Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya
Sai gobe!
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu
Sai gobe!

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Mexico Andrés Manuel López Obrador, ya caccaki Amurka kan agajin gaggawa da ta ba Ukraine yayin da ƙasarsa ke jiran taimako.
Shugaban na mayar da martani ne ga majalisar Amurka da ta amince da taimakon dala biliyan 13.6 ga Ukraine.
Shugaba Mr López Obrador ya ce ƙasashen yankin sun shafe shekara hudu suna jiran amincewar majalisar kan ɗan tallafin da suke nema daga Amurka (dala biliyan huɗu) domin rage talauci da laifuka sakamakon kwararar da mutane ke yi zuwa Amurka.
Tun da farko López Obrador ya sanar cewa Mexico ba za ta bi sahun Amurka da ƙasashen Turai ba na ƙaƙabawa Rasha takunkumi.
Gwamnatin sojin Myanmar ta yi watsi da shelar da Amurka ta yi a jiya cewa aika aikar da sojojin Bama suka yi a kan tsiraru 'yan kabilar Rohingya daidai yake da laifukan cin zarafin bil adama da kuma kisan kiyashi.
Dubban musulmi 'yan Rohingya aka kashe yayin da wasu da dama kuma suka tsere zuwa Bangladesh bayan hare haren da aka rinka kai musu a shekarar 2017.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Myanmar ta ce shelar da Amurka ta yi bata da tushe kuma ba gaskiya ba ce kuma Myanmar bata taba yin wani abu mai kama da kisan kiyashi ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wata mahaifiya mai ‘ya’ya biyar bisa zargin ƙona ‘yarta ‘yar shekara goma.
An kama matar ne bayan wani mutum ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Mowe, yana cewa matar wadda suke zaune gida ɗaya da ita, ta zazzaga wa yarinyar fetur sannan ta banka wuta.
A cewar mutumin da ya shigar da ƙorafi wajen ‘ya sanda, Moroof Ayinde, matar ta ƙona ‘yar tane bayan ta zarge ta da daukar mata wayar salula bayan ta karɓa daga hannun ɗaya daga cikin ƙannenta.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya fada wa manema labarai a Abeokuta cewa bayan samun rahoton abin da ya faru, ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kama matar.
Abimbola Oyeyemi ya ce ‘yar, ta samu mummunar ƙuna a jiki, abin ya sa aka garzaya da ita asibiti mafi kusa kafin daga bisani a mayar da ita zuwa asibitin koyarwa na Olabisi Onabanjo domin samun kyakkyawar kulawa.
‘Yan sanda sun ce daga binciken farko-farko da suka gudanar, mahaifiyar da ake zargi wadda ta yi iƙirarin cewa sun rabu da mahaifin yaran, ta fada musu cewa ba ta san me ya ingiza ta har ta ƙona ‘yar tata ba.
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole ya ba da umurnin a mayar da matar zuwa sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.
Sai dai, ‘ya sandan ba su sanar da ranar da za su gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu ba.
Cin zarafi ko musguna wa ƙananan yara, babbar matsala ce a Najeriya, inda har yanzu wasu jihohin ƙasar ba su sa hannu kan dokar kare haƙƙin ƙananan yara ba, kuma jihohin da suke da dokar ma, ba kasafai ake jin labarin hukunta masu cin zarafi ko tozarta ƙananan yara ba.


Asalin hoton, Reuters
Shugabannin kasashen Masar da Isra'ila da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna a wurin shakatawa na Sharm esh-Sheikh a gabar tekun Bahar Rum a ranar Talata.
Sun tattauna kan yadda za su inganta dangantakar tattalin arziki da tsaro sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da Firaminista Naftali Bennett da kuma Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Mohammed bin Zayed sun yi tattaunawa irinta ta farko tun bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta daidaita dangantakarta da Isra'ila shekaru biyu da suka gabata.
Shugabannin sun tattauna kan makamashi da samar da abinci da kuma tsaron yankin -- musamman dangane da Iran da kuma batun farfado da yarjejeniyar nukiliyarta da ta kulla da kasashen yammacin Turai a 2015.
Masu aiko da rahotanni sun ce kasashen uku wani bangare ne na sahun kasashen Larabawa da ke kawance da Isra'ila da ke neman dakile tasirin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce Rasha ta kai hari kan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya 60a yayin mamayar da ta ke yi a Ukraine.
Hukumar ta tabbatar da cewa an kashe mutum 15 a hare haren, a yayin da aka raunata akalla 37.
Jami'an lafiya a iyakoki sun ce mutane na fama da karancin abinci da ruwan sha kuma suna cikin whaala, yayin da wasu kuma ke tafiyar kwana da kwanaki ba tare da maganin da suke bukata ba.
Sakamakon wani binciken gaggawa da hukumar lafiya ta duniya ta yi ya nuna cewa a cikin 'yan gudun hijra rabin miliyan, kusan dubu dari biyu da hamsin a cikinsu da suka isa Poland na fama da matsananciyar damuwa wadda ke bukatar kulawar gaggawa.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce fiye da mutum miliyan uku da rabi suka bar Ukraine ya zuwa yanzu.
Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya ya yaba wa wasu jami’an ƴan sanda da suka nuna halin ƙwarai da ba kasafai ake samu ba yayin gudanar da aikinsu.
Wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar ta ce akwai ɗan sanda CSP Elemide Akinkunmi da ya mayar da N600,000 da aka tura a asusunsa na banki bisa kuskure.
Ɗan sandan wanda shi ne shugaban gudanarwa na gidan rediyon ƴan sanda ya mayar da kuɗin da aka yi kuskuren tura masa zuwa ga asusun ƙungiyar jami’an ƴan sanda.
Shugaban ƴan sandan na Najeriya ya kuma yaba wa ɗan sanda Yahaya Ahmed a kotun shari’ar musulunci a Gusau jihar Zamfara wanda sanarwar ta ce ya ƙi karɓar cin hancin N300,000 da wani Chukwuka Jude da aka gurfanar a kotun a ranar 18 ga Maris ya ba shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Birtaniya ta ba dakarun Ukraine makamai sama da 4,000 da ke tarwatsa tankokin yaƙi, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta bayyana.
Birtaniya ta ce ta taimakawa Ukraine da makaman ne domin ta kare kanta daga Rasha.
A jerin sakwanni a Twitter, ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ce ƙasar tana da isassun makamai da za ta kare tsaron ƙasa da kuma jaddada manufarta a Nato.

Asalin hoton, Other
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da babban kamfanin sarrafa takin zamani a jihar Legas, wanda attajirin Africa, Alhaji Aliko Ɗangote ya gina.
Kamfanin na yankin Ibeju Lekki a Lagos, wanda aka bayyana ya laƙume dala biliyan 2.5.
Kamfanin zai samar da ton miliyan uku na takin zamani duk shekara.
Kamfanin takin na Dangote zai taimakawa Najeriya rage dogaro da takin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Kamfanin Dangote ya kuma ce kamfaninsa na taki zai taimakawa ƙasashen Afirka dogaro da kansu wajen samar da abinci da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje.

Asalin hoton, FAAN
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Legas da misalin karfe 11 na ranar Talata.
Shugaban zai kaddamar da masana'antar hada taki a gundumar Lekki ta birnin.
Sai dai zai faara da kaddamar da sabon ginin tarbar baki a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Ikeja, baya ga duba wata sabuwar tashar jirgin ruwa mai zurfi da ke gabar teku a can Lekki.

Asalin hoton, epa
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi magana da Fafaroma Francis sanna ya ce fadar Vatican za ta iya taka rawa wajen kawo karshen yakin da Rasha take yi da su.
A wani sako da ya wallafa a Tuwita, Zelensky ya ce ya shaida wa Fafaroma irin "mummunan yanayin da mutane suka fada aciki" da kuma yadda Rasha ta hana shigar da kayan agaji kasar.
Zelensky ya kara da cewa: "Za mu yi murna idan mai alfarma Fafaroma ya taimak wajen kawo karshen wahalhalun da mutane suka fada a ciki."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa bana za a gudanar da itiƙafi a Masallatan Harami lokacin azumin watan Ramadan.
Shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa nan gaba kadan ne za a fitar da tsarin gudanar da itiƙafi a shafin intanet na hukumar da ke kula da masallatan biyu.
Wanna ne karon farko da za a gudanar da itiƙafi cikin shekaru biyu tun bayan bullar cutar korona.

Asalin hoton, Getty Images
Bari kuma mu koma kan yaƙin da ake gwabzawa a yankin arewa maso gabashin Ukraine, a birnin Kharkiv wanda Rasha ke wa ruwan bama-bamai.
Kusan gine-gine 1,000 aka yi raga-raga da su a sanadin bama-baman da Rasha ke jefa wa birnin daga wajensa, kamar yadda hukumar da ke kula da ayyukan jin kai ta Ukraine ta sanar.
Yawancin gine-ginen da aka rusa gidajen zama ne.
Dakarun Rasha sun sa birnin a gaba, inda babu ƙaƙƙautawa suke harba bama-bamai kan birnin, wanda ke da nisan kilomita 30 daga kan iyakar Ukraine da Rasha.
Akalla fararen hula 500 aka kashe, kamar yadda jami'an kasar Ukraine ke cewa.

Ma'aikatar da ke kula da jin adadin al'umma ta Najeriya ta ce za ta fara aikin raba ɗalibai da tsutsar ciki a makarantun kasar, inda ta ce fiye da ɗalibai miliyan 10 ne za su amfana da wannan shirin.
Ma'aikatar ta kuma ce za ta gudanar da wannan aikin ne hannu da hannu da wanda ta ke yi na ciyar da ɗalibai a makarantun gwamnati na ƙasar.
Babban jami'i a sashen da ke kulawa da ayyukan jin dadin al'umma na ma'aikatar, Dakta Umar Bindir ne ya sanar da haka yayin wani taro na kwana biyar da ke gudana a Abuja ta hannun babbar jami'a mai kula da sashen tsare-tsare da bincike ta ma'aikatar, Safiya Sani wadda ta wakilce shi a wajen taron.
Dakta Umar ya ce za a raba ɗaliban ne da tsutsotsin ciki domin inganta lafiyarsu.
Ya kuma ce aikin zai shafi ɗalibai ne daga aji na ɗaya zuwa aji na shida na firamare, musamman waɗanda ke makarantun gwamnati.

Asalin hoton, AFP
Tsohon firaministan Mali Soumeylou Boubèye Maïga - wanda ke fuskantar shari'a saboda tuhumar da ake masa ta cin hanci da rashawa - ya mutu yana mai shekara 67 da haihuwa.
Mista Maiga ya mutu ne ranar Litinin a wani asibiti a Bamako, babban birnin kasar, kamar yadda iyalansa suka sanar.
Iyalan nasa sun ce an kama shi kuma an tsare da shi karkashin wani hali mai tayar da hankali. A watan Disamba aka kwantar da shi a asibiti.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ce gwamnatin ƙasar ta ki amincewa da bukatarsa ta zuwa kasashen waje domin a duba lafiyarsa.
Sai dai ta mika sakonta na ta'aziyya ga iyalan tsohon firaministan, bayan ta fitar da wata sanarwa da ke cewa ya mutu ne bayan wata doguwar jinya da ya yi.
An dai kama Mista Maiga ne a watan Agustan bara kuma aka tsare shi bayan da aka tuhume shi da aikata laifukan cin hanci da rashawa kan yadda aka sayo wani jirgin sama na shugaban kasa, yayin mulkin hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta.
Wata kotu a Kenya ta ci tarar wani mai mota bayan da ta same shi da laifin tuƙin ganganci a kan wata babbar hanya yayin da wata fasinja a cikin motar ke ihu da karfi kuma ɗaya daga cikin ƙofofin motar na buɗe.
An yaɗa hotunan abin da ya faru a shafukan sada zumunta:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƴan sandan Kenya sun ce matar da ke cikin motar budurwar mai motar ce, wadda ta so ya sauke ta daga motar amma ya ƙi, kuma ya nace sai ta bi shi gidansa domin su ɗan shaƙata.
Sai dai sun ce mutumin da matar sun so su janye batun daga hannun ƴan sanda bayan da suka sasanta tsakaninsu.
Amma ƴan sanda ba su amince da wannan matakin ba, domin sun tuhumi mutumin da tuƙin ganganci da kuma saka rayuwar matar da sauran masu amfani da hanyar cikin haɗari.
Mutumin mai suna James Maina Kibe ya amsa laifinsa kuma kotu ta ci shi tarar kimanin dalar Amurka 600 baya ga dakatar da lasisinsa na tuƙi na wani lokaci.
A yau Talata Shugaba Muhammadu Buhari zai isa birnin Legas domin ƙaddamar da wasu ayyuka, ciki har da sabon ginin tarbar baƙi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke birnin na Legas, a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Ga wau hotunan sabon ginin:





A yau ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a jihar Legas da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar.
Tuni wakilin BBC ya isa filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja domin aiko mana da bayanan abubuwan da ke faruwa.
Ana sa ran shugaba Buhari zai ƙaddamar da sabon kamfanin hada taki na Dangote baya ga duba wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta Legas ta yi kafin daga baya ya koma birnin Abuja.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa dukkan matafiyan da aka yi wa cikakkun alluran riga-kafin korona ba sa bukatar yin gwajin cutar na PCR COVID-19.
Wannan ne matakin farko da kasar ta ɗauka kan wannan batun na kiwon lafiya tun da ta fara ganin raguwar alƙaluman masu kamuwa da cutar.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke sa ido kan yaƙi da annobar korona a Najeriya, Boss Mustapha ya sanar cewa daga ranar 4 ga watan Afrilu wannan matakin zai fara aiki.
Sai dai ya bayyana cewa dukkan fasinjojin da ba a yi wa alluran riga-kafi ba, ko ma waɗanda ba a yi musu cikakkun alluran korona ba, tilas su yi wannnan gwajin akalla sa'a 48 kafin su bar ƙasar, ko kuma su yi gwaji na rana ta biyu ko rana ta 7 bayan sun isa ƙasar.

Asalin hoton, Iyalai
Ɗaya daga cikin ɗaliban Najeriya da suka gudu daga Ukraine ya mutu a garinsu na Sokoto da ke arewacin Najeriya.
Babu cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin mutuwar Huzaifa Habibu.
Mahaifinsa Habibu Halilu Modaci ya shaida wa BBC cewa an kai shi asibiti ne bayan da ya fara kokawa, yana cewa ba ya jin dadin jikinsa kuma bayan da aka ga alamar ya daina cin abinci sosai.
Ɗalibin, mai shekara 22, yana karatun zama likita ne a kasar Ukraine, kuma a shekara mai zuwa ake sa ran zai kammala karatun nasa, sai dai ya dawo gida mako biyu da ya gabata saboda barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine.
Wannan ne karonsa na farko na dawowa gida ciki shekara uku.
Mallam Modace ya ce ɗan nasa ya shaida ma sa irin mawuyacin halin da 'yan Najeriya suka shiga a sanadin yakin na Ukraine, da ma yadda suka rika takawa a kafa na lokaci mai tsawo domin ficewa daga kasar.
Har yanzu Najeriya na da ɗalibai kumanin 100 da rikicin ya rutsa da su a birnin Kherson na Ukraine, sai dai ta riga ta kwaso fiye da dalibai 1,500 tun bayan da yakin ya barke a watan jiya.