Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Karshen rahotannin kenan a yau

    A nan muka kawo karshen rahotannin namu na yau.

    Sai kuma gobe Lahadi idon Allah ya kaimu.

  2. Cikin Hotuna: Rana ta farko ba tare da wuraren cin abinci da shakatawa ba a Birtaniya

    A Birtaniya, ‘yan kasar na hutunsu na karshen sati a gida bayan farai ministan kasar yayi umarnin a rufe ko wuraren shakatawa da na cin abinci.

    Kazalika an rufe kulob-kulob da gidajen kallo da wuraren atisaye da dai sauransu.

    Piccadilly Circus

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Tashar jirgin kasa ta Piccadilly Circus dake tsakiyar birnin Landan-tana yawan cika a ranar Asabar-yau babu kowa
    getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Babban kantin zamani na Bull ring da ke Birmingham shi ma babu kowa
    BBC
    Bayanan hoto, Babban kantin sayar da kayayyaki na John Lewis da ke kan titin Oxford a tsakiyar London, shi ma babu kowa
    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A Glasgow, taron mutane ne suka hau layi a wajen kantin Costco suna son shiga ciki
    getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Graffiti a Brighton - inda aka rubuta mutane su daina rige-rigen siyan abinci
    reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ma'aikata a kanfanin Brewery na lika takardar sabon tsarin yadda mutane za su rika sayan kaya daga cikin motocinsu
    reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Sai dai a wasu wuraren da ba shaguna ba mutane na ta kai komo - kamar bakin ruwan Thames da ke kudu maso arewacin Landan
  3. Labarai da dumi-dumi, Hukumar lafiya ta Ingila ta tabbatar da mutuwar mutum 53

    Wasu karin mutam 53 da ke dauke da coronavirus sun mutu a Ingila, wanda ya kai adadin mutanen da suka mutu a kasar 220.

    Baki dayan wadanda suka mutu a ingila ‘yan tsakanin shekara 41 ne zuwa 94.

    Gabanin nan, an samu rahoton mutuwar mutum biyu a Wales, yanzu dai mutum biyar ne suka mutu a yankin, haka kuma an samu karin mutum daya, a Scotland abin da yakai adadin wadanda suka mutun zuwa bakwai.

    A yankin arewacin Ireland mutum daya ne ya mutu.

    Idon aka hada duka a Burtaniya, adadin wadanda suka mutun yakai mutum 233.

  4. Kimanin mutum 800 ne suka mutu a Italiya cikin awa 24

    Mutuwa na ci gaba da dauki dai-dai a Italiya. Adadin da hukumomi suka bayyana yakai 793, wadanda suka mutu saboda Covid- 19 cikin awa 24.

    Yanzu mutum 4,825 ne suka mutu a fadin kasar.

    Sama da mutum 53,500 aka tabbatar suna dauke da cutar a kasar ranar Juma'a, yanzu adadin ya karu zuwa 65,500.

  5. Za a yi wa mataimakin Trump gwajin coronavirus

    Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence wanda ke jagorantar kwamitin kar-ta-kwana na fadar White House kan coronavirus ya ce, za a yi masa gwajin cutar shi da matarsa a yammacin Asabar, hakan na zuwa ne bayan an gano daya daga cikin mambobin kwamitin na dauke da cutar.

    Mr Pence ya ce mutumin, wanda bai fadi sunansa ba, jajurtacce ne kuma tun ranar Litinin rabonsa da White House.

  6. Har yanzu ana yin musabaha a Rasha

    Vladimir Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban Rasha daga hagu na gaisawa da wani jami'i : an dauki hoton ranar 19 ga watan Maris

    A Moscow, wakiliayar BBC, Sarah Rainsford ta ce, mutane da yawa a Rasha na ganin ana zuzuta yadda ake tunkarar cutar coronavirus, kuma muninta bai kai haka ba a Rasha.

    Hakan na da alaka da shugabanninsu, yayin da suke kallon kulle iyakoki da takaita tarukan mutane da ake ta magana a matsayin wata barazana ga kasashen waje.

    Sun kuma tsorata da yadda kasashen Turai ke ta zuzuta cutar, inda suke ganin cewa yanzu ne daidai lokacin da ya kamata su dauki nasu matakan kariyar.

    ‘Yan Rasha har yanzu suna musabiha, ba mamaki sun ga hakan ne wajen manyan kasar, inda gidan talabijin na kasar ya yi ta nuna shugaba Vladimir Putin yana gaisawa da wani hannu da hannu, fadar Kremlin ce kadai ta yi wa ma'aikatanta gwaji.

    An hana taruka a kan tituna da kuma sauran wurare. A ranar Asabar, wuraren atisayen gina jiki, wajen ninkaya, da sauran wasanni su ma sun bi sahun hanin.

    A gefe guda kuma, wata likita da ta koma kasar daga Spaniya dauke da cutar kuma ta ki killace kanta yanzu ana ba ta kulawar cutar coronvirus.

    Rahotanni na cewa, mutanen da ta yi mu'amala da su bayan dawowarta aiki yanzu dakkansu ana yi musu gwajin cutar.

  7. Coronavirus: An samu mutuwar farko a kasashen Singapore, Finland, Mauritius

    Kasashen Singapore da Finland da Mauritius sun bayar da rahoton mutuwa na farko saboda coronavirus.

    • A Singapore, hukumomi sun ce mutum biyu sun mnutu a ranar Asabar: wata 'yar Singapore mai shekara 75 da kuma wani dan Indonesia mai shekara 64
    • A Finland, cibiyar kula da lafiya da walwala ta kasar ce ta sanar da mutuwar mutum daya a ranar Asabar
    • A Mauritius, hukumomi sun ce mutumin da ya mutu ya je kasar Belgium ne daga Dubai. Babu wani karin bayani
  8. 'Giya ta fi kashe 'yan garin Fars na Iran fiye da Coronavirus'

    Iran

    Asalin hoton, AFP/Getty/Images

    Bayanan hoto, Iran na cikin kasashen da Covid- 19 ta yi wa illa sosai

    Mutane na kara mutuwa a gundumar Fars da ke kudu maso yammacin Iran sakamakon giyar da suke sha a kokarin kare kansu daga cutar coronavirus.

    Hakan ya sa mutane yanzu suke mutuwa daga giyar da suke sha fiye da yadda cutar ke yin kisa, In ji kafafen yada labaran kasar..

    Mohammad Javad Moradian ne daraktan cibiyar agajin gaggawa ta gundumar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Isna cewa Covid-19 ta kashe mutum 13 a yankin na Fars, yayin da mutum 66 suka mutu sakamakon shan giyar da za ta kara musu karfi ta kuma kare su daga kamuwa da cutar.

    Ana ta yada jita-jita a Iran cewa, shan giya na kare mutane daga kamuwa da cutar coronavirus.

    Yanzu Iran ta tabbatar da mutum 20,610 da suka kamu da cutar, yayin da mutum 1,556 aka rawaito sun mutu saboda cutar.

  9. Coronavirus: An hana jiragen kasar waje sauka a Najeriya

    Jirage

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA ta sanar da hana jirage daga kasashen waje sauka a dukkanin filayen jirgin saman kasar sakamakon yakin da ake yi na dakile cutar Covid-19.

    "Daga ranar 23 ga watan Maris za a rufe wa jirage daga kasashen waje kofa a filayen jirgin sama na Abuja (Nnamdi Azikiwe International Airport) da na Legas (Murtala Muhammed International Airport)," NCAA ta fada a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

    Hukumar ta ce wannan kari ne kan filayen jirgin sama na Kano da na Fatakwal da na Akwa Ibom da aka rufe su ranar Asabar. Sai dai ta ce ban da jirage masu saukar gaggawa.

    Kazalika, jiragen cikin gida za su ci gaba da shiga da fita a filayen jiragen.

  10. Abubuwan da ke faruwa kan coronavirus zuwa yanzu

    Watakila yanzu kuka fara bibiyarmu, ga abubuwan da ke faruwa a duniya yayin da kasashe ke ke fadi-tashin ganin bayan cutar Covid-19, wato coronavirus.

    • Ma'aikatar Lafiya ta Najeriya ta tabbatar da mutum 10 da suka sake kamuwa da cutar coronavirus a kasar. Uku daga cikin wadanda suka kamu a Abuja suke, babban birnin kasar, sauran bakwai suna Jihar Legas.
    • A wani mataki na dakile yaduwar cutar, Najeriya ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasan fasinja daga ranar 23 da watan Maris.
    • Muatnen da coronavirus ta kashe ya ninka sau biyu a Potugal cikin awa 24. Daga karfe 6 zuwa 12 kuwa an samu rahoton mutanen da suka kamu da cutar 260. Yanzu akwai mutum 1,280 da suke da cutar a kasar.
    • ·A makociyar kasar kuwa Spain, an samu adadin wadanda suka mutu da ba a taba samu ba tun da cutar ta fara annobar, inda mutum 324 suka mutu. Mutum 1,326 ne suka mutu jumulla. Ana ganin ita ce kasa ta uku da cutar ta fi yi wa illa bayan Italiya da China.
    • Koriya ta Kudu ta yi gargadin za ta iya hana duk wasu tarukan addini da wasanni da kuma wuraren nishadi matukar ‘yan kasar suka yi watsi da shawarar da gwamnati ta bayar na a guji yawan haduwar mutane. Hukumomi sun ce an samu sabbin mutum 100 da suka kamu da cutar cikin awa 24, wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa a wannan makon.
    • ·A gefe daya kuma, karo na biyu kenan da China ke rawaito cewa babu sabon rahoton kamuwa da cutar cikin awa 24. Amma an ruwaito wasu mutum 41 da suka kamu wadanda suka shiga kasar ranar Juma’a ,14 daga cikinsu daga Beijing tara kuma daga Shanghai.
    • Firai Ministan Geogia ya shaida wa manema labarai cewa ya nemi shugaban kasar ya sanya dokar-ta-baci a kasar saboda coronavirus. Mutum 47 ne hukumomi a kasar suka tabbatar sun kamu da cutar.
  11. Coronavirus: An dakatar da jiragen kasa a Najeriya daga Litinin

    Jirgin kasa a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Najeriya sun bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

    A wata sanarwa da hukumar kula da sufurin jirgin kasa ta fitar, ta ce an dauki wannan matakin ne domin dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a kasar.

    Sanarwar mai dauke da sa hannun mataimakin babban daraktan hukumar Yakubu musa, ta kara da cewa, za a fitar da karin bayani game da zirga-zirgar jirgin fasinjan da zarar sun samu damar yin hakan.

    An samu karin mutum 10 da ke dauke da cutar a ranar Asabar a kasar, kamar yadda ma’akatar Lafiya ta Najeriya ta tabbatar a ranar Asabar. Adadin wadanda ke dauke da cutar yanzu ya 22, biyu sun warke.

    Uku daga cikin wadanda suka kamu a Abuja suke, babban birnin kasar, sauran bakwai suna Jihar Leagas.

  12. Labarai da dumi-dumi, Mutum 324 sun mutu a Spain cikin awa 24

    Spain

    Asalin hoton, AFP

    Ministan lafiya na kasar Spain ya bayyana mutuwar da kasar ta fuskanta a ranar Asabar a matsayin wadda ta fi kowacce muni, inda a rana daya mutum 324 suka mutu kuma yanzu adadin wadanda suka mutu a kasar ya zama 1,326.

    Kazalika an samu karin mutanen masu yawa da suka kamu da cutar ta Covid-19 a duka fadin kasar. A cikin sa'a 24 aka samu kimanin mutum 5,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar, abin da ya sa adadin mutanen da suke dauke da cutar a kasar ya kai 24,926.

    Ana ganin Spain ta zama kasa ta uku da wannan cuta ta fi yi wa illa a duniya, bayan Italiya da kuma China.

    Rahotanni na cewa Asibitoci musamman a sassan birnin Madrid, na ta fadi-tashi da mutanen da ke kara kamuwa da cutar.

    Gwamnatin Spain ta dakatar da shige da ficen mutane a makon da ya gabata a kokarin takaita yaduwar annobar.

  13. An wayar da kan matasa game da coronavirus a Kano

    Taron wayar da kai kan Covid-19

    Wata kungiya mai suna Basic Empowerment Support Organization ta shirya taron wayar da kai kan annobar cutar Covid-19 wato coronavirus ranar Asabar a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

    Masu shirya taron sun ce sun yi la'akari da kiran yin nesa-nesa da juna domin rage yaduwar cutar, abin da ya sa suka rage adadin mahalarta taron a wani mataki na ci gaba da yaki da cutar da ta zama annoba ta duniya.

    Taron wayar da kai kan Covid-19

    Tuni gwamnatin Kano ta dauki matakin rufe dukkan makarantu a jihar domin guje wa yaduwar cutar ta coronavirus a jihar mai yawan jama'a.

    Kwamishinan ilimi a jihar Sanusi Sa'idu Kiru ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

    Kwamishinan ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

    Ya kara da cewa iyaye su tabbata sun dauko 'ya'yansu daga makarantun kwana daga ranar Lahadi.

  14. Da gaske chloroquine zai taimaka a yaki da coronavirus?

    Kwayar chloroquine

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwaya ko kuma sinadarin chloroquine ya dade a duniya ana amfani da shi kuma yanzu wasu mutane na cewa za a iya amfani da shi wurin yin maganin cutar Covid-19.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Alhamis cewa hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka FDA ta amince a yi amfani da chloroquine wurin yi wa masu dauke da coronavirus magani, amma ba gaskiya ba ne.

    Ana yin amfani da shi wurin maganin zazzabin maleriya da cutukan da ke haddasa ciwon gabbai, su ke nan.

    Sai dai akwai fata. Wasu likitoci sun ce ya taimaka wa wasu masu Covid-19 sannan kuma takan iya toshe kwayar cutar, ta hana ta motsi.

    Ko ma dai yaya ne, har yanzu ana ci gaba da gwaji.

  15. China na murna da raguwar coronavirus

    Likitocin China

    Asalin hoton, Getty Images

    A 'yan kwanakin nan, China ta yi murna da ci gaban da ta samu saboda babu wanda ya sake kamuwa da coronavirus a cikin 'yan kasarta a tsawon rana.

    Bayanan da da aka fitar a yau sun nuna cewa kasar ta ci gaba rike wannan matsayi a kwana na uku a jere a ranar Juma'a. Wannan labari ne mai dadin ji.

    Sai dai har yanzu akwai matsala. Akwai mutum 41 da aka tabbatar sun kamu da cutar 'yan kasashen waje a Chinar da aka rawaito ranar Juma'a - 14 a Beijing babban birnin kasar, guda tara a Shanghai.

    Wannan ya sa adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar 'yan kasashen waje ya kai 269. Dalibai da 'yan cirani na ta komawa kasar daga Amurka da Turai da sauran wurare.

    Zuwa yanzu dai babu rahoton cewa masu komawar sun harbi wadanda ke cikin kasar da cutar amma China tana kara saka tsauraran dokoki domin guje wa faruwar wani sabon halin ni-'yasu.

  16. Labari mai dadin ji ga 'yan Najeriya kan coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, @jidesanwoolu

    Wani labari da zai dan karfafa gwiwar 'yan Najeriya shi ne, gwamnatin Jihar Legas ta sallami mutumin da ya fara kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya - wanda ya shigo da cutar Najeriya - bayan gwaji ya tabbatar cewa ya warke daga cutar.

    Wannan ne mutum na biyu da ya warke daga cutar a Najeriya a cikin 12 da suka kamu, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka.

    Duk da wannan nasara da aka samu, har yanzu akwai mutum 10 da ke dauke da cutar a Najeriya, ciki har da jaririya da mahaifiyarta.

    Gwamna Sanwo-Olu na Legas ya wallafa hotunan likitocin asibitin kula da cutuka masu yaduwa na Yaba tare da baturen Italiyan yana sanye da riga da gajeren wando da farar safa, a tsakiyar jami'an lafiyan.

    Ba a bayyana fuska ko sunan dan kasar Baturen ba, kuma duk da yake da duhun dare a lokacin amma ana iya ganinsa tsaye kyam da kafafuwansa ya rike hannuwansa.

  17. Mutum biyu sun sake kamuwa da coronavirus a Singapore

    Kasar Singapore ta bayar da rahoton sake bullar cutar coronavirus, inda wata 'yar shekara 75 da kuma dan shekara 64 suka kamu.

    Rahoton ya ce macen 'yar Singapore ce, shi kuma namijin dan kasar Indonesia ne. Hukumomi sun ce sun sha fama da wasu cutukan na daban.

    Hukumar Lfiya ta Duniya WHO ta yaba wa 'yar karamar kasar kan yadda take yaki da cutar - har zuwa yanzu babu wanda ya mutu a kasar duk da cewa tana cikin na farko-farko da cutar ta fara bulla.

    Sai dai duk da kokarinta, adadin wadanda suka kamu ya karu zuwa 40 a makon da ya gabata, mafi yawansu matafiya ne daga Turai da Amurka da kuma sassan Nahiyar Asiya.

  18. Barka

    Barkanmu da safiyar Asabar jama'a.

    Ku biyo mu domin ci gaba da kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da makobtanta da ma sauran sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke fatan mun tashi lafiya.

  19. Karshen rahotannin ke nan

    Mu hadu ranar Asabar domin ci gaba da samun rahotannin abin da ke faruwa a duniya kai-tsaye.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  20. Matasa ba su fi karfin coronavirus ba – WHO

    Dr Tedros

    Asalin hoton, Dr Tedros

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya gargadi matasa da su shiga taitayinsu kan coronavirus a wani taron manema labarai da yake yi a kowacce rana.

    Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce: "Daya daga cikin abin da muka gano shi ne, duk da cewa dattijai sun fi kamuwa (da coronavirus) hakan ba ya nufin matasa sun gagare ta.

    "Bayanan da muka samu daga wasu kasashe sun nuna akwai 'yan kasa da shekara 50 da yawa da suke bukatar kulawar likitoci.

    "A yau ina dauke da sako ga matasa: ba ku fi karfin wannan cuta ba. Wannan cuta ka iya kwantar da ku na tsawon makonni ko kuma ma ta halaka ku. Ko da ba ku kamu ba, zirga-zirgar da kuke yi ka iya zama sanadiyyar rayuwa ko mutuwar wani."

    Karin abubuwan da ya fada a taron manema labaran:

    • Ya nuna damuwa kan yadda cutar ka iya "samun gindin zama a kasashen da ba su da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya
    • Ya bayyana cewa "durkushewar kasuwar kayayyakin bai wa likitoci kariya ta kara ta'azzara lamarin"
    • Ya yaba wa 'yan kasuwa "bisa kokarin da suke yi na taimaka wa duniya baki daya"
    • Ya kuma ce WHO "na aiki da wasu kamfanoni domin kerawa da samar da...kayayyakin gwaje-gwaje"