Twitter ya nemi sasanci da gwamnatin Najeriya – Lai Mohammed

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Tukur and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. Morocco ta halatta noman wiwi a ƙasar

    Morocco

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Morocco ta amince da dokar da ta halatta samar da tabar wiwi a ƙasar don magani da kuma amfanin masana'antu.

    Manufar matakin ita ce shiga kasuwar duniya da bunƙasa noma da samar da ayyukan yi a yankunan karkara.

    Morocco tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu samar da tabar wiwi don haramtacciyar hanya, da kuma domin shakatawa. Wannan zai kasance ba bisa doka ba a ƙarƙashin sabuwar dokar.

  3. Ana karɓar jinin ƴan Iraƙi don gano dangin fursunonin da IS ta yi wa kisan gilla

    Ƴan Iraƙi da dama a Bagadaza suna ta bayarda jini a wani mataki na ƙoƙarin tantance danginsu daga cikin waɗanda kungiyar IS ta yi wa kisan kiyashi.

    A shekarar 2014, IS ta kai hari a wani gidan yari da ke arewa maso yammacin Iraƙi.

    Sun saki 'yan uwansu mabiya Sunni daga cikin fursunonin, amma sun kashe wasu mutum 600 yawancinsu mabiya Shi'a.

    An binne su a cikin babban ƙabari. Kisan shi ne mafi muni da IS ta aikata a Iraƙi.

    Ana karɓar samfurin jini na mutanen ƙasar domin kwatantawa da waɗanda aka kashe domin gano danginsu.

  4. Twitter ya nemi sasanci da gwamnatin Najeriya – Lai Mohammed

    Alhaji Lai Mohammed

    Asalin hoton, @FMICNIGERIA

    Ministan ƴada labaran Najeriya da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce hukumomin kamfanin Twitter sun tuntuɓi gwamnatin Najeriya domin tattaunawa kan matakin dakatar da amfani da shafin da gwamnatin Najeriya ta yi.

    Ministan ya shaida wa manema labaraibayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba cewa kamfanin Twitter na neman “tattaunawa mai ƙarfi” don warware matsalar da ta kai ga dakatar da ayyukansa a Najeriya.

    “Shugabannin gudanarwar Twitter sun tuntuɓi gwamnati a ranar Laraba,” in ji Lai Mohammed.

    A ranar juma’a gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter kan zarginsa da bayar da dama ga waɗanda ke barazana ga ɗorewar Najeriya.

    Dakatarwar na zuwa bayan kamfanin ya goge ɗaya daga cikin sakwannin shugaban Najeriya inda ya ke barazanar ɗaukar mataki kan masu da’awar ɓallewa daga Najeriya.

    An kuma ambato Lai Mohammed na cewa, dgaa yanzu duk wani kamfanin kafar sadarwa sai yi rijista tare da ba shi lasisi kafin ya fara ayyukansa a Najeriya.

  5. Amurka ta zargi Rasha China kan rigakafin korona

    Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaron kasa a Amurka, Jake Sullivan ya zargi Rasha da China da tursasawa kasashe karbar alluran rigakafinsu kan cutar korona.

    Ya shaida wa BBC cewa kasashen biyu sun yi alkawarin da ba za su iya cikawa ba game da allurar rigakafin.

    Ya ce "A karshen watan da mu ke ciki Amurka za ta raba allurar rigakafi fiye da na Rasha ko China wanda shi ne abin da ya da ce a yi."

    Ya kuma ce duk lokacin da aka kamalla komai za a ce Amurka da kasashen Yamma masu mulkin dimokradiyya ne suka fi taimakawa wajan kawo karshen annobar korona.

    Sai dai an rika sukar Amurka saboda ta boye allurar rigakafinta.

  6. Labarai da dumi-dumi, Ƙungiyar ma’aikatan shari’a a Najeriya ta janye yajin aiki

    Ƙungiyar ma’aikatan shari’a a Najeriya ta janye aikin aikin gama-gari da ta tsunduma.

    A cewar Jaridar Daily Trust, Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da shugabannin ƙungiyar da kuma Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a Najeriya NJC ƙarƙashin jagorancin Alƙalin alƙalai Mai shari’a Ibrahim Muhammad.

    Tun a farkon watan Afrilu ƙungiyar ta shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da wasu buƙatunta da suka shafi cin gashin kai a jihohi.

    Hakan na nufin za a buɗe kotuna a Najeriya bayan shafe tsawon biyu a rufe bayan janye yajin aikin.

  7. An tuɓe shugaban limaman Masallacin Annabi saboda jinkirin tayar da Sallar Asuba

    Shugaban Masallatai biyu mafi daraja a Saudiyya Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya tuɓe Daraktan da ke kula da limamai da ladanai a masallacin Manzon Allah a Madina.

    An tuɓe shi ne saboda samun jinkirin tayar da sallar Asuba bayan an kira Sallah na tsawon minti 45, kamar yadda Hukumomin da ke kula da Masallatan Makkah da Madina a Saudiyya, Haramain Sharifain suka sanar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ce shugaban Masallatan Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya buƙaci a samar da liman biyu a ko wace Sallar farilla.

    “Liman na biyu zai kasance ne idan na farko ya makara,” in ji sanarwar.

    Sabon matakin kuma ya shafi har da ladanai, inda sanarwar ta ce yanzu ladanai uku za a naɗa a ko wace Sallar Farilla. Ɗaya zai kira Sallah, ɗaya kuma ya tayar da Iƙama, ɗayan kuma zai kasance idan an samu jinkirin fitowar ladanan.

  8. Tsugune ba ta ƙare ba kan rikicin Yarbawa da Makiyaya a jihar Oyon Najeriya

    Ga dukkan alamu duk da matakan tsaro da jami'an gwamnati suke samarwa a garin Iganga cikin jiar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya, da alama zaman lafiya bai kammala dawo a yankunan ba.

    Rahotanni sun nuna wasu da ake zargin mambobin kungiyar Oodua Peoples Congress ne wato (OPC), sun kai hari tare da kashe Fulani Makiyaya hudu da ke kusa da garin Igangan.

    Ana dai zargin cewa harin na baya-bayan a matsayin daukar fansa, bayan wasu mutane dauke da bindiga suka shiga garin Igangan wanda ya zo da hallaka kabilar Yarbawa 11.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko mana da wannan rahoto:

    Bayanan sautiRahoton Umar Eleman kan rikicin Igangan
  9. Kafofin watsa labarai a Najeriya na ci gaba da saɓa dokar gwamnati kan Twitter

    Twitter

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin watsa labarai masu zaman kansu da dama a Najeriya sun bijirewa umarnin gomnati na rufe shafukansu na tuwita kuma sun cigaba da tura sakoni .

    BBC ta ce wasu daga cikin shahararun kafofin watsa labarai na kasar ciki har da jaridar Punch da ke da magoya baya miliyan hudu a shafin na twitter sun ci gaba da amfani da shafin .

    Gwamnatin Najeriya ta Dakar da shafin ne kwanaki biyar da suka gabata bayan ya cire sakon da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa saboda ya sabawa kaidojin sa.

    Sai dai fadar shugaban kasa ta musanta cewa ta dauki wannan mataki ne domin ta maida martani Kasashe da dama sun nuna rashin jin dadinsu a kan mataki amma tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yaba da matakin

  10. Iraƙi ta saki kwamandan masu ta da ƙayar baya Qasim Muslih

    Mahukunta a Iraki sun saki wani fittacen kwamandan mayaka, Qasim Muslih, wanda aka kama a watan da ya gabata a kan zargin ta'addanci.

    Wasu majiyoyin gwamnati sun ce babu isassun shaidu da za su basu damar ci gaba da binciken da suke yi a kansa.

    An tsare Qasim Muslih ne a kan abinda rahotanni suka ce na da nasaba da hare-haren makamai masu linzami da aka kai wa sansanonin sojin Amurka.

    Shi ne kwamandan wata kungiyar mayakan yan shi'a da ke goyon bayan Iran.

  11. Mutum 24 sun mutu a haɗarin mota a jigawa

    A Najeriya hukumar kashe gobara ta jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum ashirin da huɗu sakamakon wani mummunan haɗarin mota.

    Haɗarin ya auku ne da safiyar Laraba a karamar hukumar Birnin Kudu bayan da wasu motoci biyu toyota kirar hummer su ka yi taho-mu-gama a dai-dai wata kwana inda kuma nan take suka kama da wuta.

    Saurari rahoton Zahraddeen Lawal don samun ƙarin bayani:

    Gargaɗi: Wasu bayanan da ke cikin wannan rahoton na iya tayar da hankalin mai saurare.

    Bayanan sautiMummunan Hatsarin mota a Jigawa
  12. Minti Ɗaya Da BBC na Rana 09-06-2021

    Bayanan sautiMinti Ɗaya Da BBC Na Rana 09/06/2021
  13. El Salvador ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta mayar da Bitcoin kuɗinta

    El Salvadore

    Asalin hoton, Reuters

    El Salvador ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta mayar da Bitcoin kuɗinta.

    Majalisar dokokin ƙasar ta amince da buƙatar Shugaba Nayib Bukele na mayar da kuɗin kirifto kuɗin ƙasar.

    Shugaban ya ce gwamnatinsa ta kafa tarihi kuma matakin zai sauƙaƙa wa ƴan El Salvadore da ke zama a ƙasashen waje wurin aiko kuɗi gida.

    Bitcoin zai zama kuɗin ƙasar tare da dalar Amurka nan da kwanaki 90.

    Wannan sabuwar dokar na nufin dole ne duk wata sana'a ta amshi Bitcoin a matsayin kuɗi, sai dai idan ba ta da fasahar da ake buƙata a aika mata kuɗin na intanet.

    Haka kuma ya ce matakin zai buɗawa kashi 70 cikin ɗari na ƴan ƙasar damar hada-hadar kasuwanci ko da ba su da asusun banki.

    Tattalin arziƙin El Salvadore ya dogara ne kan yawan aika kuɗi da ake yi daga ƙasashen waje, wanda ya ƙunshi kusan kashi 20 cikin ɗari na gaba ɗaya kuɗin da ke shiga ƙasar.

  14. Wata ɗaliba ta rasu a ɗakin kwanan ɗalibai a Jami'ar Bayero ta Kano

    Jami'ar Bayero

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ɗaliba da ke ajin ƙarshe a ɓangaren Kimiyyar Siyasa, a jami'ar Bayero ta Kano ta rasu ranar Talata a ɗakin kwanan ɗalibai na Ramat Hall.

    Ɗalibar mai suna Mercy Sunday ta rasu ne bayan yin zazzaɓi da haraswa.

    Wata ƙawar marigayiyar ta ce Mercy ta rasu ne da safiyar Talata bayan da dafara ta fara fita daga bakinta.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Jami'i mai kula da harkokin ɗalibai, Dokta Shamsuddeen Umar ya tabbatar mata da lamarin kuma ya ce ɗalibar ta samu kulawa a asibitin cikin makaranta kwanaki biyu kafin rasuwarta.

    Kuma ta samu sauƙi kafin cutar ta dawo ranar Litinin, ranar Talata kuma rai ya yi halinsa.

  15. Gwamnan Bauchi ya sauke kwamishinoninsa da masu ba shi shawara

    GOV BALA

    Asalin hoton, GOV BALA

    Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya amince da rusa majalisar zartarwar jihar.

    A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mukhtar Gidado, Mai bai wa shugaban shawara na musamman kan kafofin yaɗa labarai, korar ta shafi Sakataren Gwamnati da Shugaban Ma'aikata da Masu ba da shawara.

    Sai dai sanarwar ta ce korar ba ta shafi Masu ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro da zuba jari da kafofin yaɗa labarai.

    Gwamnan ya ba bayar da umarnin cewa duka kwamishinoni su muƙa ragamar ma'aikatansu ga Manyan Sakatarori yayin da Babban Sakataren Gwamnatin da Shugaban Ma'aikata na gidan gwamnati da sauran Masu Ba da shawarwari na musamman su miƙa ayyukansu ga Manyan Sakatarorin gwamnati a gidan gwamnati.

    Gwamna Bala ya miƙa godiyarsa ga jami'an da lamarin ya shafa tare da yi masu fatan alkhairi.

  16. SERAP ta kai Buhari kotun Ecowas kan dakatar da Twitter

    SERAP

    Asalin hoton, SERAP

    Ƙungiyar SERAP mai sa fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya da wasu ƴan Najeriya 176 sun shigar da ƙara kan Shugaba Muhammadu Buhari bisa dakatar da amfani da Twitter a Najeriya da kuma ƙoƙarin hukunta ƴan Najeriya masu amfani da shafin.

    A ƙarar da aka shigar kotun ta ECOWAS, SERAP da sauran mutanen na neman a hana gwamnatin Najeriya dakatar da shafin na Twitter a ƙasar da kuma hana kowa ciki har da kafofin yaɗa labarai amfani da shafin.

    Ƙarar ta ce wannan cin mutunci ne da barazana ga ƴan ƙasar.

    A ƙarar da Mista Femi Falana ya shigar a madadin SERAP, masu ƙarar sun ce dakatarwar na yin zagon ƙasa ga ƴancin tofa albarkacin baki na ƴan Najeriya da kafofin yaɗa labarai da demokuraɗiyya.

    Haka kuma, za ta hana ƴan jarida damar gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

  17. Isra'ila ta kai harin makami mai linzami a Syria

    Kafofin yaɗa labarai a Syria sun ce an daƙile wani harin makami mai linzami na Isra'ila a yankin tsakiya da yankin kudancin Syria, inda ake tunanin an yi ƙoƙarin kai harin ne kan sansanonin soji a Damascus babban birnin ƙasar.

    Kamfanin dillanci na Sana ya ce akwai wasu makaman Isra'ila da ke zuwa daga sararin samaniyar Lebanon da aka daƙile bayan ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare.

    Hukumar da ke sa ido kan kare haƙƙin Ɗan Adam a Syria ta ce An ji "munanan fashewa" a Damascus da kusa da birnin bayan hare-haren Isra'ila kan sansanonin sojoji.

    Lamarin na zuwa ne kusan wata guda bayan da kafar yaɗa labaran Syria ta ruwaito wani harin jirgi mai saukar ungulu na Isra'ila a Quneitra a yankin Golan Heights na Syria.

  18. Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kashe 'Kiristoci' da 'ƴan leƙen asiri' a Mali da Nijar

    ISWAP

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar IS ta fitar da wasu hotuna shidda da ta ce suna nuna kisan wasu Kiristoci biyar da wasu maza da ta ce ƴan leƙen asiri ne a Mali da Nijar.

    IS ta fitar da hotunan ne ranar 8 ga watan Yuni a shafinta na manhajar Telegram.

    A jikin hotunan an rubuta sunan ƙungiyar IS a Afrika ta Yamma wato ISWAP.

    Kiristocin guda biyar da aka kashe ana zargin an kama su ne a wani titi da ke haɗa birnin Gao a Mali da Niamey babban birnin Nijar ran 1 ga wata Yuni- zargin da IS ta amince da shi ran 5 ga Yuni.

    IS ba ta fayyace idan a Mali ko a Nijar ta kama kuma ta kashe mutanen ba.

    Wani hoton ya nuna kisan wasu "ƴan leƙen asiri" a Tongo Tongo, wani ƙauye a yankin Tillabery na Nijar da ke da iyaka da Mali.

    Hoto na uku ya nuna kisan wani "ɗan leƙen asiri" a "garin Menaka", babban birnin yankin Menaka a gabashin Mali, ba tare da bayyana yaushe ne ba.

  19. Shugaban Uganda ya ƙaddamar majalisar zartarwarsa mai mutum 81

    Yoweri Museveni

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya naɗa sabbin ministoci 31 da masu taiamkawa 50.

    Cikin majalisar zartarwar har da mata sama da 10.

    Jessica Alupo, wata tsohuwar soja da ta yi ritaya ita ce sabuwar mataimakiyar shugaban ƙasar, mace ta biyu a kasar da ta riƙe wannna muƙamin.

    Ta taɓa yin ministan ilimi.

    Majalisar Mista Museveni na da tsoffin soja da dama.

    Shuagban ya ƙara mutanen da ba a sani ba a majalisar tasa, bayan sama da ministoci 20 na wancan wa'adin nasa, ciki har da mataimakin shugaban ƙasar suka rasa kujerunsu a zaɓen da aka gudanar a watan Janairu.

  20. Makarantu 62,000 ne a Najeriya ke cikin hatsarin harin ƴan bindiga- NSCDC

    Hare-haren makarantu

    Shugaban runudunar NSCDC a Najeriya, Ahmed Audi, ya bayyana damuwarsa inda ya ce makarantu 62,000 ne a ƙasar ke cikin hadarin hare-haren ƴan bindiga.

    Ya ce a Najeriya akwai makarantu 81,000 a ƙasar kuma mafi yawansu na gwamnati ne.

    Audi ya kuma bayyana cewa hukumarsa ta kammala bincike kan makarantun da ke cikin wannan haɗari a faɗin ƙasar.

    Ya ce binciken zai taimaka wajen samar da hanyoyin tsare makarantu a faɗin Najeriya.

    A farkon wannan makon ne dama aka ƙaddamar da wata runduna ta mata zalla a hukumar don tsare makarantu da kare yara da ɓarayin daji da masu garkuwa da mutane suka taso a gaba.