Yadda gabatar da kasafin kudin Najeriya ya kasance

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai kan yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na 2020 a zauren majalisar dokokin kasar.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Mustapha Musa Kaita

  1. To a nan mu ma muka kawo karshen wannan shirin na kai tsaye. Ku ci gaba da kasance wa da BBC Hausa.

  2. Girman kasafin 2020

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an samu karin kaso 9.75 cikin 100 a kan kasafin kudin shekarar 2019 na kusan naira tiriliyan 9.

    Hakan na nufin kasafin kudin Najeriya zai kama fiye da naira tiriliyan 10.

    Buhari
    Bayanan hoto, Lokacin da shugaba Buhari yake mika kasafin kudin 2019
  3. Buhari ya yi kira ga majalisa

    Shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokoki da ta guji yin tsaiko wajen amince wa da kasafin kudi, al'amarin da ya janyo tsaiko a kasafin kudin shekarun da suka gabata.

  4. Buhari ya mika daftarin kasafi

    Shugaba Buhari ya kammala jawabi inda ya mika kundin daftarin kasafin kudin na 2020 ga majalisar dokokin Najeriya

    @Presidency

    Asalin hoton, @NigeriaPresidency

  5. Kasafi ga ma'aikatu

    Aiki da gidaje – Biliyan N262

    Sufuri – Biliyan N123

    Hukumar ilmin matakin farko ta UBEC – Biliyan N112

    Tsaro – Biliyan N100

    Aikin gona – Biliyan N83

    Albarkatun ruwa – Biliyan N82

    Ilimi – Biliyan N48

    Lafiya – Biliyan N46

    Hukumar Raya Arewa maso gabas – Biliyan N38

    Birnin tarayya – Biliyan N28

    Neja Delta – Biliyan N24

  6. Ra'ayoyinku daga shafin Twitter, Kasafin kudin 2020

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  7. Kasafin ma'aikatu

    Shugaba Buhari ya ce an kara wa hukumar Kare hakkin dan adam kudi da fiye da kaso 50 cikin 100, a daftarin kasasfin kudin na 2020.

  8. Kun san kasafin majalisar dokokin Najeriya?

    Shugaba Buhari ya ware wa majalisar dokokin Najeriya naira biliyan 125, inda aka ware naira biliyan 110 ga ma'aikatar shari'a a daftarin kasafin na 2020.

  9. Yadda aka gina daftarin kasafin kudi

    Shugaba Buhari ya ce an gina kasafin kudin ne a kan dala 57 na farashin gangar danyen mai.

  10. Abin da ya sa nake son kara haraji a Najeriya—Buhari

    Shugaba Buhari ya ce daftarin kasafin kudin zai kara harajin kaya daga kaso 5 cikin 100 zuwa 7.5 cikin 100.

    Ya ce za a yi amfani da harajin ne wurin inganta fannin kiwon lafiya da ilimi da gine-ginen hanyoyi.

    BBC

    Asalin hoton, Channelstv

  11. Buhari ya fara jawabi

    Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin gabatar da daftarin kasafin kudin 2020, inda da farko ya fara yaba wa majalisar dokokin kasar bisa kokarinsu na aiki tare da bangaren zartarwa.

    BBC

    Asalin hoton, Channelstv

  12. Kasafin kudin 2020 zai inganta rayuwar 'yan Najeriya - Lawan

    BBC

    Asalin hoton, Channelstv

    Shugaban Majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ce yana kyautata zaton kasafin na 2020 zai inganta rayuwar 'yan kasar sannan ya bunkasa tattalin arzikinsu.

    Ya bukaci majalisa da bangaren zartarwa da su yi aiki tare wajen ganin an aiwatar da kasafin cikin nasara.

  13. An fara bayanai a Majalisa

    Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan yana jawabin maraba ga shugaban kasa da 'yan tawagarsa.

    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Getty Images

  14. 'Sai Baba!'

    Wasu 'yan majalisa sun kaure da kiran 'Sai Baba' lokacin da Shugaba Buhari ya isa zauren majalisar wakilan kasar.

    Buhari
    Bayanan hoto, Buhari ya shiga Majalisa
  15. Abin da ya faru a baya

    A baya dai an kai ruwa rana tsakanin tsoffin majalisun da suka gabata da bangaren shugaban kasar inda aka yi zarge-zargen yin cushe a kasafin kudin 2016.

    A 2018 kuma an samu hatsaniya a zauren majalisar dokokin inda wasu 'yan adawa suka yi wa Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin shekarar.

    Shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar, Hon Abdulmumini Jibril, wanda ya zargi shugabannin majalisar da yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na 2016 ya janyo cece-ku-ce.

    Wannan al'amarin dai ya janyo kwamitin da`ar majalisar wakilan yin bincike dangane da zargin da Hon Abdulmumini Jibril ya yi na cushen.

    Majalisar wakilan ta zargi dan majalisar da bata wa shugabanninta suna da kuma saba wa ka`idojinta, al'amarin da ya janyo har aka dakatar da shi na watanni kafin kotu ta nemi a janye dakatarwar.

    Buhari
    Bayanan hoto, An yi wa shugaba Buhari ihu a 2017 lokacin gabatar da kasafin ga majalisa
  16. Majalisa ta yaba da kasafin bana

    Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da shugaban kasar zai gabatar da daftarin kasafin kudi a kan lokaci.

    Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sanya bangaren dokoki a cikin sha'anin kasafin kudin tun ma kafin shugaban ya je zauren majalisar.

    A cewarsa, shugaban ya amince a sanya kudin yi wa mazabu aiki (constituency projects) a kasafin kudin 2020, yana mai cewa ba za a samu matsala wurin amincewa da kasafin kudin a wannan karon ba.

    Buhari
    Bayanan hoto, Buhari a majalisar zartarwa lokacin sanya hannu kan daftarin kasafi ranar Litinin
  17. Kasafin kudin Najeriya

    Ranar Talatar nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na 2020 ga 'yan majalisar dokoki.

    Shugaban zai gabatar da kasafin kudin ne a zauren majalisar wakilai, inda 'yan majalisar dattawa za su hadu tare da na wakilai domin sauraren jawabin shugaban.

    Zai gabatar da kasafin kudin ne da misalin karfe biyu a agogon Najeriya.

    Buhari
    Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya sa hannu a kan daftarin kasafin kudin na bana