Rufewa
Nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kai-tsaye. Ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.
Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau
Nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kai-tsaye. Ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Hukumar da ke kula da makamashin Nukiliya a Iran ta tabbatar da cewa an harba wani makami a tasharta da ke Natanz.
Gwamnatin Tehran ta ce babu tantama harin ta'addanci ne aka kai mata.
Harin na zuwa ne kwana daya bayan da shugaba Rouhani ya kaddamar da sabon shirin Iran na ci gaba da tara sinadarin Uranium wanda aka nuna kai tsaye ta gidajen talabijin.
Rahotanni sun ce babu wanda harin ya jikkata, kuma tuni hukumomi a Iran din suka zargi Israila da kai shi.

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga da ake tunanin ƴan Boko Haram ne sun kashe sojojin Najeriya biyu a jihar Borno yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Bayanai sun ce an kashe sojojin ne a wani kwantan ɓauna da aka yi masu yayin da suke farautar mai taimakawa Boko Haram da bayanai.
Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da jami’an tsaron Najeriya ta ce ƴan bindigar sun kai harin ne a garin Damasak a ranar Asabar.
Sun kuma kwashi kayayyakin jin ƙai tare da kashe wasu mutane biyu. Sun kuma cinna wuta a gidan babban jami’in ƴan sanda na yankin wuta da kuma gidan basarake.
Kafar ta ce an kashe ƴan Boko Haram da ISWAP da dama a harin sama da aka kai masu
Hukumomin Saudiyya sun ce ba a ga watan Ramadan ba a ranar Lahadi 29 ga watan Sha'aban kiɗayar Umm Al Qurra kuma 29 ga watan Sha'aban ƙidayar bayan Hijra wanda ya yi daidai da 11 ga watan Afirlu a kalandar nasara.
Shafin Haramain Sharifain na intanet wato hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya ya ce Kotun Ƙoli ta bayar da umurnin ci gaba da duban watan a gobe Litinin.
Hukumomin sun ce dalilin rashin ganin watan ya shafi yanayin da aka fuskanta na ƙura da hazo.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Chadi Idriss ya yi watsi da zargin danne ƴan dawa da kuma kiran ƙauracewa zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a yau Lahadi.
Shugaba Deby bayan kaɗa ƙuri’arsa tare da matarsa Hinda Deby ya zanta da manema labarai inda ya ce “ina jiran sakamakon hukuncin da masu zaɓe suka yanke.”
Ana na sa ran Idriss Deby zai lashe zaɓen a wa’adi na shida.
An zargi Shugaba Deby wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki da aka yi a 1990 da muzgunawa yan adawa gabanin zaben.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch na cikin ƙungiyoyin da suka zargi shugaban ƙuntatawa yan hamayya da masu zanga-zanga.
Kungiyar ta ce an yi amfani da karfi a zanga-zangar kin jinin gwamnatin da aka yi a kwanakin baya.
Daga cikin ƴan takarar da ke fafatawa da Deby sun haɗa da tsohon Firaminista Albert Pahimi Padacke, yayin da sauran ƴan adawa suka ƙauracewa zaɓen ciki har da babban mai hamayya da shi a zaɓen 2016 Saleh Kebzabo.
Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Najeriya, NSCIA ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi ta bukaci a dakatar yin I'tikaf lokacin azumi saboda annobar korona.
Sanarwar da Majalisar ƙolin ta wallafa a Twitter ta yi kuma yi kira ga al'ummar musulmi su kiyaye matakan rage yaɗuwar korona musamman bayar da tazara tsakani a lokacin azumin Ramadan.
Tuni kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da sanarwar cewa a ranar Litinin ne za a fara duban watan azumi a ƙasar.
A ranar Talata kuma Al’ummar Musulmi ke fatan soma Azumin watan Ramadan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umurnin rage raka’o’in sallar taraweeh a Masallacin Harami na Makkah da kuma na Madina.
Jaridar Saudi Gazette ta ce shugaban da ke kula da harakokin Masallatan biyu Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais, ya ce za a rage yawan raka’o’in zuwa 10 daga 20 da aka saba yi.
Sannan za a yi Sallar ne bisa bin ka’idojin da aka gindaya na kariya daga yaɗuwar cutar korona.
A ranar Talata Al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke fatan soma Azumin watan Ramadan.
A azumin da aka gudanar a bara an dakatar da yin Salloli biyar na farilla da Sallar taraweeh da kuma Umrah.
A bana hukumomin Saudiyya sun amince a gudanar da Umrah, amma an hana yin I’tikaf da kuma buɗa baki a Masallatan biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Al’ummar Benin sun kaɗa kuri’ar zaɓen zaben shugaban kasa a ranar Lahadi
Shugaba mai ci Patrice Talon shi ne ake sa ran zai sake lashe zaben a wa'adi na biyu.
Ƴan na zarginsa da shirya magudi a zaben ta hanyar dakatar da manyan masu adawa da shi tsayawa takara.

Asalin hoton, Getty Images
An yi ta zanga-zanga gabanin ranar zaben a yankin arewacin ƙasar.
Rahotanni sun ce an kashe mutum biyu a lokacin da sojoji suka tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Savey.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin duban wata na Najeriya ya ce a gobe Litinin 29 ga watan Sha'aban za a fara duban watan Ramadana.
Cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a shafinsa na Twitter ya ce Litinin ce za ta kasance 29 ga watan Shaaban dan haka ko ba a ga wata ba a ranar dole a dauki azumi idan watan ya cika 30.
Saudiyya ma ta fitar da sanarwa cewa a ranar Lahadi wadda a tata kalandar ta ce ta kasance 29 ga Shaaban, daga ranar za a fara duban wata a kasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, TheCable
Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yi taro a jihar Imo kan matsalar tsaro da ke damun yankin.
Mataimakiyar gwamnan Imo Amaka Okafor shi ne ya tabbatar wa kafar yada labari TheCable batun.
Ta ce gwamnonin sun fara zuwa Owerri da safiyar yau, babban birnin na Imo, ta kara da cewa ana sa ran tattaunawar za ta fi mayar da hankali a kan yadda za a karfafa harkokin tsaro.
A baya-bayan nan yankin yana ta fama da hare-haren 'yan bindiga kan gine-ginen gwamnati.
An ta akai wa ofishin 'yan sanda hari a wurare daban-daban cikin yankin a makon da ya gabata.
An kuma rawaito an kashe jami'ai hudu a watan Maris a jihar Anambra.
A makon da ya gabata ne 'yan bindiga suka kai hari gidan yari da hedikwatar 'yan sanda a Imo.
Maharan sun saki fursunoni sama da 1,500 daga gidan yarin.
Daga baya kuma rundunar 'yan sandan kasar ta fitar da sanarwar cewa 'yan kungiyar IPOB masu rajin kafa kasar Biafra ne suka kai harin.

Asalin hoton, EPA
Kafafen yada labaran Iran sun ruwaito cewa wani hadri ya faru a cibiyar hada makaman kasar kwana guda bayan an yanke wata waya daga wajen hakar sinadarin uranium.
Jami'ai a cibiyar hada nukiliya ta Iran sun ce wata matsala da aka samu ta wutar lantarki ce ta haifar da wannan hadari.
Babu wanda aka ruwaito ya jikkata a hadari.
A shekarar da ta gabata ne lokacin da wuta ta kama a cibiyar Natanz, jami'ai suka ce an yi kokarin yin kutse ne a shirin samar da nukiliya na Iran.
Wannan hadari ya zo ne lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar makamai ta 2015 da manyan kasashen duniya.

Asalin hoton, AFP
Akalla mutum hudu aka kashe har da wani jami'i guda a wani hari da masu ikirarin jihadi suka kai garin Damasak da ke arewa maso gabashin Najeriya kusa da kan iyaka da Nijar.
Rahotanni na cewa maharan yan kungiyar ISWAP sun kutsa tare da kwashe kayayyaki a ofisoshi da rumbunan ajiye kaya mallakin kungiyoyin ba da agaji tare da cinna musu wuta.
Dakarun Najeriya na yakar masu ikirarin jihadin ta sama. Mazauna garin dai na tserewa zuwa Nijar domin samun mafaka.

Asalin hoton, @GovBorno
Jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo a kudancin Najeriya ta bai wa Gwamnan jihar Borno Lambar yabo ta tsofaffin daliban makarantar.
An bai wa Zulum kyautar tsohon dalibi na shekarar 2020 wanda shi ne na biyar da ya taba lashe wannan kyauta tun 1973.
Kungiyar tsofaffin dalibai ta makarantar ce ta yanke hukuncin bayar da lamabar yabon bayan tuntubar mambobinta da ke fadin duniya baki daya.

Asalin hoton, @GovBorno
Zulum wanda farfesa ne a ilimin kasa da ruwa ya yi jami'ar ne tsaknain shekarar 1997 zuwa 1998 kafin ya koma jami'ar Maiduguri ya yi digirin-digirgir a 2009.
Shugaban kungiyar ya ce la'akari da yadda Zulum ke kokari a shugabancin jihar Borno da ya zama abin misali shi yasa aka yanke shawarar a bashi kyautar, wanda aka yi bikin a babban dakin taro na jami'ar.
Zulum ya ce ya dauki wannan kyauta a matsayin "Kalubale".
"Bari na tabbatarwa da wannan taron cewa wannan kyautar babu abin da za ta kara mani sai karfin gwiwa da hazakar na yi abin da nake yi yanzu," in ji Zulum.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamnan jihar Osun da kuma na Kwara.

Asalin hoton, Getty Images
An ci tarar kamfanin Alibaba da ya fi ko wanne harkar sayar da kayayyaki a intanet tarar $ 7.2 billion
Masu lura da harkokin kasuwanci a China sun ce Alibaba, ya "Karya dokokin" kasuwancin kasar na tsawon shekaru, kuma kamfanin bai ja da wannan tuhuma ba.
Masu sharhi kan harkokin kasuwanci sun ce, wannan wata manuniya ce karara yadda gwamnatin China ke neman durkusar da kamfanin Intanet din.
Wannan tarar ta kai kimanin kaso 4 cikin 100 na ribar da kamfanin ya samu a 2019.

Asalin hoton, FMOT
Ma'aikatar sufuri ta Najeriya ta ce za ta kaddamar da aikin layin dogo da zai taso daga Ibadan ta jihar Oyo zuwa jihar Kano da ke arewwacin kasar.
Ma'aikatar ta bayyana hakan ce cikin jerin sakonnin Twitter da ta wallafa a shafinta.
Cikin fatan da gwamnati mai ci take da shi na hade duka bangarorin kasar ne da layin dogo yanzu za ta kaddamar da aikin jirgin kasan da zai taso daga Ibadan zuwa Kano.
Ministan Sufuri na kasar Amaechi ya ce gwamnatin Najeriya ta bayar da nata kason, yanzu ana jiran bankin China-Exim ya gabatar na nasa sannan a fara aiki gadan-gadan.
Ministan ya ce ba za a sauya yadda aka tsara yin wannan layin dogon ba, kamar yadda aka sauya wanda aka yi tsakanin Legas da Ibadan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta ce ta janye yajin aikin da ta fara a ranar 1 ga watan Afrilun da muke ciki.
Shiugaban kungiyar na kasa Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi, ya tabbatarwa da manema labarai hakan.
Yace an cimma wannan matsaya ne a wata tattaunawa da aka yi da kwamitin zartarwa na kasa ta intanet da kuma kungiyar a ranar Asabar.
Ya kuma ce "An dakatar da yajin aikin ne har nan da makonni biyu".
Dakta Okhuaihesuyi ya ce duka manyan jami'ansu da ba a biya ba, za a biya su nan da ranar Litinin.
Ya kara da cewa "Duka mambobinmu za su koma kan tsarin biyan kudin bai daya na IPPIS za kuma a biya su albashinsu.

Asalin hoton, Haramain
Kotun kolin Saudiyya ta ba da umarnin a fara duban jaririn wata Ramadana daga ranar Lahadi 29 ga watan Sha'aban kamar yadda kalandar Umm Al Qura ta bayyana.
Idan ba a ga watan ba a ranar 29 to babu shakka ranar 30 ga watan Sha'aban za a bada umarnin a tashi da azumin watan Ramadana.
Kamar yadda yake cikin koyarwar addinin Islama idan ba a ga watan ba a ranar 29 to 30 ga wata za a dauki azumi domin kuwa watannin musulunci ba sa yin 31.
A ko wacce shekara Saudiyya na da hukumar duban wata da ke jan ragammar wannan aiki, ta hanyar amfani da na'urorin zamani.
Ka zalika dukkanin kasashen musulmai za su fara duban nasu watan daga ranar 29 ga watan Sha'aban domin fara Azumin watan Ramadana mai albarka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa kan karagar mulki shi ake sa ran zai ci zabe a wa'adi na shida yayin da masu zabe ke zaben shugaban kasa a Chadi a yau.
Ana zargin Shugaba Idris Derby wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki da aka yi a 1990 da muzgunawa yan adawa gabanin zaben.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta yi bayani kan wani zalunci da aka yi wa yan hamayya da masu zanga-zanga. Kungiyar ta ce an yi amfani da karfi a zanga-zangar kin jinin gwamnatin da aka yi a baya-bayan nan.
A cewar wakilin BBC, Shugabannin adawa hudu ciki har da Saleh Kebzabo wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa a 2016 sun janye daga takarar saboda zargin hare-haren sojoji.
Sun kuma nemi magoya bayansu su kauracewa zaben kuma su yi zanga-zanga.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kashe kaji sama da 329,000 a cikin gidajen gona 62 a fadin kasar, biyo bayan wata cuta da ake alakantawa da murar tsuntsaye, wadda kuma ke ci gaba da yaduwa a kasar tun bayan bullarta a ranar 29 Janairu.
Alkaluma sun nuna cewa daga watan Janairu da cutar ta bulla zuwa ranar 5 ga watan Afrilu akwai tsuntsaye 421,947 da suka kamu da wannan cuta, yayin da 92,422 suka mutu dalilin cutar, wadda yanzu ta bulla a kananan hukumomi 20 a jihohi takwas na kasar.
Wata majiya daga ma'aikatar noma ta ce a ranar 9 ga watan Afrilu da muke ciki ne aka kashe kaji 329,556 a gonaki 62.
A ranar 29 ga watan Janairu ne Daraktan da ke lura da harkokin dabbobi Dakta Adeniran Alabi, ya tabbatar da bullar cutar a yankin karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Mutuwar Yarima Philip kuma Duke na Edimburgh ranar Juma'a ta sa yin addu'oi domin tunawa da shi a majami'u da ke fadin duniya.
A Sydney, Firaministan Australia ya halarci wani taron addu'oi da aka yi wa Yarima Philip da Sarauniya Elizabeth.
Shugaban darikar Anglican ta duniya, Rabaran Justin Welby zai jagoranci addu'oin da za a gudanar nan gaba a yau.
Ana kuma sa ran shi ne zai jagoranci jana'izar Yarima Philip a karshen makon gobe a Fadar Windor.