'Yan sandan Najeriya sun kama matashiyar da ta yi iƙirarin ƙarya na sacewa da yi mata fyaɗe

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muke kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Kano Pillars za ta koma buga wasa a Kano

    Pillars

    Asalin hoton, @pillarsfc

    Hukumar kula da gasar firimiya ta Najeriya, Nigeria Professional Football League (NPFL), ta bai wa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars damar ci gaba da buga wasanni a filin wasanta na Sani Abacha da ke Kano.

    Wata sanarwa da hukumar ta aike wa kulob ɗin ta ce an ba shi damar ce bayan duba na tsanaki.

    Hukumar ta ce wajibi ne Kano Pillars ta tanadi wani filin wasan da za ta ci gaba da buga wasanni da zarar an fara aikin gyara ciyawar filin taka leda ta filin kafin kammala shi.

    Pillars ta ce ta amince da sharaɗin, har ma ta ce za ta buga wasanta na gaba tare da Katsina United a gida Kano ranar 16 ga watan Afrilu.

    Pillars ba ta buga wasa a gida ba a kakar bana sakamakon matakin da NPFL ta ɗauka, inda ta umarci a sauya ciyawar filin taka ledar.

    Yanzu haka Pillars na mataki na 13 da maki 26 bayan buga wasa 22 a kakar bana ta 2022/23.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. 'Yan sandan Najeriya sun kama matashiyar da ta yi iƙirarin ƙarya na sacewa da yi mata fyaɗe

    Omotoyosi

    Asalin hoton, Omotoyosi

    Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Legas a kudancin Najeriya ta kama wata matashiya da ta yi iƙirarin ƙarya cewa an yi garkuwa da ita tare da yi mata fyaɗe, a cewar rahotannin da jaridun ƙasar suka ruwaito.

    Budurwar da aka bayyana da suna Omotoyosi ta wallafa a shafinta na Twitter mai suna @_misteriouss da misalin ƙarfe 7:15 na safiyar Alhamis agogon Najeriya cewa ana garkuwa da ita da kuma yi mata fyaɗe a loƙacin.

    Daga baya ma ta wallafa adireshi da kuma lambar wayar mutumin da ta ce yana garkuwar da ita. Sai dai ta goge saƙon daga baya, tana mai neman afuwa a cikin wani bidiyo.

    Rahoton Daily Trust ya ambato mai magana da yawun 'yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, na cewa suna bincike kan matashiyar.

    Tun daga safiyar yau Alhamis sunan Toyosi ke waɗari a dandalin na Twitter sakamakon saƙon da ta wallafa, inda akasarin masu amfani da shafin ke Allah-wadai da abin da ta aikata.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Sojojin Isra'ila sun harbe Falasɗinawa biyu

    Sojojin Isra'ila sun harbe wasu Falasdinawa biyu a wani gumurzu da aka yi a gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye.

    Jami'an Falasdinawa sun ce wasu matasa biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka samu a wani samame da jami'an tsaron Isra'ila suka kai a Jenin.

    Sun ce adadin mutanen da sojojin Isra'ila suka kashe a gabar yammacin kogin Jordan ya kai biyar zuwa yanzu.

    Sojojin Isra'ilar na gudanar da ayyukan "yaki da ta'addanci" a yankin, bayan wasu hare-hare da suka janyo mutuwar mutum 14 a Isra'ilar.

    Kungiyar Fatah da ke jagorancin yankin da Hamas mai iko da Gaza sun yi kira ga Falasdinawa su tunkari sojojin Isra'ila.

  5. Za mu sauya alƙiblar kasuwanci zuwa nahiyar Asiya - Shugaban Rasha Putin

    Putin

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kiran a faɗaɗa kasuwancin makamashi na ƙasar zuwa nahiyar Asiya.

    Putin ya yi gargaɗin cewa ƙasashen Turai na hautsina kasuwar ta hanyar daina sayen gas da man fetur na Rashar.

    "Yunƙurin kawar da makamashin Rasha da kuma maye gurbinsa da wasu dole ne ya shafi tattalin arzikin duniya," a cewarsa.

    Da yake magana a yau, Putin ya ce Rasha za ta sauya alƙiblar kasuwancinta "sannu a hankali" zuwa "kasuwar gabashi da kuma kudanci mai bunƙasa cikin sauri".

    A shekarar da ta gabata, hauhawar farashi ta sa Rasha ta samu kashi 36 cikin 100 na kuɗin shiga daga fetur da gas.

  6. Ana shirin rantsar da zababbun 'yan majalisar Somaliya a Mogadishu

    President Mohamed Abdullahi Farmajo is eligible for re-election
    Bayanan hoto, Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo na Somaliya

    Ana shirin rantsar da wasu cikin sababbin 'yan majalisar kasar Somaliya a yau Alhamis a cikin babban birnin kasar Mogadishu, bayan kammala zabukan da aka yi na tsawon watanni.

    Za a rantsar da su cikin filin jirgin sama kasar - wanda wuri ne da yafi tsaro a fadin birnin - domin har yanzu ana fama da matsalar tsaro a kasar.

    Majalisar kasar ta hada da majalisar wakilai mai mambobi 275, da kuma majalisar dattawa mai mambobi 54.

    Babban aikin da ke gabansu shi ne na zaban shugaban kasar, wanda zai jagoranci wannan kasar a shekaru hudu masu zuwa.

    Shugaba mai-ci Mohamed Abdullahi Farmajo ya ci gaba da rike mukami bayan karewar wa'adinsa saboda kauce wa matsalar siyasa a kasar, inda tun a watan Fabrairun bara wa'adin shugaba Farmajo ya kare

    Shekara 30 ke nan da Somaliya ta shafe babu zaman lafiya, tun bayan da aka hambarar da gwamnatin marigayi Siad Barre a 1991, matakin da ya haifar da yakin basasa.

  7. Ukraine ta ce ta lalata wani babban jirgin ruwa Rasha kuma ta ce 'ya fara nutsewa'

    July 2017: Moored in the Crimean port Sevastopol, Moskva is decorated with bunting for a Navy Day parade

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hoton jirgin ruwan yaki na Moskva yayin da yake cikin tashar jirgin ruwa ta Sevastopol gabanin yakin Ukraine

    Dazu-dazu BBC ta sami rahoto cewa dakarun Ukraine sun harba wasu makamai kan wani babban jirgin ruwan yaki na Rasha mai suna Moskva.

    To ma'aikatar tsaron Ukraine ta kara fitar da wani bayani, tana cewa jirgin ya fara nutsewa bayan da makaman Ukraine masu linzami samfurin Neptune suka lalata shi.

    Sai dai Rasha ta musanta cewa Ukraine ce ta harbi jirgin ruwan, tana cewa gobara ce ta kama a sanadin wani hadari da ya auku a cikin jirgin.

    Ta kuma ce tuni aka kashe gobarar kuma jirgin ruwan na kan hanyarsa ta komawa wata tashar jiragen ruwa a Rasha.

    Ga wasu hotunan jirgin na Mosva, wanda ke cikin manyan jiragen yakin kasar da ta ke afahari da shi.

    August 2014: Russia's President Vladimir Putin and Egyptian President Abdul Fattah al-Sisi on board in the Russian port Sochi

    Asalin hoton, Kremlin

    Bayanan hoto, A watan Agustan 2014 Shugaba Putin ya karbi bakuncin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi a bisa jirgin ruwan na Moskva
    April 2021: Moskva tests supersonic anti-ship cruise missiles in the Black Sea. The ship is equipped with 16 Vulkan missile launchers.

    Asalin hoton, Russian defence Ministry

    Bayanan hoto, A wannan hoton ana iya ganin jirgin ruwan na Moskva yana gwajin wasu makamai masu linzami a watan Afrilun 2021
    7 April: This satellite image shows the Moskva at port in Sevastopol, Crimea

    Asalin hoton, Maxar Technologies

    Bayanan hoto, A nan kuma ga hoton da aka dauka daga tauraron dan Adam da ke nuna jirgin ruwan na Moskva yayin da yake tashar jirgin ruwa na Sevastopol a yankin Crimea
  8. Ana taron Majalisar Magabata a Fadar Shugaban Najeriya ta Aso Rock

    Majalisar magabata ta kasa na gudanar da taronta a Fadar Aso Rock ta shugaban Najeriya da ke Abuja babban birnin Najeriya.

    Shugaba Muhammadu Buhari ne ke jagorantar taron majalisar wato (Council of State) a ranar Alhamis.

    Fadar Shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Bayanan hoto, Tsofaffin shugabannin Najeriya (daga hagu) Yakubu Gowon da Abdulsalam Abubakar da Goodluck Jonathan
  9. Fiye da mutum 50 da aka kashe a harin Filato na kusa da ni ne - Dan Majalisa

    Yusuf Babayo Gagdi

    Asalin hoton, Yusuf Babayo Gagdi / Facebook

    Bayanan hoto, Yusuf Adamu Gagdi, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanam/Kanke

    Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Pankshin-Kanke-Kanam, Yusuf Adamu Gagdi, wanda al’umarsa ne wannan lamari ya shafa, ya ce kawo yanzu an tantance mutane fiye da dubu hudu da suka tsere wa tashin hankalin.

    Ya kuma ce kawo yanzu ya tabbatar da mutuwar mutane fiye da cas’in:

    "Mutum fiye da 50 cikin wadanda aka kashe a hare-haren ‘yan-bindiga a Kanam ta jihar Filato, na sansu kuma sun san ni."

    Dan Majalisar Tarayyar ya kuma ce wasu fiye da mutum 4,000 sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren na ranar Lahadi.

    Danna hotonsa a kasa domin sauraren hirarsu da wakilin BBC Ishaq Khalid ta wayar tarho yayin da ya kai kayayyakin agaji na gaggawa da ya samar ga al'ummar yankin.

    Bayanan sautiYusuf Adamu Gagdi
  10. Musulmi za su yi azumi har sau biyu a shekarar 2030

    Muslims breaking their fast in Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Masu ilmin taurari sun ce a shekarar 2030 mai zuwa, Musulmin duniya za su yi azumin watan Ramadan har sau biyu.

    Masanan sun ce watan Ramadana zai bayyana har sau biyu a cikin shekarar - na farko a watan Janairu, na biyu kuma zai bayyana ne a karshen watan Disambar shekarar, yanayin da tun 1997 ba a taba gamuwa da shi ba.

    Babban dalilin aukuwar haka shi ne bambancin da ke tsakanin shekarar Musulunci da ake lissaftawa da bayyanar wata, da kuma shekarar nasara wadda aka danganta da kwanakin da duniya ke dauka kafin ta zagaya rana.

    Sannan wannan yanayin a aukuwa ne sau daya cikin shekara 30 saboda shekarar Hijira ba ta kai tsawon ta nasara da kwanaki 11 ba, kamar yadda Khaled al-Zaqaq, wani mai nazarin taurari dan kasar Saudiyya ya bayyana a Twitter.

    Tsawon shekara guda ta Hijira kwana 354 ne, inda shekarar nasara kuwa ke da kwana 365.

  11. Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da hukuncin da ya wanke AA Zaura bisa zargin zambar $1.3m

    Zaura da jami'an EFCC

    Asalin hoton, Facebook/EFCC

    Wata Kotun Daukaka Kara da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya ta yi watsi da hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya ta Jihar, wanda ya wanke mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2023, Abdulsalam Sale Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani AA Zaura bisa zargin zamba.

    Kotun ta yi hukuncin ne ranar Laraba 13 ga watan nan na Afrilu.

    Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ce ta gurfanar da Zaura a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zarge-zarge biyar da suka shafi zamba cikin aminci.

    EFCC t a zargi Zaura da yi wa wani dan kasar Kuwait zambar dala miliyan daya dubu dari uku da ashirin bayan ya yi ikirarin cewa yana harkar kasuwancin gidaje a Dubai, Kuwait da wasu kasashen Larabawa.

    Wata sanar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce ranar 9 ga watan Yunin 2020, Mai Shari'a A. L Allagoa ya wanke Zaura wanke shi daga dukkan zarge-zarge.

    Sai dai mai shigar da kara, Musa Isah, wanda bai gamsu da hukuncin ba, ya nemi Kotun Daukaka Karar ta soke hukuncin karamar kotun.

  12. An sace fiye da dalibai 1,500 a Najeriya - Amnesty International

    Daliban makarantar Chibok

    Asalin hoton, EPA

    Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin da Adam ta Amnesty International ta ce shekara takwas bayan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan makarantar Chibok 276, fiye da dalibai 1,500 wasu kungiyoyi suka sace, kuma hukumomin kasar sun kasa kare su.

    Amnesty International ta bayyana haka ne cikin wani rahoto da ta fitar a shafinta.

    Rahoton kungiyar ya ce a cikin dalibai 276 na Chibok da aka sace, an kashe 16 kuma har yau ba a san inda 109 suke ba.

    Sannan a dalilin sace daliban da ake yi an sun kulle makarantu masu yawa kuma an fara yi wa dalibai mata auren wuri.

    Amnesty ta kuma ce an sace dalibai 1,500 cikin wata 22 ne, kuma har zuwa wannan lokacin akwai dalibai kimanin 120 da ke hannun wadanda suka sace su.

    Cikin dalibai 102 da aka sace a makarantar gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri, har yanzu tara na hannun masu garkuwa da su, haka kuma ba a sako daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna cikin dalibai 121 da aka sace ba.

    Sannan an kashe dalibai biyar na jami'ar Greenfield ta Kaduna, kuma wani dalibin makarantar sakandaren Kankara ma ya rasa ransa.

    Akwai kuma dalibai biyar na makarantar Islamiyar Salihu Tanko da ke Tegina da masu garkuwa da su suka kashe, inda a karshe rahoton ya bayyana cewa daliba Leah Sharibu ta makarantar gwamnati da ke Dapchi ce kadai ba a sako ba cikin dalibai 276 da aka sace.

  13. Ukraine ta yi ikirarin Rasha ta yi garkuwa da mutum 300 a makarantar garin Yahidne

    Ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta sanar cewa kimanin mutum 300 ne dakarun Rasha suka yi garkuwa da su a wani dakin karkashin kasa da ke wata makaranta a kusa da Chernihiv a arewacin Ukraine.

    Ciin wani sako na Twitter da ta wallafa, ma'aikatar ta ce dakarun Rasha sun kama wasu mazauna kauyuka a Yahidne wanda ke da nisan kilomita 140 arewa da Chernihiv, kuma ta yi ikirarin mutum 18 cikinsu sun mutu.

    BBC ba ta iya tabbatar da sahihancn wadannan bayanan na ma'aikatar tsaron Ukraine ba.

    Sai dai mazauna Yahidne su shaida ma wakiliyar BBC cewa kimanin mutum 130 Rashawa suka tsare a wani karamin daki na karkashin kasa.

    Rasha ba ta mayar da martani kan wannan ikirarin na Ukraine ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Mummunar ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutum 300 a Afirka ta Kudu

    Many Durban streets remain underwater

    Asalin hoton, AFP

    Alkaluman wadanda ambaliyar ruwa ta halaka a yankin KwaZulu-Natal na Afirka ta Kudu sun zarce mutum 300.

    Hukumomi a yankin sun bukaci gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci, bayan da mamakon ruwan sama ya fadi a cikin yini guda.

    Ruwan sama da laka sun danne mutane a gidajensu, kuma ana sa ran karin ruwan sama zai ci gaba da zuba.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya ziyarci yankin kuma ya yi alkawarin taimaka wa al'ummar yankin.

  15. Maraba lale-lale!

    Barkanmu da wayewar gari a yau Alhamis daga Sashen Hausa na BBC.

    Suna na Sani Aliyu kuma a yau nine zan jagoranci sanar da ku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a yankin Afirka ta Yamma da nahiyar Turai.

    Sai ku kasance tare da BBC Hausa.