Ƙasashen duniya sun kashe kusan tiriliyan 10 kan cutar korona – IMF

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau Alhamis a wannan shafi.

  2. Ƙasashen duniya sun kashe kusan tiriliyan 10 kan cutar korona – IMF

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce gwamnatoci a faɗin duniya sun kashe kusan tiriliyan 10 wurin neman mafita game da rugujewar tattalin arziki da annobar korona ta haifar.

    Babbar manajar asusun Kristalina Georgieva ta ce akwai bukatar kara yin hubbasa wurin ganin an rage rashin ayyukan yi.

    Ms Georgieva ta yi gargaɗin cewa kusan mutun miliyan 100 ne za su iya faɗawa mummunan talauci saboda annobar.

    A kan haka ta bada shawarar cewa akwai buƙatar zuba jari kan harkar lafiya da ilimi da kuma kare muhalli.

    Ms Georgieva ta ce ya kamata a fito da hanyoyin kare kananan sana'o'i.

  3. An kama wasu 'yan sanda a Kenya bayan sun ja wata mata a ƙasa

    An kama wasu 'yan sanda uku a Kenya bayan wani bidiyo ya nuna su suna cin zarafin wata 'yar shekara 21 ta hanyar janta a ƙasa bayan sun ɗaure hannuwanta a jikin babur.

    An kuma nuna wani dan sandan yana dukanta da bulala yayin da take rokonsu da su sake ta.

    Matar da a yanzu ke jinya a asibiti ta samu karaya, kuma ana zarginta ne da satar tukunyar gas, abin da tuni ta musanta.

    'Yan sanda a Kenya na shan suka kan cin zarafin al'umma.

    Wata kungiyar masu fafutuka ta ce jami'an tsaron sun kashe a kalla mutane sha biyar a lokacin kullen annobar Korona.

    .
  4. Korona: Kasuwanci tsakanin ƙasa da ƙasa zai ragu

    Hukumar ci gaban kasuwanci ta Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta ce annobar korona za ta sa kasuwancin ƙasa da ƙasa ya ragu da kashi 27 cikin 100 nan da yan watanni.

    Hukumar ta ce za a samu a kalla faɗuwa da kashi 20 cikin 100 a kasuwancin duniya zuwa ƙarshen shekara matuƙar abubuwa basu canza ba.

    Ta kuma ta'allaka matsalar kan durƙushewar masana'antar ƙera motoci da kuma makamashi.

    To amma hukumar ta UNCTAD ta ce fannin kayan gona bai samu irin wannan matsala ba.

  5. Hotunan zaman Majalisar Dattawan Najeriya a yau

    ...

    Asalin hoton, @NGRSenate

    ..

    Asalin hoton, @NGRSenate

    ..

    Asalin hoton, @NGRSenate

  6. MDD na so a yi bincike kan kashe-kashen da aka yi a Libiya

    .

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da bincike kan kashe-kashen da aka gudanar ba bisa ka'ida ba a yankin da Janar Khalifa Haftar ke da iko da shi a Libiya.

    MDD da ke aiki a Libiya ta bayyana damuwarta matuƙa dangane da wasu ƙaburbura takwas da aka binne mutane da dama a cikinsu inda akasarinsu a garin Tarhouna.

    MDD ta bayyana cewa ta samu rahotanni da dama kan sata da kuma lalata gidajen mutane a yankin inda ake ganin wasu hare-haren an yi su ne na ramuwar gayya.

  7. Majalisar Dattawan Najeriya ta amimnce da kasafin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima

    Sanata Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima saboda annobar korona.

    Majalisar ta amince da naira tiriliyan 10.8, sai dai ta sauya ɓangarori da dama, inda suka ƙara yawan kasafin a ma'aikatu ba kamar yadda Buhari ya gabatar musu ba a ƙarshen watan Mayu.

    An samu ƙarin naira biliyan biyar (N5,256,207,430) a kan wanda Buhari ya miƙa musu tun farko - yanzu ya zama naira tiriliyan N10,810,800,972,72 maimakon ‪N10,805,544, 664,642.

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage yawan kasafin ne sakamakon halin da annobar korona ta jefa tattalin arzikinta.

    Hukumomi da ma'aikatun da sauyin ya shafa:

    • Hukumar Tsarin Ilimin Bai-Ɗaya: N816,517,124
    • Ma'aikatar Lafiya a Matakin Farko: N897,641,688
    • Hukumar Ci Gaban Yankin Arewa Maso Gabas: N816,517,124
    • Hukumar Ci Gaban Neja-Dalta: N1,743,411,240
  8. Yau za a ci gaba da gasar La Liga

    La Liga

    Asalin hoton, Getty Images

    Da ƙarfe 9:00 agogon Najeriya da Nijar za a ci gaba da wasanni a gasar La Liga mako na 28 bayan kwana 95 da dakatar da ita saboda annobar korona.

    Za a fara da wasan hamayya ne tsakanin Sevilla da Real Betis a filin wasa na Estadio Ramon Sanchez da ke Sevilla kuma za mu kawo muku shi kai-tsaye a shafinmu.

    Ana ganin wasan zai yi zafi sosai kodayake dai ba 'yan kallo za a yi shi.

  9. Labarai da dumi-dumi, Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya ranar Juma'a

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi a gobe Juma'a wadda ita ce ranar dimokradiyya a ƙasar

    A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na shugaban Femi Adesina ya fitar, shugaban zai yi jawabin ne ta kafar talabijin ta ƙasar wato NTA da kuma kafar rediyo ta ƙasar FRCN.

    Shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na safe.

    Wannan ne karo na biyu da za a yi bikin ranar dimokradiyya a ranar 12 ga watan Yuni.

    A baya dai ana bikin ranar dimokradiyya ne a ranar 29 ga watan Mayu.

  10. Hannayen jari sun faɗi warwas a Amurka

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Hannayen jari sun faɗi warwas a Amurka sakamakon tunanin da ake yi na sake ɓarkewar cutar korona karo na biyu.

    Hukumar da ke kula da asusun ko ta kwana na gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta tallafa wa tattalin arziƙin ƙasar na wasu shekaru masu zuwa.

    Shugaban hukumar, Chair Jerome Powell ya yi gargaɗin cewa akai lokaci mai zuwa da zai yi wuya mutane su samu aikin yi.

    Alƙaluman baya-bayan nan a Amurka sun nuna cewa kusan mutum miliyan 1.5 sun rasa aikin yi a Amurka a makonnin da suka gabata.

  11. Majalisa ta amince da Monica a matsayin Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara

    .

    Asalin hoton, MONICA DONGBAN-MENSEM

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya.

    Monica ta fara shugabancin Kotun ne bayan ritayar da Zainab Bulkachuwa ta yi wacce ita ce tsohuwar shugabar kotun.

    A kwanakin baya ne dai Shugaba Buhari ya ƙara wa'adin kujerar da Monica take a kai na rikon ƙwarya.

    A yanzu haka Mai Shari'a Monica ta zama mace ta biyu da ta shugabanci Kotun Daukaka kara ta Najeriya.

    Monica Dongban-Mensem 'yar asalin Jihar Filato ce, kuma ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu kafin yanzu.

    Ta yi karatun digirinta na farko da na biyu a bangaren shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.

    Tarihin Rayuwar Monica Dongban-Mensem a takaice:

    • An haifi Monica Bolna'an Dongban-Mensem ranar 13 ga watan Yunin 1957
    • A garin Dorok na Karamar Hukumar Shendam aka haife ta
    • Tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu
    • Marubuciyar littafin The Defendant a shekarar 1991
    • A Jami'ar Ahmadu Bello Zaria ta yi digiri na farko da na biyu
    • Ta yi difiloma a cibiyar Advanced Legal Studies, ta Jami'ar London, Russel Square
    • Tsohuwar mai shari'a ce a kotun Abuja
    • Tsohuwar rijistira a Babbar Kotun Jihar Filato a shekarar 1979
    • Tsohuwar malama a cibiyar Catholic Media Centre da ke Kaduna
    • Tsohuwar malama a Jami'ar Jos
    • Ta kafa gidauniyar Pa William Mensem Education
  12. Labarai da dumi-dumi, Kaduna: An saka dokar hana fita a Zangon Kataf kan rikicin ƙabilanci

    Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun kafa dokar hana fita ta tsawon awa 24 a Masarautar Atiyep da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf da Masarautar Chawai a Ƙaramar Hukumar Kauru.

    Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Alhamis ta ce hakan ya biyo bayan wani rikici mai nasaba da ƙabilanci tsakanin Hausawa da 'yan ƙabilar Atiyep kan wata gona.

    Rahotanni sun ce lamarin ya kai ga matasa rufe hanyoyin mota.

    Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan wanda yanzu haka yake yankin, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce al'amura sun lafa.

  13. An kori janar ɗin soja a Chadi bayan ya soki shugaban ƙasa

    Chadi

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin ƙasar Chadi ta kori Janar Ahmat Koussou Moursal daga aiki bayan ya rubuta wata wasiƙa yana sukar Shugaba Idriss Deby.

    Gwamnati ta ce ba za a bai wa janar ɗin wani kuɗin sallama daga aiki ba amma ba ta faɗi dalilinta na yin hakan ba.

    A cikin wasiƙar, Janar Moursal ya zargi Idriss Deby da yin watsi da tsofaffin abokan aikinsa sojoji na yankin Guera, wani gari da ke kudu maso gabashin Chadi.

    Kazalika ya zargi gwamnati da ƙin biyan diyya ga waɗanda gwamnatin tshohon shugaban ƙasa Hissene Habré ta ci zarafinsu.

  14. Mutum 3,717 sun kamu da korona a Saudiyya cikin kwana ɗaya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya ta bayar da rahoton adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar korona cikin kwana ɗaya tun bayan ɓarkewarta a ƙasar, inda birnin Riyadh kaɗai yake da mutum 1,317.

    Sabbin mutum 3,717 ne suka kamu da cutar ranar Laraba, a cewar kamfanin dillancin labaran ƙasar na SPA wanda kuma jaridar Saudi Gazette ta rawaito.

    Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya Dr. Muhammad Al-Abdel Ali ya ce akwai sabbin mutum 36 da suka rasu, sai kuma 1,615 da suka warke daga cutar.

    Yanzu jumillar adadin waɗanda suka kamu da cutar ya zama 112,288.

  15. Koriya ta buƙaci Amurka ta fita harkarta idan tana son gudanar da zaɓe lafiya

    Trump da Kim Jung Un

    Asalin hoton, Getty Images

    Koriya Ta Arewa ta bukaci Amurka ta tsame kanta daga harkokin kasashen Koriya biyu matukar Amurkan na son zaben shugaban kasarta da za a yi bana ya tafi yadda ya kamata.

    Lamarin na zuwa ne bayan Amurkar ta ce ba ta ji dadin yadda Koriya Ta Arewa ta dakatar da hanyoyin sadarwa da Koriya Ta Kudu ba.

    Wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewan KCNA ya fitar ta ce ya kamata Amurka ta yi gum tare da mayar da hankali kan magance matsalolinta na gida, idan dai ba so take ta gamu da abin da zai daga mata hankali ba.

  16. Labarai da dumi-dumi, An dakatar da Dele Alli daga buga wasa saboda saƙonsa kan cutar korona

    Dele Alli

    Asalin hoton, Getty Images

    An dakatar da ɗan wasan tsakiyar Tottenham, Dele Alli, wasa ɗaya sakamakon wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta kan cutar korona.

    Hukumar FA ta dakatar da Alli mai shekara 24 bayan ya wallafa bidiyo a dandalin Snapchat a watan Fabarairu game da cutar korona sannan ya yi wa wani ɗan asalin Nahiyar Asiya ba'a.

    Haka ma an ci tarar ɗan ƙasar Ingilan fan 50,000 kuma aka umarce shi da ya zauna a ajin wayar da kai a makaranta.

    Hakan na nufin ba zai buga wasan da Tottenham za ta fafata da Manchester United ba ranar 19 ga watan Yuni a gidanta.

    Mutum sama da 416,000 ne suka mutu sakamakon annobar a faɗin duniya.

  17. An rufe makaranta 31 a Afirka ta Kudu saboda korona

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu makarantu har 31 sun kulle a yankin Eastern Cape na Afirka ta Kudu saboda cutar korona, a cewar kafar yaɗa labarai ta gwamnatin ƙasar.

    Kafar South African Broadcasting Corporation ta ce malami 15 da ɗalibi biyu da wasu ma'aikata sun kamu da cutar korona.

    Mai magana da yawun sashen ilimi na yankin, Loyiso Pulumani, ya ce an rufe wasu makarantun ne saboda a yi musu feshi.

    Ya ce an faɗa wa makarantu abubuwan da ya kamata su yi idan aka rufe makarantunsu don yin feshi kuma za su sake buɗewa bayan 'yan kwanaki.

    Yankin Eastern Cape ne ke da adadi na biyu mafi yawa na waɗanda suka harbu da cutar.

  18. British Council ta kammala bikin cika shekara 75 da kafuwa a Najeriya

    British Council

    Asalin hoton, British Council

    Hukumar raya al'adu ta Birtaniya - British Council - ta kammala bikin cika shekara 75 da fara ayyukanta a Najeriya.

    British Council

    Asalin hoton, British Council

    Bikin wanda ta yi wa laƙabi da “Thanks to You”, an shafe shekara guda ana yinsa kuma British Council ta ce ta shirya shi ne domin taya waɗanda suka ci gajiyar shirye-shiryenta murna a tsawon waɗannan shekaru.

    British Council

    Asalin hoton, British Council

    An kafa hukumar British Council a shekarar 1944 a Najeriya da zummar raya al'adun Birtaniya a ƙasar tare da bai wa 'yan Najeriya tallafin karatu da na tattalin arziki da na zamantakewa.

  19. Lufthansa zai kori mutum 22,000 daga aiki

    Lufthansa yana da ma'aikata fiye da 135,000 a fadin duniya

    Asalin hoton, DEFODI IMAGES / GETTY IMAGE

    Kamfanin jirgin saman Lufthansa na kasar Jamus ya ce zai sallami mutum 22,000 daga aiki a yayin da yake fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon annobar korona.

    Kamfanin ya ce ya yi hasashe zai fuskanci tafiyar hawainiya yayin farfadowa daga matsalar tattalin arziki kuma yana sa ran zai rika amfani da jirage kasa da 100 bayan annobar.

    Lufthansa ya kara da cewa rabin ma'aikatan da zai kora daga aiki a kasar Jamus suke. Yana sa ran kulla yarjejeniya da kungiyar kwadago kan matakan sallamar mutanen daga aiki ya zuwa ranar 22 ga watan Yuni.

    "Makasudin yin hakan shi ne a kare ayyuka da dama daga rushewa a Lufthansa Group," in ji kamfanin.

    Lufthansa yana da ma'aikata fiye da 135,000 a fadin duniya. Kusan rabinsu suna Jamus.

  20. 'An tuhumi sojojin Kamaru uku da laifin kisa'

    An tuhumi sojojin Kamaru uku bisa laifin kisan kan a yankin Arewa maso Yammacin kasar a watan Fabrairu, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

    Da farko hukumomin kasar sun musanta hannun soji a kisan farar hula 13, cikinsu har da yara 10 a garin Ntumbo, amma a watan Afrilu fadar sugaban kasar ta amince cewa sojoji uku da 'yan bijilante sun kai samame a yankin 'yan a-waren kasar.

    Ta ce ba da gangan aka yi kisan ba ko da yake sojoji sun yi yunkurin yin rufa-rufa kan kisan.

    Gwamnatin Kamaru ta kwashe sekara uku tana kai ruwa rana da masu fafutukar ballewa daga kasar da ke yankin masu magana da turancin Ingilishi.

    AFP ya ambato mai magana da yawun rundunar sojin kasar Kanar Cyrille Atonfack Guemo yana cewa: "An daure sojojin Kamaru uku a gidan yarin sojoji da ke Yaounde."

    Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images