Canada za ta ɗage haramcin hana ƴan Najeriya shiga ƙasarta

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Canada ta ce za ta ɗage haramcin shiga ƙasarta ga dukkanin ƙasashe 10 da ta hana a watan da ya gabata daga cikin matakan dakile bazuwar sabon nau’in korona na Omicron.
Ministan lafiyar ƙasar Jean-Yves Duclos wanda ya tabbatar da matakin a ranar Juma’a ya ce duk da haka duk wanda zai shiga ƙasa ƙasa da sa’a 72 sai ya gabatar da gwajin da ya nuna ba ya ɗauke da cutar.
Yawan masu kamuwa da korona na ci gaba da ƙaruwa a Canada kuma gwamnatin ƙasar ta nemi ƴan ƙasarta su gujewa yin tafiye tafiye ƙasashen waje.
Masu suka sun ce matakin haramta wa ƴan Afrika ta Kudu da Najeriya da Masar da wasu ƙasashe bakwai ba ya da wani amfani saboda yadda cutar ta riga ta bazu.
















