'Yan bindiga sun sace mai unguwa, sun kashe mutane a Jihar Neja

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafin.

    Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku gobe da safe.

    Kafin nan, ku duba ƙasa don ganin abubuwan da suka faru a faɗin duniya ranar Lahadi.

  2. Shugaban Tanzania ya yi amai ya lashe kan korona

    Shugaban Tanzania

    Asalin hoton, STATEHOUSE TANZANIA

    Shugaban Tanzaniya John Magufuli, wanda sau da yawa yake watsi da barazanar annobar korona yanzu ya sauya ra’ayi game da annobar.

    Ya gaya wa masu ibada a cocin Dar es Salaam da su ci gaba da yin taka tsan-tsan, kuma ya bukace su da su yi amfani da abin rufe fuska amma wanda ake samarwa a cikin gida, yana mai cewa wadanda aka shigo da su suna da hadari.

    Yau ce rana ta karshe cikin kwanaki uku na azumi da addu’o’i da Shugaba Magufuli ya kira don kare Tanzania daga cutar.

    Sauya ra’ayin shugaban ya yi daidai da kiran da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi wa Tanzaniya don inganta matakan kariya domin fadakar da al’umma kan rigakafin cutar.

    Mista Magufuli ya ce rigakafin na tattare da hadari.

  3. Buhari na alhinin sojojin da suka mutu a hatsarin jirgi a Abuja

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa ta'aziyyar rasuwar fasinojin jirgin sojan nan da ya yi hatsari a Abuja ranar Lahadi.

    Shugaban ya bayyana alhininsa ne cikin wani saƙon Twitter, inda ya kwatanta sojojin a matsayin "jajirtattu".

    "A madadin Gwamnatin Tarayya, ina miƙa ta'aziyyata ga 'yan uwa da abokan waɗanda suka rasu," in ji Buhari.

    Mai magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya ya faɗa wa BBC cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa ceton mutum 42 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Neja kafin ya juya zuwa Abuja saboda matsalar na'ura.

    Da tsakar ranar yau Lahadi ne jirgin mai suna King Air B350i ya faɗo ƙasa a kusa da garin Basa da ke babban birnin ƙasar, Abuja.

    Hukumomi sun ce dukkan mutum bakwai da ke cikinsa sun mutu.

    Babban Hafsan Sojan Sama ya bayar da umarnin ƙaddamar da binciken abin da ya haifar da hatsarin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Labarai da dumi-dumi, An kashe ma'aikatan hukumar zaɓe bakwai a Nijar

    Zaɓen Nijar

    Aƙalla ma'aikatan hukumar zaɓen Nijar bakwai ne suka mutu a yau Lahadi yayin da motarsu ta taka wani abin fashewa kuma ta tarwatse.

    Lamarin ya faru ne a yammacin Jihar Tillaberi da ke da iyaka da Mali, kamar yadda gwamnan jihar ya shaida wa kamfanin labarai na AFP.

    Kazalika, mutum uku sun jikkata bayan taka nakiyar. Sai dai babu tabbas ko motar tasu aka hara.

    "Na samu labarin ne da misalin ƙarfe 11:00 na rana cewa akwai mutum bakwai lokacin da motar ta tarwatse," Gwamna Tidjani Ibrahim Katiella ya faɗa wa AFP.

    Ya ce mutanen shugabannin rumfunan zaɓe ne da sakatarorinsu, waɗanda hukumar zaɓe ta CENI ta ɗauka aiki.

    A yau ne masu zaɓe ke jefa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar ta Nijar bayan rashin samun wanda ya ci fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un zagayen farko da aka kaɗa a watan Disamba.

  5. Labarai da dumi-dumi, An saki fasinjojin motar gwamnatin Jihar Neja da aka sace

    Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sakin fasinjojin nan da aka sace a cikin motar safa ta gwamnatin jihar.

    Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya sanar da sakin fasinjojin guda 20 waɗanda aka sace a ƙauyen Kundu na jihar.

    Sai dai bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba kafin sakin nasu, yana mai cewa "akwai ƙarin bayani nan gaba kaɗan".

    Tun ranar 14 ga watan Fabarairun nan ne aka samu rahoton sace matafiyan a cikin motar sufuri ta gwamnatin jihar mallakar hukumar Niger State Transport Authority.

    Sai dai babu batun sakin ɗaliban makarantar Kagara da malamansu guda 42 da 'yan fashi suka sace ranar Talata da ta gabata.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Najeriya ka iya samun rigakafin korona nan da kwana 10 - Ministan Lafiya

    Rigakafin cutar korona

    Asalin hoton, Pfizer

    Ministan Lafiya na Najeriya ya ce ƙasar ka iya karɓar rigakafin cutar korona a cikin kwana 10 masu zuwa.

    Yayin da yake tattaunawa da manema labarai lokacin duba aiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Legas, Dr Osagie Ehanire ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin karɓar rigakafin.

    "An faɗa mana cewa nan da ƙarshen watan nan, nan da kwana 10 kenan daga yanzu, za mu karɓi rigakafin," a cewarsa, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

    "Ba mu muke samar da rigakafin ba. An samar da su ne a ƙasashen waje, ƙasashe kusan huɗu ko biyar.

    Mista Ehanire ya ƙara da cewa ƙasashen Amurka da Rasha da Birtaniya da China, waɗanda suka samar da rigakafin, sun bai wa wasu ƙasashen izinin kwaikwayar nasu domin ƙara yawan alluran.

    Mutum 18 ne suka mutu a Najeriya ranar Asabar sakamakon cutar korona, yayin da 645 suka kamu, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

  7. Tarihin 'yan Najeriya biyu da suka samu manyan muƙamai a makon nan

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya bayar da tambayoyi kan tarihin 'yan Najeriya biyu da suka samu manyan muƙamai a wannan makon; Ngozi Okonjo Iweala da Abdulrasheed Bawa.

    Ngozi Iweala, ita ce sabuwar shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya wato World Trade Organisation.

    Abdulrasheed Bawa mai shekara 40 kuma ɗan asalin Jihar Kebbi, shi ne wanda Shugaba Buhari ya miƙa sunansa ga Majalisar Dattawa domin tantance shi a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC.

  8. 'Yan bindiga sun sace mai unguwa, sun kashe mutane a Jihar Neja

    'Yan fashin daji

    Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun afka wa garin Gurmana da ke Jihar Neja, inda suka kashe mutane da dama tare da sace mai unguwar Shakana.

    Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na ranar Asabar yayin da ake tsaka da cin kasuwar garin, kamar yadda Kansilan Gurmana Mamman Iliyasu ya shaida wa BBC Hausa.

    Ya ƙara da cewa 'yan bindigar sun toshe hanya domin hana mutane guduwa sannan suka fara harbi a kan mai tsautsayi, abin da ya sa wasu suka faɗa cikin kogin da ke kusa da wurin har ma wasu suka nitse a ruwan.

    "Ko a safiyar yau ma (Lahadi) mun ɗauko gawar mutum ɗaya daga cikin ruwan," in ji shi.

    "Har yanzu ba mu san adadin waɗanda suka mutu ba amma waɗanda suka tafi da su za su kai mutum 11."

    Kazalika kansilan ya ce 'yan fashin sun yi awon gaba da mai unguwar Shakana kuma 'yan bindigar ba su tuntuɓe su ba domin neman kuɗin fansa.

    Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, jami'an tsaro ba su je wurin da abin ya faru ba, in ji Mamman Iliyasu.

    Har yanzu ba a saki ɗaliban makarantar sakandare ta Kagara ba, waɗanda aka sace a daren Talatar da ta gabata tare da malamansu da ma'aikata guda 42 a jihar ta Neja.

  9. An kashe mutum uku yayin harbe-harbe a Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum uku aka kashe tare da jikkata biyu yayin wasu harbe-harbe a Jihar Louisiana ta Amurka.

    Wani ɗan sandan jihar ya ce mutum na farko ya buɗe wuta a kan wasu mutum biyu, abin da ya jawo waɗanda ke cikin shagon su ma suka mayar da wuta.

    Mutum biyun da kuma wanda ya buɗe musu wuta sun mutu. Sai dai zuwa yanzu ba a bayyana ko su wane ne ba.

    Lamarin ya faru ne a shagon sayar da bindiga na Jefferson Gun Outlet da ke yankin New Orleans kuma mahukunta sun ce an ƙaddamar da bincike.

    "Da alama mutane ne da yawa suka mayar wa da wanda ya fara harbin martani," a cewar ɗan sanda Joseph Lopinto.

  10. Dan takarar jam'iyya mai mulki Bazoum Mohamed ya jefa kuri'arsa

    Yadda Bazoum ya zabi kansa a zaben Nijar
    Bayanan hoto, Yadda Bazoum ya zabi kansa a zaben Nijar

    Dan takarar jam'iyya mai mulki Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya ya jefa wa kansa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Nijar.

    Yana fafatawa ne da ɗan takarar jam'iyyar adawa ta RDR Tchanji Mahamane Ousmane.

    Tun misalin ƙarfe 8 na safe aka fara jefa kuri'a a zaɓen.

  11. Labarai da dumi-dumi, Wani Jirgin soji ya yi hatsari a Abuja

    Wani jirgin sama na soja ya yi hatsari a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.

    Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce jirgin mai suna King air 350 ya yi hatsari ne bayan yasamu matsalar na’ura a lokacin da ya tashi sama, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

    Ministan ya ce jirgin ya tashi ne zuwa Minna kuma akwai yiyuwar hasarar rai.

  12. Yadda ake cin kasuwar Tahoua a ranar zaɓen shugaban ƙasa a Nijar

    Yayin da ake ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a jamhuriyar Nijar zagaye na biyu, ‘yan kasuwa kuma sunbake kolin su a kasuwar garin Tahoua da ke ci duk ranar Lahadi.

    Ƴan takara biyu ne a zaɓen da Mohammmed Bazoum na jam`iyyar PNDS Tarayya mai mulki, da kuma Mahaman Ousman na babbar jam`iyyar hamayya ta RDR Tchanji.

    Masu magana na cewa bikin Magaji ba ya hana na Magajiya, don haka zaɓe bai hana al'ummar Nijar gudanar da harakokinsu ba na yau da kullum.

    Birnin Tahoua
    Birnin Tahoua
    Birnin Tahoua
    Birnin Tahoua
    Birnin Tahoua
  13. Atiku ya goyi bayan gwamnatin Buhari na sayar da matatun mai da kadarorin Najeriya

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar Ya yaba wa gwamnatin Tarayya kan matakin da aka ruwaito ta ɗauka na ƙokarin sayar da kadarorin kasar da suka kunshi har da matatun mai.

    Atiku ya ce ya daɗe yana goyon bayan mayar da ragamar tafiyar da tattalin arziki ga ƴan kasuwa.

    Ya ce duk da yana da saɓanin ra’ayi da gwamnatin APC a tsawon shekaru amma yanzu ya samu gamsuwa yadda gwamnatin yanzu ta dawo kan hanya.

    “Burina shi ne zaman lafiya da ci gaban Najeriya, zan yi farin ciki na bayar da shawarwari ga wannan gwamnatin domin ci gaban ƙasarmu da jama’arta,” in ji Atiku.

    Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta PDP wanda ya fafata da Buhari a zaɓen 2019, ya ce "gara ace an samu jinkiri da ace ba a yi ba tare da yin kira ga gwamnati ta baje komi a faifai domin ita ce kawai hanyar da Najeriya za ta girbi babbar fa’idar tattalin arzikinta daga manufar."

    An ruwaito gwamnatin Najeriya cewa ta yanke shawarar sayar da kadarorinta tsakanin Janairu 2021 zuwa ƙarshen 2022 domin kasafin kuɗinta na 2021.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Ɗan takarar jam'iyyar adawa Mahamane Ousmane ya kaɗa ƙuri'arsa

    Mahamane Ousmane ya kaɗa ƙuri'arsa

    Dan takarar RDR Tchanji Mahamane Ousmane ya jefa wa kansa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Nijar.

    Yana fafatawa ne da ɗan takarar jam'iyya mai mulki Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya.

    Tun misalin ƙarfe 8 na safe aka fara jefa kuri'a a zaɓen.

  15. Shugaba Mahamadou Issoufou ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen Nijar

    Shugaba Mahamadou Issoufou yana jefa kuri'a
    Bayanan hoto, Shugaba Mahamadou Issoufou yana jefa kuri'a

    Shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou ya kada kuri’arsa a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da ake gudanarwa a ranar Lahadi.

    Ƴan takara biyu ne a zaɓen da Mohammmed Bazoum na jam`iyyar PNDS Tarayya mai mulki, da kuma Mahaman Ousman na babbar jam`iyyar hamayya ta RDR Tchanji

    Wannan ne karon farko da wata gwamnatin farar hula za ta miƙa mulki ga wata gwamnatin farar hula a tarihin Nijar.

    Yadda ake gudanar zaɓen a Nijar

    Shugaban CENI Na Damagaram, Chaibu Moussa ya kada kuri’a
    Bayanan hoto, Shugaban CENI Na Damagaram, Chaibu Moussa ya kada kuri’a
    Mata sun fito zaɓen
    Bayanan hoto, Mata sun fito zaɓen
    Wakilan kungiyoyin farar hula da jami’in hukumar zabe ta CENI suna sa ido ga gudanar zabe
    Bayanan hoto, Wakilan kungiyoyin farar hula da jami’in hukumar zabe ta CENI suna sa ido ga gudanar zabe
  16. Iran ta gindaya wa Amurka sharaɗi

    Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya ce za a iya fara tattaunawa da Amurka lokacin da dukkan bangarorin suka cika alkawuransu a karkashin yarjejeniyar nukiliyar Iran, wacce Amurka ta fice 2018.

    Mista Zarif yana magana ne kafin cikar wa’adin Iran ga Amurka a yau Lahadi don cire mata takunkumi.

    Majalisar dokokin Iran ta zartar da dokar da za ta takaita ba tawagar Hukumar makamashi ta Majalisar Ɗinkin DuniyaIAEAdomin sa ido kan nukiliya ƙasar idan har Amurka ba ta yi komi ba.

    Shugaban hukumar ta IAEA yana Tehran don tattaunawa.

    Mista Zarif ya ce bincikenba shi zai tabbatar da Iran ta yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar ba.

  17. An gwabza ƙazamin faɗa tsakanin IS da Boko Haram

    Wata kafa da ke nuna goyon baya ga kungiyar al-Qaeda ta ba da rahoton cewa ƙungiyoyin ta’adda da ke hamayya da juna sun gwabza faɗa a Najeriya kuma wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin shugabbanin IS a Somalia.

    Kafar Thabat ta wallafa labari a mujallarta ta mako mako a kafar RocketChat da ta saba turo labarai game da rikicin.

    Ta ce mayakan IS sun gwabza faɗan ne a ƙauyen Sunawa da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

    Kuma rikicin ya ɓarke ne bayan mayaƙan IS sun sace mata da dama da ke da alaƙa da Boko Haram inda kuma Boko Haram ta ƙaddamar da hari kan sansanin IS kuma a cewar kafar ta kashe mayaƙan IS da dama tare da kuɓutar da matan.

    A 2015 shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya sanar da goyon bayansa ga IS kafin daga baya ɓangaren ƙungiyar ya sauya suna zuwa ISWAP.

    Daga baya Shekau da wasu mabiyansa suka ɓalle daga IS bayan ta naɗa sabon shugaba. Kuma an sha bayar da rahotannin faɗa tsakanin ƙungiyoyin a yankin Tafkin Chadi.

    Kafar Thabar kuma ta bayar da rahoton cewa an gwabza ƙazamin fada tsakanin mayaƙan IS a Somalia kan neman shugabanci. Kuma a cewar kafar rikicin ya ɓarke ne bayan ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar Abdel Qadir al-Mumin ya kwanta rashin lafiya a watan Disamba.

    Mayakan ISWAP

    Asalin hoton, Others

  18. An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen Nijar

    Zabe a Nijar

    Al'ummar Jamhuriyar Nijar na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu.

    Mutum miliyan bakwai da rabi ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen inda za su zaɓi sabon wanda zai gaji Mahamadou Issoufou a zaɓen mai tarihi inda wata gwamnatin farar hula za ta miƙa mulki ga wata gwamnatin farar hula a karon farko

    Ƴan takara biyu ne a zaɓen da Mohammmed Bazoum na jam`iyyar PNDS Tarayya mai mulki, da kuma Mahaman Ousman na babbar jam`iyyar hamayya ta RDR Tchanji.

    A zagayen farko na zaɓen ɗan takara Mohammmed Bazoum na jam'iyya mai mulki ya samu kashi 39.3 yayin da tsohon shugaba Mahamane Ousmane yake da kashi 16.9 cikin ɗari.

    Yadda al'ummar Jamhuriyyar Nijar suka fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen

    An fara kada kuri’a a birnin Damagaram. Nan mazabar Unwala ce da ke shiyya ta hudu
    Bayanan hoto, An fara kada kuri’a a birnin Damagaram. Nan mazabar Unwala ce da ke shiyya ta hudu
    An fara zabe da misalin karfe 8 na safe a mazaba ta 14 a unguwar Zulanke, a di’irar birnin Tahoua

    Asalin hoton, bb

    Bayanan hoto, An fara zabe da misalin karfe 8 na safe a mazaba ta 14 a unguwar Zulanke, da ke cikin birnin Tahoua
    Wata Dattijiya ta kada kuriarta
    Bayanan hoto, Wata Dattijiya ta kada kuriarta a birnin Tahoua
    Ana tantance masu kada kuri'a a birnin Damagaram
    Bayanan hoto, Ana tantance masu kada kuri'a a birnin Damagaram
    Zabe a Nijar
  19. Cutar Korona ta sake kashe mutum 18 a Najeriya

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 645 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Asabar.

    Cutar kuma ta sake kashe mutum 18 cikin sa'a 24 a Najeriya kamar yadda alkalumman na NCDC suka nuna

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas da ta fi yawan masu fama da cutar a Najeriya ce ke kan gaba da mutum 282 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Budewa

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a cikin wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu.