Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta sanar da wanda zai tsaya mata takara a zaben 2019, Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta sanar da wanda zai tsaya mata takara a zaben 2019
An zabi gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia a matsayin dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben da za a yi a 2019 bayan kuri'in da ya samu da suka kai 1,991, wanda jami'in hukumar zabe Raymond Dokpesiya bayyana. A wani labarin kuma, an daga zaben fitar da gwani na gwamna a jihar ta Abia zuwa ranar Litinin sakamakon rashin isar jami'an hukumar zabe daga Abuja zuwa jihar saboda matsalar jirgi.


























