ma'aikatan gwamnati hutun kwana ɗaya saboda matsanancin zafi a Iraƙi

    Iraq

    Asalin hoton, Getty Images

    A Iraki an ba ma’aikatan gwamnati a jihohi da ke tsakiya da kudancin kasar hutun kwana guda bayan da yanayin zafi ya kai digiri 50 na maunin celtuis.

    An rufe ofishoshin gwamnati a birnin Bagadaza sai dai matakin bai shafi jamain tsaro da wadanda suke ayuika na musaman ba.

    A garin Basra mai tashar jirgin ruwa an ayanna hutun kwanaki hudu.

    Matsanancin zafi ba sabon abu ba ne a Iraƙi saboda yana daya daga cikin wurare mafiya zafi a duniya.

    Sai mazauna yankin sun ce lamarin yana kara yin muni ta hanyar daukewar wutar lantarki wanda ya sa ba a samun nauarar sanyaya iska watau AC.

    Sun kuma ce alamarin na kara taazara a kowace shekara.

  12. Burkina Faso ta ce sojojinta sun kashe fararen hula 30 bisa kuskure

    Sojojn Burkina Faso sun amince da kisan fararen jula da ba a san iya adadinsu ba yayin hare-haren sama da sojoji suka kai a kudu maso gabashin kasar, kamar yadda wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ta Lefaso.net ta ce.

    "Cikin rashin sa'a a lokacin harin na jiya, wanda aka hallaka ƴan ta'adda masu yawa, an yi kashe wasu fararen hula," Lefaso ta ce tana mai ambatar sanarwar sojojin.

    Rediyon Faransa na RFI ya ce an kashe akalla fararen hula 30 a hare-haren sama tsakanin Komoenga da Pognoa, kusa da kan iyakar Togo.

    Sojojin sun ce za a yi bincike don a gano wanda suka aikata laifin.

    A makon jiya, Togo ta bayar da hakurin kashe akalla fararen hula bakwai, waɗnda aka dauka ƴan ta'adda ne, abun da ya ƙara jawo tsoro da fargaba a kan yaɗuwar rikici daga Burkina Faso.

  13. Majalisar Dattijai ta bai wa hafsoshin tsaro wata hudu su kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Senate

    Majalisar Dattijan Najeriya ta bai wa manyan hafsoshin tsaron kasar wa’adin wata hudu su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar.

    Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi wata doguwar ganawa da shugabannin a jiya, duk da cewa majalisar tana hutu.

    A baya-bayan nan dai lamarin tsaro ya sukurkuce, al’amarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin bai sauya salo ba.

    Majalisar dokoki ta bayyana tsor da damuwarta game da ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, musamman harin da ƴan ta'adda suka kai kwanan nan a Abuja.

    Shugaban majaliar dattijai, Ahmad Lawan, ya kira shugabannin tsaro taron gaggawa a jiya, inda ya lamari ne mai ban tsoro.

    A taron, sanatoci sun bai wa shugabannin tsaro shawarwari a kan yadda za a kare Birnin Tarayya da ƙasar gaba daya.

    Mafi yawan kwamitocin majalisar dokokin su ma sun gana da shugabannin tsaro akan matsalolin tsaron a Juma'ar da ta wuce don sanin me ake ciki a ƙasar.

    Majalisar wakilai ta ce ƴan ta'adda suna barazanar kai hari Abuja inda fadar shugaban ƙasa take, inda suka ce dole hukumomin tsaro su yi maganin masu tayar da ƙayar bayan.

    A cikin makonnin da suka wuce, birnin tarayya ya fuskanci barazana daga wurin ƴan ta'adda akan kai hari kan wasu dakarun sojji da gidan yarin Kuje.

    A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ma, ƴan ta'adda sun kai wa sojojin da ke shingen bincike na Dutsen Zuma mai nisan kilomita kadan daga cikin birnin Abuja.

    Ga wani labari da za ku so ku karanta kan tsaro a Abuja - Abu hudu da suka jawo zaman fargaba a Abuja

  14. An kama mutum 130 da hannu a fyaɗen taron dangi da aka yi wa wasu mata

    SA Rape Protest

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a Afirka ta Kudu sun ce sun kama fiye da mutum 130 a wani bincike da ake yi kan fyaɗen taron dangi da aka yi wa wasu mata a wani wajen haƙar ma'aidnai a gundumar Gauteng.

    A baya ƴan sandan sun ce mutum 80 aka kama, amma sai aka ƙara kama wasu bayan nan.

    An tare matan ne a yayin da suke naɗar bidiyon wata waƙa da suk yi.

    Har yanzu ana ci gaba da yin bincike kuma ba a kai ga gurfanar da kowa kan zargin fyaɗe ba tukunna.

    Mafi yawan wadanda aka tsare ɗin sun sha gurfana a gaban kotu kan tuhume-tuhumen shige da fice, inda ake zargin su da shiga Afirka ta Kudu ba bisa ƙa'ida ba daga maƙwabciyarta Lesotho.

    An yi wata zanga-zanga a Krugersdorp da ke yammacin birnin Johannesburg, inda lamarin ya faru, ana yin kira da a sake ɗaukar matakai kan hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

  15. Ƴan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

    Abuja Tsaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sandan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja sun fara hai hare-hare dazuzzuka da gine-ginen da babu kowa a cikin gari da unguwannin bayan gari.

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Josephine Adeh ne ya faɗi hakan a jiya Laraba, kamar yadda kafar yaɗa labaran Channel ta ruwaito.

    A yayin da take ƙaryata jita-jitar cewa akwai mafakar masu garkuwa da mutane a cikin Abuja, ta ce a kwanaki masu zuwa mazauna birnin za su ga an tsaurara matakan tsaro.

    Harin ya zo ne ƙasa da sa'a 24 ba bayan da rundunar ƴan sanda ta yi alkawarin za ta fara tattara bayanan sirri da kuma kai samame da ɗaukar sauran matakan tsaro.

    "A yau ƴan sandan birnin tarayya sun fara kai hari dazuka da da gine-ginen da ba mutane a ciki a cikin gari da unguwannin bayan gari. Kuma yanzu muka fara," in ji mai magana da yawun ƴan sanda.

    "Mutane za su ga an tsarara tsaro a wurin shige da fice a birnin."

    Ƴa ƙara da cewa duk wanda aka kama za a tantance sa dauki bayanansu sannan a kai su kotu.

  16. An kama mai fataucin namun dajin bayan saka tukuicin dala miliya ɗaya kan neman sa

    Karkanda

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a kasar Kenya sun kama wani mutum da ake zargi da alaƙa da wata ƙungiya mai reshe a kasashe daban-daban ta fataucin namun dajin dawa da mugayen ƙwayoyi, wanda ake tuhuma a wata kotun Amurka.

    Abdi Hussein Ahmed wanda aka fi sani da Abu Khadi, ya shiga hannu ne a wannan makon a gundumar Meru sakamakon bayanan da jama'a suka bayar a cewar 'yan sanda.

    Amurka ta saka tukuicin dala miliyan ɗaya ga duk wanda zai bayar da bayanan da za su kai ga kama shi.

    A shekarar 2019, an tuhumi Mr Ahmed a wata kotun New York da hannu wajen fataucin ƙahon karkanda.

    An kuma tuhume shi da hannu wajen fataucin a kalla kilo daya na hodar iblis.

    Haka zalika an tuhumi wasu mutane uku tare da shi: Moazu Kromah (Ayoub) da Amara Cherif (Bamba Issiaka) da Mansur Mohamed Surur (Mansour).

    A cikin wasu shekaru bakwai, an ba da rahoton cewa suna da hannu wajen fataucin kilo 19 na ƙaho da tan 10 na ƙahon giwa da ke da darajar dala miliyan bakwai, daga Kenya da Uganda da Janhuriyar Demokradiyyar Kwango da Guinea, da Mozambique da Senegal da Tanzania.

  17. Jirgin Ruwa na yaƙi 'Ronald Reagan' da tawagar jiragen yaƙi na kan hanya

    Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce jirgin yaƙin USS Ronald Reagan ya nufi wani sashen teku da ya ƙunshi ruwan kudu maso gabashin Taiwan.

    USS Ronald Reagan da tawagar jiragen yaƙinta na kan hanyarsu a Tekun Philippine inda su ke cigaba da tafiyar su kamar yadda aka shirya, domin yin zagayen nuna goyon bayan bude tekun Indo-Pacific," a cewar wani kakakin soji a yau.

    USS Ronald Raegan

    Asalin hoton, Reuters

  18. Ruwan sama na kwana uku ya hana Kanawa fita neman na abinci

    Ruwan sama

    Al’ummar jihar Kano a arewacin Najeriya na ci gaba da bayyan ra’ayoyinsu dangane da yadda aka yi ta mamakon ruwan sama na kwanaki uku a jere.

    Ruwan saman ya tsayar da harkokin ciniki da dama a babban birnin jihar.

    Ba kasafai ba dai ake samun mamakon ruwan sama da za a jera irin wadnan kwanaki har uku ana ruwa ba, da ya wuce awanni ba.

    Wannan mamakon ruwan saman da aka samu a jihar ya jefa wasu daga cikin iyali halin ƙunci sakamakon rashin samun damar fita a samo abin kai wa baka saboda ruwan da ake yi.

  19. Manufofin gwamnatin Burtaniya na kara ingiza masu neman mafaka fadawa hannun masu safarar mutane – MDD

    Thail immigrants

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya da kungiyar Agaji ta Red Cross a Burtaniya sun ce manufofin gwamnatin Burtaniya na kara ingiza masu neman mafaka fadawa cikin hadarin shiga hannun masu safarar mutane da kuma bauta.

    A wani rahoton hadin-gwiwa da suka fitar, hukumomin biyu sun ce masu neman mafaka kan fada hannun kungiyoyin masu aikata laifi kasancewar ba za su iya neman aiki bisa ka'ida ba a yayin da suke jiran hukuma ta amince da bukatunsu.

    Wakilin BBC ya ce rahoton ya kawo hujjojin da ke nuna masu aikata laifi suna kokarin janyo hankalin 'yanmata a cibiyoyin masu neman mafaka domin yin aiki a gidaje, ko yin lalata da su domin ba su muhalli ko kuma safarar matasa domin yin aiki a gonakin da ake noman wiwi.

  20. China ta tabbatar da harba makami mai linzami

    Dakarun sojin roka dake gabashin kasar ta harba wani roka mai linzami daga gabashin gabar tekun Taiwan, a cewar ma'aikatar yaɗa labaran China, ta kuma kara da cewa ta yi nasarar samun wajen da ta yi niyyar harba wa.