Sai an jima
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo ma ku kai-tsaye, sai wani lokacin.
Zidane Zidane da Pochettino na Tottenham da Simone na Atletico Madrid ake tunanin za su maye gurbin Jose Mourinho a Old Trafford bayan ya raba gari da Manchester United.
Awwal Ahmad Janyau
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo ma ku kai-tsaye, sai wani lokacin.
Masharhanta na ganin Manchester United za ta yi la’akari da wasu bukatu kafin ta dauki sabon koci
Bukatun sun hada da:
Samun wanda zai yi amfani da ‘yan wasan da ta sayo da ke kasa domin farfado da kungiyar.
Wanda zai tayar da matasa.
Wanda ya fahimci tsarin kulub din musamman salon kai hare-hare.
Wanda kuma zai samar da yanayi mai kyau tsakanin shi da ‘yan wasa da kuma abokan aikinsa.

Asalin hoton, Reuters
Manchester ta raba gari da kocinta Jose Mourinho bayan tabarbarewar abubuwa a kulub din
A watan Mayun 2016 ne Mourinho ya zo Old Trafford, inda ya lashe kofin kalubale da Europa.
Amma yanzu tazarar maki 19 ke tsakanin Manchester United da Liverpool da ke saman teburin Premier.
Manchester ta kori Mourinho ne bayan ta kasa ganin sauyi duk da kudi fam miliyan £400 da ya kashe ya sayo ‘yan wasa 11.
Yanzu United tana matsayi na shida a tebur, kuma ta fi kusa da kasan tebur fiye da saman tebur idan aka yi la’akari da tazarar maki.
Kungiyar ta ce za ta maye gurbinsa da wanda ta san zai fahimci tsarin kulub din musamman salon wasan kai hare-hare.

Asalin hoton, Reuters
Korar Mourinho na zuwa ne bayan sun samu sabani da Pogba, dan wasan da kocin ya karbo daga Juventus kan fam miliyan £89.
Pogba ya soki salon Mourinho a wasan da Wolves ta rike United 1-1. Dan wasan na Faransa ya ce ya so ne ace suna kai hare-hare a wasan da aka fafata a Old Trafford. Wannan dalilin ne ya sa Mourinho ya karbe mukamin mataimakin kaftin daga Pogba.
Mournho ya ajiye Pogba a wasan da Manchester ta sha kashi hannun Liverpool a Anfield a ranar Lahadi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan sanar da korar Mourinho, Pogba ya wallafa wani sako a Twitter wanda ya janyo ce-ce-ku-ce.
Daga baya ya goge sakon.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi tsokaci game da korar Jose Mourinho.
Ya ce "Mutum ne mai son hamayya, kuma mai buri da yawa. Ban yi tunanin cewa watanni baya bai kasance cikin farin ciki ba.Ba dadi ka fuskanci irin wannan kalubale."
"Amma babu wanda zai karbe nasarorin da ya samu. Ina fatan ya san da haka a yayin da zai tafi."
"Koci ne da babu kamarsa," in ji Klopp.

Asalin hoton, Getty Images
“Da farko ina mika sakon fatan alheri a gare shi,” in ji Pochettino.
“Ina da kyakkyawar dangantaka da shi kuma wannan labari ne marar dadi”.
“Na san abin da ke faruwa a wata kungiya bai dame ni ba. Ina amika fatan alheri ne ga Jose.”
Da aka tambaye shi game da rade-radin da ake yi cewa zai koma United, sai ya ce “an dade ana yada irin wannan jita-jitar game da aikina a Tottenham – ba zan iya amsa irin wannan tambayar ba”.
Ya kara da cewa “Ina mayar da hankali a kan aikin da nake yi a nan.”

Asalin hoton, Getty Images
Kuna iya shiga shafinmu na Facebook ku bayyana ra'ayinku.
Tsohon fitaccen dan wasan Manchester United Rio Ferdinand ya ce ya kasance wadanda suke matukar kaunar Mourinho shekaru biyu da rabi da zuwansa Old Trafford.
Ya ce ya daidaita abubuwa a kulub din a lokacin da ake bukata. Ya ce kamar yadda ba za iya mantawa da nasarorinsa ba haka kuma lokaci ne na kawo sauyi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Michael Carrick zai jagoranci atisaye kafin Manchester United ta nada kocin rikon kwarya.

Asalin hoton, Getty Images
Maki 26 a wasanni 17 na Premier, shi ne mafi muni a tarihin Manchester tun kakar 1990-91.
Tazarar maki 11 tsakaninta da matsayi na hudu a tebur, kuma tafi kusa da kasan tebur fiye da saman tebur
An ci Manchester United kwallaye 29 karkashin jagorancin Mourinho fiye da kwallayen da aka ci Huddersfield da ke matsayi na biyun karshe a teburin Premier wacce aka ci kwallaye 28 a kakar bana.
Jose Mourinho ya amsa cewa akwai bukatar gyara a Manchester United, amma yana ganin ba adalci ba ne a kwatanta su da martabar kungiyar a shekarun baya.
Mourinho ya ce wasa ya canja a yanzu, don haka yana da wahala a iya maimaita abin da ya faru a baya.
"Yanzu akwai wahalar sayen manyan 'yan wasa," in ji shi.
"A shekarun baya, kananan kulub har rokon manyan kulub suke yi su saye zaratan 'yan wasannsu suna son sayarwa."
Ya ce ko Manchester United yanzu tana son 'yan wasan Tottenham Harry Kane da Dele Alli, ba za ta iya sayensu ba, sabanin yadda zamanin Sir Alex Ferguson ya karbo Michael Carrick kan fam miliyan 18 domin maye gurbin Roy Keane.

Asalin hoton, Reuters
Liverpool za ta hadu da zakarun Jamus Bayern Munich a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, yayin da kuma aka hada Manchester United da Paris St-Germain.
Karon farko ke nan da Manchester United ta hadu da PSG, wacce ta jagoranci rukuninsu da Liverpool.
Kungiyoyin gasar Premier, Manchester City da Tottenham za su hadu ne da kungiyoyin Bundesliga na Jamus, inda aka hada City da Schalke, Tottenham kuma da Borussia Dortmund.
Za a yi karawa ta farko ne a ranakun 12 da 13 da 19 da 20 a watan Fabrairu, karawa ta biyu kuma a ranar 5 da 6 da 12 da 13 na watan Maris.

Asalin hoton, Getty Images
Zidane ko Simeone ko Pochettino ko Arsene Wenger?
Wa Manchester United za ta dauka?
