Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, Imam Saleh ke fatan za ku kasance da mu a gobe Talata idan Allah ya kai mu, don ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • An harba wa masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye
    • Hotunan zanga-zangar #EndSARS a Kano
    • Ana zargin 'yan sanda da kashe matashi a Kano ranar Lahadi
    • #EndSARS: Masu kutse sun yi ikirarin toshe shafukan Intanet na bankunan First Bank da Access
    • Masu zanga-zanga sun rufe filin jrigin sama na Legas
    • Hotunan zanga-zangar #EndSARS a Kano
    • 'Yan daba sun jikkata masu zanga-zanga a Abuja

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Kusan Amurkawa miliyan 30 sun jefa kuri'a a zaben shugaban kasa

    Biden da Trump
    Bayanan hoto, Biden da Trump

    Yayin da ya rage makwanni biyu kacal a gudanar zaben shugaban kasa a Amurka, tuni 'yan kasar kusan miliyan 30 sun jefa kuri'a a zaben wurwuri da ake ci gaba da gudanarwa.

    Kuri'un jin ra'ayin jama'a daban daban sun nuna cewa Joe Biden na kan gaban Trump da tazara mai yawa, sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa ''Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare''.

  3. Evo Morales ya ce zai koma gida

    Evo Morales

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban Bolivia, Evo Morales, ya ce zai koma kasar bayan nasarar da Luis Arce ya yi a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

    Mista Morales ya bar Bolivia ne bayan soke zaben mai cike da takaddama saboda zargin magudi.

    Wakiliyar BBC ta ce babu tababa cewa Mista Morales yana da matukar tasiri a zaben.

    Luis Arce wanda tsohon ministan tattalin arziki a gwamnatin Morales ne ya ce akwai bukatar ya tabbatar da hadin kai a kasar.

    Ya fada wa wani taron manema labarai a Buenos Aires, babban birnin Argentina, cewa nan da wani dan lokaci ne zai koma Bolivia.

    Carlos Mesa, ya amince da shan kaye a zaben bayan da sakamako ya nuna Mista Arce ne ya samu gagarumar nasara.

  4. Yan sandan Faransa sun kama mutum 15 da zargin kisan malamin da ya nuna hoton ɓatancin Annabi SAW ga ɗalibai

    yan sandan faransa

    Asalin hoton, Getty Images

    Yan sandan Faransa da ke bincike kan kisan wani malamin makaranta sun kama mutum 15 a samamen da suke gudanarwa.

    Wata majiya ta bayyana cewa hudu daga cikin mutanen da aka kama yara ne da ake zargin mutumin da ya yi kisan ne ya biya su domin su nuna marigayi Samuel Paty, dan shekara 47.

    Firaministan Faransa ke nan ya ce muna yaki kuma za mu ci gaba da yaki da masu tsatstsauran ra'ayi. Daga safiyar yau, yan sanda sun dauki kwararan matakai kan masu tsatstsauran ra'ayi.

    Wani matashi ne ya kai wa marigayin hari a ranar Juma'ar data gabata a wajen makarantar da yake koyarwa da ke Paris.

    Ministan cikin gida na kasar ya ce ba za a ragawa makiyan Faransa ba.

  5. Kwankwaso ya bude sabon gidan rediyo a Kano

    Kwankwaso

    Asalin hoton, Premium Times

  6. Kotun Ƙolin Amurka ta amince da buƙatar Shugaba Trump ta taƙaita shigar baƙi

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Trump

    Kotun Ƙolin Amurka ta amince ta saurari wasu ƙararraki biyu da suka shafi kokarin Shugaba Trump na taƙaita baƙi daga Mexico.

    Kotun za ta saurari karar da gwamnati ta daukaka kan hukuncin wata karamar kotu cewa yin amfani da kudaden soji wajen gina katanga a kan iyakar kasar ya sabawa doka.

    Kotun Kolin ta kuma sanar da sake yin nazari kan ikon da gwamnati take da shi na tilastawa masu neman mafaka zama a Mexico har sai an yanke shawara kan bukatarsu.

    Ba a sa ran yanke hukunci a kararrakin biyu kafin watan Yunin badi.

  7. Labarai da dumi-dumi, Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

    Endsars
    Bayanan hoto, Mutane na cikin fargaba a birnin tarayyar

    Ana fargabar an samu asarar rayuka yayin zangar-zangar da ta koma tarzoma a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan banga ne suka kai hari kan masu jerin gwano a wasu sassan Abuja.

    An kuma yi ƙone-ƙonen dukiya da lalata ababen hawa yayin zanga-zangar.

    Abokin aikinmu Zahraddeen Lawan ya ziyarci daya daga cikin wuraren da lamarin ya afku wato rukunin shgunan Banex da ke Wuse a Abuja, kuma ya tabbatar da cewa ya ga kusan mutum huɗu a kwance magashiyyan a ƙasa.

    Sannan wasu rahoranni sun tabbatar da cewa a Unguwar Apo Mechanic ma an smu hargitsi tsakanin Hausawa masu sayar da kayan miya da ƴan ƙabilar Ibo masu gyaran motoci.

    Wata mazauniyar unguwar da ta dawo daga bulaguro da nufin isa gidanta, ta shaida wa BBC cewa dole ta sa ta juya ta koma cikin gari.

    ''Mun hango hayaƙi na tashi sannan an yi wa masu sayar da kayan miya da kayan marmari ɓarna sosai su kuma masu gyaran mota su ma an yi musu ɓarna an ƙona shagunansu.

    ''Na hango hayaƙi yana ci sakamakon ƙone-ƙone da aka yi. Dole ta sa muka juya don gudun kar abin ya rutsa da mu.''

    Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba dangane da lamarin.

    Sai dai mazauna birnin na cike da fargaba sosai na tsoron abin da ka je ya zo.

    Endsars
    Endsars
  8. #EndSARS: Masu kutse sun yi ikirarin toshe shafukan Intanet na bankunan First Bank da Access

    Wani mai kutse

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani mai kutse

    Wani mai kutse a shafukan Intanet da ke amfani da sunan @Litemods ya yi ikirarin cewa ya toshe shafukan Internet na manyan bankunan Najeriya da suka hada da First Bank da Access Bank.

    Wannan na zuwa ne sa'o'i bayan sanar da cewa ya karɓe ikon shafin Internet na kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

    Kungiyar masu kutsen ta ‘hacktivist’ ta ce wannan wani goyon baya ne ga masu zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin‘ yan sanda.

    Hare-haren masu kutsen da aka yi wa laƙabi da #OpNigeria sun janyo karɓe shafukan hukumomin gwamnati musaman a makon da ya gabata, amma wasunsu sun musanta.

    Jim kadan bayan masu kutsen sun sanar da karbe shafin Internet na kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, hukumar ta fito ta musanta, inda ta ce tana ci gaba da harkokinta a Intanet.

    Sannan ƙungiyar masu kutsen ta ce ita ce ta kutsa kamfanin Airtel, har ma ta riƙa raba wa masu amfani da layin kyautar katin naira dubu-dubu.

  9. Masu zanga-zanga sun rufe filin jrigin sama na Legas

    Filin jirgin saman Legas

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Filin jirgin saman Legas

    Masu zanga-zangar #EndSARS dake adawa da cin zalin 'yan sanda sun rufe filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Legas, abin da ya janyo tsayawar harkoki cak !

    Tun kusan karfe 9 na safe ne mutanen suka kakkafa shingaye tare da tare hanyar isa filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad, dalilin da yasa matafiya suka fara nemawa kansu mafita.

    Sun rika rera wakoki dauke da alluna masu rubutu dake kushe jami'an na 'yan sanda.

    Wani ma'aikaci a filin jirgin saman da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce mutanen basu kutsa harabar filin ba.

  10. Zanga-zangar #EndSARS : Gwamnan Edo ya kafa kwamitin bincike

    Gwamnan Edo Godwin Obaseki

    Asalin hoton, OBASEKI

    Bayanan hoto, Gwamnan Edo Godwin Obaseki

    Gwamnatin jihar Edo ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike game da zanga-zangar da ta haifar da rikici a jihar.

    Lamarin dai ya janyo gwamna Godwin Obaseki ya kafa dokar ta baci ta tsawon awa 24 wadda tuni ta fara aiki.

    Gwamnan ya ce kafa kwamitin wani bangare ne na biyan bukatun matasan da ke gudanar da zanga-zangar #EndSARS.

  11. An fake da zanga-zangar End Sars an saki fursunoni daga kurkukun 'yan sanda

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce mutanen Jaguda da suka fake da zanga-zangar #ENDSARS a birnin Benin sun saki fursunonin da ake tsare da su a wasu ofisoshin 'yan sanda da suka hadar da na Idogbo.da na kasuwar Oba da kuma wanda ke Ugbekun.

    Rundunar ta ce mutanen sun kuma yi awon gaba da bindigogi da harsasai.

    Ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter, sai dai babu wani karin bayani dangane da asarar da lamarin ya haifar.

    Rundunar ta kuma yi zargin cewa mutanen sun cinnawa ofisoshin 'yan sandan wuta.

    Ta kara da cewa yanzu haka tana yin dukkanin mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a fadin Najeriya baki daya.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  12. Masu zanga-zanga a Thailand sun yi shuri da dokar ta baci

    thailand zanga-zanga

    Asalin hoton, Reuters

    Masu zanga-zanga sun sake hallara a Bangkok, babban birnin Thailand yayin da gwamnati take barazanar rufe kafafen yada labarai.

    Masu zanga-zangar dai sun shafe tsawon kwanaki suna bijirewa umarnin gwamnati na haramta gudanar da taruka.

    Suna neman Firaministan kasar Prayuth Chan-ocha ya yi murabus sannan kuma a yi wa tsarin siyasar kasar garambawul wanda ya hada da masarautar wadda take da kariya daga suka a kasar.

    Wakilin BBC ya ce kari kan haramta gudanar da taruka, dokar ta bacin ta kuma haramta wa kafafen yada labarai wallafa duk wani abu da zai zama makarkashiya ga tsaron kasar.

    Domin dakile masu gangamin, jami'ai sun yi barazanar rufe wasu kafafen yada labarai guda hudu inda aka zarge su da yada labaran bogi.

    Firaministan ya kuma yi kira ga majalisa ta zauna domin tattauna halin da kasar ke ciki.

  13. Ɗalibai sun koma makarantu a Habasha

    Habasha

    Asalin hoton, Reuters

    An sake buɗe makarantu a Habasha yau Litinin bayan rufe su tsawon wata bakwai sakamakon annobar korona.

    Makarantun za su ci gaba da buɗewa sannu-sannu, yayin da ɗalibai mazauna ƙauyuka za su fara komawa.

    An rufe azuzuwan ne a watan Maris bayan ƙasar ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar. Habasha na son buɗe dukkanin makarantun nan da tsakiyar Nuwamba.

    Wasu iyayen na ɗari-ɗarin tura yaransu makarantun amma ma'aikatar ilimi ta ce tana duba damuwarsu tare da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar a makarantu.

  14. Bidiyo: Yadda Kanawa suka fito zanga-zangar #EndSARS ranar Litinin

    Bayanan bidiyo, Yadda Kanawa suka fito zanga-zangar #EndSARS ranar Litinin
  15. An harba wa masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye

    Abuja

    Asalin hoton, Channels TV

    'Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye a kan masu zanga-zanga a Abuja, a cewar rahoton gidan talabijin na Channels.

    'Yan zanga-zangar sun yi ƙoƙarin shiga Fadar Shugaban Ƙasa ta Villa ta ƙofar baya, yayin da 'yan sanda suka tare su a kan Titin John Kennedy.

    A yunƙurin tarwatsa su, 'yan sandan sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

    Kazalika, sojoji sun saka shingen duba ababen hawa a shahararren shataletalen A.Y.A da ke Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Hotunan zanga-zangar #EndSARS a Kano

    Kano
    Bayanan hoto, Matasa sun hau tituna a Jihar Kano domin yin zanga-zangar #EndSARS
    Kano
    Bayanan hoto, Zanga-zangar Kano ta ƙara ƙamari ne bayan an wayi garin Litinin da zargin 'yan sanda da kashe wani matashi a Unguwar Ƙofar Mata da ke ƙwaryar birnin
    Kano
    Kano
  17. Labarai da dumi-dumi, An saka dokar hana fita a Jihar Edo bayan ƙona ofishin 'yan sanda

    Gwamnatin Jihar Edo ta saka dokar hana fita tsawon awa 24 biyo bayan harin da aka kai wa 'yan sanda da kuma kuɓutar da fursunoni daga gidan yari a Benin, babban birnin jihar.

    Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Edo Osarodion Ogie ya fitar, ta ce dokar hana fitar "za ta ci gaba da kasancewa har baba ta gani".

    Ogie ya ce 'yan daba sun ƙwace iko da zanga-zangar #EndSARS kuma gwamnati "ba za ta zira ido ba yayin da ake kai hare-hare".

    Ya ce: "Dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe 4:00 na yammacin 19 ga watan Oktoban 2020. Wannan matakin ya zama dole saboda abubuwan da ke faruwa na ɓarna da hare-hare a kan mutane da ma'aikatu da sunan zanga-zangar #EndSARS.

    "Yayin da gwamnatin Edo take mutunta haƙƙin 'yan ƙasa na yin zanga-zangar lumana, ba za ta ƙyale 'yan daba su riƙa ɗaukar doka a hannunsu ba domin cuzguna wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da kuma jihar baki ɗaya.

    "Bisa wannan umarni, makarantu da wuraren kasuwanci za su kasance a rufe."

  18. An kai wa ofisoshin 'yan sanda hari a Edo, an kuɓutar da fursunoni

    Benin

    Asalin hoton, Others

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce an kai wa ofisoshinta guda uku hari tare da yin awon gaba da makamai a birnin Benin na Jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.

    Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna fursunoni na tsallake katanga daga wani gidan yari.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kazalika, maharan sun saki wasu da ake tsare da su a ofisoshin kafin daga bisani su cinna musu wuta, a cewar 'yan sanda.

    Ofisoshin da aka kai harin sun haɗa da Ugbekun Police Station da Oba Market Police Station da Idogbo Police Post, in ji rundunar, wanda aka kai a yau Litinin, 19 ga watan Oktoban 2020.

    "Rundunar na yin bakin ƙoƙarinta zuwa yanzu domin shawo kan lamarin da kuma kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa," a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  19. 'Yan daba sun jikkata masu zanga-zanga a Abuja

    Rahotanni na cewa 'yan daba sun kai wa masu zanga-zanga hari a kusa da Babban Bankin Najeriya da ke Abuja, babban birnin ƙasar, a daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.

    Hotuna da bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka ƙona wasu motoci cikin dare.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Ita ma ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International a Najeriya ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an jikkata masu zanga-zangar da dama a safiyar Litinin.

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    A ranar Lahadi wani mai suna Anthony Onome ya mutu a asibiti bayan wasu 'yan daba sun ji masa rauni da wuƙa yayin zanga-zangar a yankin Kubwa da ke birnin na Abuja.

  20. 'Yan daba sun mamaye wurin zanga-zangar #EndSars a Benin

    Zanga-zangar Benin

    Asalin hoton, Timothy Ojon

    Rahotanni daga birnin Benin na Jihar Edo ta kudancin Najeriya na cewa wasu tsageru sun mamaye zanga-zangar #EndSars.

    Wani ɗan jarida Timothy Ojon ya shaida wa BBC Pidgin cewa babu zirga-zirgar ababen hawa a safiyar yau Litinin a birnin.

    Zanga-zangar Benin

    Asalin hoton, Timothy Ojon

    "Suna ƙwace jakunkunan mutane da kuɗi tun daga yammacin Juma'a. Kusan ko'ina suna nan a Benin amma ya fi ƙamari a Ring Road, inda suke ƙona tayoyi," in ji Oyo.