Sai da safe
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Sai gobe za mu ɗora daga in da muka tsaya.
Mun gode da kasancewa tare da mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Sai gobe za mu ɗora daga in da muka tsaya.
Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asalin hoton, APC
A Najeriya, a gobe Asabar ne jam`iyyar APC mai mulki ke babban taronta na kasa, inda wakilai daga sassan kasar za su zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin jam`iyyar nan da shekaru hudu masu zuwa.
Mutum tara ne suka nuna sha`awar takarar shugabancin jam`iyyar, amma jiga-jiganta sun yanke shawarar bin hanyar maslaha yayin zaben.
Sau biyu ana saka rana ana dage ranar taron bayan an ci wani zamani ana hayaniya da ta da kura.
Bakwai daga cikin mutum tara da ke takarar sun fito ne daga arewa ta tsakiyar Najeriya. Su ne: Mallam Saliu Mustapha, Mallam Mohammed Etsu, Senata Mohammed Sani Musa, Senata Tanko Al-Makura, Senata George Akume, Senata Abdullahi Adamu.
Sai na takwas, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar arewa maso yamma. Sannan akwai Senata Ali Madu Sharif, wanda `yan kwanaki gabannin taron ya ce ya janye.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, kuma jami`i a kwamitin yada labarai na babban taron ya ce maslaha za a bai wa fifiko.
Wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai kan ƙauyuka shida a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna sun yi sanadiyyar kashe gwamman mutane a yankunan.
Gwamnatin Kaduna ta bakin Ma'aikatar Tsaro ta tabbatar da kai harin a ranakun Alhamis da Juma'a amma ba ta bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, tana mai cewa suna jiran cikakken rahoto kan lamarin.
Wasu rahotanni na cewa an kashe mutum kusan 50 a hare-haren.
Garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗa da Dillalai, da Barebari, da Dokan Alhaji Ya'u, da Durumi, da Kaya da kuma Fatika.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Kaduna ta cire dokar hana fita da ta saka kan Ƙaramar Hukumar Jema'a sakamakon ƙaruwar rikicin ƙabilanci a yankin na Kaduna ta Kudu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Cikin wannan bidiyon na sama, Saddiqa Bkeke ta yi bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sa Rasha ta afka wa maƙociyarta Ukraine, inda ake fafata yaƙi yanzu haka.
Rasha ta fara kai hare-haren ne a ranar 24 ga watan Fabarairu.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, 'yan gudun hijira fiye da miliyan uku ne msuka tsere daga Ukraine ɗin zuwa ƙasashe maƙota, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Ivory Coast ta shiga sahun kasashen Afirka da suka kawo karshen tilasta wa mutane amfani da takunkumi.
Kasar ta ce daga yanzu za a rika sanya takunkumin ne kawai a wuraren taron jama’a saboda raguwar masu kamuwa da cutar korona.
Har wa yau, ta ce mutanen da ke shiga kasar da wadanda ke halartar taruka ba sai sun nuna shaidar gwajin cutar ba.
Sabbin alkaluma da ke fitowa daga Ivory Coast din sun nuna cewa mutum tara ne ke kamuwa da cutar a rana, wanda ya tasamma mutum 796 da ke dauke da cutar a fadin kasar da ke Afirka ta Yamma.
Kawo yanzu, allura miliyan 10 aka shiga da su kasar – inda aka yi wa mutum miliyan huu rigakafi a kasar mai al’umma da ta haura miliyan 23.

Asalin hoton, EPA
Firaministan Hungary Viktor Orban ya yi watsi da buƙatar Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ta neman ƙasar ta ba su makamai da kuma saka wa Rasha tsauraran takunkumai, yana mai cewa "hakan ya saɓa wa muradun Hungary".
Orban ya ƙi amincewa da buƙatar ta Zelensky a wurin taron Majalisar Turai "saboda sun saɓa wa muradun Hungary", a cewar wani magana da yawun gwamnatin Hungary cikin wata sanarwa.
"Hungary ba ta son ta goyi bayan wani ɓangare a yaƙin nan, saboda haka ba za ta bari a kai makamai Ukraine ba," in ji Kovacs.
Orban ya ce 'yan asalin Hungary da ke zaune a yammacin Ukraine za su shiga cikin zullumi idan ƙasarsu ta kai wa Ukraine ɗin makamai.
Hungary wadda mamba ce a ƙawancen tsaro na Nato, ta ƙi aika wa Ukraine makamai da kuma ƙyale ta ta bi sararin samaniyarta. Sai dai ta bar rabin miliyan na 'yan Ukraine sun shiga ƙasarta.
Orban ɗan jam'iyyar kishin ƙasa, ya ƙulla ƙawance da Shugaban Rasha Vladimir Putin a 'yan shekarun nan.

Ƙungiyar Muryar Talaka ta karrama Sashen Hausa na BBC albarkacin cikar sashen shekara 65 da fara yaɗa shirye-shiryensa ta rediyo.
Ƙungiyar ta masu sauraron kafofin yaɗa labarai na ƙasashen waje, ta kai ziyara ofishin BBC na Abuja a yau Juma'a, inda ta gabatar wa Editan BBC Hausa Aliyu Tanko kyauta ta musamman.
Kazalika akwai babban allon talla ɗauke da sunan BBC da kuma sunan ƙungiyarsu.
Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Zaidu Bala ne ya jagoranci tawagar yayin ziyarar.



Babban hafsan hafsoshin dakarun kasa na Rasha ya ce daga yanzu sojojinsa za su mayar da hankalinsu ne kan yankin gabashin kasar, musamman "domin ta 'yantar da yankin Donbas na kasar baki dayansa."
Ma'aikatar tsaron kasar ta ce Rasha na duba hanyoyi biyu ne a wannan aiki na musamman da sojojinta ke yi - na farko ya shafi dukkan kasar Ukraine inda na biyu kuwa zai mayar da hankali ne a yankin Donbas.
Sergey Rudskoy, wanda shi ne shugaban rundunar gudnarwa ta sojojin Rasha ya ce kashi 93 cikin 100 na Luhansk Oblast da kashi 54 cikin 100 na Donetsk Oblast na hannun dakarun Rasha ne.
Rasha ta lalata yyawancin jiragen sama na yaki na kasar Ukraine tare da jiragen yaki na ruwa, wanda ya ce ya kawo karshen kashi na farko na aikin da Rasha ke som cimma wa a kasar, kamar yadda ya ce.
Sai dai ma'aikatar tsaron ta Rasha ba ta ce za ta fasa kutsawa cikin biranen Ukraine da ta yi wa kawanya ba. Ta kuma yi gargadi cewa za ta mayar da mummunan martani nan take idan kasashen yamma suka yi yunkurin hana jiragen kasarta yin shawage a sararin samaniyar Ukraine.

Asalin hoton, AFP
Wata kotu a Angola ta yanke hukuncin daurin shekara tara a kurkuku kan Carlos de São Vicente, wani dan kasuwa mai alaka da tsofaffin shugabannin kasar biyu.
Kotun ta daure shi ne kan satar dala miliyan 900, kamar yadda mujallar Novo mai zaman kanta ta ruwaito.
Sai dai lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara kan wannan hukuncin.
An tsare Mista De São Vicente na tsawon fiye da shekara guda kafin aka fara shari'arsa watan Fabrairu.
Ya kasaance surukin shugaban Angola na farko Agostinho Neto ne, inda aka mika ma sa ikon gudanar da bangaren man fetur na kasar a karkasshin mulkin shugaba José Eduardo dos Santos.
Amma gwamnati mai ci karkashin shugaba João Lourenço ta maka mutanen da ke da alaka da tsohon shugaban kasar Dos Santos.
Sai dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa na shan suka saboda yadda ake amfani da ita a matsayin makamin siyasa a cikin kasar.

Asalin hoton, Reuters
Fadar Kremlin ta mayar da martani kan kalaman Shugaba Joe Biden na Amurka wanda ya ce yana goyon bayan a kori Rasha daga kungiyar G20 ta kasashe mafi karfin tattalin arziki 20 na duniya kan mamayar da ta yi wa Ukraine.
A cewar Fadar Kremlin, tasirin wannan matakin ba wanda zai dame ta ne ba.
"Tsarin G20 yana da muhimmanci, amma a halin da ake ciki, kuma ganin cewa yawancin mambobin kungiyar na yakar mu ta bangaren tattalin arziki, babu wani abin da zai faru," inji kakakin Fadar ta Kremlin Dmitry Peskov yayin da yake jawabi ga manema labarai.
Peskov ya kuma ce duniya ta zarce Amurka da Turai, kuma ya yi hasashe cewa yunkurin da kasashen ke yi na mayar da Rasha saniyar ware ba zai yi nasara ba.

Asalin hoton, Getty Images
Mawuyacin halin da ake ciki a Mariupol da aka yi wa kawanya na ci gaba da ta'azzara, yayin da Rasha ta hana shigar da kayan agaji, a cewar Magajin birnin.
Sojojin Rasha sunb yi kawanya a birnin wanda ke kusa da tashoshin jiragen ruwa tun daga farkon soma mamayar kasar, babu wutar lantarki da ruwan sha da iskar gas. Galibin birnin yanzu ya zama kufayi.
“Yanayin birnin yana da matukar wahalar sha'ani. Yanayi ne da ke matukar bukatar agaji,” a cewar Vadym Boychenko. “Dakarun Rasha sun mamaye wani bangaren birnin amma sojojinmu na ci gaba da tafiyar da birnin, amma ana ci gaba da yaki babu kakkautawa.”
Kusan mutum 100,000 aka rutsa a Mariupol kuma duk wani yunkuri na fitar da mutane da dama daga birnin ya ci tura.
Dubban mutane sun yi nasarar ficewa daga birnin a motocinsu. Da dama daga cikin su sun ce babu ruwan sha da abinci, sanna kuma dakarun Rasha suna kai hare-hare babu kakkautawa.
“Muna aiki domin kwashe mutane da dama kuma na yi amannar cewa hakan ne kawai zai sa mutane su tsira,” a cewar Magajin birnin. “An rusa birnin. Za a kwashe shekaru da dama kafin a sake gina shi.”

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS na shirin hallarar wani taron koli a Ghana a yau Juma'a, domin duba halin da Mali ke ciki bayan da sojojin suka hambare gwamnatin kasar.
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Mali Assimi Goita, ya ki amincewa da gayyatar da aka mika ma sa na halartar taron kolin.
A watan Janairu kasashen yammacin Afirka suka rufe kan iyakokinsu da Mali, kuma suka sanar da za su kaurace ma ta bayan da gwamnatin mulkin sojin kasar ta sanar cewa ta dage alkawarin da ta dauka na gudanar da zabukan da za su mayar da kasar bisa tafarkin dimokradiyya.
Ranar Alhamis wata kotu ta bayar da umarnin a janye matakan ladabtarwan da aka kakaba wa jagororin gwamnatin mulkin soja ta Malin.

Asalin hoton, Reuters
Mun sami karin bayanai kan harin sama da dakarun Rasha suka kai a birnin Mariupol na kudancin Ukraine.
Kawo yanzu, ba a san yawan wadanda suka mutu daga harin ba saboda ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa da sojojin Rasha ke yi kan birnin.
Amma jami'an Ukraine a yanzu sun ce kimanin mutum 300 ne suka rasa rayukansu yayin wancan harin, wanda ya fada kan wani ginin gidan wasannin kwaikwayo, inda daruruwan 'yan Ukraine ke neman mafaka.
Jami'an Ukraine na cewa Rasha ce ta kai harin, sai dai Rashar ta musanta ikirarin nasu.
Ofishin Magajin Garin Mariupol ya ce "Daga bayanan da shaidu suka sanar da mu, kimanin mutum 300 ne suka halaka a ginin Drama Theatre na Mariupol wanda ya biyo bayan hare-hare da jiragen yakin Rasha suka kai."
Sai dai kafofin sadarwa da birnin na Mariupol sun kasance 'yan kalilan, saboda haka ne babu yadda za a iya tantance sahihancin rahotannin da ke fitowa daga can.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Rasha Dmitry Medvedev, wanda a yanzu shi ne mataimakin shugaban kwamitin tsaro na kasar, ya ce "abin dariya" ne a dauka cewa matakan ladabtarwar da kasashen Yammacin Turai suka dauka kan kamfanoni da 'yan kasuwar Rasha za su yi tasiri kan gwamnatin kasar.
Kasashen Yamma sun saka jerin takunkumai kan Rasha, wasunsu an saka wa manyan attajiran kasar ne wadanda a tunaninsu akwai wata alaka ta kut-da-kut tsakaninsu da Shugaba Vladimir Putin.
Ya ce "Bari mu tambayi kanmu: Shin akwai wani karfin fada a ji da wadannan 'yan kasuwar ke da shi kan jagororin gwamnatinmu?"
"A bayyane, amsar ita ce: babu."
Sai dai masu nazari na cewa matsawa 'yan kasuwar na iya yin tasiri.
Stanislav markus, wanda ya dade yana nazarin attajiran na Rasha,ya shaida wa mujallar Amurka Vox cewa matakan ladabtarwan na damunsu sosai su kuma babu makawa gwamnatin Rasha za ta ji a jikinta."

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaron Sudan sun kashe wani mai zanga-zangar nuna kiyayya ga juyin mulki a ranar Alhamis a Khartoum.
Mutumin mai shekara 28 da haihuwa na cikin mutane 90 da aka kashe tun bayan da zanga-zanga ta barke domin nuna adawa da juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa gwamantin fara hula ta Abdalla Hamdok a watan Oktobar bara.
Sai dai duk da kashe-kashen, masu zanga-zangar ba su karaya ba.
A ranar Alhamis, dubban masu zamga-zanga sun yi maci zuwa fadar shugaban kasa a Khartoum, inda jami'an tsaro suka tarbe su da harsasai da hayaki mai sa hawaye.
Masu zanga-zangar na son sojojin su sauka, kuma su mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Asalin hoton, UKRAINE PRESIDENT'S OFFICE
Dazu-dazu cikin dare shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gabatar da wani jawabi ga taron kolin majalisar tarayyar Turai a birnin Bruussels.
Shugaban ya bayyana yadda Rasha ke ragargazar kasarsa, kuma ya gode wa Turai saboda hada kan da suka yi kan goyon bayan Ukraine.
Amma kwatsam sai ya fara sukar shugabanin da ke halartar taron, yana cewa sun makara a kokarinsu na taka wa Rasha birki.
"Kun kakaba jerin takunkumai. Mun gode. Wadannan matakai ne masu kyau."
Sai dai kun makara... akwai wata 'yar dama," inji shi.
Daga nan ne ya saka bukatarsa ga kasashen da ke makwabtaka da Ukraine, yana kira a garesu da su shigar da ita cikin tarayyar Turai:
"A nan ina rokonku - kada ku makara."

Asalin hoton, gett

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Masu bibiyarmu barka da tashi da fatan an wayi gari lafiya.
A yau ma Sani Aliyu ne a yau ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya. Sai ku kasance da Sashen Hausa na BBC cikin wannan yini.