Yadda aka fafata a muhawarar jihar Nasarawa

Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An kawo karshen muhawara

    Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a mako mai zuwa don ganinj yadda za ta kaya a muhawar jihar Gombe.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper nake cewa sai mun sake haduwa.

  2. Za a yi muhawar ta gaba a Gombe

    A ranar Alhamis 17 ga watan Janairu BBC za ta je jihar Gombe don yin muhawara da 'yan takarar kujerar gwamnan jihar.

    Da fatan za ku tara don kawo muku muhawarar kai tsaye.

  3. An kawo karshen Muhawar

    An baiwa yan takara yan minti daya don tsokaci na karshe

    BBCGovDebate
  4. Ibrahim Isa ne ke jan ragamar muhawarar

    BBCGovDebate
  5. Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Abba Bara'u Mukhtar: BBC kinyi fice da har kika fara tinanin yin wannan muhawara a Nigeria wanda tini yakamata a ce gidajen talabijin dama na radio sun fara amma duk da haka yanxu kun bude kofa.

    Elbany Mohd Isah: Allah yasa yadda wannan abu yake kyau a Nasarawa yayi kyau a kano ameen

    Aminu Salihu Isa: Yayi kyau sosai BBC ina kallon wannan program daga Abbare, Lau a taraba state.

  6. Yadda wasu 'yan takara ke tallata kansu

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
  7. Muhawar da ake tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Ayuba Samaila Himmm nidai bakina da taba fatana BBC Hausa su taimaka su kawo wannan muhadara a sokoto.

    Bashir Sahal Yakubu Nguru: duk dai irin wadannan alkawuran da 'yan takarkarun gwamna suke dauka idan sun lashe zabe a jihar nasarawa muna fatan zasu cika wannan alkawari.

  8. Haruna Tangaza mai kula da yadda ake gudanar da muhawarar

    BBCGovDebate
  9. An bai wa masu nakasa damar yin tambaya

    Abubakar Musa shugaban Guragu. Nakasassu na tamabaya kan tanadin da aka yi na inganta rayuwar makarantu kan ililimi da lafiya da kawar da bara

  10. Editan BBC Hausa, Jimeh Saleh

    Editan sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh tare da Editan Abuja Yusuf Yakasai a lokacin da suke saurarar muhawarar da ake yi da 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa da BBC ta shirya.

    BBCGovDebate
  11. Mata da maza ne suka halarci wajen muhawarar

    BBCGovDebate
  12. Manyan jami'an BBC da suke saurarar muhawarar

    BBCGovDebate
  13. Yarima Hamzat Lambata: PDP a lokaci da kuke Kan mulki meyasa baku kawo ma talakawa Takiba?? Sai yanzune zakukawo bamu yarda da hakan ba.

    Abdullahi Aliyu Muhammed: Allah kasan mai gaskiya Allah kabashi daga Abdullahi Aliyu muhammed Kano.

    Abdullhi Muhammad: BBC Dan Allah kuzo Katsina

  14. Ana yi wa 'yan takara tambayoyi

    BBCGovDebate
  15. Labaran Maku

    Zai kafa kwamitocin zaman lafiya a kowane kauye wanda za su dinga bayar da rahotanni ako da yaushe

    Kyakkyawar dangantaka tsakanin jamaa da jamian tsaro zai taimaka wajen samun zaman lafiya.

  16. Yadda wasu 'yan takara ke tallata kansu

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
  17. Ombugadu na PDP

    PDP za ta dauki matakan kariya. Za su karfafa matakan amincewa juna tare da sanya sarakuna cikin alamarin,.

    Za su kawar da yaduwar kananan makamai ta hanyar amfani da naura wajen gano inda makaman suke tare da karbe su

  18. Kan zaman lafiya Sule na APC

    Zaman lafiya na da muhimmanci. Gwamnati ta yi kokari wajen. Dawo da zaman lafiya. Za su sanya sarakunan gargajiya wajen tabbatar da tsaro da tabbatar da cewar duk wanda zai tayar da fituna an sanshi yadda za a dauki matakai na tsaro.

  19. Yadda masu saurare ki bibiyar Muhawar da ake yi

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
  20. Kan batun tsaro an fara da Doma

    Doma ya ce zai duba batun yin garambawul a kan ayyukan maaikatan gwamnati, tare da inganta shi Babban dalilin rashin zaman lafiya kuma shine rashin zumunci.

    Za su maida hankali wajen inganta fahimtar juna tsakanin alumma kamar manoma da makiyaya.