Ganduje ya amince a yi Sallar Juma'a da Idi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku na yau Litinin.

    Ga kanunsu:

    • An kashe 'yan Boko Haram 20 a Borno
    • An kama babbar mai tace labaran jaridar intanet a Egypt
    • Gwamnatin Najeriya ta kama jirgi mai 'fasa-kaurin jama'a zuwa cikin kasar'
    • An sallami karin mutum 20 da suka warke daga korona a Bauchi
    • 'Yan majalisa sun bai wa hammata iska a Hong-Kong
    • Jihar Kano za ta mayar da almajirai 2000 jihohinsu
    • Ambaliyar ruwa ta raba mutum 400,000 da muhallansu a Somaliya
    • Ganduje ya amince a yi Sallar Juma'a da Idi

    Ku je kasa don karanta karin labarai.

    Kada ku manta za ku iya bibiyarmu a shafukan sada zumunta da muhawara inda za ku tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.

    Mu kwana lafiya.

  2. Fifa za ta haɗa wasan samar da kuɗi don yaki da korona

    'Yan wasa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Fifa na shirin hada wani wasan da za a buga domin samun kudin da za a yaki cutar korona da su.

    Shugaban Hukumar Gianni Infantino, ya ce za a buga wasan ne lokacin da yanayin tsarin lafiyar duniya ya ba da dama.

    "Karin bayanan da suka shafi wasan za su hadar da wurin bugawa da rana, da wadanda za su buga wasan da yadda za a buga shi za a sanar da shi anan gaba, in ji Youri Djorkaeff, shugaban gidauniyar Fifa.

    Tsohon dan wasan tsakiyar na Faransa ya kara da cewa: “Ana duba yiwuwar aiwatar da matakai da dama a halin yanzu, duka da zummar mayar da hankali kan arkokin lafiya da kuma tsare-tsare na gwamnatoci daban-daban da kuma cibiyoyin kasashen duniya.”

  3. Ambaliyar ruwa ta raba mutum 400,000 da muhallansu a Somaliya

    BBC

    Ambaliyar ruwa a Somaliya ta shafi kimanin mutum miliyan daya, yayin da ta tilasta wa sama da 400,000 barin muhallansu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

    Ofishin kula da al'amuran jinkai na Majalisar Dinkin Duniyan ya ce mutum 24 sun mutu.

    Ya kuma kara da cewa akwai fargabar barkewar cuta saboda cakuduwar mutane wuri daya a tantunan wucin gadi.

    In da ambaliyar ta fi shafa shi ne Beledweyne, wanda kusan kashi 85 cikin 100 na yankin, kogin Shabelle ya yi awan gaba da shi a makon jiya.

    "Ambaliyan ta shafi ko ina na birnin, mutane a firgice suke da lafiyarsu," kamar inda wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    "Dakarun gwamnati na taimaka wa mutane, amma wadanda suka tsufa da masu rauni na bukatar karin taimakao, saboda ba za su iya tafiya a cikin ruwan ba saboda karfinsa."

  4. Ganduje ya amince a yi Sallar Juma'a da Idi

    Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya aminci da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma'a da kuma Idi.

    Sanarwar da Salihu Tanko Yakasai, mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan ya bayar da umarjin bayan ya tattauna da wakilan Malamai su 30 da kuma wasu jami'an gwamnatinsa ranar Litinin.

    Sai dai ya ce ba za a bari mutane su yi shagulgula ba lokacin Sallar Idi. yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da dokar kulle.

    "An umarci Malaman Masallatan Juma'ah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso", sanarwar.

    Gwamnatin jihar ta bi sahun wasu jihohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma'a da na Idi.

    Ganduje

    Asalin hoton, Facebook/Salihu Tanko Yakasai

  5. Ƙarin mutum 38 sun kamu da cutar korona a Ibadan

    Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya ce a gobe Talata ne za a yi cikakken bayani kan kamfanin da ma'aikatansa 38 suka kamu da cutar korona ya zuwa yanzu a jihar.

    Gwamna Seyi Makinde, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya kara da cewa kamfanin yana karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yammacin jihar.

    Ya ce daga gobe za a sanar da duk wanda ya yi mu'amala da mutanen da ke cikin kamfanin ya mika kansa domin a yi masa gwajin cutar korona.

    A cewar Gwamna Makinde, basu bayyana suna kamfanin ba zuwa yanzu saboda hukumomi su samu damar shiga cikinsa domin yin bincike.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. An kashe mutum 8,000 a arewa maso yammacin Najeriya

    Zamfara Death

    Asalin hoton, Zamfara Govt

    Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

    Kungiyar ta ce an raba wasu fiye da dubu dari biyu da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin cikin shekaru kimanin goma.

    A wani rahoto da ta fitar yau, Kungiyar ta ce kawo yanzu kokarin hukumomi ya gaza kawo karshen tashin hankalin, wanda ya fi shafar jihohin Zamfara da Sokoto da katsina da kuma Kaduna.

    Ko a jiya rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma sha biyar a jihar Zamafara.

    Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro izinin kai sabon farmaki babu kakkautawa kan 'yan bindiga a wuraren da suke.

  7. Coronavirus: 'Tawagar 'yan China za ta bar Najeriya nan gaba kaɗan'

    Shugaban kamfanin gine-gine, China Civil Engineering Construction Corporation Nigeria Ltd, Michael Yigao, ya ce tawagar mutum 15 ta 'yan kasar China da ta zo Najeriya don taimakawa wajen yaki da cutar korona tana karkashin kulawar kamfaninsa.

    Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ambato Mr Yigao yana bayyana hakan ranar Litinin a Abuja lokaci da yake raddi kan labarin da ke cewa ba a san inda 'yan Chinan suka shiga ba tun da suka iso Najeriya.

    A cewarsa, nan ba da jimawa ba za su koma kasarsu.

    A makon jiya ne aka ambato Ministan Lafiyar Najeriya, Dr Ehanire Osagie yana cewa likitocin na China ba baƙin gwamnnatin Najeriya ba ne domin kuwa sun shiga ƙasar ne da bizar kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC).

    An yi ta ce-ce-ku-ce kan likitocin da suka isa Najeriya ranar 8 ga watan Afrilu sannan suka killace kansu na tsawon kwana 14 a wani wuri da ba a bayyana ba, kamar yadda dokar hukumar NCDC ta tanada.

    "Ina tunanin ba dukansu ne likitoci ba, na ji cewa wasu daga cikinsu injiniyoyi ne kuma ma'aikatan kamfanin CCECC," in ji ministan.

    'Yan China

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Mummunar guguwa na fuskantar kasar Indiya

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Da alamun guguwar za ta iya isa yankin a ranar Laraba

    Hukumomi a India sun tura jami'an hukumar ba da agajin gaggawa zuwa jahohi biyu da ke gabashin kasar da ke fuskantar mahaukaciyar gugguwa a wannan makon.

    Ana shirin kwashe sama da mutun miliyan daya a jahohin Odisha da Bengal ta Yamma kafin isowar guguwar.

    Rahotanni sun ce guguwar Amphan na kan gangarowa doron kasa kuma ana sa ran za ta sauka a daren Talata ko kuma ranar Laraba.

    Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta India ta sanar da cewa kusan mil 500 ya ragewa guguwar ta iso, kuma tana gudun kilomita 220 ne a cikin awa daya.

    Masu hasashen yanayi sun ce guguwar Amphan na iya zama mai hadari sosai, kuma za ta kawo cikas ga humumomin ba da agajin gaggawa da ke yakar annobar Korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. An gaza samun fahimta tsakanin Amurka da kamfanin Huawei

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Guo Ping

    Kamfanin Huawei na Chana ya yi gargadin cewa matakin Amurka na hana sayar masa da kayan aiki zai kawo nakasu ga fannin fasaha na duniya.

    A ranar Juma'a ne Amurka ta sanar da cewa za ta bukaci shaidar samun lasisi ga masu sayar da kayan fasaha ga kamfanin Huawei da ake shigowa da su daga waje.

    Masana na ganin wannan wani salo ne na kara tsaurara takunkumi da kuma tsokano wani sabon rikicin kasuwanci.

    Shugaban Huawei Guo Ping ya ce ''an dauki wadannan matakai ne da nufin karya kamfanin, kuma ba makawa matakin zai haifar da rashin jituwa tare da jaow koma baya ga fannin fasaha.

    To Mr Ping ya ce yana da yakinin cewa za su samu mafita.

  10. Labarai da dumi-dumi, Rikici ya raba Firaiministan Lesotho da kujerarsa

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An tuhumi matar Thomas Thabane - Maesaiah, da hannu cikin kisan

    Firaiministan Lesotho Thomas Thabane, ya sanar da zai yi murabus daga mukamunsa, yayin da aka kwashe watannin ana fama da rashin tabbas a siyasar kasar.

    Sai dai bai bayyana takamaimai yaushe zai aje mukamin nasa ba.

    Mista Thomas Thabane ya yi ta fama da matsin lambar ya yi murabus biyo bayan zargin da ake masa na hannu cikin kisan gillar da aka yi wa matarsa Lipolelo Thabane, a 2017.

    Matar shugaban ta yanzu mai shekara 80, wadda take nan lokacin da aka yi kisan, ita ma an tuhumeta da hannu cikin lamarin da ya faru a watan Fabirairu.

    A baya Mista Thabane ya ce zai aje aikinsa a watan Yuli saboda shekaru da yake fama da su.

    Duka daga shi har matarsa sun musanta hannu cikin kisan da aka yi wa Lipolelo Thabane.

  11. Celtic aka bai wa kofin Scotland

    SNS

    Asalin hoton, SNS

    Bayanan hoto, Celtic taqna mataki na daya da tazarar maki 13 bayan wasa 30 a lokacin da aka dakatar da gasar a cikin watan Maris

    An bai wa Celtic kofin gasar kwallon kafar Scotland kuma karo na tara a jere, yayin da Hearts ta fadi daga wasannin bana, bayan da aka hakura da karawar da suka rage.

    An cimma wannan matsaya ne, bayan wani taro da aka yi ranar Litinin, inda kungiyoyi 12 da ke buga gasar a makon jiya suka amince ba za a iya kammala sauran karawar da suka rage ba ta 2019-20.

    An yi amfani da matsakaicin maki da kungiya ta samu a kowanne wasa wajen zakulo Zakara da wadanda suka fadi daga wasannin shekarar nan.

    Sauyin da aka samu daya ne kafin a tsayar da gasar ranar 13 ga watan Maris, shi ne St Johnson da ta koma mataki na shida ita kuwa Hibernian ta koma ta bakawi a teburi.

    Celtic ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 13 tsakaninta da Rangers ta biyu, bayan buga wasa 30 da ya rage saura fafatawa takwas a karkare kakar bana.

    An dakatar da dukkan wasannin tamaula a Scotand zuwa 10 ga watan Yuni, yayin da UEFA ta bukaci mambobinta su sanar da ita ko za su iya kammala kakar bana.

    Ana sa ran fara kakar 2020=21 a gasar kwallon kafa ta Scotland ranar 1 ga watan Agusta.

  12. 'Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Zamfara

    Bayanan sautiLatsa hoton sama domin cikakken rahoton Imam Saleh

    Wasu rahotani daga Jihar Zamfara sun bayyana cewa da misalin karfe 6:00 na yamma ne wasu 'yan bindiga suka kutsa garuruwan Rogo, da Bidda da Kagera, inda suka buɗe wuta kan mazauna garuruwan.

    Lamarin da ya sa mazauna garuruwan ficewa daga mahallansu, kamar yadda wani da ya ga lokacin da 'yan bindigar ke shiga garuruwan ya tabbatar wa BBC.

    Kawo yanzu, bayanai na cewa mutanen da ke waɗannan garuruwan sun fice daga garuruwan baki daya, tare da neman mafaka a wasu kauyuka da ke maƙwabtaka.

  13. China da Koriya ta Kudu za su tara wa WHO miliyoyin daloli

    Dr Tedros

    Asalin hoton, Getty Images

    Zuwa yanzu ƙasashe na ci gaba da tallafa wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), yayin da China da Koriya ta Kudu suka yi alƙawarin ba ta miliyoyin daloli domin yaƙar cutar korona a duniya baki ɗaya.

    Shugaban hukumar ya yi maraba da kiraye-kirayen ƙasashe na yin cikakken bincike kuma mai zaman kansa a kan matakan da WHO ke ɗauka na yaƙi da cutar.

    Ƙasashen Koriya ta Kudu da Australia sun ce ya kamata kuma Majalisar Harkokin Lafiya ta Duniya ta ƙara wa WHO 'yancin cin gashin kanta, inda Australia ta fayyace cewa a ƙara mata ikon sa ido kan al'amura.

  14. Labarai da dumi-dumi, An tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyu

    Kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona ya sanar da cewa an tsawaita dokar kulle a Kano da mako biyu biyo bayan ƙarewar wa'adin dokar a yau Litinin.

    Boss Mustapha, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnati, shi ne ya sanar da hakan a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan daƙile cutar korona a yau Litinin a Abuja.

    Kazalika su ma matakan nesa-nesa da juna da aka ɗauka da suka haɗa da zirga-zirga tsakanin jihohi an tsawaita su da mako biyu.

  15. An kashe 'yan Boko Haram 20 a Borno

    Hoton makaman 'yan Boko Haram

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe 'yan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda 20 a garin Baga da ke Jihar Borno.

    'Yan kungiyar sun gamu da ajalinsu ne yayin da tawagar motocinsu ke tafiya domin kai hari a wasu ƙauyuka da ke makwabtaka, kamar yadda sojojijn suka yi ikirari.

    Kakakin sashen samar da bayanai na hedikwatar tsaron Najeriya, Kwamanda Abdussalam Sani ya shaida wa BBC cewa an yi arangamar ne ranar Lahadi, kuma rundunar ta yi nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 guda shida da gurneti 36.

    Rundunar bataliya ta 130 ce ta kai harin tare da taimakon jiragen yaƙin sojan sama, a cewar rundunar.

    Kwamanda Abdussalam ya ce sirrin nasarar da suke samu a kan 'yan Boko Haram ya ta'allaƙa ne kan sabon salon yaƙin da suka sauya, inda Hafsan Sojin Ƙasa Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya koma yankin arewa maso gabas da zama.

  16. An kama babbar mai tace labaran jaridar intanet a Egypt

    BBC

    Jaridar intanet ta Mada Masr, ta kasar masar wadda aka kama babbar mai tace labaranta ana mata kallon kafa daya da ta yi saura da ke cin gashin kanta.

    Jaridar Mada Masr ta ce an kama Lina Atallah yayin da take tattaunawa da mahaifiyar shugaban masu fafutuka Alaa Abdel Fattah, a wajen gidan yarin da ake tsare da shi.

    Mada Masr ta ruwaito cewa yanzu Misis Atallah na tsare a hannun 'yan sanda.

    Ko a watan Nowambar bara, sai da aka tsare Lina Atallah da wasu 'yan jarida biyu na wasu awanni yayin wani samame da jami'an tsaro suka kai ofishin jaridar Mada Masr da ke Cairo.

  17. Italiya na ci gaba da sassauta dokar kulle

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Italiya na ci gaba da sassauta matakan kullen da aka dauka saboda cutar korona, makonni 10 bayan zama kasa ta farko a duniya da ta fara sanya dokar hana fita a fadin kasarta.

    An sake bude shaguna da wuraren cin abinci da gyaran gashi, tare da dawo da wasu hanyoyin nuna al’adun kasar.

    Fafaroma Francis ya jagoranci wani taron ibada a sirrance a fadar Vatican, wadda aka yi wa feshi kafin sake bude ta domin masu ziyarar bude ido.

    Firaiministan Italiya Giuseppe Conte, ya ce sai da aka yi dogon nazari kafin a dauki matakan sassauta dokar.

    Kimanin mutum 32,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan annoba a fadin kasar, kuma an yi hasashen tattalin arzikinta zai ragu da kusan kashi 10 cikin 100 a wannan shekarar.

  18. Labarai da dumi-dumi, China ba ta yi rufa-rufa ba tun daga farkon annobar korona – Xi Jinping

    Shugaban China Xi Jinping ya yi jawabinsa a wurin taron lafiya na shugabannin duniya, kuma ya ce China ba ta yi wata rufa-rufa ba tun daga farkon al'amari.

    "Mun gudanar da abubuwa a bayyane da kuma sanin ya kamata tun daga farkon wannan annoba," in ji shi.

  19. Gwamnatin Najeriya ta kama jirgi mai 'fasakaurin jama'a zuwa cikin kasar'

    Hadi Sirika

    Asalin hoton, Twitter

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta kama wani jirgin sama mallakar wani kamfani da ke Burtaniya bisa zarginsa da yin jigilar Fasinjoji zuwa cikin kasar duk da hanin da aka saka na yin hakan saboda annobar korona.

    Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika wanda ya sanar da hakan, ya ce an ba jirgin na kamfanin Flair Aviation ne iznin jigila zuwa cikin kasar don taimaka wa wajen ayyukan jinkai, amma kuma ya fake da hakan wajen soma jigila irin ta kasuwanci.

    Hadi Sirika ya kara da cewa abin ya ba su mamaki inda suka tsare jirgin sannan ana gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ke faruwa.

    Ministan dai ya yi zargin abin da ya kira "suna bincike domin gano ko akwai wani abu da ake rufe musu kuma idan muka same kamfanin da laifi za mu hukunta shi daidai gwargwado."

    Ya ce gwamnatin Najeriya ta yi shigar burtu inda ta gano yawan kudin da ake biyan jirgin domin kai jama'a Najeriya.

    Sai dai kuma ministan bai fadi tsawon lokacin da jirgin ya kwashe yana gudanar da 'haramtattun ayyukan' da gwamantin Najeriyar ke zargin kamfanin.

    Har kawo yanzu dai kamfanin Flair Aviation bai ce uffan ba dangane da zargin kuma da zarar ya mayar da martani za mu sanar da jama'a.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Coronavirus: Tarayyar EU za ta tattauna da hukumar lafiya ta duniya

    Tedros

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Tarayyar Turai za ta jagoranci wani yunkurin gudanar da bita mai zaman kanta kan matakan da ake dauka wajen yaki da annobar korona a duniya, da kuma hada-kai wajen binciken riga-kafi a yayin taron Hukumar lafiya ta duniya, WHO.

    Kakakin Kungiyar, Virginie Battu Henriksson ta ce ana bukatar amsoshi masu gamsarwa kan yadda za a kiyaye sake barkewar annobar nan gaba koda yake ta ce yanzu ba lokaci ba ne na zargin juna ko dora alhaki bala'in da duniya ta tsinci kanta kan wani.

    Kusan kasashe dari biyu ne za su shiga tattaunawar ta internet kuma akwai yiwuwar a samu rabuwar kawuna kan yadda WHO ta tunkari annobar, da kuma Taiwan da za ta shiga taron a matsayin mai sa ido, al'amarin da China ba za ta so ba.

    Amurka dama dai ta ce ta daina bai wa WHO tallafi, sannan tana ci gaba da tallata nata shirin samar da riga-kafin