Buhari ya sake yin 'kakkausan gargaɗi' ga 'yan fashin daji

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da suaran ƙasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Nan muke rufe shafin

    Mun kawo ƙarshen rahotannin kai-tsaye a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe domin ɗorawa daga inda aka tsaya.

    Umar Mikall ke cewa sai da safenku.

  2. Benzema ya sake ceto Real Madrid da ƙayatacciyar ƙwallo

    Karim Benzema

    Asalin hoton, Getty Images

    Karim Benzema ya ci ƙwallo mai ɗan karen kyau a mintunan ƙarshe, inda ya ceto Real Madrid daga hannun Elche a wasan La Liga mako na 27.

    Real Madrid wadda ta fara wasan na Asabar da tazarar maki takwas tsakaninta da Atletico ta saman teburi, ta sha mamaki lokacin da Dani Calvo ya zira mata ƙwallo a raga a minti na 61.

    Benzema ne ya farke ƙwallon bayan wani kurosin da Luka Modric ya yo cikin raga a minti na 73.

    Yayin da lokaci ya fara ƙure wa Madrid, ɗan ƙasar Faransan ne ya sake ɗaɗata wata ƙwallo da ta daki tirke sannan ta gangara raga biyo bayan wani wasan ba-ni-in-ba-ka da suka yi da Casemiro.

    Da wannan sakamako, Real ta koma matsayi na biyu da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Barcelona, wadda za ta buga nata wasan ranar Litinin da Huesca.

    Ita kuwa jagorar teburin, Atelico Madrid, za ta fafata da Getafe a yau Asabar da ƙarfe 9:00 agogon Nijar da Najeriya.

  3. 'Yan sanda sun kama tsohuwar Shugabar Bolivia Jeanine Áñez

    Jeanine Áñez

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan sandan Bolivia sun kama tsohuwar shugabar rikon kwaryar kasar, Jeanine Áñez, don cika umarnin wata kotu na kama ta tare da wasu tsoffin ministocin gwamnatinta biyar.

    Ana tuhumarsu da laifin tawaye da ta'addanci da kuma haɗa baki don yamutsa kasa.

    Masu gabatar da kara sun zarge su da shiga juyin mulkin da ya janyo hambarar da tsohon shugaban kasar Evo Morales a 2019.

    Tuni aka damke mutum biyu daga cikin tsoffin ministocin nata.

    An ga tarin 'yan sanda a wajen gidanta da ke arewacin birnin Beni, amma wasu rahotanni sun ce ba a same ta ba.

    Mista Morales ya ce ya tsorata ainun yayin da ya fahimci juyin mulkin da ake kitsa masa, abin da ya sanya shi sauka tare da ficewa daga kasar don tsira da ransa.

  4. Buhari ya sake yin 'kakkausan gargaɗi' ga 'yan fashin daji

    Buhari

    Asalin hoton, NG Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake yin "kakkausan gargaɗi" ga 'yan bindiga da ke kai wa makarantu hari, a cewar mai magana da yawun fadar shugaban, Malam Garba Shehu.

    Buhari na yin gargaɗin ne yayin da yake yaba wa dakarun sojojin ƙasar bisa yunƙurin da suka yi na ceto 180 daga cikin ɗaliban kwalejin harkokin noma ta Kaduna a lokacin da 'yan fashin daji suka yi yunƙurin yin garkuwa da su.

    Sai dai maharan sun samu tserewa da mata 23 da kuma maza 16 cikin daji, a cewar gwamnatin Jihar Kaduna.

    "Kazalika, shugaban ƙasa ya yaba wa mutanen gari kan bayanan sirri da suka bayar wajen daƙile ayyukan 'yan fashi, yana mai cewa duk ƙasar da ke da hanyoyin tattara bayanan sirri masu ƙarfi ita ce ƙasa mai kwanciyar hankali," in ji sanarwar da Garba Shehu ya fitar.

    "Sojojinmu ka iya samun kayan aikin da suke buƙata amma wajibi ne mutanen gari su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan ƙalubale."

    'Yan bindigar da suka sace ɗaliban na Federal College of Forestry Mechanisation a daren Alhamis sun buƙaci ba su naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa.

    An ga ɗaliban cikin wasu bidiyo da 'yan fashin suka fitar suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Hukumar NYSC a Najeriya ta kori ma'aikata daga aiki

    Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim

    Asalin hoton, @officialnyscng

    Hukumar yi wa ƙasa hidima a Najeriya ta National Youth Service Corps (NYSC) ta hukunta ma'aikata 34 bayan zarginsu da laifuka ciki har da haɗa baki da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima wurin saɓa ƙa'idar aiki.

    Shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, shi ne ya tabbatar wa da BBC korar ma'aikatan, inda ya ce wasu daga cikinsu horo aka yi musu.

    Ya ƙara da cewa an ɗuki matakin ne domin tabbatar da ɗa'a da bin ƙa'idojin aiki a hukumar.

    "Akwai wasu ('yan hidimar ƙasa) da ke haɗa baki da ma'aikatan domin a kai su wani wuri da ba su cancanta ba, mu kuma a doka sai mun duba mun ga ko suna zuwa, idan ba sa zuwa ba za mu yarda da haka ba," in ji shi.

    "Wasu na ɓata mana suna a shafukan sada zumunta suna cewa idan mutum yana so a kai shi Abuja ga abin da zai bayar. Duk ma'aikatanmu masu haɗa baki da irin waɗnnan mutane za mu ɗauki mataki a kansu.

    "Akwai wasu da suka yi laifuka daban-daban, ba sa zuwa aiki shekara ɗaya ko biyu. Mun tura musu wasiƙa ba su dawo da martani ba."

    Janar ɗin ya ce sun bi doka kafin aiwatar da hukuncin ta hanyar tuntuɓar hukumar ɗukar aiki ta ƙasa, sannan kuma hukumar ƙoli ta NYSC ta amince da hukuncin.

  6. 'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan adawa tare da kama shugabanninsu a Rasha

    Rasha

    Asalin hoton, AFP

    'Yan sanda a Rasha sun tarwatsa wata zanga-zangar 'yan adawa tare da kama mutum 200, ciki har da ƙusoshin adawar.

    Jim kaɗan bayan fara taron a wani otel da ke birnin Moscow 'yan sanda suka afka kuma suka ce za su tsare kowa da kowa.

    A cewar 'yan sandan, an karya dokar kariya daga cutar korona kuma wata ƙungiya ce "wadda ba a yarda da ita ba" ta shirya taron.

    Lamarin na zuwa ne a lokacin da hukumomi ke ci gaba da daƙile harkokin 'yan adawa, yayin da zaɓe ke ƙara ƙaratowa.

    A watan da ya gabata aka ɗaure jagoran adawar ƙasar, Alexei Navalny. An zarge shi da karya ƙa'idojin belin da aka ba shi.

  7. 'Manufar China kan Hong Kong za ta daƙile dimokuraɗiyya'

    Kungiyar manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ta ce shawarar da China ta yanke na sauya tsarin zabe a Hong Kong zai dakile dimukuradiyya da hakkin 'yan adawa a yankin.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen sun bukaci China ta mutunta dokar da ke karkashin yarjejeniyar da ta kulla da Birtaniya yayin mayar da yankin karkashin kulawarta a shekarar 1997.

    A ranar Alhamis ne majalisar dokokin China ta amince da matakan da ke bai wa kwamitin da ke goyon bayan kasar damar tantance 'yan takarar majalisar dokokin Hong Kong, da kuma rage yawan mambobin da jama'a ke zaba.

    China ta ce sauye-sauyen za su tabbatar da cewa "masu kishin kasa" ne kawai ke mulkin Hong Kong.

  8. Har yanzu ba labarin ɗalibai 39 da aka sace a Kaduna

    Kwalejin ilimin gandun daji a Kaduna

    Har yanzu ba a ji ɗuriyar ɗalibai 39 da ƴan bindiga suka sace a ranar Alhamis a wata kwaleji a jihar Kaduna ba a arewa maso yammacin Najeriya.

    Harin da aka kai a wata kwalejin ilimin gandun daji da ke kusa da makarantar sojoji a wajen garin Kaduna shi ne karo na biyar da aka sace daliban makaranta tun watan Disamba.

    Wani jami’i ya ce mata 23 da maza maza 16 suka salwanta .

    Sojojin sun ce bayan harin an kubutar da mutane da dama.

    Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce akwai yiwuwar yawancin wadannan daliban sun gudu daga kwalejin a yayin farmakin, kila ba a sace su ba ko kuma a kubutar da su ba.

    Kodayake jami'ai galibi suna musanta biyan fansa amma ƴn bindiga da ke yawan kai hare-hare yawanci sukan saki wadanda suka kama ne bayan tattaunawa.

  9. Ministan lafiya ya yi murabus bayan mutuwar majinyatan korona

    Ministan Lafiya na Jordan

    Asalin hoton, @DrNathirObeidat

    Ministan lafiya na Jordan ya yi murabus bayan mutuwar wasu majinyatan cutar korona a asibiti sakamakon ƙarancin iskar oxygen.

    Nathir Obeidat ya sanar da yin murabus sakamakon mutuwar majinyatan a wata asibiti kusa da babban birnin ƙasar Amman.

    Kafofin watsa labaran ƙasar sun ce mutum shida suka mutu, lamarin da ya fusata al’umma a Jordan.

    Firayiministan ƙasar ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa.

  10. Ƴan sandan Rasha sun yi wa wani taron ƴan adawa dirar mikiya

    Ƴan sanda a Moscow sun kama kansiloli masu zaman kansu sama da 100 daga sassan ƙasar da ke taro, matakin da ƴan adawa suka kira haramtacce.

    Wasu hotunan sun nuna yadda jami'ai ke tura wakilan a taron na United Democrats daga wani otal zuwa motocin 'yan sanda.

    Daga cikin wadanda aka tsare har da Vladimir Kara-Murza, wani babban mai adawa da shugaba Putin da kuma attajiri ɗan kasuwar da ya tsere daga ƙasar Mikhail Khodorkovsky.

    Ƴan sanda sun ce taron da ke samun goyon bayan ƙasashen waje ya saɓa wa dokokin Rasha.

  11. Tarihin Manjo Janar Ibrahim Attahiru da tarihin mawaƙi Namenj

    A wannan makon Umaymah Sani Abdulmumin ce ta amsa wasu tambayoyin masu sauraro da ke neman sanin tarihin Babban Hafsan sojan ƙasa na Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru da kuma tarihin Mawaki Namenj.

    Bayanan sautiFilin Amsoshin Takardunku
  12. An nada tsohon Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniya a Najeriya

    An naɗa tsohon sarkin Kano Sanusi na II a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

    Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin a matsayin Khalifa a babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato.

    Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya

    Tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu ba a naɗa sabon Khalifa ba a Najeriya.

    Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya na Najeriya da wajen ƙasar da suka haɗa babban malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

    Taron Tijjaniya a Sokoto

    Asalin hoton, Other

  13. ISWAP ta yi wa sojojin Najeriya ‘kwanton ɓauna’ a Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu sojojin ƙasar sun ji 'mummunan rauni' lokacin da mayaƙan ISWAP suka yi wa ayarin motocinsu kwanton-bauna a ranar Juma’a.

    Jaridar PRNigeria ta ce an kai wa sojojinna Najeriya harin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kukawa daga Kauwa.

    “Sojojin sun yi nasarar murƙushe harin a Kukawa da Gudunbali tare da kashe mayaƙan da dama a musayar wutar da suka yi,” a cewar jaridar.

    Sai dai jaridar ba ta bayyana adadin sojojin da suka ji rauni da ba da kuma yawan ƴan ta'addan ISWAP da aka kashe.

  14. Sri Lanka za ta haramta saka burƙa

    Burƙa

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Sri Lanka ta ɗauki wani gagarumin mataki na hana sanya burƙa ko niƙabi (da duk wani mayafin da zai rufe fuska a bainar jama'a, bisa dalilan na tsaro.

    Ministan tsaron jama'a na ƙasar, Sarath Weerasekara, ya shaida wa BBC cewa ya sanya hannu kan umarnin majalisar ministocin kasar wanda a yanzu yake bukatar amincewar majalisar.

    Sri Lanka mai yYa ce yana sa ran aiwatar da dokar nan ba da daɗewa ba.

    Kusan shekaru biyu da suka gabata sama da mutane 250 aka kashe a cikin jerin hare-haren da masu kaifin kishin Islama suka kai wa cocin Kirista da otal-otal na da yawanci ƴan kasashen waje ke sauka.

    An taɓa haramta saka burƙa a Sri Lanka mai yawan mabiya addinin Budda bayan harin 2019 a coci.

    Mista Weeasekara ya kuma ce gwamnati na shirin rufe ɗaruruwan makarantun islama da ba su da rajista.

  15. Matsalar ilimi a jihar Sakkwato

    Jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriya na daga cikin wadanda ake kallo a matsayin na sahun baya a bangaren ilimi duk kuwa da muhimmancinsa a kowane fanni na rayuwa.

    Daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga bangaren na ilimi kuwa shi ne rashin makarantu masu inganci.

    Cikin shirin BBC na A fada A cika a watan Satunban shekarar 2020, wani daga cikin wadanda suka halarci taron ya shaida wa gwamnan cewa Jihar na fama da lalacewar makarantu na firamare da sakandare.

    Yanzu haka shekarar gwamnatin shida akan mulki, kuma daya daga cikin bangarorin da gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hanakali a kai shi ne ilimi.

    To ko ya wannan alwashi na Gwamnan yake a kasa. Haruna Ibrahim Kakangi ya duba wannan batu a cikin rahotonsa na musamman, wanda BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar MacArthur suka ɗauki nauyi

    Bayanan sautiRahoton Haruna Ibrahim Kakangi
  16. New Zealand na tuna harin masallacin Christchurch

    Ƙasar New Zealand na gudanar da addu’o’i da tunawa da mummunan harin da aka kai a masallacin Chriscurch shekaru biyu da suka gabata.

    Mutum 51 aka kashe a hare-haren da aka kai a masallatai biyu a Christchurch ranar 15 ga watan Maris din 2019, yanzu shekaru biyu kenan cur.

    Daruruwan mutane ne suka halarci bikin na addu’o’i cikin tsauraran matakan tsaro domin karrama waɗanda aka kashe.

    Sannan bikin ya shafi ware minti ɗaya, don tunawa da mutanen da suka mutu a harin.

  17. An yi wa gwamnan Legas rigakafin korona

    Gwamnatin Legas ta fara gudanar da rigakafin korona a ranar Asabar.

    Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce za a fara ne da ma'aikatan kiwon lafiya waɗanda suka fi hadarin kamuwa da cutar.

    An yi wa gwamnan jihyar allurar Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat, da kuma kwamishinan Lafiya Prof. Akin Abayomi a asibitin kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Yaba

    Gwamnatin Legas inda cutar korona ta fi ƙamari a Najeriya ta ce ta karɓi allurar rigakafin 507,742 ta AstraZeneca daga cikin miliyan huɗu da aka ba Najeriya

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. A fara dibon watan Sha’aban – Fadar Sarkin Musulmi

    Babban kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ranar Asabar ta kama 29 ga watan Rajab wanda ya yi daidai da 13 ga watan Maris.

    Sanarwar mai dauke da sa hannun Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu, kuma shugaban kwamitin bai wa Sarkin musulmin shawara ta buƙaci al’ummar musulmi su fara dibon watan Sha’aban daga ranar Asabar.

    Idan an ga watan a sanar da Hakimi mafi kusa ko Mai Gari wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

    Daga watan Sha’aban dai sai watan Azumi na Ramadan.

    Sanarwar Fadar Sarkin Musulmi
  19. Ba mu yi ƙarin kuɗin mai ba - NNPC

    Kamfanin mai na Najeriya, wato NNPC ya jaddada cewa, ba a ƙarin farashin man fetur ba a ƙasar kamar yadda ake faɗa.

    Fargabar ƙarin farashin ne ya haddasa dawowar dogayen layukan motoci a gidajen mai musamman a Abuja babbar birnin Tarayya.

    Kamfanin na NNPC ya ce babu alamun za a yi karin nan da dan wani lokaci, har sai an zauna da masu ruwa da tsaki an tattauana kan lamarin a yanke shawar.

    Babban manajan daraktan kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce naira 162 shi ne har yanzu farashin gwamnati.

    Bayanan sautiHirar BBC da Mele Kyari
  20. Korona ta sake kashe mutum 8 a Najeriya

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 399 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Juma'a.

    Alƙalumman hukumar kuma sun nuna cewa cutar ta sake kashe mutum 8 a ranar Juma'a.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 101 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙalumman da hukumar ke fitarwa sun nuna cewa cutar na raguwa a Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X