PDP ta ce ba ta dakatar da Kwankwaso ba

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Buhari Muhammad Fagge

  1. Bankwana

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafi.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan an sha ruwa lafiya.

  2. PDP ta ce ba ta dakatar da Kwankwaso ba

    @Twitter/Kwankwaso

    Asalin hoton, @Twitter/Kwankwaso

    Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta musanta wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke cewa jam'iyyar ta dakatar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da takwaransa Babangida Aliyu na jihar Neja.

    Cikin wata sanarwa da PDP ta fitar a shafinta na Twitter ta ce, akwai wasu ka'idoji da kundin tsarin jam'iyyar ya tanada gabanin dakatar da duk wani mamba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    PDP ta ce ba za ta amince da irin wadannan karyace-karyacen ba, wadanda za su iya kawo hargitsi cikin jam'iyyar ko kuma su haifar da rikici tsakanin mambobinta.

    Haka kuma ta musanta dakatar da tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu tana cewa duka bayanan da aka fitar na dakatar da shi basu da tyshe bare makama.

    Others

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, PDP ta ce ta ba san daga ina wannan takaradr ta samo asali ba

    Jam'iyyar ta shawarci shugabanninta a jihohin Kano da Neja da su hada kai wuri guda su kuma yaki irin wadannan bayanan da za su iya kawo rabuwar kai, a lokacin da 'yan Najeriya ke bukatar jam'iyyar.

  3. Idan ka gina mace tamkar ka gina al'umma ne - Gwamna Bagudu

    Yusuf Sarki

    Asalin hoton, Yusuf Sarki

    Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa mata domin idan ka gina mata tamkar ka gina al'umma ne maki daya.

    Bagudu ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya fitar, yana ruwaito cewa Bagudu ya ce "Yawan taimakon da za mu iya bai wa mata yanayin yadda al'umarmu za ta habaka".

    Bagudu ya bayyana mata a matsayin wadanda duk wahalar da aka sha ta annobar korona ta matsin tattalin arziki ta kare a kansu.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wata makala da jihar ta shirya wa mata domin zuwan watan Ramadana, wadda aka yi wa taken "Muhimmiyar rawar da mata za su iya taka wa a Musulunci."

    Makalar da aka yi ta mayar da hankali ne kan yadda mata za su tafiyar da gida a lokacin annobar korona, wajibin da ke kan mata na kula da iyali a yayin matsin tattalin arziki da kuma yadda za a kawo karshen cin zarafin mata.

    Yusuf Sarki

    Asalin hoton, Yusuf Sarki

  4. Wani hadarin jirgin kasa a Masar ya jikkata mutane da dama

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Gwamman fasinjoji ne suka jikkata a wani hadarin jirgin kasa da ya rutsa da su a birnin Al-Kahira na Masar.

    Hadarin ya faru ne a lardin Qalyubia da ke arewacin Al-Kahira babban birnin kasar.

    Motocin asibiti da dama ne suka isa wurin da abin ya faru cikin gaggawa, suna kwashe wadanda suka raunata zuwa asibitoci uku da ke yankin domin yi musu magani.

    Ana yawan samun hadarin jirgin kasa a Masar saboda rashin kyawun layin dogon.

    Ko a watan jiya sai da akalla mutum 20 suka mutu a wani taho mu gama da aka yi tsakanin jiragen kasa biyu.

  5. Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukanta a Damasak da Dikwa

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya ce hare-haren masu ikirarin jihadi sun tilasta masa dakatar da ayyukansa na jinkai a garuruwan Damasak da Dikwa a yankin arewa maso gabashin kasar.

    Shugaban Ofishin Edward Kallon ya ce za a kwashe ma'aikatan ofishin a sauya musu wuri, amma za a ci gaba da aikin anan kusa.

    Sama da mutane 60,000 ne suka tsere daga Damasak a baya-bayan nan, kimanin kashi takwan na mazauna garin kenan. Sau uku ana kai hari garin cikin mako guda.

    MDD ta ce maharan na kai hari ne kan ma'aikatanta inda suke bincike gida-guda domin neman masu aikin bayar da agaji.

  6. Buhari ya yi hakuri da mutane da yawa - Masari

    @GOVERNORMASARI

    Asalin hoton, @GOVERNORMASARI

    Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya Aminu Bello Masari ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi hakuri da mutane da dama a kasar.

    Cikin wata hira da gidan talabijin na TVC Masari ya ce ya yin da wasu shugabanni suka gaza jurewa sukar da ake musu, Buhari ya jima yana hakan.

    Masari ya kara da cewa Buhari bai gaza ba wajen cika duka alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabe, yana kuma bayyana jam'iyyar APC a matsayin abar dogaro ga 'yan Najeriya.

    "Duk wanda yake cewa farin jinin jam'iyyar ya ragu to ya bari a zo lokacin zabe. Kuma yadda APC ke kara amsar mutane ya nuna wannan zargin ba daidai ba ne.

    "Ina ganin har yanzu APC ce jam'iyyar da ta fi ko wacce karfi,kuma wadda za a iya dogara da ita a Najeriya a yau." in ji Masari

  7. An sauya wa Fir'auna da sauran sarakunan masar ƙabari

    Gawar Fir'auna na cikin waɗanda aka sauya wa wuri

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Gawar Fir'auna na cikin waɗanda aka sauya wa wuri

    An sauya wa gawwakin tsoffin sarakunan Masar wurin kwanciya zuwa kudancin birnin al Ƙahira babban birnin kasar.

    Kwararru da ke gidan tarihin kasar sun ce ya dauke su mako biyu domin nazari da kuma sauyawa sarakunan wuri, bayan kwashe su da aka yi a wani gagarumin biki.

    A karon farko, An nuna hotunan sarakunan a kusa da akwatin gawar da suke ciki, an kuma nuna ne domin taimakawa wajen fahimtar labarinsu kafin mutuwarsu sama da shekara 3,000 baya.

    Ko wane akwatin an sassakata ta yadda ta yi kama da na cikinta.

    Hukumomin kasar na fatan wannan bajakolin da aka yi na nuna su zai taimaka wajen farfado da harkokin yawon bude idon kasar ta Masar.

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

  8. Ƴan bindiga sun buɗe wa masu jana’iza wuta a Nijar

    Rahotanni daga Nijar sun ce fararen hula 19 aka kashe a wani hari da aka kai a yammacin kasar, kusa da kan iyaka da Mali.

    Jami'ai sun ce ƴan bindiga ɗauke da makamai a kan babura ne suka afkawa kauyen Gaigorou suka buɗe wa mutane wuta da ke wurin jana’iza sannan suka shiga cikin garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

    Hare-haren ƴan bindiga sun zama ruwan dare a yankin da ya haɗa kan iyakokin Mali da Nijar da Burkina Faso.

    Mayaƙan sun kuma sace dabbobi tare da tilasta wa mutane biyan haraji.

  9. Majalisa ta tsayar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Syria

    Majalisar dokoki a Syria ta tsayar da ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wanda da alama Shugaba Bashar al-Assad zai ci gaba da mulki a ƙasar mai fama da yaƙi.

    'Yan Syria za su je rumfunan zabe a ranar 26 ga Mayu domin zaɓen shugaban ƙasa karo na biyu da za a yi cikin yaƙin basasa.

    Duk da ƙaruwar matsalar tattalin arziki a kasar, ba a tunanin Mr Assad zai fuskanci wani babban ƙalubale

    Tun shekarar 2000 Bashar al-Assad ke mulki a Syria

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Tun shekarar 2000 Bashar al-Assad ke mulki a Syria
  10. Yaya helikwaftan da aka aika duniyar Mars ke aiki?

    A filinmu na Amsoshin Takardunku na wannan mako, mun amsa tambayoyi kan yadda helikwaftan da aka aika duniyar Mars ke aiki, da kuma ko ƴan Najeriya suna da ikon sa a raba ƙasar.

    Bayanan sautiAmsoshin Takardunku 16/04/2021:
  11. Amurka ta umarci ƴan ƙasarta su fice Chadi

    Amurka ta umarci ƴan ƙasarta su fice daga Chadi yayin da ƴan tawayen ƙasar suka doshi babban birnin kasar, Ndjamena daga ɓangarori biyu.

    Birtaniya ma ta buƙaci ƴan kasartasu fice Chadi.

    Dosowar ƴan tawayen na zuwa ne yayin da sakamakon zaɓen Chadi ya nuna Shugaba Idriss Deby na kan hanyarsa ta lashe zaɓe a wa’adin mulkinsa na shida.

    An girke jami’an tsaro ɗauke da muggan makamai suna sintiri a babban birnin kasar.

    Kungiyar ƴan tawayen Front for Change and Concord a Chadi, wacce ke kudancin Libya, ta ce ta kame sansanin soji a ranar Juma'a.

    Sojojin Chadi sun ce sun tarwatsa wani ayarin motocin ƴan tawaye a ranar Asabar.

    Idriss Deby na kan hanyar lashe zaɓe domin yin wa'adi na shida a Chadi

    Asalin hoton, Getty Images

  12. 'Za a yi fama da yunwa saboda tsadar abinci a yammacin Afrika'

    Hukumar samar da abinci ta duniya, WFP ta ce fiye da mutum miliyan 31 a yankin yammacin Afirka za su fuskanci barazanar ƙarancin abinci.

    Rahoton hukumar WFP ya ce farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi ga kuma rikici da ke haifar da yunwa a sassan yammacin Afirka.

    "Yunwa za ta yi ƙamari a lokacin bazara na watan Yuni zuwa Agusta mai zuwa" a cewar rahoton.

    Rahoton ya ce an samu ƙarin kashi 30 na ƙarancin abinci fiye da bara.

    Hukumar WFP ta yi kiran ɗaukar matakan gaggawa don hana aukuwar abin da ta kira bala'i.

    Rahoton ya ce faɗuwar darajar kuɗin Saliyo shi ya haifar tsadar kayayyakin abinci inda aka samu ƙarin farashin shinkafa zuwa kashi 70, adadin da ba a taɓa gani ba tsawon shekaru biyar.

    Rikici kuma da ake fuskanta a wasu ƙasashen yammacin Afirka wanda ya tilastawa mutane ƙauracewa gidajensu da gonaki ya ƙara jefa ƙasashen cikin barzanar fuskantar ƙarancin abinci.

    Matsalar ta fi shafar ƙasashe kamar arewacin Najeriya da Burkina Faso da Mali da Nijar da Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da kuma ƙasar Kamaru, a cewar rahoton.

    Rahoton ya ce farashin abinci ya lunlunka a ƙasashen, wanda ke jefa masu ƙaramin ƙarfi cikin mawuyacin hali na samun abin da za su kai baka.

  13. Saudiyya da Iran sun ‘tattauna yadda za su sasanta’

    Yariman Saudiyya da Shugaban Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Jaridar Birtaniya ta ruwaito cewa jami'an Iran da na Saudiyya sun tattauna a wannan watan a wani yunƙuri na sasantawa tsakaninsu.

    Jaridar Financial Times ta ce an fara tattaunawar farko tsakanin ɓangarorin biyu da ke gaba da juna a Bagadaza a ranar 9 ga Afrilu.

    Tattaunawar kamar yadda aka ruwaito ta shafi batutuwa da dama, ciki har da hare-haren da ƴan tawayen Houthi a Yemen ke kai wa Saudiyya.

    Jaridar ta ce wani jami'in Saudiyya ya musanta cewa ba a yi wata tattaunawa ba.

    Iran ba ta ce komai ba kawo yanzu.

    Ƙasashen biyu sun katse huldar jakadanci tsakaninsu shekaru huɗu da suka gabata.

  14. Likitoci sun ce Navalny zai iya mutuwa

    Alexei Navalny

    Likitocin Alexei Navalny, mai fafutika da aka ɗaure a gidan yari a Rasha, sun ce "zai iya mutuwa nan da ƴan kwanaki" idan har bai samu kulawar da ta kamata ba.

    Mista Navalny ya shiga yajin cin abinci kusan mako uku yanzu - kuma likitocinsa sun ce gwajin da aka yi masa ya tabbatar yana cikin barazana saboda kodarsa da zuciya na iya daina aiki.

    Navalny ya shiga yajin cin abinci domin adawa da ƙin amincewa da buƙatarsa ta neman magani kan ciwon kafa da baya da yake fama da shi.

    Mahukunta gidan yarin Rasha sun ce ya ƙi aminta likitocinsu su duba shi.

    A shekarar da ta gabata Mr Navalny ya tsira daga harin gubar da aka kai masa a Siberia.

  15. An kashe Masallata a Afghanistan

    An kashe masu ibadah 8 a wani hari da aka kai a wani masallaci a Jalalabad da ke gabashin Afghanistan.

    Gwamnan lardin Nangarhar, wanda Jalalabad shi ne babban birnin kasar, ya ce cikin waɗanda suka mutu har da ƴanuwa biyar da ke Sallah a Masallacin.

    Ya ce ana gudanar da bincike kan harin, amma binciken farko ya nuna cewa an kai harin ne sakamakon rikicin fili.

  16. Tsawon mako ɗaya korona ba ta yi kisa ba a Najeriya

    Alƙalumman da hukumar ɗakile cutaka a Najeriya ta fitar sun nuna cewa kwana bakwai a jere cutar korona ba ta yi kisa ba a ƙasar.

    Jimillar mutum 2,061 cutar ta kashe a Najeriya. Kuma tun ranar Lahadin makon da ya gabata zuwa Asabar cutar ba a samu wanda ya mutu ba sakamakon cutar.

    Sabbin alƙalumman sun nuna cewa mutum 60 suka kamu da korona a ranar Asabar, kuma jihar Legas inda cutar ta fi yin ƙamari ne adadin suka fi yawa inda ta kama mutum 22.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Maraba

    Muna maku maraba da kasance da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye da ke faruwa a wannan rana ta Lahadi a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu