'Za muyi amfani da jiragen Super Tucano lokacin da ya dace' - Fadar Shugaban Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Bankwana

    Da haka muke bankwana da ku...sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke fatan ku kwana lafiya.

  2. Tarayyar Turai ta ce za ta dakatar da ayyukanta a Mal

    Hukumar Tarayyar Turai ta ce za ta dakatar da ayyukanta a Mali, amma za ta ci gaba da kasancewa a yankin na Sahel mai fama da karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi.

    Babban jami'in hukumar Joseph Borrel, ya ce shigar sojojin hayar Rasha kasar na daga cikin dalilan daukar wannan mataki, da ya hadar da soke shirin horar da dakarun sojin kasar.

    Hukumomin kare hakkin dan adam sun yi amannar cewa sojojin Mali da na hayar Rashar sun kashe gwamman fararen hula yayin artabu da masu ikirarin jihadi a tsakiyar kasar, a karshen watan jiya.

  3. Gwamnatin Najeriya na tattauna da ASUU kan yajin aiki

    Gwamnatin Najeriya ta hannu Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, na ganawa da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa wato ASUU, a yau Litinin.

    Jaridar Punch ta Najeriya ta rawaito cewa ana ganawar ne da yammacin yau Litinin tsakanin wakilan gwamnati da na ASUUn.

    Kwanaki 56 kenan da ASUU ta shiga yajin aiki a Najeriya sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.

    ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.

    Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

    Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

  4. Tarayyar Turai za ta ba Ukraine ƙarin makamai

    Tarayyar Turai za ta ƙara ba Ukraine ƙarin makamai, kamar yadda ministan harakokin wajen Jamus Annalena Burbock ta bayyana.

    "Tarayyar Turai matsayinta aminiyar Ukraine nan gaba za ta ƙara ba ta makamai," kamar yadda Burbock ta shaida wa manema labarai a Luxembourg bayan kammala taron ministocin harakokin waje.

    ƙarin makaman na da nasaba da fargaba kan halin da ake ciki a gabashin Ukraine, in ji Josep Borrell.

    Ya ce za su fi mayar da hankali kan ƙarfin Ukraine na kare kanta fiye da takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha.

  5. Abin da Tinubu ya tattauna da gwamnonin APC

    Tinubu

    Asalin hoton, Twitter/Jubril

    Jagoran jam'iyyar APC kuma ɗan takarar shugabancin kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayyani kan abin da ya sa ya gana da gwamnonin APC a Abuja.

    Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ne sa'o'i bayan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbanjo ya fito ya bayyana anniyarsa ta karawa a neman kujerar shugabancin Najeriya.

    Cikin gwamnonin da suka halarci tattaunawar da Tinubu ya shirya a gidan gwamnatin Kebbi da ke Asokoro a Abuja sun hada da gwamnan Kebbin da na Kaduna da Legas da Kano da Osun.

    Sai kuma gwamnonin Jihohin Yobe da Plateau da Jigawa, da sauransu.

    A lokacin ganwa da manema labarai Tinubu ya ce ya gayyaci gwamnoni ne domin sake neman goyon-bayansu ga anniyarsa ta takarar shugaban kasa.

    Tsohon gwamnnan na Legas na sake jadada cewa yanzu ba shi da buri sama da ganin ya gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

    Da aka yi masa tambaya kan matsayarsa na shiga takara da yaron gidansa Yemi Osinbajo ya yi, sai ya amsa da cewa "shi ba shi da wani ɗa da ya girma ya kara da shi".

  6. 'Mutum 68 ke hannun 'yan bindigar da suka kai hari kan jirgin kasan Abuja-Kaduna'

    A

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, 'Yan bindiga tare da Alwan Hassan lokacin da suka sake shi a daji

    Akalla mutum 68 rahotanni ke cewa na hannun 'yan bindiga da suka kai hari jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

    Wani bidiyo da aka fitar wanda ya rinka yawo har a kafofin sada zumunta, na tabbatar da cewa 'yan bindigar na rike da mata 41 da maza 22, sai kuma yara biyar.

    Wannan na zuwa ne mako biyu bayan kai kazamin harin bam a jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, mutane da dama sun rasa rayukansu baya ga wadanda aka jikkata.

    Mako guda bayan harin hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya ta fitar da sanarwar da ke cewa har yanzu akwai fasinjoji 146 da ba a ji duriyarsu ba.

    Sai dai shugaban bankin manoma, Mallam Alwan Hassan, da ya samu kubuta a makon da ya gabata shi ya bada alkaluman mutanen da ke hannun 'yan bindigar a lokacin da ya ke bayyani kan halin da ya tsinci kansa.

    Bayan kai harin, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sun san da cewa za a kai harin, sannan ya shaida cewa dama mayakan Boko Haram yanzu na cin karensu babu babbaka a dazukan yankunan Kaduna har zuwa Neja.

  7. Faransa za ta taimakawa Ukraine a binciken zargin laifukan yaƙi da ake yi wa Rasha

    Jakadan Faransa a Ukraine ya ce wata tawagar 'yan sandan ƙasar goma sha biyar ta isa kasar domin taimakawa takwarorinsu na Ukraine wajen binciken laifukan yaki da ake zargin Rasha da aikatawa a kusa da birnin Kyiv.

    An dauki hoton tawagar jami'an a wata babbar motar a birnin Lviv.

    Jami'an Faransa sun ce wannan shi ne rukunin kwarraru na farko daga kasashen waje da ke ba da irin wannan taimako.

    A ranar Lahadi mai gabatar da kara na Ukraine Iryna Venediktova, ta ce an gano gawarwakin mutane sama da dari biyu a yankin Kyiv, tun bayan da sojojin Rasha suka janye.

    Rasha ta musanta kai wa fararen hula hari, kuma ta ce bidiyon gawarwakin na boge ne, hada shi aka yi.

  8. Pakistan: An nada Shehbaz Sharif a matsayin firaminista bayan da majalisa ta sauke Imran Khan daga mukaminsa

    Shehbaz Sharif (centre) led an opposition alliance to vote Imran Khan out

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Shehbaz Sharif ne ya jagoranci hadakar jam'iyun siyasa da suka raba Imran Khan da mukaminsa

    Majalisar kasar Pakistan ta zabi Shehbaz Sharif a matsayin sabon firaministan kasar, bayan da ta kada kuri'ar rashin amincewa da mulkin Imran Khan da safiyar Lahadi.

    A yanzu Shehbaz Sharif zai kafa sabuwar gwamnati wadda za ta mulki kasar zuwa watan Agustan 2023 - lokacin da ake sa ran gudanar da zabuka a kasar.

    Mista Sharif zai kasance firaministan Pakistran na 23 cikin jerin firaministocin da suka mulki kasar.

    Abokin hamayyarsa Shah Mahmood Qureshi ya sanar da cewa jam'iyyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf za ta kauracewa zaman majalisar kuma mambobinta sun fice daga zauren majalisar.

  9. Amurka ce ummul-aba'isin dakatar da Rasha daga hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya - Koriya ta Arewa

    UN general assembly members passed a resolution to suspend Russia from the human rights council

    Asalin hoton, EPA

    A makon jiya aka dakatar ta Rasha a hukumar kula da hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, bayan da yawancin mambobin kungiyar suka kada. Wannan matakin ya biyo bayan hujjojin da ke cewa dakarun Rasha sun aikata laifukan yaki.

    Sai dai kasar Koriya ta Arewa - wadda ke cikin kasashe 24 da ba su goyi bayan matakin dakatarwar ba - ta soki matakin.

    "Abin da Amurka ke son gani shi ne... a mayar da kasashe masu 'yancin kansu shanun ware, domin ta ci gaba da kakaba ma duniya haramtaccen ikonta," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar, KCNA da Reuters suka ruwaito.

  10. Kamfanin MTN ya sami amincewar bude bankin MoMo a Najeriya

    Karl Toriola, CEO, MTN Nigeria

    Asalin hoton, Karl Toriola / MTN Nigeria

    Bayanan hoto, Karl Toriola, Shugaban kamfanin sadarwa na MTN Nigeria

    Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sami amincewar hukumomin Najeriya domin ya bude banki, kamar yadda kamfanin ya sanar ranar Litinin.

    MTN ya ce "Babban bankin Najeriya ne zai sanar da ranar da aka amince mu fara aiki, kamar yadda doka ta samar."

    Kamfanin ya ce sunan sabon bankin nasa MoMo Payment Service Bank Limited.

    Kamfanin sai da ya jira amincewar na tsawon shekara biyu kafin aka amince ma sa ta hanyar ba shi lasisi.

    A watan Nuwamba aka ba MTN Nigeria tare da Airtel Africa amincewa ta wucin gadi domin su bude bankuna, inda suke sa ran jawon hakulan 'yan Najeriya kimanin miliyan 38 da ba su da asusun ajiyar banki a kasar.

  11. Afirka ta Kudu: Jacob Zuma bai bayyana a kotu domin halartar shari'arsa ba

    South Africa's ex-president says he was too ill (archive photo)

    Asalin hoton, AFP

    Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma bai bayyana a kotun da ke masa shari'a kan tuhumar cin hanci da rashawa ba, yana cewa yana fama da rashin lafiya.

    Mista Zuma dai ya musanta cewa ya aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

    A ranar Lahadi, tsohon shugaba ya ce yana son a nada wani sabon mai shigar da kara mai zaman kansa, domin ya ce na yanzu ya karkata ga baangare guda, kuma ba zai ma sa adalci ba.

    Sai dai a watan jiya Kotun Kolin kasar ta ki amincewa da wannan bukata ra sauya mai shigar da karar.

  12. Yana yiwuwa Rasha ta kashe daruruwan dubban mazauna birnin Mariupol - Zelensky

    Wrecked car and buildings in Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce yana yiwuwa an kashe daruruwan dubban mazauna birnin Mariupol da ke kudancin Ukraine tun bayan da yaki ya barke, inji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Yayin wata ganawa da yayi da 'yan majalisar kasar Koriya ta Kudu ta intanet, Mista Zelensky ya ce, "An lalata Mariupol, akwai daruruwan dubban mamata a cikin birnin, amma duk da haka Rasha ta ki daina kai hare-hare."

    BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin kalaman Mista Zeelnsky ba; sai dai abin da muka sani shi ne wadanda suka tsere daga birnin sun bayyana cewa mazauna birnin na cikin mawuacin hali matuka.

  13. Ƴan sanda sun kama mijin mawaƙiya Osinachi Nwachukwu, ana tuhumarsa da kashe ta

    Late gospel singer, Osinachi wit her husband, Peter Nwachukwu

    Asalin hoton, PETER NWACHUKWU/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Marigayiya mawaƙiyar yabo Osinachi tare da mijinta Peter Nwachukwu

    'Yan sandan Najeriya sun kama Peter Nwachukwu, wanda shi ne mijin matar nan fitacciyar mawaƙiyar yabo na addinin Kirista mai suna Osinachi kan tuhumar yana da hannu a mutuwar matar tasa.

    Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya da ke Abuja, DSP Josephine Adeh ce ta sanar da BBC haka.

    Ta ce sun fara binciken lamarin.

    Ta kuma ce an kama mijin marigayiyar ce bayan da wani ɗan uwanta ya shigar da ƙara a ofishin 'yan sanda.

    Kafin mutuwar matar, rahotanni sun rika yawo cewa mai gidan Osinachi ya rika dukanta a gida, lamarin da wasu ke cewa shi ne sanadin mutuwarta.

    Osinachi mace ce mai shekara 42 da haihuwa kuma ta mutu ne ranar Juma'a bayan an kwantar da ita a wani asibiti da ke Abuja.

    Marigayiya mawaƙiya Osinachi

    Asalin hoton, PETER NWACHUKWU/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Marigayiya mawaƙiya Osinachi

    Tun bayan mutuwarta, masu bibiyar wakokin mawakiya Osinachi sun rika aika wa sakonnin ta'aziyya ga iyalanta.

    Wasunsu sun bayyana muryarta kamar ta mala'iku, domin tana ratsa su matuka.

    Kafin mutuwarta, ita ce babbar mawakiya a cocin Dunamis International Gospel Centre.

  14. Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kafar yaɗa labarai ta mata zalla a Somaliya

    Nasrin Mohamed Ibraham is Bilan’s chief editor.

    Asalin hoton, UNDP/Said Fadhaye/2022

    Bayanan hoto, Nasrin Mohamed Ibraham ita ce babbar editar Bilan

    An kafa wata kafar yada labarai a Somaliya da zummar sauya halin da mata ke ciki da matsalolin da suke fuskanta a kasar.

    Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya P ce ta kaddamar da kafar yada labaran, inda ta sanar cewa ta yi haka ne domin samar ma mata "wani wuri na musamman da mata 'yan jarida za su iya yin aiki da jagorantar ayyukan jarida b tare da tsangwama ba.

    Mata zalla ne ke tafiyar da kafar mai suna Bilan - wadda ke nufin mai haske kuma bayyananne a harshen Somali - inda akwai ma'aikata shida a halin yanzu.

    Bilan za ta kasance kafa mai zaman kanta kuma za a rika watsa labarai da shirye-shiryensu a talabijin da rediyo da jaridu da kuma a intanet a wata babbar kafar yada labarai mai suna Dalsan Media Group da kuma wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa.

    UNDP/Said Fadhaye/2022

    Asalin hoton, UNDP/Said Fadhaye/2022

    "An dade ana nuna ma mata 'yan jarida bambanci a Somaliyya kuma tashoshin rediyo da talabijin na Somaliya ba sa mayar da hankali kan labaran da suka shafi mata wadanda sune rabin al'ummar kasar," inji Nasrin Mohamed Ibraham wadda ita ce babbar editar Bilan.

    UNDP/Said Fadhaye/2022

    Asalin hoton, UNDP/Said Fadhaye/2022

    Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya na kuma son sauya tunanin 'yan jarida maza kan cin zarafin abokan aikinsu 'yan jarida mata.

  15. Rasha ta harbo jiragen saman Ukraine biyu

    JIrgin yakin Ukraine

    Asalin hoton, IMAGE SOURCE,MIL.GOV.UA

    Bayanan hoto, JIrgin yakin kasar Ukraine

    Rasha ta harbo jiragen saman Ukraine biyu kusa da birnin Izyum, kamar yadda ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar.

    Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kuma ce dakarun Rasha sun lalata wasu makaman da ke harbo rokoki wadanda wata kasar Turai ta ba Ukraine a matsayin tallafin yaki a kusa da garin Dnipro, kuma kamfanin dillancin labarai na Interfax ya ce an kashe sojojin Ukraine 25 yayin harin.

    Baya ga wadannan, Rasha ta kuma harbo wasu jiragen yaki marasa matuki da helikwafta guda a gabashin kasar Ukraine.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin wadannan rahotannin ba kawo yanzu.

  16. Yau ake ci gaba da shari'ar tsohon shugaba Zuma a Afirka ta Kudu

    Mr Zuma has denied all the charges

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mista Zuma ya musanta tuhumar da ake ma sa.

    A Afrika ta Kudu, hukumomi sun kulle hanyoyin mota a yankin wata kotu da ke Pietermaritzburg wadda ke sauraren karar da aka kai tsohon shugaban kasar Jacob Zuma kan cin hanci da rashawa, wadda kotun za ta ci gaba da saurare a yau Litinin.

    Mista Zuma ya musanta dukkan tuhumar da ake ma sa.

    A watan Yulin bara tarzoma ta barke a wasu sassan kasar bayan da aka kama Mista Zuma.

    Cikin tuhume-tuhumen da ake ma tsohon shugaban, akwai na cewa ya karbi cin hancin fiye da dala biliyan biyu daga wasu kamfanonin Turai da suka sayar ma Afirka ta Kudu makamai.

    Ana fuskantar jinkiri mai tsawo a shari'ar da ke jan hankulan al'ummar kasar.

  17. Hotunan wasu abubuwa da suka faru a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a Ukraine

    Medical workers assist evacuated and wounded people who arrived in Lviv from the cities of Bakhmut and Slovyansk

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya na kula da wata mata cikin wadanda suka isa Lviv daga biranen Bakhmut da Slovyansk
    Rescuers search for bodies in the rubble of a residential building destroyed by Russian shelling in Borodyanka

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Masu aikin ceto na neman gawarwakin wadanda gini ya rufta kansu a Borodyanka
    Despair as a woman tries to find her son's body in the town of Borodyanka

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata uwa na kuka yayin da ta ke neman gawar danta a garin Borodyanka
    Another mother waits for her son's body to be recovered from a well at a fuel station in the village of Buzova

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata matar na jiran a fito da gawar danta daga cikin wata rijiya a kauyen Buzova
    Pope Francis calls for an Easter truce in Ukraine to allow a push for peace during Palm Sunday Mass in St Peter's Square

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Fafaroma Francis ya yi kira ga a sasanta a Ukraine yayin da yake gabatar da bkin Palm Sunday a dandalin St. Peter
    One of many buildings that have been heavily damaged by shelling in Kharkiv, Ukraine's second largest city

    Asalin hoton, reu

    Bayanan hoto, Daya dga cikin gidajen da aka lalata a Kharkiv, birnin na biyu mafi girma na Ukraine
    Ukrainian refugees cross into Poland at the border village of Medyka, Poland

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu 'yan gudun hijira sun isa kasar POland a garin Medyka da ke kan iyakar Ukraine da Poland
  18. Maraba a gareku!

    Muna maku maraba da kasancewa da BBC Hausa a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faru a sassan duniya.

    Suna na Sani Aliyu, kuma nine zan jagoranci gabatar muku da abubuwan da ke wakana a sassan duniya kai tsaye.