Kungiyar Ipman ta mayar da farashin man fetur 162

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin karanta wasu labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kansu.

  2. Saudiyya ta fitar da wasu sharuɗa kan dawowa da zirga-zirgar jirage

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Saudiyya ta bayyana sharuɗa ga ƙasashe 25 da akwai yiwuwar ta amince jiragensu su ci gaba da zirga-zirga zuwa Saudiyyar.

    Mujallar Life in Saudi ta ruwaito cewa cikin sharuɗan har da tabbatar da duka fasinjojin da ke cikin jirgin da aka ɗauko ba su ɗauke da cutar korona.

    Kuma dole duka fasinjojin su killace kansu na mako guda idan suka shiga Saudiyyar.

    Haka zalika, dole kowane fasinja ya amince da cewa zai biya tarar riyal dubu 500 idan ya karya dokokin da aka saka da kuma zama gidan yari na shekaru biyu.

    Cikin ƙasashe 25 da aka aika wa sharuɗan har da Najeriya.

  3. Yadda tsadar rayuwa ta fara ƙure haƙurin wasu 'yan Najeriya

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton Ibrahim Isa kan tsadar rayuwa a Najeriya

    A Najeriya, `yan kasar da dama sun fusata sakamakon tsadar rayuwa, suna kokawa da yadda farashin man fetur da wutar lantarki ke karuwa.

    Tuni dai farashin kayan masarufi, irin su shinkafa da masara ya yi tashin-gwauron zabo.

    Ita ma ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta nuna rashin jin daɗinta game da wannan lamari, har ta fara tunanin daukar mataki.

    Yayin da wasu ma`aikata ke kukan ana zaftare masu dan albashin nasu, wasu kuma aikin ne ɗungurungum suka rasa, sakamakon annobar korona.

    Ana haka sai ga hukumar wutar lantarki ta yi ƙarin kuɗin wuta da kusan ninkin farashinta, kuma ko numfasawa `yan kasar ba su yi ba sai farashin litar man fetur ya tashi daga naira 148 zuwa dari 151.

    Kodayake kungiyar daillalan mai cewa ta yi idan ba ta sayar da lita a naira 162 ba za ta kwan-ciki.

  4. MINTI ƊAYA DA BBC - LABARAN YAMMA 02/09/2020

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron labaran
  5. Amurka ta saka takunkumi ga babbar mai shigar da ƙara ta kotun ICC

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Amurka ta saka takunkumi ga babbar mai shigar da ƙara a kotun aikata manyan laifuka ta duniya wato Fatou Bensouda.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana ICC a matsayin wata kotu da aka kafa bisa wata manufa daban.

    Ya kuma ce ICC na yi wa Amurkawa bita-da-ƙulli ta hanyar ci gaba da bincikar 'yan ƙasar kan zargin aikata laifukan yaki a Afghanistan.

    A yanzu gwamnatin Amurkar ta kwace duk wata kadara ta Ms Bensouda da kuma babban jami'in da ke aiki da ita Phakiso Mochochoko.

    Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta bayyana matakin gwamnatin a matsayin wani yunkuri na kauce wa hukunci.

  6. Sudan na tattaunawa da 'yan tawaye kan aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin rikon ƙwarya a Sudan Ta Kudu da 'yan tawayen da aka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su a kwanakin baya sun fara tattaunawa ta yadda za a fara aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma.

    Ana sa ran cewa yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyoyin 'yan tawaye biyar na ƙasar ƙarkashin inuwar Sudanese Revolutionary Front (SRF) za ta kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe shekaru 17 ana gwabzawa a yankin gabashin Darfur da kuma yaƙin da aka kwashe shekaru tara ana yi a kudancin Kordofan.

    Waɗanda suka rattaɓa hannu a yarjejeniyar sun haɗu ne a Juba babban birnin ƙasar inda suka amince kan burin nasu.

  7. Jam'iyyun adawa a Nijar sun ƙulla ƙawance

    ..

    Jam'iyyun adawa a Jamhuriyyar Nijar sun ƙulla kawance inda suka rataɓa hannu tare da saka wa ƙawancen suna CAP 2021, da niyyar fuskantar gwamnati a Jamhuriya ta bawaki a ƙasar.

    Wannan ƙawance dai ya zo ne bayan kiran da madugun adawa a ƙasar Hama Amadou ya yi na cewa lokaci ya yi da za su fito su yi gwagwarmaya don kawo ƙarshen wariyar siyasa da ya ce ake yi cikin kasar.

  8. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 15 a Sokoto

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An tabbatar da mutuwar mutum 15 sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta faru a wasu ƙananan hukumomi shida a jihar Sokoto.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar wato NEMA inda ta ce sama da mutum 27,000 wannan bala'i ya shafa.

    Ƙananan hukumomin da bala'in ya shafa sun haɗa da Goronyo da Rabah da Arewacin Sokoto da Wamakko da Silame da Binji.

    Rahoton da jaridar ta samu daga hukumar ya nuna cewa mutum 5,254 sun rasa muhallansu inda wasu mutum 12 kuma suka samu raunuka sakamakon rugujewar gine-gine.

  9. Buhari ya jajanta wa al'ummar Kebbi

    Kebbi

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan ambaliyar ruwan da ta yi ajalin rayuka ta kuma shafe gonaki.

    Shugaban ya ce ya damu sosai kan matsalar ta ambaliya saboda ta mai da hannun agogo baya a yunkurin gwamati na bunkasa noman shinkafa a cikin gida da nufin hana shigar da abinci kasar daga kasashen waje.

    Buhari ya ce asarar rayuka shida da aka yi - da kuma har yanzu ba a gama tantance yawan wadanda suka mutu ba, da dubban kadada da ruwa ya mamaye da kuma asarar da manoman shinkafa suka yi ta akalla fiye da Naira biliyan guda, wasu alamu ne dake nuna gagarumin koma baya wajen bunkasa noman abinci.

    A wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya ce labarin da ya fito daga Kebbi ba mai dadi ba ne, kuma ya zo a lokacin da tasirinsa zai fi kowanne muni.

    Buhari ya jajanta wa iyalan da suka suka rasa danginsu da kuma manoman da suka yi asara, sannan ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki da gwamnatin jihar Kebbi wajen taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa.

  10. Ethiopia za ta yi gagarumin rabon burodi kyauta

    Sheger Bread

    Asalin hoton, Sheger Bread

    Hukumomi a kasar Habasha sun yi shirin raba dubban kunshin burodi kyauta a Addis Ababa babban birnin kasar, a wani bangare na murnar shiga sabuwar shekarar kasar ta 2013.

    Za a raba burodin ne a ranar Litinin 7 ga Satumba, a ranar farko ta bikin da za a kwashe kwanaki biyar ana gwangwajewa a watan karshe na shekarar ta Habasha ko kuma Ethiopia.

    A watan Yulin da ya wuce ne gwamnati ta kaddamar da wani katafaren gidan burodi a wajen babban birnin kasar.

    Hukumomi sun ce za a iya gasa matsakaicin burodi miliyan biyu a kowace rana a gidan.

    Wani jami'in gwamnati ya yada bidiyon yadda ake aiki a gidan burodin na Sheger lokacin kaddamar da shi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Kungiyar IPMAN ta mayar da farashin man fetur 162

    IPMAN

    Asalin hoton, Others

    Kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta kasa IPMAN, ta umarci 'ya'yanta su kara kudin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

    Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.

    Wata sanarwa da reshen kungiyar na shiyyar kudu masu yamma ya fitar ta ce ba su da wani zabi illa su kara kudin man domin gudun kada su yi asara.

    Shugaban kungiyar ta Ipman reshen Kano mai kula da wasu jihohin arewacin Najeriya Alhaji Bashr Dan Malam ya ce dole ne su yi karin, domin cike fansshe karin da za su samu daga wajen da suke sayo man fetur din sakamakon matakin gwamnati na mayar da fetur din N151.56k.

    Wannan ne karo na uku da gwamnati take sauya farashin mai a 'yan watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu lokutan da ake rage farashin, karin na man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan nan.

  12. Isra'ila ta yi tur da danne wuyan Bafalasdine da wani sojanta ya yi

    Khairi Hanoon said he was detained at a peaceful protest, but Israel's military called it a violent riot

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Khairi Hanoon ya ce an kama shi ne a yayin wata zanga-zangar lumana, amma sojojin Isra'ila sun ce ta tarzoma ce

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana yin duba kan lamarin da ya faru wanda aka dauki bidiyon wani soja ya danne wuyan wani Bafalasdine da gwiwar kafarsa, yayin da mutumin ke kwance a kasa hannayensa cikin ankwa a yayin wata zanga-zanga a Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.

    Bidiyon ya nuna yadda sojan ya danne Khairi Hanoon, wani fitaccen mai fafutuka mai shekara 60 da 'yan kai a kasa.

    Daga nan sai sojan ya sanya giwarsa ya danne wuya da kan mutumin na kusan dakika 50.

    Lamarin ya jawo yin tur da Allah-wadai daga Falasdinawa, amma rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun sun yi hakan ne don shawo kan lamarin da ke neman rincabewa.

    Ta ce bidiyon bai nuna abin da ya faru gaba daya ba, don bai nuna yadda masu zanga-zangar suke tunkara da jifan sojojin ba, dalilin da har ya kai su ga kama mutane.

  13. Ba mu fitar da sunayen ɗaliban da aka bai wa tallafin karatun ƙasar waje ba - Ma'aikatar Ilimin Najeriya

    Jerin sunayen da ke yawo a intanet na ɗaliban Najeriya da aka bai wa tallafin karatun ƙasar waje ba na gaskiya ba ne, a cewar Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya.

    An fara yaɗa jerin sunayen da ke yawo ne daga wata wasiƙa da aka ce wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar waje ne ya rubuta wa Ministan Ilimi Adamu Adamu domin yin ƙorafi game da yadda ake bayar da tallafin karatun.

    Me ƙorafin ya yi zargin cewa abin kunya ne ga arewacin Najeriya a cikin wasiƙar da aka yi wa take da JUSTICE TO ONE IS JUSTICE TO ALL wato YIN ADALCI GA MUTUM ƊAYA ADALCI NE GA AL'UMMA BAKI ƊAYA.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasiƙar na cewa a jerin sunayen, mutum 21 ne kawai suka fito daga jihohin arewa 19, yayin da jihohin kudu suka samu mutum 70.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan zumunta, Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya ta ce har yanzu ba ta saki sunayen waɗanda aka bai wa tallafin karatun ƙasar wajen ba na 2020 ƙarƙashin shirin 2020 Bilateral Education Agreement.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Labarai da dumi-dumi, Guba aka saka wa jagoran 'yan adawar Rasha

    Ƙasar Jamus ta ce an saka wa jagoran 'yan adawar Rasha, Alexei Navalny gubar Novichok.

    Gwaji ya nuna akwai "hujja ƙarara" cewa an saka masa guba ta rukunin Novichok.

    An kai Mista Navalny birnin Berlin na Jamus don duba lafiyarsa bayan ya yanke jiki ya faɗi a cikin wani jirgi a watan da ya gabata.

    Tun daga wannan lokaci yake a sume.

  15. Cristiano Ronaldo ya cashe da waƙar Jerusalema

    Ɗan ƙwallo Cristiano Ronaldo ya zama tauraro na baya-bayan nan da ya tallata waƙar Master KG ta Jerusalema.

    Mawaƙin ɗan ƙasar Afirka ta Kudu ya gode wa Ronaldo a shafinsa na Twitter.

    Ronaldo ya wallafa wani bidiyo ne mai tsawon minti huɗu a Instagram ana cashewa da waƙar kuma ya rubuta: "Rayuwa ta fi daɗi da masoya❤️ Ku ji daɗi tare da masoyanku cikin nishaɗi."

    Waƙar ta Jerusalema wadda ta addinin Kirista ce, ta karaɗe Nahiyar Afrika da wajenta.

  16. Wani da korona ta kashe 'yan uwansa bakwai za a yi gwajin rigakafin cutar a kansa

    Jacob Serrano na da dalili mai ƙwari sama da kowa domin taimakawa wurin samar da rigakafin annobar cutar korona saboda ta kashe 'yan uwan matashin har guda bakwai.

    Jacob mai shekara 23 na cikin wani rukunin 'yan sa-kai da za a yi gwajin rigakafin cutar a kansu.

    Yana cikin mutum 31 'yan Amurka da aka yi wa ragakafin a Florida a ƙarshen makon da ya gabata yayin gwajin maganin a mataki na ƙarshe.

    "Na san cewa akwai hatsari saboda kamar gwaji ne," in ji shi a cikin wata hira da kafar CBS News. "Amma na gwammace na bayar da gudummawata ko ma mene ne zai faru."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Ƙungiyar Kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya soke dokar CAMA

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya soke dokar CAMA wadda ya saka wa hannu ranar 7 ga watan Agusta.

    Dokar mai suna Companies and Allied Matters Act (CAMA) 2020, ta tanadi cewa shugaban hukumar kula da kuma bai wa kamfanoni lasisi ta Corporate Affairs Commission (CAC) zai karɓe ragamar duk wata ƙungiyar addini idan har aka tabbatar akwai rashin gaskiya a shugabancin ƙungiyar.

    Kazalika dokar ta bai wa CAC ikon dakatar da kwamitin amintattun ƙungiyar addini sannan ta naɗa shugabannin riƙo idan ta aminta cewa ba a gudanar da ayyukan ƙungiyar yadda suka dace ko kuma akwai almundahana.

    Jaridar TheCable ta ruwaito shugaban ƙungiyar yana bayyana matsayinsu a cikin wata wasiƙa da ya aike wa mai bai wa Buhari shawara kan Majalisar Dattawa ranar Talata.

    Ƙungiyar ta haƙiƙance cewa ba a tuntuɓi waɗanda ya abin ya shafa ba kafin amincewa da dokar.

    "Muna kallon wannan doka a matsayin wani kundi mai cike da batutuwan da za su kawo tarnaƙi ga tsaro da jin daɗin Najeriya," CAN ta bayyana a wasiƙar.

  18. Kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na amfani da intanet

    Facebook

    Asalin hoton, Getty Images

    Farfesa Umar Danbatta, shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ya ce masu amfani da layin wayar salula a Najeriya sun ƙaru zuwa milyan 199.3.

    An samu ƙaruwar ne daga miliyan 184 a watan Disamban 2019 zuwa Mayun 2020.

    Dambatta ya bayyana haka ne yayin miƙa lamunin kuɗi da NCC ta bai wa wasu cibiyoyin sadarwa biyu da za su gudanar da bincike kan annobar korona ranar Talata, wanda ya gudana ta intanet.

    Ya ƙara da cewa masu amfani da intanet ma sun ƙaru a tsawon wannan lokacin daga miliyan 126 zuwa 147.1, yayin da masu sayen layin intanet a dunƙule wato broadband suka ƙaru daga miliyan 72 zuwa 80.2.

    Kasancewar Najeriya na da al'umma kusan miliyan 200, hakan na nuna cewa kashi biyu cikin uku na 'yan ƙasar na amfani da intanet.

    "Irin waɗannan [bincike] za su taimaka wurin samar da yiwuwar gudanar da taruka ta intanet da za su riƙa samar da tazara [tsakanin mutane]," in ji shi.

  19. 'Yan adawar Venezuela sun yarda su shiga zaɓen ƙasar

    Turkiyya da ke sasanta rikicin siyasar Venezuela ta ce biyu daga cikin fitattun jagororin 'yan adawar ƙasar sun amince su shiga zaɓen da za a yi na watan Disamba.

    Ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Kavusoglu ya ce Henrike Kapriles da Stalin Gonzalez sun nemi a bai wa masu sanya ido na ƙasashen waje damar duba yadda zaɓen zai gudana.

    'Yan adawa dai sun ki shiga zaɓen, kana sun zargi shugaba Nicolas Moduro da ƙoƙarin yin maguɗi.

    Kwanan nan ne shugaban ya yafe wa ɗaruruwan 'yan hamayya da suka shafe watanni a garƙame, domin ba su damar tsayawa takara idan suna da ra'ayin yin hakan.

  20. PSG na son Bellerin, Chelsea ta sanya farashi kan Kante, Juve na zawarcin Suarez

    Bellerin

    Asalin hoton, Getty Images

    Paris St-Germainta yi tayin biyan £25m da kuma ƙarin £5m kuɗin talla kan ɗan wasan Arsenal Hector Bellerin, a yayin da Bayern Munich da Juventus su ma suke zawarcin ɗan wasan na Sufaniya mai shekara 25.(Guardian)

    Everton ta amince ta ɗauko ɗan wasan Colombia James Rodriguez, 29, daga Real Madrid a kwangilar shekara uku.(Telegraph)

    Chelsea za ta sayar da N'Golo Kante kan £80m a yayin da Inter Milan take zawarcin ɗan wasan na Faransa mai shekara 29.(Express)

    Sai dai tsohon ɗan wasan Leicester Kante yana son ci gaba da zama a Chelsea.(Goal)