Sai da safe,
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

Asalin hoton, Reuters
An fara kidaya kuri'un da aka kada a Hong Kong a zaben 'yan majalisar kananan hukumomi inda dukkanin 'yan takarar China ce ta amince da su.
Ba a samu fitowar mutane sosai ba a zaben.
Zaben ya nuna cewa mutum daya a cikin masu kada kuri'a uku ne ya kada kuri'arsa a zaben wanda 'yan adawa suka kaurace ma wa.
Shugabannin Hong Kong din sun samar da motoci kyauta domin karfafawa mutane gwiwa a kan su je su kada kuri'arsu.
Duk da karancin fitowar masu kada kuri'ar, kafar yada labaran China ta Xinhua ta ce fitowar mutanen ta nuna amincewar da mutane suka yi da sabon tsarin.

Gwamnatin jihar Neja ta bayar da umarnin rufe duka makarantun firamare da sakandire da na gaba da sakandire a Ƙaramar Hukumar Wushishi da ke jihar.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito Shugaban Ƙaramar Hukumar Wushishi, Danjuma Suleiman Nalango inda shi ne ya bayar da umarnin sakamakon zargin da ake yi na yunƙurin sace ɗalibai a Zungeru da makwafta.
Shugaban ƙaramar hukumar ya shaida cewa an samu bayanan sirri daga hukumomin tsaro a kan lamarin na yunƙurin ƴan bindiga shiga kwalejin kimiyya da fasaha da makarantar ƴan mata ta sakandire duka da ke a wajen garin Zungeru.
Ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin guje wa irin abin da ya faru a Tegina inda a kwanakin baya aka sace ɗaliban islamiyya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Najeriya bayan tafiyar da ya yi zuwa Turkiyya.
Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da babban sakataren fadar shugaban ƙasa Alhaji Tijjani Idris Umar ne suka tarbi shugaban.
Bayan shugaban ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ya hau jirgi mai saukar ungulu zuwa fadarsa da ke cikin garin na Abuja.
Ko da shugaban ya isa fadarsa, ya karbi kyaututtuka na cikarsa shekara 79 da haihuwa.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, Getty Images
Dubu ɗaruruwan mutane ne suka fito kan tituna a Khartoum babban birnin Sudan domin nuna rashin goyon bayansu ga sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar da kuma tunawa da cika shekara uku da soma zanga-zangar da ta jawo aka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir.
Mutane da dama sun taru a wajen kofar shiga fadar shugaban ƙasar wanda a nan ne Janar Abdel Fattah al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a ƙasar a watan Oktoba yake zama.
A wurare da dama, jami'an tsaro sun harba hayaƙi mai sa hawaye da kuma gurneti mai sa kiɗimewa.
Hakazalika masu goyon bayan dimokraɗiyya na ci gaba da gudanar da tattaki a birane da dama na ƙasar.
A watan da ya gabata ne aka mayar da firaiministan ƙasar Abdallah Hamdok bayan juyin mulkin da aka yi masa a watan Oktoba.
Sai dai ƴan ƙasar Sudan da dama ba su ji daɗi ba kan cewa Mista Hamdok ya yi yarjejeniya da sojoji inda suke kira da a gudanar da mulkin dimokraɗiyya zalla.

Asalin hoton, Reuters
Sri Lanka za ta rufe ofisoshin jakadancinta a ƙasashe uku saboda ta rage kashe kuɗin gudanarwa da kuma adana dalar Amurka da take matuƙar buƙata.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce za ta rufe babban ofishin jakadancinta a Najeriya sannan ta rufe ƙanana a Jamus da Cyprus.
Ministan Harkokin Wajen Sri Lanka, Farfesa G.L Peiris ya faɗa wa Daily Mirror cewa za a mayar da ayyukan ofishin da ke Frankfurt a Jamus zuwa birnin Berlin.
A ranar Litinin ne Majalisar Ministoci ta tattauna kan ƙarancin dalar Amurka da ƙasar ke fama da ita da kuma matakan da za a bi wajen kauce mata.
A shekarar 2017 ne Najeriya ta rufe nata ofishin da ke birnin Colombo na Sri Lanka, matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai sake duba shi.

Asalin hoton, KSTG
Rahotani daga Jihar Kadunan Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe mutum 38 a Ƙaramar Hukumar Giwa.
Ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ce ta sanar da hakan inda ta ce jami'an tsaro sun ba ta rahoton cewa mutum 38 aka kashe a kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya da Idasu duk a Ƙaramar Hukumar Giwa.
An bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙona gidaje da manyan motocin ɗaukar kaya da ƙananan motoci da amfanin gona.
Tuni dai gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bayar da umarni ga hukumar ayyukan gaggawa ta jihar da ta binciki lamarin da kuma kai ɗauki ga waɗanda lamarin ya shafa.

Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu da ta kira gawurtattun masu garkuwa da mutane 11 a Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya tare da ƙwace makaamai da dama.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi ta ce mutanen suna da hannu a hare-hare da dama, ciki har da satar wani jami'in hukumar kwastam da wani ɗan uwan sarkin Jalingo da kuma ɗan sanda mai muƙamin saja duka a Jalingo, babban birnin jihar.
Kakakin 'yan sanda Frank Mba ya ce dakarunsu sun yi nasarar ƙwace bindiga tara jumilla, ciki har da AK-47 bakwai, da ɗumbin harsasai da ƙwayoyi da takunkumi yayin samamen da suka kai.
"Kamen waɗanda ake zargin ya biyo bayan tura rundunar gaggawa ta Intelligence Response Team zuwa Taraba domin taimaka wa 'yan sandan Taraba wajen kawo ƙarshen satar mutane cikin gaggawa," in ji Frank Mba.
Kazalika, sanarwar ta zargi biyu daga cikin mutanen da hannu wajen kashe wani ɗan sanda da kuma raunata wani yayin wani hari da suka kai, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Hong Kong sun fara jefa kuri'a a karon farko tun bayan da China ta yi sauye-sauye ga tsarin siyasar yankin.
Sai da duka 'yan takara suka samu amincewar wani kwamiti da ke goyon bayan China kafin tsayawa takara.
Sai dai 'yan adawa sun kaurace wa zaben kwatakwata.
Ana hasashen cewa ba za a fito jefa kuri'a sosai ba duk da shugabar gwamnatin Hong Kong din Carrie Lam ta ce ya yi wuri a yanke hukunci.
"Da ma gwamnati ba ta yi hasashen adadin masu fitowa wannan zabe ba da kuma wanda ya gabace shi saboda abubuwa da dama ka iya tasiri wajen fitowar jama'a ko akasin haka," in ji Carrie Lam.
A lokacin da ta jefa kuri'arta, shugabar ta bayyana sauye-sauyen da China ta kawo musu a matsayin ci gaba.

Asalin hoton, SHALI REDDY
"Sun yi ihu a kaina suna cewa kin kashe shi."
A lokacin da mahaifin Monica Paulus, ya yanke jiki ya fadi saboda bugun zuciya, dan uwanta ya zargeta da kashe shi ta hanyar maita.An yi ta yi mata barazanar za a kasheta.
Monica ta ce: "Abin ya ba ni tsoro, dukkan kawayena da 'yan uwana sun guje ni in da suka mai da ni mai muguwar manufa, a lokacin da aka zarge ni na ji matukar kunya ga kuma kyama".
An tursasa mata barin gidansu inda ta nemi mafaka a wata gunduma da ke Papua New Guinea, wata kasa da ke kudu maso yammacin facific.

Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaro a Khartoum babbar birnin Sudan sun toshe manyan hanyoyi sakamakon zanga-zangar da 'yan ƙasa ke shirin yi ta cika shekara uku da hamɓarar da tsohon Shugaban Ƙasa Omar Al-Bashir.
Tuni aka fara zaga-zangar a wasu biranen ƙasar.
Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a watan Oktoba, an yi ta samun kiraye-kirayen dawo da mulki hannun farar hula, yayin da 'yan ƙasar suka yi watsi da yarjejeniyar da shugaban riƙon ƙwarya Abdalla Hamdok ya yi da sojojin ta yin mulkin haɗin gwiwa.
Mutane da dama sun shirya maci a unguwanninsu, yayin da suke jiran ƙarasowar 19 ga watan Disamba da zimmar tunawa da abin da ya fara a matsayin ƙarami har ya zama babba - zanga-zangar da ta jawo hamɓarar da Omar Al-Bashir da ya shafe shekara kusan 30 a kan mulki.
Ɗaruruwan 'yan ƙasar ne ke tururuwa zuwa Khartoum duk da cewa sojoji sun rufe manyan hanyoyi a birnin, abin da ke nuni da cewa za a iya yin ƙazamar arangama a gobe Litinin.
Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi kan ko 'yan wasan ƙwallon ƙafa suna saka sabuwar riga a duk wasa, da kuma tambaya kan wani Bature tsohon ma'aikacin BBC Hausa
Latsa hoton ƙasa ku saurari Shirin Amsoshin Takardunku:
Shirin Zamantakewa da Halima Umar Saleh ke gabatarwa duk mako ya duba hanyoyin da iyaye za su bi wajen rage afkuwar bala'in satar yara da ke addabar wasu birane a arewacin Najeriya, musamman Kano.
Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon Shirin Zamantakewa:

Asalin hoton, FRSC
Hatsarin mota ya yi ajalin aƙalla mutum takwas a Jihar Bauchi ranar Asabar.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗura a Bauchi, Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da kamfanin labarai na NAN a yau Lahadi.
A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ƙauyen Goltukurwa da ke kan titin Das zuwa Bauchi, inda ya ritsa da ƙaramar mota ƙirar Opel Vectra da kuma tifa ƙirar Mercedes Benz.
Kwamandan ya alaƙanta lamarin da yin lodi fiye da kima, yana mai cewa jami'ansu sun isa wurin cikin minti bakwai da faruwarsa.
Mutum tara ne hatsarin ya ritsa da su; maza biyu, mata shida da kuma yaro ƙarami, a cewarsa.

Asalin hoton, Channels TV
Rundunar sojan Najeriya ta samu sabbin dakaru biyo bayan bikin yaye mutum 4,800 da aka gudanar a Jihar Kaduna ranar Asabar.
Ana sa ran sabbin hannun za su kama wa abokan aikinsu a ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a sassan Najeriya daban-daban, a cewar Babban Hafsan Sojan Ƙasa Laftanar Janar l Farouk Yahaya.
"Sun fara horonsu a watan Agusta kuma sun samu horon ƙwararru na soja bisa tsarinmu na aiki, musamman ma idan aka yi la'akari da halin da muke ciki yanzu," in ji shi.
"Muna fatan ba za su gaza ba yayin da muke shirin rarraba su wuraren aiki."
Ya ƙara da cewa har yanzu shafin ɗaukar aiki na rundunar a buɗe yake na waɗanda ake sa ran za su fara ɗaukar horo a watan Janairu mai zuwa.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 828 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Asabar.
Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa babu wanda cutar ta kashe a Asabar ɗin.
Ya zuwa yanzu, jumillar adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 223,483 amma an sallami 211,522 daga asibiti bayan sun warke.
Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar kuwa ya kai 2,984.
Jihohin da aka samu sabbin kamuwar:

Asalin hoton, Getty Images
Wata mahaukaciyar guguwa haɗe da ruwa ta halaka mutun 75 a Philippines.
Wadanda ta kashe ɗin da yawansu 'yan gundumar Bohol ne da ke tsakiyar ƙasar.
Wakilin BBC ya ce tuni Shugaba Rodrigo Duterte ya ziyarci wasu daga wuraren da guguwar ta afka wa, inda ya gane wa idonsa mummunar ɓarnar da ta yi.
Tun ranar Alhamis ne Typhoon Rai ta isa Philippines, kuma yanzu haka ta nufi Vietnam inda ake fargabar za ta yi wata mummunar barnar.
Maraba da shigowa shafin rahotanni kai-tsaye.
Za mu ci gaba da bayyana muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi.