Biden ya nemi a gurfanar da Putin kotun hukunta laifukan yaƙi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu
Mutum 5 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota

Asalin hoton, JOYNEWS
An tabbatar da mutuwar mutum biyar da jikkatar wasu bakwai a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yau a kan babban hanyar Accra zuwa Kumasi.
Lamari ya faru ne bayan wata motar fasinja ta ci karo da gefen hanya yayin kaucewa arangama da wata babbar motar daukar kaya.
Wakilin BBC ya ce cikin wadanda suka mutu, har da direban motar ta haya, yayin da wasu da yawa suka yi muguwar jikkata.
Jam’iyyun siyasar Najeriya za su iya fara tsayar da ƴan takara – INEC

Asalin hoton, @Inec
Hukumar zaɓen mai zaman kanta a Najeriya ta ce jam'iyyun siyasa da ke son shiga babban zaben 2023 za su iya fara gudanar da zaben fitar da gwani a hukumance.
Hukumar ta ce daga yau 4 ga wannan watan zuwa 3 ga watan Yunin 2022 aka keɓe domin jam’iyyun siyasa su gabatar da zaɓukan cikin gida tare da warware dukkan wani rikici da ka iya tasowa sakamakon zaɓukan.
Jami’a a hukumar zaɓen Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta ce lokacin da aka ware na fitar da ƴan takara na cikin kundin dokokin zaɓe na ƙasar.
Ana son jam’iyyun siyasar su tsayar da ƴan takara tare da warware duk wani saɓani kafin cikar wa’adin da aka ƙayyade.
Faransa ta nemi a yi bincike kan kashe fararen hula a Mali
Faransa ta yi kira a gudanar da wani binciken ƙasashen duniya kan rahotannin da ke cewa dakarun gwamnatin Mali da sojojin haya na Rasha sun kashe daruruwan fararen hula.
Tarayyar Turai ma da Amurka sun yi irin wannan kira sakamakon mace-macen da aka samu a yankin Moura na tsakiyar kasar.
A ranar Juma'ar da ta gabata, rundunar sojan Mali ta ce ta kashe masu ikrarin jihadi fiye da 200 a cikin kwana 10 da suka kwashe suna yakar su a yankin.
Ba zai yiyu cikin sauƙi a iya tantance wadanda aka kashe da kuma wadanda suka yi kashe-kashen ba.
Mali dai ta musanta cewa sojojin haya daga Rasha na taimaka mata wajen yakin da 'yan ta da kayar baya da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.
Harin da aka kai wa jirgin ƙasa abin tsoro ne – JNI

Asalin hoton, NRC
Ƙungiyar Jama`atul Nasrul Islam ta yi tir da harin da `yan bindiga suka kai kan jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a makon jiya.
Cikin wasu kausasan kalamai na rashin jin dadin abin da ya faru, Kungiyar ta ce babban haƙƙin da ke wuyan gwamnati shi ne kare rayukan al`umma, kuma alama ce ta rauni a ce gwamnati ta gaza yin hakan.
Dr Khalid Abubakar Aliyu babban sakataren kungiyar ya ce an daɗe ana ruwa ƙasa na shanye wa, domin daɗe ana fama da matalar tsaro amma ba sauƙi.
Ya ce: “Wurare da yawa an hana noma da cin kasuwanni, wanda ke nuna kamar gwamnati ta gaza, lamarin da kan iya jefa al’umma cikin wani hali."
Biden: A gurfanar da Putin kotun hukunta laifukan yaƙi

Shugaban Amurka Joe Biden ya sake kiran Vladimir Putin a matsayin “mai laifukan yaƙi” tare da kiran a gurfanar da shi kan kisan al’ummar Ukraine a birnin Bucha.
Ko a watan jiya mista Biden ya zargi Putin da aikata laifukan yaƙi.
Kalamansa na yanzu na zuwa ne bayan rahotannin gawawwaki da ke yashe a garin Bucha.
Kotu ta sake tura Mubarak Bala gidan yari

Asalin hoton, IHEU
Wata babar kotu da ke Kano ta sake aike wa da Mubarak Bala gidan yari saboda rashin gabatar wa kotu kwararan hujojin da za su gamsar da ita cewar ba shi da lafiya.
An kama shugaban kungiyar wanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya Mubarak Bala, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.
Ya musanta zargin yin batanci ga addini da ake masa.
Ana sa ran ci gaba da shari’ar zuwa ranar Talata.
Dunkulewar wasu bankunan Indiya biyu ya samar da banki mafi girma a kasar

Asalin hoton, INDRANIL MUKHERJEE/AFP via Getty Images
Banki mafi girma a Indiya ya kara girma, yadda har ya hadiye kamfanin da ya kafa shi.
Kamfanin HDFC - wanda shi ne yafi samar wa jama'ar Indiya basussuka - zai hade da bankin HDFC wanda a baya abokan huldar juna ne.
Kwamitin daraktocin kamfanonin biyu sun amince da hadewar bankunan inda kowane mutumin da ke rike da hannun jarin kamfanin HDFC guda 25 zai sami hannayen jari 42 na HDFC Bank.
Wannan ya kasance hadewar kamfanoni mafi girma da aka yi a tarihin kasar.
Masana na ganin bayan hadewar kamfanonin, sabon kamfanin da za a samar zai sha gaban kamfanin TCS a girma, wanda zai sa ya zama kamfani na biyu a girma a Indiya.
Shugaban Ukraine ya ziyarci garin Bucha da 'dakarun Rasha suka yi wa fararen hulla kisan gilla'

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine Volodynyr Zelensky ya ziyarci garin Bucha da ke kusa da Birnin Kib, inda aka yi zargin cewa dakarun Rasha sun yi wa fararen hulla kisan gilla.
Ya sake nanata zargin da yake musu na aika laifukan yaki da kisan kiyashi.
Amma duk da haka da BBC ta tambaye shi, ya ce Ukraine za ta ci gaba da kokari kawo karshen yakin ta hanyoyin diplomasiyya da kuma na soji.
An dai yi Allah-wadai da kashe-kashen na Bucha a kasashen daban-daban na duniya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macro y ace akwai alamu karara da ke nuna cewa an aikata laifukan yaki a wajen.
Ya yi kiran da a saka ma Rasha sabbin takunkumai na fitar da kwal da danyen mai.
Faraministan Poland Meteusz Morawiecki ya ce ya kamata a kira kazamin kisan kiyashin da sunansa na yanka kuma a hukunta wada nda suka aikata shi.
Ya ce "Dole ne a tattara bayanan wannan laifin na kisan kiyashi kuma hukunta wadanda suka yi shi.
"Saboda haka muna tayin kafa wata hukumar bincike ta kasa da kasa da za ta binciki wannan laifi.
"Laifin kisan kiyashi da aka tafka a wadannan birane na Ukraine."
An tafka asarar miliyoyin daloli a gobarar Somaliland

Asalin hoton, afp
Bayanai na kara bayyana kan girman asarar da aka tafka yayin wata gobarar da ta lakume babbar kasuwar Hargeisa, babban birnin kasar Somaliland ranar Juma'a.
Wata hukumar bincike da hukumar birnin ta kafa ta ce an yi asarar dukiyar da gobara ta cinye da ta fi dala biliyan daya.
Sai dai ba a san dalilin tashin gobarar ba.
'Yan kasuwar Waheen sun dogara ne kacokan kan hada-hadar da suke yi a kasuwar, inda daruruwan dubbansu suka yi asarar dukkan dukiyar da suka mallaka.
Ana hasashen ita ce kasuwa ta uku mafi girma a yankin arewa maso gabashin Afirka, wanda ya hada da Habasha da Djibouti da Somaliya.
Shugabannin kasashe, ciki har da firaministan Birtaniya Boris Johnson sun yi alkawurran sake gina kasuwar.
Firaministan Somalia Mohamed Hussein Roble ya ce gwamnatinsa za t afitar da dala miliyan 11.7 a matsayin tallafin gaggawa.
Somaliland ta balle ne daga Somaliya shekara 30 da ta gabata bayan faduwar gwamnatin Siad Barre a 1991, sai dai har yanzu babu kasar da ta amince da ballewar da kasar ta yi daga Somaliya.
Shugaba Zelensky ya kai ziyara Bucha

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya kai ziyara Bucha, a yayin da ake samun karin shaidu kan ta'asar da aka yi a kusa da Kyiv.
Ya zagaya kan hanyar da aka yi wa dakarun Rasha kwanton-bauna kuma ya yi magana da mutanen yankin.
Ya jaddada ikirarin da ya yi cewa Rasha ta aikata laifukan yaki da kuma kisan kare-dangi a Ukraine.
Da BBC ta tambaye shi kan ko akwai yiwuwar tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da Rasha, sai ya ce: "Eh, saboda dole Ukraine ta samu zaman lafiya. Muna Turai a karni na 21. Za mu ci gaba da yunkurin difilomasiyya da soja."
Ba ma goyon bayan dakatar da Sheikh Nuru Khalid – Malamai

Asalin hoton, Others
Bayanan hoto, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun (hagu) da Malam Rashid bn Al-Qasim (Asadul Islam) a dama Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Izala a Najeriya (mai hedkwata a Jos), Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce ba ya goyon bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Nuru Khalid, limamin Masallacin Apo da ke Abuja.
Ya ce idan har malamin ya yi ba daidai ba, kamata ya yi a kai korafi a gaban majalisar malamai da ke Abuja. Sai dai ba kwamitin masallaci ya dauki matakin dakatar da shi kai-tsaye ba.
“Don ita majalisar malamai ta zauna da shi, ta duba damuwar. Idan abin da ya shafi a yi mai nasiha ne, sai a yi masa nasiha. Idan wanda ya shafi a yi masa gargadi ne, a yi masa... ko idan abin da ya shafi dakatarwa ne na dan wani lokaci, sai a yi masa,” in ji Shekih Sambo.
Hakazalika shi ma wani malamin addini a Abuja, Malam Rashid bn Al-Qasim (Asadul Islam) ya ce duk da cewa yana da bambancin ra’ayi tsakaninsa da Sheikh Nuru Khalid amma a cewarsa ba a yi malamin adalci ba.
“Duka maganganunsa dari bisa dari gaskiya ne,” in ji Malam Rashid kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
A ranar Asabar ne kwamitin Masallacin Apo ya sanar da dakatar da Sheikh Nuru Khalid bayan wata huduba da ya yi ranar Juma’a, wadda a cikinta ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya.
Mawaƙa Angélique Kidjo da Black Coffee sun sami lambobin yabo a bikin Grammys

Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mawaƙiya Angélique Kidjo Mawaƙiya Angélique Kidjo ƴar Benin da mawaƙi Black Coffee ɗan Afirka ta Kudu sun sami lambobin yabo a bikin Grammy Awards na bana.
Kidjo ta sami lambar yabo a rukunin kundin waƙar da yafi yin fice a duniya mai suna Mother Nature. Akwai wasu mawaƙa uku yan Najeriya - Burna Boy, Yemi Alade da Mr Eazi.
Mawakiyar mai shekara 61 ta doke Wizkid da Femi Kuti da Rocky Dawuni dan kasar Ghana wadanda suka fafata da ita. Wannan ne karo na biyar tana lashe lambar yabo ta Grammys.
Shi kuma Black Coffee dan Afirka ta Kudu ya sami lambar yabo a rukunin kundin kidan rawa na zamani. Sunan kundin 'Subconsciously album'.
Wannan ne karonsa na farko na samun lambar yabo ta Grammys. Ɗansa ya raka shi yayin da ya karbi lambar yabon, kamar yadda ake iya gabi a bidiyon da aka wallafa a Twitter.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kashe-kashen Bucha sun gigita shugabannin Turai, sun yi kira da a kara ladabtar da Rasha

Asalin hoton, EPA
Kamar yadda muke sanar da ku, wasu kasashen yammacin Turai na yin kiraye-kiraye da a kakaba wa Rasha wasu sababbin takunkumai kan kashe-kaashen da ake tuhumarta da yi kan fararen hula a birnin Bucha da ke kusa da Kyiv.
Ukraine ta tuhumi dakarun Rasha da "kisan fararen hula da gangar" bayan da aka gano gawarwakin akalla mutum 20 a titunan birnin.
An kuma ce an gano gawarwakin daruruwan fararen hula a wasu garuruwan da ke wajen birnin Kyiv bayan da dakarun Rasha suka janye daga yankin. Rsha ta musanta aikata wadannan kashe-kashen.
Ga halin da ake ciki a baya-bayan nan:
- Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bukaci a sake kakaba wa Rasha takunkumi, musamman a bangaren makamashin kwal da man fetur - inda ya gaya wa kafafen yada labaran Faransa cewa akwai "bayyanannun alamu an aikata laifukan yaki:
- Ministan tsaron Jamus Christine Lambrecht ta ce tilas tarayyar Turai ta tattauna kan hana sayen iskar gas daga Rasha baki daya - matakin da kasashen Tuurai ba sa son dauka duk da cewa Ukraine ta nemi su yi haka - suna cewa matakin zai shafi Turawan yamma
- Sakataren harkokin waje na Amurka Anthony Blinken ya bayyana hotunan gawarwakin a matsayin tamkar "naushi a ciki"
- Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi Allah-wadai daa abin da ya kira "abin takaici". Rahotanni na cewa Birtaniya na iya sanar da daukan matakin kakaba sabbin takunkumi kan Rasjha cikin wannnan makon
- Shi kuma shugaban kwamitin gudanarwa na Tarayyar Turai Charles Michel ya ce tarayyar na shirin saka wa Rasha wasu takunkuman.
Gwamnatin Aljeriya ta yi wa fursunoni 1,000 afuwa albarkacin watan Ramadan

Asalin hoton, Other
Bayanan hoto, Mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Zaki Hannache na cikin waɗanda gwamnatin ta sako Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya yi wa fursunoni fiye da 1,000 afuwa domin watan azumin Ramadan.
Wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa ta ce gwamnati za ta yi afuwa ga wasu masu zanga-zanga 70 wadanda mambobin kungiyar Hirak mai fafutukar kafa dimokuraɗiyya ne.
Cikin wadanda aka saki akwai Zaki Hannache wanda aka kama a watan Fabrairu saboda tuhumar da aka yi masa cewa yana yada labaran kanzon kurege baya ga tunzura mutane su aikata laifukan ta'addanci.
Kungiyar Hirak ta fara zanga-zanga ne amanyan biranen kasar ta Aljeriya tun farkon 2019, matakin da ya tilasta wa tsohon shigabna kasar Abdelaziz Bouteflika sauka daga mukaminsa bayan wasu watanni.
Hirak ta ci gaba da zanga-zanga bayan da Tebboune ya zama shugaban kasa, sai dai ya yi watsi da matakin kungiyar da ke tuhumarsa da bin sahun tsohuwar gwamnatin kasar.
Ukraine ta ce Rasha za ta tura ƙarin dakaru 60,000 fagen yaƙi a Ukraine a sirrance

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar tsaron Ukraine ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki take cewa Rasha ta fara tura karin wasu dubban sojojinta zuwa Ukraine.
"Sanarwar ta ce "Yayin da Rasha ke tace sojojin, ta kan mayar da hankali kan wadanda suka fi kwarewa a fagen yaki."
Ukraine ta ce bayan ta kammala tace su, Rasha na son tura kimanin sojoji 60,000 ne zuwa fagen daga a Ukraine.
Sai dai Rashar ba ta ce komai ba kan wannan tuhumar, kuma BBC ba ta tabbaar da sahihancin rahoton ba, amma a farkon watan jiya Shugaba Putin ya sanar cewa zai tura sojoji sababbin dauka zuwa Ukraine.
Gwamnatin Najeriya ta doɗe layukan waɗanda ba su yi rajistarsu ba

Asalin hoton, NCC Nigeria
Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke cikin kasar su hana masu amfanin da layukan tarho yin waya daga layukansu idan har ba su yi rajistarsu ba kuma ba su hada su da lambar zama dan kasa ba (NIN) daga yau Litinin 4 ga watan Afrilun 2022.
Hukumar da ke kula da batutuwan sadarwa a Najeriya NCC tare da hukumar da ke kula da kuma yin rajistar 'yan Najeriya (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa ta hadin gwuiwa da suka fitar.
Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe layukansu saboda rashin hada su da lambar dan kasa ba za su iya kiran kowa ba, sai dai za a iya kiransu.
Ministan sadarwa na kasar Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kawo yanzu, ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.
Sanarwar ta ce "Muna ba dukkan wadanda aka dode layukansu daga yin waya, da su tafi cibiyoyin da ake yin rajista domin hada lambobin nasu da lambar dan kasa domin kamfanonin sadarwa su iya bude musu layukan nasu.
Matsalar tsaro ta fi karfin Buhari - Obasanjo

Bayanan hoto, Toshon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a jiya ya bayyana rashin tsaro da ke addabar kasar a matsayin 'babbar matsala', kuma ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe domin magance matsalar.
Tsohon shugaban ya furta kalaman ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta a jihar Ogun, yayin da yake karbar Dakta Ugochukwu Williams, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP da tawagarsa.
Tsohon shugaban ya ce matsalar tsaron ta gagari gwamnatin Muhammadu Buhari. "Idan wani ya zo nan ya ce ina son ganinka, zan amsa ma sa da cewa gani, saboda halin da muke ciki a Najeriya yafi karfin wani mutum daya ya ce yana da mafita. Na yi imanin sai mun zauna tare kuma mun duba al'amarin tare."
Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ruwaito shi yana cewa, "Cikin wannan halin babu wanda ke da cikakken tsaro ko a kan hanyar mota, ko a cikin jirgin kasa, ko ma a filin jirgin sama. Lalali akwai babbar matsala."
"Ya kamata dukkan 'yan Najeriya su sani cewa mun fda cikin wata matsalar da ta gagari gwamnati mai-ci, amma bai kamata mu bari matsalar ta fi karfin Najeriya ba, inji shi".
Budewa
Barka da shigowa shafinmu na rahotanni kai-tsaye daga BBC Hausa.
Sani Aliyu ne zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tun daga wannan hantsi na Litinin har zuwa yammacin yinin. Sai ku kasance tare da mu domin jin yadda abubuwa ke kasancewa.
