Buhari ya tafi Daura domin yin hutun Babbar Sallah

Wannan shafi ne da zai rika kawo muku labarai kai-tseye daga Najeriya da filin Arfah a Saudiyya ma sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo bayanai kai-tsaye.

    Sai ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni da suka shafi rayuwarku.

    Mu kwana lafiya.

  2. Buhari ya tafi Daura domin halartar Babbar Sallah

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Daura da ke Jihar Katsina domin yin bikin Babbar Sallah.

    Shugaban kasar ya tafi mahaifarsa ne ranar Juma'a.

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaba Buhari ya samu tarba daga Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk da wasu sarakunan gargajiya.

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Buhari ya isa Daura ne kwanaki uku bayan wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari kan ayarin motocinsa a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

    An kai harin ne kan ayarin motocin da ke dauke da jami'an da ke yi wa shugaban hidima da kuma 'yan jarida, a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.

    Sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin.

  3. Muna sa ran samun karuwar mahajjata a 2023 - Saudiyya

    Mahajjata

    Asalin hoton, Saudi Gazette

    Ministan Lafiya na Saudiyya, Fahd Al-Jalajel, ya ce kasar na sa ran samun karuwar mahajjata a shekara mai zuwa saboda ganin ana samun nasara a kokarin dakile cutar korona.

    A wata tattaunawa da gidan talabijin na Al-Arabiya, ministan ya ce ma'aikatar aikin Hajji a kasar na yin tsare-tsaren aikin Hajji duk shekara sannan a wannan shekara ma ma'aikatar ta yi shiri tun da wuri duba da barazanar cutar korona da aka dauki shekara biyu ana fama da ita.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, kasar ta yi tsare-tsare da za su kare lafiyar mahajjata, inda ya ce kawo yanzu ba a samu mahajjata da suka bukaci agajin lafiya na gaggawa ba. Amma ya ce an samu mutum uku da suka sami 'yar matsala saboda zafin rana da aka yi a filin Arfa.

    A cewar ministan, an sami gagarumar ci gaba a aikin Hajjin bana tun bayan bullar annobar korona, inda aka samu karuwar alhazai da suka je aikin Hajji.

  4. Dalibai sun yi zanga-zanga a Ondo kan kisan dan uwansu

    Taswirar Ondo

    Asalin hoton, OTHERS

    Daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Rufus Giwaa, a jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zanga yau Juma'a domin nuna bacin rai kan mutuwar dan uwansu, Folarera Ademola.

    Ana zargin jami'an tsaro na Amotekun da kashe dalibin, Folarera Ademola da ke ajin farko a Kwalejin da kuma ke sashin kimiyyar gwaje-gwaje.

    Bayan faruwar lamarin, daliban da ke zanga-zanga sun bai wa gwamnatin jihar wa'adin sa'a 24 na ganin ta gudanar da bincike kan lamarin.

    Daliban dai na bukatar a mika jami'in rundunar tsaron ta Amotekun da ake zargi da harbin Ademola ga 'yan sanda domin ya fuskanci hukunci da kuma biyan diyya zuwa ga iyayen dalibin.

    Rahotanni sun ce an harbi dalibin ne a ran 27 ga watan Yuni, a gaban gidansu, nan take aka garzaya da shi asibitin gwamnatin tarayya da ke Owo, inda ya mutu a jiya Alhamis.

    Shugaban daliban Kwalejin, Olorunda Oluwafemi ya ce za su garzaya zuwa fadar sarkin Olowo kafin su zarce da zanga-zangar zuwa ofishin rundunar tsaro ta Amotekun domin ganin an hukunta jami'in da ya harbi dalibin.

  5. Tinubu ya amince ya dauki mataimaki Musulmi – Ganduje

    Ganduje da Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Campaign organisation

    Bayanan hoto, Ganduje ya na daya daga cikin mutanen da ake hasashen zama mataimakin Tinubu

    Gwamanna jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya amince zai dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa.

    Ganduje ya yi wannan bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai masa ranar Juma'a a gidan gwamnatin jihar.

    Gidan talabijin na Channel TV ya ambato gwamnan na cewa ''Mun ba shi shawara ya dauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Najeriya''.

    Ya kumna yi kira ga taron malaman da su rika yi wa Tinubu addu'o'in samun nasara a zaben 2023.

  6. Kungiyar dillalan man fetur ta arewacin Najeriya ta yi barazanar soma yajin aiki

    petroleum pump

    Asalin hoton, OTHERS

    Kungiyar masu dakon man fetur masu zaman kansu ta arewacin Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki kan bayanai da hukumar kula da harkokin man fetur a kasar NMDPRA ta fitar cewa ta biya mambobin kungiyar kudadensu da suke bin gwamnati.

    Shugaban kungiyar, Musa Yahaya ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.

    Yana mayar da martani ne kan furucin da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur a kasar Farouk Ahmad ya yi cewa sun biya dillalan man fetur kudin da ya kai naira biliyan 74 a tsawon watanni bakwai da suka gabata inda kungiya reshen arewacin Najeriya suka sami naira biliyan 42.

    Maikifi ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a bangaren da su tabbabatar an biya mambobin kungiyar kudadensu daga nan zuwa karshen wata Yuli, ko kuma su tsunduma yajin aiki.

  7. Gwamnonin APC uku sun ziyarci Wike a Fatakwal

    Gwamnoni

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, Wasu Gwamnonin APC

    Wasu gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun ziyarci gwamnan Ribas Nyesom Wike a Fatakwal, babban birnin Jihar.

    Gwamnonin sun hadar da Kayode Fayemi na Ekiti, da Rotimi Akeredolu na Ondo sai kuma Babajide Sanwo-olu na Legas.

    Ko da yake ba su yi bayani kan dalilansu na ziyayar ba, sai dai ba za ta rasa nasaba da kokarin ganin ya fita daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

    Wike ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a PDP.

    Kazalika Atiku ya dauki gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa, lamarin da wasu ke ganin shi ya sanya ran Wike ya kara baci.

    Sai dai jam'iyyar ta PDP ta sha alwashin rarrashinsa ya ci gaba da zama a cikinta.

  8. Saudiyya ta maido da wasu Mahajjatan Najeriya gida saboda bizar bogi

    Mhajjatan Najeriya

    Asalin hoton, @NIGERIAHAJJCOM

    Bayanan hoto, ''Muna kan layin tantancewa ne aka gano bizar bogi aka ba mu''

    Hukomomin Saudiyya sun maido da alhazan Kano bakwai gida daga kasar saboda sun yi amfani da bizar bogi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa biyar daga cikinsu sun je Saudiyya ne ta hanyar kamfanonin shirya tafiye-tafiyen aikin hajji masu zaman kansu, sai kuma biyu wadanda suka je ta hannun hukumar alhazan jihar Kano.

    Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa ba su san bizar bogi aka ba su ba, sai bayan da suka isa Saudiyya.

    ''Muna kan layin tantancewa da aka zo kaina sai aka ce na koma gefe, daga nan kuma suka shaida mana cewa bizar bogi muke dauke da ita'', in ji shi.

  9. Jihar Lagas ta soke sabbin dokokin zubar da ciki

    The publication of the abortion guidelines prompted a protest in Lagos

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta jihar Lagos ta soke sabbin dokokin zubar da ciki ta amintacciyar hanya, domin bayar da damar tuntubar bangarorin da suka dace.

    An dai tsara dokokin ne shakara hudu da suka gabata domin bai wa kwararrun jami'an lafiya damar samar da hanyoyin zubar da ciki marasa hadari, to sai dai ba a tuntubi jagororin addini ba yayin tsara dokokin .

    A farkon makon nan ne dai aka jiyo wani Fasto a jahar na cewa dokokin na kokarin halasta zubar da ciki ne kawai a fakaice.

    A ranar Alhamis ne Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ce ana bukatar karin wayar da kan jama'a da masu ruwa da tsaki sosai domin kara fahimtar sabbin dokokin.

    Dokokin jihar Lagos dai sun bayar da dama da a zubar da ciki matukar aka fuskanci ran mahaifiyar ko na dan tayin na cikin hadari, wadda kuma ake ganin ba lallai ne ya rayu ba.

  10. Ghana ta killace gwamman mutane saboda fargabar cutar Marburg

    jemage

    Asalin hoton, getty

    Bayanan hoto, Hukumomin na sanya ido game da barkewar cutar

    Hukumomin lafiya a kasar Ghana sun killace mutum 34 saboda barkewar cutar Marburg mai alaka da cutar Ebola wacce ke saurin yaduwa.

    An killace mutanen ne bayan sun yi mu'amala da mutunen da ake zargi cutar ta kashe.

    Hukumomin sun ce suna sanya ido game da barkewar cutar Marburg a kasar, wacce aka bayyana samunta a wurare biyu a yankin Ashanti da ke kudancin kasar.

    A wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar, ta ce mutum biyu ne suka mutu bayan da gwaji ya tabbatar suna dauke da kwayar cutar.

    Jami'an daga hukumar lafiya ta duniya tare da hadin gwiwwar likitocin kasar suna fadada bincike tare da yin aiki tukuru domin ganin cutar ba ta yadu ba.

  11. Tsohon shugaban Angola Dos Santos ya rasu

    Santos

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, An dai shafe lokaci mai tsawo ana yakin basasa a kasar a zamanin mulkinsa

    Tsohon Shugaban Angola José Eduardo dos Santos ya rasu, sakamakon wata doguwar jinya.

    Shafin Facebook na fadar gwamnatin kasar ne dai bayar da sanarwar rasuwar tasa da safiyar yau Juma'a

    Shugaba Dos Santos, mai shekara 79, ya shafe kusan shekara 40 yana jagorantar kasar, wacce ke da tarin arzikin mai da ma'adinai.

    An shafe lokaci mai tsawo ana yakin basasa a kasar a zamanin mulkinsa.

  12. Hotunan yadda alhazai ke tsayuwar Arfa

    Kalli wasu daga cikin hotunan tsaiwar Arfa da ke gudana yau a Saudiyya.

    Hotuna daga shafin Haramain Sharifain da jaridar Saudi Gszette.

    Mahajjata

    Asalin hoton, Saudi gazzet

    Bayanan hoto, Mahajjata kan gudanar da addu'o'i yayin tsaiwar Arafat
    Mace

    Asalin hoton, Saudi gazzet

    Bayanan hoto, Tsaiwar Arfa dai na daga cikin rukunan aikin hajji
    mutum na karanta Kur'anin

    Asalin hoton, Saudi gazzet

    Bayanan hoto, Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji
    Mutum na addu'a

    Asalin hoton, Twitter/ haramain Sharafain

    Bayanan hoto, Idan rana ta fadi kuma ba za su yi sallar magriba a filin Arfa ba
    Mahajjata

    Asalin hoton, Twitter/ Haramainsharafain

    Bayanan hoto, Kimanin mutum miliyan daya ne ke gudananr da aikin hajjin bana
    Mutane a filin Arfa

    Asalin hoton, Twitter/ haramain Sharafain

    Bayanan hoto, Akan shafe yinin gaba daya a filin Arfa
  13. Peter Obi ya zabi Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakinsa

    Datti Baba-Ahmed

    Asalin hoton, bbc

    Dan takara shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Peter Obi, ya bayyana Datti Baba-Ahmed. a matsayin mataimakinsa.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa an zabi sanata Datti Baba-Ahmed, wanda shi ne mamallakin jami'ar Baze da ke Abuja a matsayin mataimakin shugaban kasa a jam'iyyarsa ta Labaour ranar Juma'a a Abuja.

    Datti Baba-Ahmed, mai shekarar 46 tsohon Sanata ne daga jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

    Nadin nasa na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan da babban daraktan yakin neman zaben Peter Obi, Doyin Okupe, ya sanar da ajiye mukaminsa.

  14. Mahajjata sun sallaci azahar a filin Arfah

    Ga wasu hotuna na yadda Mahajjata suka sallaci azahar a Masallacin Namirah da ke filin Arfah.

    Sallar arfa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Sallar arfa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  15. Ministan harkokin cikin gida na Saudiyya na sa ido kan tsaro a Mina

    Ministan cikin gida na Saudiyya

    Asalin hoton, Saudi gazzet

    Ministan harkokin cikin gida na Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Saud bin Naif, na sa ido game yadda harkokin tsaro ke gudana yayin da mahajjata ke gudanar da tsaiwar Arfa.

    A wata ganawa da ya yi da kwamandojin tsaron aikin hajjin bana a Mina, ministan ya mika sakon gaisuwar shugabannin da ke kula da Masallatai Biyu Mafiya daraja wato Sarki Salman da kuma Yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman, ga mahajjatan bana.

    Haka kuma ministan na sa-ido game da matakan da ake bi domin aiwatar tsare-tsaren da aka yi game da sha'anin tsaro a lokacin gudanar da aikin hajjin na bana. kamar yadda jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito.

  16. Mummunar cutar Marburg mai kisa ta ɓulla a Ghana

    Marburg Virus

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a Ghana sun tabbatar da bullar cutar Marburg mai saurin yaduwa da ke da alaƙa ƙwayar cutar Ebola.

    An tabbatar da bullar cutar ne bayan wani gwaji da aka yi wa wasu majinyata biyu da suka mutu a kasar

    Duka mutanen biyu wadanda suka fito daga yankin Ashanti sun rika nuna alamomin da suka hadar da gudawa, da zazzabi, da kuma amai.

    Inda aka garzaya da su asibitin Ashanti kafin daga bisani su mutu. Kamar yadda jakadan hukumar lafiya ta duniya a Ghana Dr Francis Kasolohe ya tabbatar.

    An dai daukin samfurin kwayoyin cutar da aka samu daga jikin mutanen biyu zuwa cibiyar bincike ta Pasteur da ke Senegal domin zurfafa bincike. in ji Dr Francis Kasolohe.

    In dai ta tabbata cutar Marburg ce, wannan ne karo na farko da kasar ke samun bullar cutar a cikinta, kuma kasa ta biyu a yammacin Afirka bayan da a bara ta bulla a Guinea .

    Hukumar lafiya ta duniya dai ta tura tawagar likitoci domin taimaka wa takwarorinsu na Ghana dakile yaduwar cutar a kasar.

    Duk da cewa babu riga-kafin wannan cutar, ana bai wa wadanda suka kamu da ita shawarar su yawaita shan ruwa, yayinda likitoci ke kokarin lalubo hanyoyin maganceta.

    A shekaraun bayan cutar ta bulla ne a kasashen DR Kongo, da Kenya, da Afirka ta kudu tare da kuma Uganda.

  17. 'An cutar da mu kan rashin samun tafiya Hajji'

    Maniyyatan na komawa garuruwansu

    A yayin da mahajjatan da ke Saudiyya suke hawan Arfa a yau Juma'a, a Najeriya kuwa wasu daga cikin maniyyata hajjin banan da ba su sami damar isa Saudiyyan ba sun bayyana damuwarsu dangane da yadda Arfar ta riske su a Najeirya.

    Wasu daga cikin maniyyatan a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar, sun ce ba su ji dadin yadda hukumar alhazan jihar ta sa suka fito daga gidajensu har na tsawon kwana uku ba, alhalin babu wani shiri da aka yi musu.

    Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta ce kimanin maniyata 600 ne a Kano ba su samu tafiya ba.

    Maniyyatan na komawa garuruwansu
    Bayanan hoto, Maniyyatan na komawa garuruwansu

    Wakilinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ji ta bakin wasu daga cikin maniyyatan kamar haka:

    Aminu:"Sunana Aminu Ashiru Muhammad daga Ƙaramar Hukumar Warawa. Ba abin da za mu ce sai Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Wanna al'amari hakika an cutar da mu, amma muna fatan Allah Ya sa hakan shi ya fi alheri.

    Daidai muke da wadanda suka yi Arfan tun da mu ma mun samu ladan niyya in sha Allahu. Kuma duk addu'ar da muka yi in Allah Ya yarda Allah zai biya mana buƙatunmu akai.

    Amma dai haƙiƙa gwamnatin jihar Kano da hukumar alhazai ba su yi mana adalci ba. Ba su tausaya mana ba. Kuma gaskiya zan karbi kudina."

    Mace:"A gaskiya kudina shekararsa ta uku kenan, kuma ba a kai mu ba, kuma ba a gaya mana ba. Muna zaman zamanumu a gida har mun hakura tun da lokaci ya ƙure, amma aka kirawo mu. To wannan Arfar da za su yi tamu ce.

    Kuma anko da jakar da aka ba mu ma ba ma so sai an biya mu kuɗinmu daidai wa daida. Shekarata 60 suka ɗisa min polio."

    Maniyyatan na komawa garuruwansu

    Maryam Abdullahi:"Haka Allah Ya nufa. Kwanana biyu a sansanin alhazai ga sauro ga ruwan sama ga shi guzurinmu ya ƙare, yanzu ma sai da karo-karo muka samu kuɗin komawa gida.

    Ban sani ba ko zan karbi kudina ko a'a, tun da dai dama biya min aka yi."

    Sani Auwalu:"Ni tun da nake a duniya ban taba jin rashin dadi irin yau ba. Ana nan ana ta karanta mana ana yaudararmu a ce akwai jirgi a hanya.

    Idan mun kira waya sai su kashe. Tun shekarar 2020 na ba da kudina amma saboda annobar korona ba a tafi ba."

    Aisha:"Ana can ana Arfah babu ni, gaskiya ban ji daɗi ba kuma na ce Allah Ya saka min. Kwanana uku a sanasanin alhazai, zaman ba daɗi ba daɗin kwana.

    Karbar kudina zan yi, shekara uku fa kenan da biyan kudin. Wannan ne dama niyyata ta farko. Gaskiya an zalunce mu."

    Haka dai duk sauran maniyyatan da BBC ta zanta da su suka bayyana ɓacin ransu kan lamarin.

    Maniyyatan na komawa garuruwansu
    Maniyyatan na komawa garuruwansu
    Maniyyatan na komawa garuruwansu
  18. Labarai da dumi-dumi, Tsohon firaministan Japan Shinzo Abe ya rasu

    Abe

    Asalin hoton, Reuters

    Tsohon firaministan Japan Shinzo Abe ya rasu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta sanar.

    An harbi Abe mai shekara 67 ne a yayin da yake jawabi a wajen wani gangamin yakin neman zabe.

  19. Gwamnan Makkah ya ce babu mahajjacin da ya kamu da cutar korona

    Gwamnan Makkah Yarima Khaled Al-Faisal, ya ce babu mahajjacin da ya kamu da cutar Korona a kwanan Mina da aka sani da ranar Tarwiyya wanda suka gudanar jiya Alhamis.

    Gwamnan ya ce yana godiya ga Allah da ya bai wa mahajjata damar yin kwanan Tarwiyya ba tare da samun wata matsala da ta danganci cutar Korona ba kamar yadda jaridar Sadi Gazzet ta ruwaito.

    yarima Khaled Al-Faisal, wanda kuma shi ne shugaban babban kwamitin aikin hajjin bana, da wasu manyan jami'an gwmnatinsa na birnin na Mina domin sa ido game da yadda kwamitin ke gudanar da ayyukansa

    Gwamnan ya yaba wa duka mutanen da ke aikin taimaka wa mahajjatan domin samun damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali, Musamman masu aikin sa-kai wadanda ya ce sun jajirce wajen ganin sun hidimta wa mahajjatan.

    Gwamnan Makka

    Asalin hoton, saudi Gazzet

  20. Yau ake hawan Arfah a Saudiyya

    Mahajjata na gudanar da addu'o'i a tsauwar Arfa

    Asalin hoton, getty

    Yau ne alhazai ke fita filin Arfa a ci gaba da gudanar da ayyukan hajjin bana.

    Kimanin alhazai miliyan guda ne suka fita domin tsayuwar ta arfa inda za su kwashe yinin ranar wato tun daga zawali zuwa faduwar rana suna addu’oi kafin daga bisani su wuce zuwa Musdalifa.

    Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji. Ko a hadisi ma ya zo, Annabi SAW yace Arfa ita ce hajji.

    Don haka duk alhajin da bai shiga filin arfa ba har rana ta fadi a yau to ba shi da aikin hajji, sai ya sake.

    Hakan ta sa a kowane irin hali mutum ya ke ciki sai ya je filin, hatta ma marasa lafiya ana kai su.

    Hukumomin Saudiya sun yi wani tanadi na daukar marassa lafiya da ke cikin mawuyacin hali a kai su filin a cikin motocin daukar marassa lafiya, domin su dace da samun ranar.

    A Arfah dai alhazai suna hada sallar Azahar da La’asar, kuma raka’a bibbiyu.

    Daga nan za su zauna suna ta addu’o’I da karatun kur’ani da zikiri har zuwa faduwar rana.

    Idan rana ta fadi kuma ba za su yi sallar magriba a filin Arfa ba, sai su kama hanyar tafiya Muzdalifa.