APC ta cinye kujerun shugabancin majalisar dokoki

Labarai da rahotanni game da rantsar da 'yan majalisar dattawa da wakilai na Najeriya, da kuma zaben shugabannin majalisun guda biyu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Karshe!

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotanni kai tsaye game da rantsar da 'yan majalisar dattawa da wakilai na Najeriya, da kuma zaben shugabannin majalisun guda biyu.

    Ku kasance da mu gobe Laraba wato Ranar Dimokradiyya a Najeriya don za mu sake kawo maku labarai da bayanai kai-tsaye game da abubuwan da za su faru a ranar. Mun gode.

  2. Ndume ya rungumi kaddara

    Sanata Ali Ndume ya rungumi kaddara bayan da ya fadi zaben neman shugabancin majalisar dattawa Najeriya, wanda Sanata Ahmed Lawan ya lashe.

    Bayanan bidiyo, Ali Ndume ya rungumi kaddara yayin da ya fadi zaben jagorancin majalisar dattawa
  3. An rantsar da Ahmed Wase

    Babban akawun majalisa ya rantsar da Ahmed Wase na jam'iyyar APC a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai.

  4. An rantsar da Gbajabiamila

    Babban akawun majalisa ya rantsar da Femi Gbajabiamila na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya.

    Gbajabiamila, wanda ke wakiltar mazabar ‎Surulere a jihar Legas, ya doke Umaru Bago daga jihar Naija, shi ma dan jam'iyyar APC.

  5. Ahmed Wase ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai

    Ahmed Wase ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai ne ba tare da an yi wani zabe ba saboda yadda aka kasa samun wanda zai kalubalance shi a zauren majalisar.

    Doka ta amince a rantsar da shi ba tare da gudanar da zabe ba saboda an kasa samun wanda zai fafata da shi a neman kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai.

  6. Gbajabiamila ya doke Umaru Bago

    Femi

    Asalin hoton, Facebook

    An bayyana sunan Femi Gbajabiamila na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin mutumin da aka zaba Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya.

    Gbajabiamila, wanda ke wakiltar mazabar ‎Surulere a jihar Legas, ya doke Umaru Bago daga jihar Naija, shi ma dan jam'iyyar APC.

    Gbajabiamila ya samu kuri'u 281 yayin da Umar ya samu kuri'u 76.

  7. An fara kidaya kuri'u

    An fara kidaya kuri'un zaben shugaban majalisar wakilan Najeriya.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

  8. Har yanzu ana cigaba da zabe

    Ana ci gaba da zaben Kakakin Majalisar Wakilai ta kasa inda ake fafatawa tsakanin Femi Gbajabiamila da kuma Umaru Bago - dukkansu 'yan APC ne.

    Za mu kawo muku yadda sakamakon zai kasance.

  9. Jawabin godiya daga Ahmed Lawan

    Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan na gabatar da jawabin godiya bayan zaben da aka yi masa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. An fara kada kuri'a

    An fara kada kuri'a a majalisar wakilai domin zaben Kakakin majalisar.

    Ana takara tsakanin Femi Gbajabiamila daga Legas da Umaru Bago daga Naija.

    Dukkansu 'yan jam'iyyar APC ne.

  11. Zaben Kakakin majalisa

    Ganin yadda 'yan majalisar wakilai suke da yawa, da alama za a dauki lokaci kafin gama kada kuri'a har zuwa kirga su.

    Akwai 'yan majalisa 360, wadanda ake sa ran dukkaninsu za su kada kuri'ar.

    Saboda yawansu ne ma ake kiran mutum hudu a lokaci guda domi su fito su kada kuri'arsu.

    Majalisar Wakilan Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  12. An gabatar da takarar Umaru Bago

    Dan majalisa Abubakar Yunusa na jam'iyyar APC daga Gombe ya gabatar da takarar Umar Mohammed Bago daga jihar Naija domin zama Kakakin majalisar wakilai.

    Sannan wani dan majalisa daga Benue ya goyi bayansa.

    Umar Muhammad Bago shi ne dan takarar da PDP ke mara wa baya.

    Ita kuwa jam'iyyar APC takarar Femi Gbajabiamila take goyon baya.

    Tuni kuma Hon Umar Bago ya amince da bukatar ya tsaya wannan takara.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

  13. An gabatar da takarar Gbajabiamila

    Dan majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin ya gabatar da takarar Femi Gbajabiamila daga jihar Legas domin zama Kakakin majalisar wakilai.

    Sannan kuma wata 'yar majalisa ta tashi domin goyon bayan matsayin na Abdulmumini.

    Magoya bayan dan takarar sun barke da tafi.

    Kuma tuni Gbajabiamila ya amince ya tsaya takarar kamar yadda aka nemi ya yi.

    Femi

    Asalin hoton, Twitter

  14. Gwamnan Legas ya taya Lawan murna, Ahmed Lawan ya doke Ndume

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. APC ta taya 'ya'yanta murna

    Jam'iyyar APC mai mulki reshen Birtaniya ta taya Sanata Ahmed Lawan da OMo-Agege murnar lashe zabe a matsayin shugaba da mataimaki na majalisar dattawa.

    Sun yi nasara ne a zaben da aka kada a dazu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Zaben Kakakin Majalisar Wakilai ne ya rage

    Bayan kammala zaben majalisar dattawa, a yanzu akawun majalisar zai tafi ne zuwa majalisar wakilai domin gudanar da zabe a can.

    Femi Gbajabiamila ne dai dan takarar da jam'iyyar APC ke mara wa baya, inda PDP ke mara wa Umar Mohammed Bago baya.

  17. Ahmed Lawan ya hau kujerarsa

    Sabon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya hau kan kujerarsa bayan an zabe shi kuma an rantsar da shi.

    Ya umarci akawun majalisar da ya fara rantsar da sabbin sanatoci a madadinsa.

    Za a yi rantsuwar ne jiha uku-uku a lokacin guda, wato sanatoci tara-tara.

    Lawan

    Asalin hoton, Channels

  18. An rantsar da Omo-Agege

    Sanata Omo-Agege na APC ya sha rantsuwa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, bayan da ya kayar da Sanata Ike Ekweremadu na PDP.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

  19. Omo-Agege ya yi nasara

    Sanatoci 105 ne suka kada kuri'a a zaben mataimakin shugaba - daya ya kaura ce - yayin da kuri'a daya kuma ta lalace.

    Omo-Agege ya samu kuri'u 68 yayin da Sanata Ike Ekweremadu ya samu 37.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

  20. Labarai da dumi-dumi, Omo-Agege ya lashe zabe

    Da alamu Sanata Omo-Agege na jam'iyyar APC ya lashe zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa, inda ya doke Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar PDP.

    Yanzu ana jiran a kammala kirge bayan an ware kuri'un da aka kada.