Rasha da Ukraine sun fara musayar fursunoni

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo ƙarshen rahotannin a wannan shafin. Ku biyo mu gobe Juma'a don samun wasu sababbi.

    Kafin lokacin, Umar Mikail ne ke muku fatan mu kwana lafiya.

  2. Rasha da Ukraine sun fara musayar fursunoni

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Ukraine ta ce ta kammala dukkan shirye-shirye na gudanar da musayar fursunoni da Rasha tun bayan fara yaƙi tsakaninsu wata ɗaya ke nan.

    A cewar, mataimakiyar firaministan kasar, Iryna Vereshchuk, an yi musayar sojojin Ukraine 10 da kuma masu mamayar Rasha 10 a tsakanin kasashen biyu.

    A bangare guda kuma, an yi musayar ma'aikatan jirgin ruwan Rasha 11 wadanda aka ceto daga wani jirgi da ya nitse a gabar ruwan Odesa da kuma 'yan Ukraine 19 ma'abota tafiya ta ruwa wadanda Rasha ta kama tun a farkon yakin.

  3. Ghana za ta zaftare albashin ministoci don farfaɗo da tattalin arziƙinta

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta sanar da sabbin matakai na saka dala biliyan biyu cikin tattalin arzikinta don farfaɗo da darajar kuɗinta da ke faɗuwa.

    Sauran matakan sun haɗa da zaftare albashin ministoci da kuma shugabannin ma'aikatun gwamnati da kashi 30 cikin 100.

    Ministan Kuɗi Ken Ofori-Atta ya ce matakan za su taimaka wa Ghana wajen yaƙi da annobar korona da kuma tashin farashin ɗanyen man fetur da yaƙin Ukraine ya haifar.

    Yayin wani taron manema labarai, Mista Ofori-Atta ya sanar da ƙara rage kashi 10 cikin 100 wajen kashe kuɗaɗe da kuma rage kashi 1 na farashin man fetur ɗin.

    Ƙasar da ke Yammacin Afirka na fama da hauhawar tsadar rayuwa saboda tashin farashin kaya da kuma faɗuwar darajar kuɗinta na cedi.

    A ranar Litinin, babban bankin Ghana ya ƙara kuɗin ruwa kan bashin da yake bai wa bankunan kasuwanci da kashi 17 cikin 100.

  4. An zargi gwamnatin Habasha da kashe fararen hula 50

    Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi gwamnatin Habasha wato Ethiopia da kashe fararen hula sama da 50 a arewacin yankin Tigray a farkon watan Janairun bana.

    Wasu ƙarin 50 kuma suka jikkata a wani hari da jirgi maras matuki ya kai kan wata makaranta dauke da dubban ‘yan gudun hijira da rikicin ya kora daga gidajensu.

    Da yawa daga cikin wadanda suka mutu da kuma jikkata tsofaffi ne. Sai dai akwai kuma mata da kananan yara da ke rayuwa a tantuna da aka samar.

    HRW ta kuma zargi Ethiopia da aikata laifukan yaki na kai hare-haren kan farar hula da gangan kasancewar babu sansanin jami’an soji a yankin ballanta ma a kai musu hari.

  5. Za mu ƙara yawan manyan makamai da muke bai wa Ukraine - Firaministan Birtaniya

    Birtaniya

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson na gudanar da jawabi ga manema labarai yanzu haka yayin taron ƙawancen tsaro na Nato.

    Ya ce ƙasarsa za ta yi aiki tare da ƙawayenta don "ƙara yawan agajin manyan makamai ga Ukraine".

    Ya ce Birtaniya ta yi alƙawarin ƙarin makamai masu linzami 6,000 kuma za ta ninka yawan waɗanda ta bayar a baya kuma masu haɗari.

    "Wajibi ne mu taimaka wa ƙasa mai 'yanci da ke gudanar da dimokuraɗiyya a shekaru masu zuwa," in ji shi.

  6. Sojojin Najeriya sun ce sun tarwatsa sansanin Boko Haram

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, NG Army

    Rundunar sojan Najeriya ta ce ta tarwatsa sansanin ƙungiyar Boko Haram a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Wani saƙo da ta wallafa a shafukanta na zumunta sun nuna yadda aka tarwatsa motar mayaƙan da ake kai harin bam da ita da ake yi wa kaƙabi da Vehicle Borne Improvised Explosive Device (VBIED).

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun rundunar Operation Desert Sanity ne suka kai harin a jiya Laraba a yankin Njimia-Alafa.

    A cewar rundunar, har yanzu suna ci gaba da aikin zaƙulo 'yan ƙungiyar a dazukan da suke ɓoye.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Ghana Akufo-Addo

    Buhari da Nana Akufo-Addo

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a Abuja babban birnin ƙasar a yau Alhamis.

    Shugaban na Ghana ya halarci bikin cika shekara 20 da kafa cibiyar Shehu Musa Yar'Adua a Abuja.

    Bikin ya samu halartar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Mutum 30 ne suka mutu a hare-haren bam a Somaliya

    Mutum fiye da 30 aka kashe yayin wasu hare-hare biyu da aka kai ranar Laraba da yamma, a cewar 'yan sandan Somaliya.

    Shugaban 'yan sandan gundumar Beledwyne, Kanar Isak Ali Abdulle, ya faɗa wa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa harin farko ɗan ƙunar-bakin-wake ne ya kai shi, inda ya kashe wata 'yar majalisa Amina Mohamed Abdi da wasu masu gadinta.

    Na biyu kuma an kai shi da wata mota cike da bama-bamai, wadda ta haddasa fashewa mai ƙarfin gaske da ta lalata wani asibiti da ke kusa, kuma mutane da dama suka ji raunuka.

    Hakan ya biyo wani hari da aka kai kan filin jirgi da ke wajen birnin Mogadishu, inda mutum takwas ciki har da 'yan ƙasar waje suka mutu.

    Ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta al-Shabab ta ce ita ce ta kai hare-haren.

  9. Rasha na tilasta wa mutane shiga ƙasarta daga Mariupol, a cewar Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Mahukunta a birnin da dakarun Rasha suka yi wa ƙawanya Mariupol sun ce dakarun na kokarin tursasa mayar da mutum fiye da 15,000 zuwa Rasha daga lardin da ta kwace wanda ke gabashi.

    Adadin ya kai rabin mutanen da ke gundumar wadda ta fi kusanci da iyakar Rasha.

    Jami'an Ukraine sun ce tuni aka kai mutum 6,000 zuwa Rashar.

    Sun ce ana ƙwace wa mutanen fasfonsu na Ukraine kafin a saka su a bas a kai su inda za a tantance su.

    Daga nan kuma sai a kai su wasu garuruwa da ke wajen biranen kasar.

  10. Wadanne abubuwa ne Sakatare Janar Stoltenberg ya sanar?

    Sakatare-Janar na Nato Jens Stoltenberg

    Asalin hoton, EPA

    Idan yanzu ku ka fara bibiyar BBC Hausa, ga takaitaccen bayani kan kalaman Sakatare-Janar na Nato Jens Stoltenberg a ganawarsa da 'yan jarida bayan taron kolin da kungiyar ta yi kan Ukraine:

    • Ya ce mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine ita ce "matsalar tsaro mafi girma a wannan zamanin" kuma ya ce "mun tsaya tare da juna domin karfafa tsaronmu da kula da al'ummarmu"
    • Stoltenberg ya ce Nato ta amince ta karfafa tsaronta ta hanyar tura sojoji 40,000 zuwa ga kan iyakarta ta gabas, wanda martani ne ga mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine
    • Ya kuma tabbatar da za a tura rundunonin yaki hudu zuwa kasashen Slovakiya da Hungary da Bulgariya da Romaniya
    • Stoltenberg ya kuma ce Nato za ta inganta tsaro ta bangaren intanet kuma za ta taimaki Ukraine ta kare kan ta daga hare-haren "guba da na haramtattun sinadarai har ma da na nukiliya"
    • Mamayar da Putin ke yi a Ukraine ya sauya tsarin tsaron yammacin Turai na lokacin mai tsawo kuma ya ce Nato ta shirya wa dukkan abubuwan da ke tafe a bangaren tsaro
  11. Shugabannin Nato na daf da yin jawabin bayan taro

    Sakatare-Janar na kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg

    Muna sa ran Sakatare-Janar na kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg zai gabatar da jawabin bayan taro yayin da shugabannin kasashen turai masu wakilci a kungiyar ke gudanar da taron ƙolinsu na musamman kan Ukraine.

    A baya Stoltenberg ya ce shugabannin za su tattauna batun sauya alkibla a fagen tsaro.

    Za a tura wasu jiragen ruwa na yaki hudu zuwa Slovakiya da Hungary da Bulgariya da kuma Romaniya domin karfafa tsaron kasashen yammacin Turai.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da mu domin jin yadda al'amura za su kaya a wajen da za a yi jawabin bayan taron.

  12. Ukraine ta yi iƙirarin nutsar da jirgin ruwan yaƙin Rasha

    Rundunar sojojin ruwa ta Ukraine ta sanar cewa ta yi nasarar lalata wani babban jirgin ruwa na yaki mallakar Rasha kusa da tashar jirgin ruwar birnin Berdyansk da ke kudancin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a Facebook, ta ce ta harbi wani babban jirgin yaki mai suna "Orsk" wanda ke aikin jigilar dakarun Rasha, kuma jirgin ya kama da wuta a cikin tekun Azov da safiyar yau Alhamis.

    Kafofin yada labarai na Ukraine sun wallafa rahotanni da ke cewa an nutsar da wani jirgin ruwan Rasha kuma wasu biyu sun kama da wuta, kana wata ma'adanar makamai da na man fetur ma sun kama da wuta.

    Sai dai kawo yanzu babu yadda za a iya tabbatar da sahihancin wannan rahotaon daga wasu kafofin.

    Rasha ta kama birnin Berdyansk ne cikin makonnin da suka gabata kuma tana amfani da shi ne domin shayar da jiragen yakinta man fetur. Birnin na tsakiyar yankin Crimea da birnin Mariupol.

    The Ukrainian navy said the landing ship Orsk had been destroyed in Berdyansk early on Friday

    Asalin hoton, UKRAINIAN NAVY

  13. Sojan Najeriya ya harbe ƙaramar yarinya da wasu fararen hula

    Nigerian soldier

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Wani sojan Najeriya da ake zargin yana tu'ammali da miyagun kwoyoyi ya harbe akalla fararen hula uku har lahira kuma ya raunata wasu mutum 13 yayin wani harbin mai-uwa-da-wabi da ya yi.

    Wannan al'amarin ya auku ne a tsakiyar garin Mafa da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

    Ganau sun ce cikin wadanda sojan ya halaka, akwai wata yarinya 'yar shekara uku, sannan sauran mutum 13 na asibiti inda ake kula da su saboda raunukan da suka samu daga harbin da ya yi musu.

    Wani rahoto ya ce sojan na cikin sojojin Najeriya da aka tura yankin domin yakar 'yan kungiyar Boko Haram da na ISWAP.

    Shaidu sun kuma ce an yi nasarar kwace bindigar daga hannun sojan kuma a halin yanzu yana hannun hukumomin soji.

    Sai dai rundunar sojojin Najeriya ba ta ce uffan ba dangane da al'amarin.

  14. Hukumomi sun ƙwace otel da helikwaftoci daga hannun tsohon minista a Zambia

    Mr Malanji served in the cabinet of former President Edgar Lungu

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomi sun kama tsohon ministan harokoin waje na Zambia Joseph Malanji kan tuhumar da suke ma sa ta halarta kudin haram.

    Gwamnatin kasar ta ce Mista malanji ya shiga hannu ne bayan da bincike ya bankaɗo cewa ya mallaki wani otel da ake tuhumarsa da mallakarsa da kudaɗen al'ummar ƙasar.

    Ana kuma tuhumarsa da sayen wani helikwafta kan dalar Amurka 700,000, kudaden da hukumomi suka ce na sata ne.

    A baya, Mista Malanji ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.

    Sai dai 'yan sanda sun bayar da belin Mista Malanji, kamar yadda tashar talabijin ta Diamond TV ta sanar.

    Ya rike mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaba Edgar Lungu, wanda ya fadi a zaben shugabban kasar da aka yi a 2021.

  15. NATO: Shugabannin ƙasashe sun isa Brussels domin taron ƙoli kan ƙasar Ukraine

    Nato leaders arrive in Brussels for Ukraine summit

    Shugabannin kasashen da ke mambobin kungiyar tsaro ta Nato sun isa birnin Brussels domin duba matakan da suka dace su dauka domin mayar wa Rasha martani kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.

    Mambobin ƙungiyar sun dauki hoto tare, kamar yadda suka saba gabanin fara taron, wanda ake cewa yana cikin tarurruka mafi muhimmanci a tarihin kungiyar.

    A yau Alhamis yakin na Ukraine ya shiga wata na biyu tun bayan da Rasha ta tura dakarunta cikin kasar domin ta hana ta shiga kungiyar ta Nato da kuma zama mamba a tarayyar Turai, wadanda ke cikin wasu bukatu da Rashar ta bayyana a matsayin dalilinta na mamaye kasar.

  16. Mayaƙan al-Shabab sun kashe wata 'yar majalisa yayin harin kunar bakin wake a Somaliya

    Akalla mutum 15, ciki har da wata 'yar majalisar kasar Somaliya sun halaka, bayan da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai hare-hare biyu a garin Beledweyn na tsakiyar kasar.

    Firaminista Mohamed Hussein Roble ya bayyana kashe Amina Mohamed Abdi a matsayin "kisan gilla". Shi kuma shugaban kasar Abdullahi Farmajo ya aika da sakonsa na ta'aziyyar ta Twitter:

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Cikin mamatan akwai tsohon dan majalisa Hassan Dhuhul da wasu sojojin Somaliya.

    Kafofin yada labarai a yankin na cewa yawan mamatan na iya zarce alkaluman wadanda aka sanar a yanzu.

    Babbar tashar talabijin ta Somaliya ta wallafa wasu hotuna na wadanda aka kashe yayin harin.

    Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai hare-haren - wadanda aka kai a biranen Mogadishu da tsakiyar Beledweyne.

  17. Yadda 'yan Ukraine ke dogon layi domin neman abinci

    Dozens of Ukrainians queue for food and other supplies in a Russian-controlled part of Mariupol

    Asalin hoton, reu

    Yayin da ake kokarin samar da hanyoyi na jin kai domin fararen hula su fice daga birnin Mariupol ke cin karo da matsaloli, an sami shiga da tallafin abinci da magunguna a birnin da Rashawa ke iko da shi a jiya Laraba.

    Fiye da muutum 100 sun yi layi yayin da suke jimirin samun abin da za su ci wanda aka kai cikin wata motar dakon kaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sanar.

    Wata mata mai 'ya'ya biyu mai suna Angelina ta ce an ba su biredi da abinci, kuma ta ce ta yi sa'ar isa wurin kafin abincin ya kare. "Ba ko yaushe za ka sani ba... sai kawai ka ji cewa ya kare," inji ta.

    Ta kuma kara da cewa, "ficewa daga nan a motar bas na da matukar wahala a yanzu."

    A Russian soldier stands guard as Mariupol residents who queue for humanitarian aid delivered by lorry

    Asalin hoton, Reuters

  18. Koriya ta Arewa ta harba haramtaccen makami mai linzami, mai dogon zango

    North Korea missile launch

    Asalin hoton, Reuters

    A karon farko tun shekarar 2017, Ƙasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani makami mai linzami kuma mai dogon zango - wanda ke cikin rukunin makaman da kasashen duniya suka haramta yin amfani da su.

    Makwabciyarta Koriya ta Kudu ce ta sanar da wannan lamarin, inda ta kara da cewa makamin ya fada cikin teku a kudu da kasar Japan bayan da ya yi tafiyar fiye da sa'a guda, kuma ya kai kololuwar nisan kilomita 6,000.

    Jami'an ƙasar Japan sun kiyasta cewa rokan na iya yin tafiyar kilomita 1,100 - wanda ka iya ba shi damar isa Amurka.

  19. Idan 'ya'yan jam'iyyar APC ba su yarda da a yi sulhu a zaben fitar da gwani ba, to zabe ne kawai mafita

    Bisa dukkan alamu jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shuwagabannin jam’iyyar da ake shirin yi a ranar Asabar mai zuwa.

    Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai daban-daban – inda misali aka kebe wa yankin arewa ta tsakiya kujerar shugaban jam’iyya na kasa.

    Haka nan, shugaban kasar Muhammadu Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a wajen zaben shuwagabannin, a maimakon haka a sasanta tsakanin ‘yan takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.

    To sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba, misali tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.

    To dazu bayan da gwamnonin jihohi na jam’iyyar ta APC suka gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya yi wa wakilin BBC Ishaq Khalid karin bayani.

    Sai ku latsa alamar lasifika a jikin hoton da ke ƙasa.

    Bayanan sautiAbubakar Bagudu ya ce baki bai zo daya ba kan wanda zai zama shugaban APC
  20. Budewa

    Masu bibiyarmu barka da tashi da fatan an wayi gari lafiya.

    A yau ma Sani Aliyu ne a yau ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya. Sai ku kasance da Sashen Hausa na BBC cikin wannan yini.