An tarar da gawarwakin yara takwas cikin mota a Legas

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. An tarar da gawarwakin yara takwas cikin mota a Legas

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An tarar da gawarwakin yara takwas a cikin wata babbar mota ƙirar Lexus a gaban gidan mai motar a Legas.

    Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar.

    Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Legas Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da faruwar lamarin.

    Ya shaida cewa yaran sun yi kuskuren kulle kansu ne a cikin motar a yayin da suke wasa.

    Ya kuma bayyana cewa tuni aka ɗauki gawarwakin yaran aka kai su wajen ajiye gawarwaki na babban asibitin Badagry da ke Legas domin gano musabbabin mutuwar yaran, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

  3. Rangnick ya fara jan ragamar Man United da kafar dama

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta yi nasarar doke Crystal Palace da ci 1-0 a wasan mako na 14 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

    Wasan farko da sabon koci Ralf Rangnick ya fara jan ragama a matakin rikon kwarya zuwa karshen kakar bana, bayan korar Ole Gunnar Solskjaer.

    Palace ta samu damar makin cin kwallo daga baya United ta zura kwallo a raga ta hannun Fred a minti na 77.

    Haka kuma bayan da Fred ya ci kwallo, Palace ta samu damar farkewa ta hannun Jordan Ayew, wanda ya buga kwallo ya yi fadi ya fita waje.

  4. Babbar motar soji ta afka wa masu zanga-zanga da buɗe musu wuta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojoji a Myanmar sun afka da wata ƙatuwar mota cikin masu zanga-zanga tare da buɗe musu wuta a birni mafi girma na ƙasar wato Yangon.

    Rahotanni na cewa an kashe mutane da dama da kuma raunata gwammai.

    Wani da ya shaida lamarin ya bayyana cewa motar ta zo ne da gudu kafin ta shige cike taron mutanen mintuna kaɗan bayan an soma zanga-zanga kan ƙwace mulkin da soji suka yi.

    Jami'an tsaro sun kama mutane da dama inda suka ɗora alhakin soma zanga-zangar kan matattun masu zanga-zangar da suka mutu.

    Ana kyautat zaton an kashe sama da fararen hula 1,300 tun bayan da aka soma zanga-zanga a ƙasar a watan Fabrairu bayan juyin mulkin da aka yi.

  5. An kashe sojan Najeriya bakwai a Jihar Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Bayanan hoto, Gawar Janar Dzarma Zurkushu da wasu bakwai da suka rasu a watan Nuwamba

    Sojojin Najeriya bakwai ne suka rasu ranar Juma'a lokacin da dakarun rundunar Operation Hadin Kai suka fafata da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno.

    Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan ranar Asabar, yana mai cewa lamarin ya faru ne a garin Kala Balge.

    Wasu soja uku sun ji raunuka, in ji shi.

    Sai dai Janar Nwachukwu ya bayyana cewa dakarunsu sun kashe gomman 'yan bindigar da suka far wa sansanin sojan a motoci masu manyan bindigogi da kuma babura.

    A cewarsa, 'yan bindigar sun kai wa dakarunsu harin ne a sansanin rundunar da ke Rann a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

  6. Dubban 'yan Austria na zanga-zangar adawa da dokokin kulle

    Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da dokokin kullen korona a Austria.

    Yan sanda sun ce mutun 40,000 ne ke bore a fadin Vienna, babban birnin na Austria.

    Wannan ne mako na uku a jere da ake boren amma cikin lumana.

    Sai dai daga baya an samu wasu tsiraru da suka dinga jifan jami'an tsaro, inda su kuma suka baɗe su da hayaƙi mai sa hawaye.

    Masu zanga-zangar sun kuma nuna adawa da shirin gwamnati na sharɗanta cewa ya zama dole kowa ya yi allurar rigakafin korona daga watan Fabrairu.

  7. Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

    Aliko Dangote

    Asalin hoton, STEPHANE DE SAKUTIN

    Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru matuƙa yayin da yake yunƙurin kammala shekarar 2021 da arzikin da bai taɓa samu ba cikin shekara bakwai sakamakon haɓakar ribarsa a ɓangaren siminti.

    Haɓakar kasuwar hannun jari a kamfaninsa na siminti da kuma tashin farashin man fetur da takin zamani sun taimaka wa Dangote inda dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 2.3 a 2021 zuwa biliyan 20.1 jumilla, kamar yadda mujallar Bloomberg ta ruwaito.

    Rabon da dukiyarsa ta kai yawan haka tun 2014, lokacin da ta kai dala biliyan 26.7 a watan Yunin shekarar, a cewar jaridar.

    Tashin farashin kayayyakin gini a Najeriya, wadda ke da mafi girman tattalin arziki a Afirka, sun haɓaka ƙarfin jarin kamfanin Dangote Cement plc.

    Nan gaba kaɗan ake sa ran Dangote zai kammala ginin matatar man fetur kan dala biliyan 19, wadda za ta dinga samar da fetur fiye da abin da kasuwar Najeriya ke buƙata.

    A wannan shekarar ce kuma Dangote ya fara fitar da takin zamani zuwa Amurka da Brazil bayan kammala ginin ma'aikatar taki da ke iya samar da taki tan miliyan uku duk shekara.

  8. Adama Barrow ya lashe Gundumar Wulli

    Ɗan takarar jam'iyya mai mulkin Gambia kuma shugaba mai-ci, Adama Barrow, ya lashe zaɓen Gundumar Wulli.

    Da ma dai shugaban ne kan gaba tun da aka fara sanar da sakamakon a safiyar Lahadi bayan kammala jefa ƙuri'a ranar Asabar.

    Gundumar Wulli:

    • Adama Barrow NPP 7,489
    • Ousainou Darboe UDP 995
    • Mama Kandeh GDC 871
    • Khalifa Sallah PDOIS 762
    • Abdoulie Jammeh NUP 182 Essa Faal Independent 126
  9. Jami'an tsaro sun kashe fararen hula 13 a Indiya

    Indiya

    Jami'an tsaro a Jihar Nagaland da ke arewa maso gabashin Indiya sun harbe aƙalla mutum 13 a wani kwanton-ɓauna da suka yi a kusa da iyakar ƙasar da Myanmar, a cewar hukumomi.

    Wata tawagar sintiri ce cikin kuskure ta buɗe wa wasu masu haƙar ma'adanai wuta yayin da suke komawa gida daga aiki, inda suka kashe shida.

    Wasu fararen hula bakwai da soja ɗaya sun mutu lokacin da mazauna yankin suka fusata kuma suka yi arangama da dakarun.

    Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah ya ce yana cikin "ƙunci" kuma ya sha alwashin ƙaddamar da bincike.

    Sojojin Indiya na yawan fafatawa da 'yan aware a yankin na Nagaland, amma an sha zargin su da kai wa fararen hula hari.

  10. Dalilin da ya sa jarirai ke barci kodayaushe

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa jarirai ke barci kodayaushe da kuma hikimar saka tallafin man fetur a Najeriya.

  11. Mutum 13 ne suka rasu sakamakon aman wutar dutse a Indonesia

    Indonesia

    Asalin hoton, Daffa Aminullah

    Ya zuwa yanzu mutum 13 ne suka rasu yayin da gommai suka ji raunuka sakamakon aman wutar dutse a Tsibirin Java na ƙasar Indonesia ranar Asabar.

    Wani bidiyo da aka ɗauka ya nuna yadda jama'a ke gudu daga wani hadarin hayaƙi a tsaunin Semeru.

    An yi gargaɗi ga jiragen sama kan yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya tsawon ƙafa 50,000.

    Aman wutar ya soma ne kusan ƙarfe 2:30 na dare agogon ƙasar.

    Haka kuma tuni jami'an ƙasar suka killace kilomita biyar daga inda lamarin ke faruwa.

  12. Shugaba Adama Barrow ne kan gaba a zaɓen Gambia

    Adama Barrow

    Asalin hoton, @BarrowPresident

    Shugaban Ƙasar Gambia Adama Barrow na jam'iyyar NPP ne ke kan gaba a sakamakon zaɓen ƙasar da aka gudanar ranar Asabar.

    Ya zuwa yanzu hukumar zabe mai zaman kanta IEC ta sanar da sakamakon gunduma 16 cikin 55.

    Ga sakamakon kamar haka:

    • Adama Barrow (NPP) 73,284
    • Ousainou Darboe UDP 43,252
    • Mama Kandeh GDC 10,259
    • Khalifa Sallah PDOIS 6,665
    • Abdoulie Jammeh NUP1,302
    • Essa Faal Independent2,295

    Sai dai akwai yiwuwar al’kaluman su sauya idan aka samu sakamakon manyan gundumomin Kombo ta Arewa da ta Yamma.

    Za a ci gaba da sanar da sakamakon da misalin karfe 11:00 agogon Gambia wato karfe 12:00 kenan agogon Najeriya da Nijar.

  13. Ko kafafen sada zumunta na rage wa mata matsananciyar damuwa?

    Bayanan sautiKu latsa hoton da ke sama don sauraron shirin Lafiya Zinariya

    Likitoci a fannin lafiyar kwakwalwa sun ce matsananciyar damuwa na janyo kisan kai da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin al'umma.

    Sai dai wasu mata masu dubban mabiya a shafin sada zumunta na da ra'ayin dandalin na kawo mafita ga matan da ke fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa.

    Masana a fannin kiwon lafiya sun ce mata sun fi maza fuskantar matsalar matsananciyar damuwa.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake nuna bukatar karin fadakarwa ga al'umma cewa, rashin lafiyar kwakwalwa matsalar kiwon lafiya ce da ke bukatar ganin likita.

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce rashin lafiyar da ke samun kwakwalwar bil'adama ta kasu kashi-kashi.

    Sai dai matsananciyar damuwa ita ce ke kan gaba a fadin duniya.

    Inda hukumar ta yi kiyasin cewa, mutane miliyan 264 na fama da matsananciyar damuwa a duniya.

  14. An sace yarinya 'yar shekara biyar a birnin Kano

    Hanifa Abubakar

    Asalin hoton, Family

    Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wata yarinya mai shekara biyar a birnin Kano ranar Asabar, a cewar rahoton jaridar Daily Nigerian.

    Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a unguwar Kawaji bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma Adaidaita-Sahu.

    Wani kawun Hanifa ya shaida wa jaridar cewa mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

    BBC Hausa ta yi yunƙurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Kano amma mai magana da yawunta ya ce yana cikin wata ganawa.

    "Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu," a cewar Suraj Zubair.

    "Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a Adaidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida. Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita."

    Birnin Kano ya sha fuskantar sace-sacen ƙananan yara a 'yan shekarun nan, abin da ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa kwamatin bincike domin ganowa da kuma bin haƙƙin yaran da ake sacewa.

    A Oktoban 2019, rundunar 'yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin sacewa da kuma safarar yara 'yan asalin jihar zuwa garin Onitsha na Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar, inda ake tilasta musu sauya addini da al'ada.

    Hanifa

    Asalin hoton, Family

  15. Tsohon Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Janar Wushishi ya rasu

    Janar Mohammed Inuwa Wushishi

    Asalin hoton, Mary Noel-Berje

    Tsohon Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, ya rasu.

    Marigayin ya rasu ne a birnin Landan, kamar yadda iyalansa suka shaida wa manema labarai.

    Janar Wushishi ya yi aiki ne da gwamnatin Shehu Shagari a shekarar 1981 zuwa 1983.

    An haife shi a Ƙaramar Hukumar Wushishi da ke Jihar Neja a arewacin Najeriya a shekarar 1940.

    Tsohon sojan ya riƙe muƙamai da dama a rundunar sojan Najeriya, inda har ya kai muƙamin laftanar janar.

  16. An fara sanar da sakamakon zaɓen shugaban Gambia

    Gambia

    Asalin hoton, Getty Images

    A Gambia, yayin da aka fara sanar da sakamakon zaɓen shugaban kasar da aka gudanar jiya Asabar, Shugaba Adama Barrow ne ke kan gaba a sakamakon gundumomin da aka bayyana zuwa yanzu.

    Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta IEC, Alhaji Alieu Momar Njai, ya ce Adama Barrow na NPP yana da kuria’a 14,599.

    Sai kuma madugun adawa Ousainou Darboe na UDP da ke bi masa da 6,188.

    Nan gaba kadan za a ci gaba da sanar da sakamakon.

  17. Ƙasashen duniya fiye da 20 na matsa wa Taliban kan kisan 'yan adawa

    Taliban

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da wasu kasashe sama da 20 sun yi kira ga Taliban da ta daina kashe dakarun tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ta shude.

    Cikin sanarwar haɗin gwuiwa da suka fitar, sun nuna damuwa kan rahotannin da ke fitowa daga Kabul cewa ana kashe 'yan adawa.

    Wakilin BBC ya ce Taliban ta shiga ƙarin matsin tattalin arziki tun bayan da kasashe da dama suka dakatar da tallafin da suke bai wa gwamnatin kasar, a kan haka ne kuma suka bayyana afuwa ga 'yan adawa.

  18. Ƙarin mutum 54 sun kamu da korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 54 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya ranar Asabar, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Sai dai annobar ba ta kashe ƙarin mutum ko ɗaya ba.

    Rahoton na NCDC ya ce an samu sabbin kamuwar ne daga jiha tara, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

    • Lagos-25
    • Oyo-11
    • Abuja-6
    • Kwara-3
    • Rivers-3
    • Bauchi-2
    • Delta-2
    • Kano-1
    • Ogun-1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 214,567 ne suka harbud a cutar a Najeriya, yayin da 2,980 suka rasu. Sai kuma 207,427 da suka warke.

  19. Assalamu Alaikum

    Maraba da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye tare da Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin sanin yadda duniya ke ciki a wannan rana ta Lahadi.

    Muna fatan hutun ƙarshen makonku yana tafiya yadda ya kamata.