Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta hana fita ranar Asabar

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin kanun labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Brazil ta zama ƙasa ta huɗu a yawan masu korona a duniya
    • Waɗanda na ƙuntata wa da dokar kulle su gafarce ni – El-rufai
    • Wasu daga cikin 'yan Najeriya da aka kwaso daga Dubai na da korona
    • Tarar dala 55,000 ga masu karya dokar rufe fuska a Qatar
    • 'Akwai yiwuwar buɗe makarantu a Tanzania'
    • An tsawaita dokar kulle da mako 2 a Indiya
    • Birtaniya za ta bayar da karin fam miliyan 84 kan riga-kafin korona
    • Buhari ya bayar da umarnin fatattakar 'barayi' a Katsina
    • Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta hana fita ranar Asabar

    Ku duba kasa domin karanta labaran. Mu kwana lafiya....

  2. Za a rinka biyan masu mukaman siyasa rabin albashi a Kano

    .

    Asalin hoton, Abba Anwar

    Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za a rinka biyan masu rike da mukaman siyasa a jihar rabin albashi sakamakon kalubalen da annobar korona ta jawo.

    Sakataren watsa labarai na jihar Abba Anwar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda ya bayyana cewa faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya zai shafi asusun kudi na gwamnatin tarayya wanda hakan zai iya kawo cikas ga kudin da gwamnatin jihar za ta samu.

    Ya kuma kara da cewa raguwar kudin shiga na haraji da jihar ke samu na cikin dalilan da ya sa aka dauki wannan mataki.

    Ana sa an matakin zai fara aiki daga watan Mayu na wannan shekara.

  3. Jami'an tsaro sun tarwatsa taron daurin aure a coci

    Jami'an tsaro a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya sun tarwatsa wani taron daurin aure da ake cikin gudanarwa a wata coci a jihar.

    Ana tsakiyar gudanar da daurin auren ne kwatsam sai jami'an suka afko cikin cocin, jama'ar cikin cocin ba shiri suka gudu.

    Shugaban runduna ta musamman da aka kafa domin tabbatar da bin ka'idoji a lokacin annobar korona a jihar Potrait Peterson ya shaida wa BBC cewa suna cikin tafiya sai suka hangi taron motoci.

    Wannan ne ya sa suka je inda motocin suke har suka shiga cikin cocin.

    Ya tabbatar da cewa sama da mutum 300 sun halarci wannan biki da aka gudanar a cocin.

  4. Labarai da dumi-dumi, Cutar korona ta sake kashe mutum 1,394 a Amurka

    Mutum 1,394 sun sake mutuwa sakamakon cutar korona a Amurka.

    A halin yanzu waɗanda suka mutu sakamakon cutar a kasar sun kai 88,709.

    Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaduwa ta Amurka CDC a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa mutum 1,467,065 suka kamu da cutar a kasar.

    Amurka ce kasar da cutar ta fi kisa a duniya kamar yadda kididdiga ta nuna.

    Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki Shugaba Trump sakamakon yadda yake tafiyar da lamuran cutar korona a kasar.

  5. Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta hana fita ranar Asabar

    .

    Asalin hoton, FACEBOOK/THE GOVERNOR OF KADUNA STATE

    Gwamnatin jihar Kaduna ta sauya ranakun fita ga 'yan jihar zuwa Laraba da Alhamis domin ba su damar zuwa kasuwanni sayen kayan abinci.

    A wata sanarwa da daraktan hukumar bunkasa kasuwani ta jihar Hafiz Bayero ya fitar, ya jaddada cewa kasuwanni za a bude su daga 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

    Ya bayyana cewa wannan sauyin da aka gudanar na nufin babu kasuwar da za ta bude ranar Asabar,

    Tun bayan da aka saka dokar takaita zirga-zirga saboda cutar korona a jihar, ranakun da aka bari na fita tun asali su ne Talata da Laraba, sai daga baya aka sauya zuwa Talata da Asabar, a halin yanzu kuma an mayar Laraba da Alhamis.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Buhari ya bayar da umarnin fatattakar 'barayi' a Katsina

    .

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar umarnin gudanar da wani shiri na musamman domin fatattakar barayi da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa a halin yanzu dakaru na musamman na nan na aiki, sai dai a cewarsa ba za a fallasa irin abubuwan da suke yi ba.

    Ya shaida cewa tuni dakarun da ke da alhakin tsare-tsare suka isa jihar domin tsara wuraren da sojojin za su fi mayar da hankali domin yin wannan aiki.

    Jihar Katsina na cikin jihohin Najeriya da barayi da kuma masu garkuwa da mutane suka addaba.

    A 'yan kwanakin nan an samu rahotanni da dama na hare-hare da 'yan bindiga ke kai wa musamman a kauyukan Batsari da Faskari da Jibiya da Safana da wasu kauyuka da ke jihar.

  7. Shugaba Buhari ya tattauna da kwamamitin yaki da korona

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da kwamitin da ya kafa kan yaki da cutar korona karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

    Cikin kwamitin, har da ministan lafiya na kasar Osagie Ehanire da kuma shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu.

    .

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    .

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

  8. Birtaniya za ta bayar da karin fam miliyan 84 kan riga-kafin korona

    .

    Asalin hoton, PA Media

    Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa za ta bayar da karin fam miliyan 84 domin taimaka wa wajen samar da riga-kafin cutar korona cikin gaggawa.

    Sakataren kasuwanci na kasar Alok Sharma ne ya sanar da hakan a wani jawabi da kasar ke yi kullum kan cutar ta korona.

    Ya bayyana cewa kudin za su taimaka wajen samar da riga-kafin da yawa ta yadda idan aka tabbatar riga-kafin na aiki, za a fara amfani da ita kai tsaye.

  9. Labarai da dumi-dumi, Najeriya ta kama wani jirgi daga Birtaniya

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren tattaunawa da Hadi Sirika

    Gwamnatin Najeriya ta kama wani jirgi na kamfanin Flair Aviation na kasar Birtaniya bayan zargin jirgin da laifin jigilar 'yan Najeriya zuwa kasashen ƙetare da kuma shiga da su ƙasar.

    Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar wa BBC da kama jirgin a wata tattaunawa inda ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike kuma jirgin zai biya tara mai matukar yawa.

    Ministan ya tabbatar da cewa jirgin yana jigilar mutane cikin Najeriya har zuwa jihohi kamar Abuja da Legas da kuma Oyo duk da annobar korona da ake ciki.

    Ya bayyana cewa an bai wa jirgin dama gudanar da ayyukan jin ƙai, amma ya ɓige da jigilar fasinjoji.

  10. Za a tsaurara matakan kulle a Masar a ƙarshen Ramadana

    Masar

    Asalin hoton, Getty Images

    Masar za ta ɗauki tsauraran matakai a kwanakin ƙarshe na watan Ramadana daga 24 ga watan Mayu, yayin da 'yan kasar ke shirye-shiryen gudanar da bikin Ƙaramar Sallah.

    Firaminista Mostafa Madbouly ya ce za a hana manyan motocin haya zirga-zirga sannan kuma a saka dokar hana fita daga ƙarfe 5:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

    Kazalika za a rufe shaguna da gidajen cin abinci sannan haramcin zirg-zirga zai ci gaba kasancewa har aƙalla mako biyu.

    Fiye da mutum 11,700 ne suka harbu da cutar korona a Masar, inda 612 suka rasa rayukansu.

    Gwamnati ta sassauta dokar hana fita da dare da ta saka a yanzu duk da ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar a kullum.

  11. An tsawaita dokar kulle da mako 2 a Indiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Indiya ta kara wa'adin dokar kulle da ta saka a kasar da mako biyu.

    Hukumar kiyaye afkuwar bala'i ta kasar ce ta bukaci a yi hakan a wata takarda da ta aika wa ministan harkokin cikin gida na kasar

    Sama da mutum dubu 90 ne suka kamu da cutar korona a fadin kasar inda kuma kusan mutum 2,900 ne suka mutu sakamakon cutar.

    Dokar kulle da aka saka a kasar a farkon watan Maris ta jawo matsi ga 'yan kasar matuka sakamakon miliyoyin jama'ar kasar da ba su samun abincin da za su ci sai sun fita nema.

  12. Man United ka iya yin asarar fan miliyan 140 idan aka ci gaba da wasa babu 'yan kallo

    Man United

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Turai ka iya yin asarar sama da fan biliyan 3.5 saboda rashin 'yan kallo a filayen wasannin sakamakon annobar korona ko da kuwa an kammala kakar wasa ta bana.

    Manchester United ka iya yin asarar fan miliyan 140 idan aka buga wasannin ba tare da 'yan kallo ba har zuwa ƙarshen kakar bana.

    An yi wannan hasashe ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki suka yi a makon da ya gabata.

    Sun ƙayyade cewa idan har aka gaza kammala gasannin to adadin abin da za a yi asara zai iya kai fan biliyan 6.2.

    An ci gaba da gasar Bundesliga ta Jamus ranar Asabar, yayin da ake sa ran ci gaba da Firemiyar Ingila ranar 12 ga watan Yuni.

  13. 'Akwai yiwuwar buɗe makarantu a Tanzania'

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kasar Tanzania John Magafuli ya bayyana cewa mutane da dama masu ɗauke da coronavirus da ke a asibitocin kasar sun samu sauki.

    Ya bayyana cewa idan al'amura suka ci gaba a haka, akwai yiwuwar makarantu su ci gaba da aiki a cikin wannan watan na Mayu.

    Shugaban ya kuma bayyana cewa za a ba masu yawon buɗe ido damar shiga ƙasar muddin aka ci gaba da samun raguwa dangane da cutar kamar yadda ake samu a halin yanzu.

    Shugaban ya bayyana cewa ɗansa ya kamu da cutar amma ya warke bayan ya killace kansa ya yi sirace tare da shan lemun tsami da na citta.

  14. Yadda wasan ƙwallo ya sauya a Bundesliga saboda korona

    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

    Idanun ma'abota ƙwallaon ƙafa a duniya ya koma kan ƙasar Jamus a ƙarshen makon nan, yayin da Bundesliga ta zama babbar gasa mafi girma da aka buɗe a Nahiyar Turai saboda annobar korona.

    To wane sauyi aka samu a wasannin?

    • In an ci ƙwallo sai dai kawai a ɗaga gwiwar hannu domin yin murna
    • 'Yan kwallon na isa filin wasa a motoci da yawa saboda nesa-nesa da juna
    • Ana yi wa ƙwallo feshin magani yayin da ake tsaka da wasa
    • 'Yan benci da masu horarwa na sanye da takunkumi kuma zaune nesa-nesa da juna
    • An bai wa ƙungiyoyi damar yin sauyi sau biyar a wasa
  15. Fiye da mutum dubu 80 sun kamu da korona a Afirka

    Afirka

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar korona ta kama mutum 81,307 a daukacin ƙasashe mambobin ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU ya zuwa ranar Lahadi, a cewar wani rahoto da hukumar CDC Afirka ta wallafa.

    Kazalika mutum 2,704 sun rasa rayukansu sakamakon annobar, yayin da 2,306 suka rasa rayukansu.

    Afirka ta Kudu ke kan gaba a yawan waɗanda cutar ta harba a nahiyar baki ɗaya - jumillarsu 14,335.

    Yankin arewacin Afirka ne kan gaba a yawan masu cutar, inda ƙasar Masar ko kuma Egypt ke da mutum 11,719 da kuma Algeria mai 6,821.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Wasu na buga katin izinin zirga-zirga na boge a Jihar Filato

    Jihar Filato

    Asalin hoton, @PLSGov

    Gwamnatin Jihar Filato ta koka kan yadda wasu mazauna jihar ke bugo katin izinin yin zirga-zirga a jihar na jabu sakamakon dokar kulle da aka saka a jihar.

    Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Dan Manjang ya fitar ranar Lahadi ta ce hakan yana kawo tarnaƙi ga gwamnati a yaƙin da take yi da cutar korona.

    Bisa wannan dalili ne gwamnati ta sharɗanta cewa daga yanzu jami'an tsaro ba za su sake yarda da kwafi na katin izinin ba sai orijina, sannan kuma na gaskiyar dole ne ya kasance ɗauke da kwanan watan da zai daina aiki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Adadin waɗanda suka mutu a Spaniya na rana guda ya yi ƙasa da 100

    Spain

    Asalin hoton, AFP

    Spaniya, ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da annobar korona, ta bayar da rahoton samun mutum ƙasa da 100 da suka mutu sakamakon annobar a rana guda a karon farko cikin wata biyu.

    Mutum 87 ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana ranar Lahadi, abin da ya kawo jumillarsu zuwa 27,650.

    Jumillar adadin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar ya zama 231,350.

    • Tarar dala 55,000 ga masu karya dokar rufe fuska a Qatar

      Qatar

      Asalin hoton, Getty Images

      Qatar ta tsaurara matakin saka takunkumi a ƙasar a bainar jama'a, yayin da aka tanadi hukuncin shekara uku a gidan yari ga duk waɗanada suka karya dokar rufe fuskar tasu.

      Za kuma a iya cin tarar masu laifin dala 55,000 - kusan naira miliyan 21.

      Ƙasar na cikin mafiya yawan masu cutar a duniya idan aka kwatanta da yawan al'ummarta (ƙasa da miliyan uku), inda mutum fiye da 30,000 suka kamu.

      Masallatai da makarantu da manyan shagunan sayar da kayayyaki na ci gaba da kasancewa a rufe a 'yar ƙaramar ƙasar, duk da cewa wuraren gine-gine na buɗe, yayin da take shirin karɓar baƙuncin gasar ƙwallon kafa ta Kofin Duniya na 2022.

    • Mutum 23 sun warke daga korona a Abuja cikin awa 24

      Ministan Abuja - Babban Birnin Tarayyar Najeriya - Malam Mohammed Musa Bello ya ce an sallami mutum 11 daga cibiyoyin kula da masu cutar korona bayan gwaji ya nuna ba sa ɗauke da ita.

      Ya bayyana haka ne a wani saƙon Twitter da ya wallafa cikin daren Asabar, kafin daga bisani ya sake bayyana cewa an sallami wasu 12 a safiyar Lahadi, jumillarsu 23 kenan.

      Ministan ya ce ya zuwa safiyar Lahadi adadin waɗanda aka sallama a Abuja sun kai 101.

      Jumillar mutum 397 ne suka harbu da cutar korona a birnin na Abuja, a cewar hukumar NCDC, yayin da bakwai suka rasa rayukansu.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Korona ta kama ma'aikatan wani kamfani su 30 a Ibadan

      Seyi Makinde

      Asalin hoton, Twitter/Makinde

      Ma’aikatan wani kamfani mai zaman kansa guda 30 sun kamu da cutar korona a Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.

      Gwamnan jihar Seyi Makinde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa kamar yadda jaridar intanet The Cable ta wallafa.

      Sai dai gwamnan bai bayyana sunan kamfanin ba amma ya ce cibiyar kamfanin na birnin Ibadan ne.

      Bayanai sun ce tuni aka killace ɗaukacin kamfanin domin yi masa feshin magungunan kashe kwayoyin cuta.

      Zuwa jiya Asabar, mutum 131 ne suka kamu da cutar korona a faɗin jihar Oyo.