An kammala shirya ɗakin da INEC za ta sanar da sakamakon zaɓe a Ondo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Ba gaskiya ba ne cewa an harbe ni - Matar Gwamnan Ondo
    • Ana zargin APC da sayen ƙuri'u a filin zaɓe
    • Komai na hannun Allah - Jegede na PDP ya faɗa wa BBC Hausa
    • Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya lashe rumfar zaɓensa
    • Gwamnan Ondo Akeredolu na APC ya lashe rumfar zaɓensa
    • Trump ya gabatar da jawabi a karon farko bayan ya warke daga korona

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai...

  2. Majalisar Dokokin Kyrgyzstan ta naɗa sabon Firaiminista

    Majalisar dokoki a Kyrgyzstan, ta naɗa ɗan siyasa mai kishin ƙasa da aka saki daga gidan yari a matsayin sabon Firaminista, tare da fatan hakan zai kawo ƙarshen tashin hankalin da ya dabaibaye ƙasar tsawon mako guda.

    Majalisar ta yi zaman gaggawa ne bayan zaɓen ranar Lahadi da ya haddasa rikici a ƙasar.

    Sabon Firaministan Sadyr Zhaparov, na daga cikin ƴan siyasa da dama da aka saki daga gidan yari a makon da ya gabata.

  3. Trump ya gabatar da jawabi a karon farko bayan ya warke daga korona

    ..

    Shugaba Trump na Amurka, ya gabatar da jawabi a gaban ɗaruruwan magoya bayansa a harabar Fadar White House, wanda hakan ke nuni da dawowarsa yaƙin neman zaɓe gadan-gadan, bayan ya yi kwana uku a asibiti a makon da ya gabata, sakamakon cutar korona da ya kamu da ita.

    Ya caccaki Joe Biden, abokin hamayyarsa inda ya ce zai mayar da Amurka ta yan gurguzu.

    Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya ce zai halarci gangami a Florida da Iowa a mako mai zuwa.

    Makonni uku kafin zaɓen Amurka, kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna Joe biden ne kan gaba fiye da Mista Trump a muhimman jihohin ƙasar.

  4. An kammala shirya ɗakin da INEC za ta sanar da sakamakon zaɓe a Ondo

    Hukumar INEC ta kammala shirya ɗakin da za ta sanar da sakamakon zaɓe, za a sanar da sakamakon ne bayan hukumar ta kammala karɓar sakamakon kowace ƙaramar hukuma ta jihar.

    Tuni dai 'yan jarida suka fara kafa kayan aikinsu a ɗakin.

    .
    ..
    ..
  5. Gwamna Makinde ya nuna takaici kan kisan Jimoh Isiaka a zanga-zangar #EndSarsNow

    ..

    Asalin hoton, @seyiamakinde

    Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Jimoh Isiaka, wanda aka harba yayin zanga-zangar neman soke rundunar SARS a Ogbomoso da ke jihar.

    A saƙon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan ya nuna takaicinsa kan kisan Jimoh, ya kuma ce mutum bakwai sun samu raunuka kuma tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

    Gwamnan ya ce ya tuntuɓi kwamishinan 'yan sandan jihar Nwachukwu Enwonwu, da sauran hukumomin da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike kan ainahin abin da ya faru.

  6. Iga Swiatek ta lashe gasar Roland Garros

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Matashiya ƴar wasan ƙwallon Tennis ta kasar Poland, Iga Swiatek, ta lashe gasar Roland Garros ta French Open ta mata a Paris - inda ta zama ƴar Poland ta farko da ta taɓa lashe babbar gasar Grand Slam.

    Matashiyar ƴar shekara 19, ta doke Sofia Kenin ta Amurka da ci shida da huɗu da kuma shida da ɗaya.

    Swiatek, ita ce ƙaramar ƴar wasa ta farko ta fuskar matsayi da ta lashe gasar French Open - ta fara gasar ne tana matsayi na 54 a duniya.

    A ɓangaren maza. a gobe ne za a fafata tsakanin gwanayen Tennis Rafeal Nadal da Novak Djokovic a wasan ƙarshe.

  7. Hotunan bikin yaye sojoji a Kaduna

    c

    Asalin hoton, NDA Public Relations Dept & Bayo Omoboriowo

    v

    Asalin hoton, NDA Public Relations Dept & Bayo Omoboriowo

    v

    Asalin hoton, NDA Public Relations Dept & Bayo Omoboriowo

  8. Zahra Buhari da Kiki Osinbajo sun shiga zanga-zanga

    ..

    Asalin hoton, ZAHRA BUHARI INSTAGRAM

    Iyalan Shugaban Najeriya da na mataimakinsa wato Zahra Buhari da Kiki Osinbajo, sun shiga zanga-zangar kawo ƙarshen azabtarwar da ake zargin 'yan sandan SARS ke yi a Najeriya.

    'Yar gidan Shugaba Buhari, wato Zahra, ta wallafa wani hoto a shafinta na Instagram, wanda masu gudanar da irin wannan zanga-zanga musamman a shafukan sada zumunta suke wallafawa na kawo ƙarshen 'azabtarwar'.

    Ita kuwa 'yar gidan Osinbajo, ta yi amfani da duka mau'du'an guda biyu, wato na #endpolicebrutality da kuma na #endsars, ma'ana tana goyon bayan kawo ƙarshen 'azabtarwar' da 'yan sanda ke yi da kuma soke rundunar SARS.

    ..
    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

  9. Labarai da dumi-dumi, Gwamnan Ondo Akeredolu na APC ya lashe rumfar zaɓensa

    .

    Ɗan takarar Jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya samu nasarar lashe rumfar zaɓensa inda ya samu ƙur'ia 413.

    Takwaransa na PDP Eyitayo Jegede kuma ya samu ƙuri'a 12, sai kuma Jam'iyyar ADP ta samu 9.

    .
  10. Buhari ya je wa iyalan 'Yar Adua ta'aziyya a Kaduna

    ..

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan Marigayi Janar Shehu Musa 'Yar'Adua a Kaduna domin yin ta'aziyya.

    Shugaban ya jajanta wa iyalan kan rasuwar surukar Marigayi Shehu Yar'Adua, wato Hajiya Rabi.

    A yau ne dai Shugaba Buharin ya je garin Kaduna domin halartar yaye ɗaliban soji a makarantar horar da sojoji ta NDA.

  11. Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Ivory Coast

    Dubban 'yan adawa ne suka taru a wani filin wasa da ke Abidjan, babban birnin Ivory Coast yayin da suke ci gaba da zanga-zanga kan shawarar da Shugaban ƙasar Alassane Ouattara ya yanke na sake tsayawa takara karo na uku.

    Masu zangar, waɗanda suka saka kaya irin launin tutar ƙasar, sun riƙe alluna da takardu inda suke cewa ba su yarda shugaban ya sake tsayawa takara ba.

    Mista Ouattara, wanda ya zama shugaban ƙasa a 2010 bayan wani zaɓe mai cike da rikici, ya bayyana cewa sauyin da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar a 2016 ya ba shi damar sake tsayawa takara a karo na uku.

  12. Fafutukar #EndSars ta zaburar da ‘yan Arewa kan matsalarsu

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Ƴan Najeriya musamman ƴan arewacin ƙasar sun jima suna ta kiraye-kiraye kan soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

    Sun kuma sha yin zanga-zangar lumana kan tituna, a wani lokacin kuma a kafafen sada zumunta inda suke amfani da mau'du'in #ENDSARS.

    Suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon zargin da suke yi wa rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa'ida ba da kuma saɓa ƙa'idojin aiki.

    Ga cikakken labarin a nan:

  13. 'Wasu na karɓar ladan kaɗa ƙuri'a'

    Cibiyar Ɓunƙasa Dimokuraɗiyya da Cigaba ta CDD ta ce ta ga wasu rukunin mutane na rubuta sunayensu domin karɓar ladan kaɗa ƙuri'ar da suka yi daga wata jam'iyya.

    Ta wallafan hakan ne a shafinta na Twitter.

    Ko a safiyar yau ma sai da ta wallafa wani hoto kan yadda ake sayen ƙuri'a a zaɓen jihar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Labarai da dumi-dumi, Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya lashe rumfar zaɓensa

    ..

    Asalin hoton, TWITTER/EYITAYO JEGEDE

    ..

    Ɗan takarar gwamna a zaɓen Ondo ƙarƙashin Jam'iyyar PDP Eyitayo Jegede ya samu nasarar lashe rumfar zaɓensa.

    Sakamakon da aka samu daga rumfar zaɓe ta tara da ke mazaɓa ta biyu a Gbogi Isikan, ya nuna cewa Jam'iyyar PDP ta samu ƙuri'u 220, sai APC mai mulki kuma 60, sai kuma jam'iyyar ZLP kuma ƙuri'a bakwai.

  15. Sakamakon zaɓe kai-tsaye

    Ondo

    Za ku iya bin sakamakon zaɓen kai-tsaye a wannan shafin idan INEC ta fara bayyana shi nan gaba.

    Ku latsa nan domin kewaya shafin kafin lokacin.

  16. Ana ƙirga ƙuri'u

    Kazalika, an fara ƙirga a Mazaɓar Isua Akoko rumfar zaɓe mai lamba 1, a cewar Cibiyar Dimokuraɗiyya da Cigaba ta Yammacin Afirka mai suna Centre for Democracy and Development (CDD West Africa)).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Labarai da dumi-dumi, An fara ƙirga ƙuri'u

    Ƙirgar ƙuri'u ta fara a mazaɓar Osisi rumfar zaɓe mai lamba 4 da ke Ƙaramar Hukumar Akure Ta Kudu.

  18. Ƙananan hukumomin da za su bai wa ɗan takara nasara

    Ondo

    Yayin da masu zaɓe ke kammala kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen gwamnan Jihar Ondo, INEC ta ce mutum 1,822,346 ne ke da rajistar kaɗa ƙuri'a daga ƙaramar hukuma 18 - kodayake dai ba duka ne za su yi zaɓen ba.

    Ƙananan hukumomin su ne: Akoko North East, Akoko North West, Akoko South East, Akoko South West, Akure North, Akure South, Ifedore, Ile Oluji/Okeigbo, Ondo East, Ondo West, Owo, Ilaje, Okitipupa, Ose, Odigbo, Ese Odo, Idanre da Irele.

    Sai dai, ƙaramar hukuma uku ne kawai ke da ƙarfin faɗa-a-ji idan ana maganar sakamakon da zai bai wa ɗan takara nasara.

    Akure Ta Kudu

    Akure Ta Kudu ce ƙaramar hukuma mafi girma a Ondo, inda take da yawan jama'a fiye da mutum 480,000 da kuma masu katin jefa ƙuri'a fiye da 280,000.

    Ondo Ta Yamma

    Ita ce ƙaramar hukuma ta uku a yawa, inda take da yawan masu kaɗa ƙuri'a sama da 150,000.

    Ƙaramar Hukumar Owo

    Gwamna Rotimi Akeredolu ya fito ne daga Owo kuma shi ne ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen na 2020.

    Owo na da yawan masu katin zaɓe fiye da 119,000. Ana ganin mazauna yankin za su zaɓi ɗansu.

  19. Komai na hannun Allah - Jegede na PDP ya faɗa wa BBC Hausa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyon

    Ɗan takarar jam'iyyar PDP mai adawa a zaɓen gwamnan Jihar Ondo, Eyitayo Jegede ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su ci zaɓe "amma komai yana hannun Allah".

    "Kana ganin za ku kai labari kuwa," Abdulbaƙi Jari ya tambaye shi.

    "Za mu ci amma duka yana hannun Allah ai. Babu damuwa," in ji shi.

  20. Buhari ya gana da sufeto janar kan 'yan sandan SARS

    Buhari da Sufeto Janar

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhamnadu Buhari ya gana da Sufeto Janar na 'Yan sanda Mohammed Adamu a daren Juma'a game da lalubo hanyoyin sauya fasalin rundunar 'yan sanda ta SARS.

    Ganawar tasu ta biyo bayan mako guda da aka shafe ana zanga-zanga a fili da kuma shafukan sada zumunta game da zarge-zargen take haƙƙi da jami'an rundunar ke yi, wadda ke yaƙi da 'yan fashi da manyan laifuka.

    Buhari wanda ya tabbatar da ganawar tasu a daren Juma'a, ya ce ana ba shi bayanai akai-akai game da matakan da ake ɗauka na kawo ƙarshen cin zarafin da 'yan sanda ke aikatawa.

    "Mun sake ganawa da Sufeto Janar a yau, bai kamata a ɗauki yunƙurimmu na tsaftace aikin 'yan sanda da wasa ba," in ji Buhari cikin wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    "Tuni na bai wa Sufeto Janar umarnin sauraron koke-koken 'yan Najeriya tare da tabbatar da cewa an hukunta duk 'yan sandan da suka aikata laifi."

    Shi ma Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya halarci ganawar.