Karanta yadda aka yi karashen zaben gwamnan Osun
Jama'a duka-duka a nan muka zo karshen zaben wannan labarai da shairhi da muka yi ta kawo muku ta wannan shafin. Ku karanta yadda aka gudanar da karashen zaben gwamnan Osun ranar Alhamis a nan.
Labarai da sharhi game da karashen zaben gwamnan Osun inda dan takarar jam'iyyar PDP da na APC suka kara.
Abdulwasiu Hassan
Jama'a duka-duka a nan muka zo karshen zaben wannan labarai da shairhi da muka yi ta kawo muku ta wannan shafin. Ku karanta yadda aka gudanar da karashen zaben gwamnan Osun ranar Alhamis a nan.
Kakakin jam'iyyar adawa ta PDP, Kola Ologbodiyan, ya nemi hukumar zabe ta INEC da ta soke karashen zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Alhamis.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ologbodiyan ya ce abin da ya dace shi ne hukumar ta yi shelar cewar dan takaran gwamnanta ne ya ci zaben.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sakamakon zaben rumfa ta takwas a mazaba ta farko a karamar hukumar Orolu ya nuna cewar:
APC - 111
PDP - 03
ACD - 01
Kuri'un da aka soke- 03
Wani jami'i ma sa ido a zabe dan jam'iyyar APC, Olagundoye Adegboyega, ya ce babu gaskiya a zargin da 'yan PDP ke yi cewar an hana su zabe a karashen zaben gwamnan jihar da aka yi ranar Alhamis.
Adegboyega ya ce duk wanda yake da katin zabe an ba shi damar yin zabe.

An fara samun sakamakon zabe daga wasu rumfunar zabe
Zaben da aka yi a kauyen Adereti da ke karamar hukumar Ife South ya nuna cewar:
APC - 283
PDP - 15
SDP - 1
APA - 1
APGA - 1
UPN - 1
Hakazalika sakamakon zaben da aka yi a rumfar zabe ta biyar da ke Oṣogbo ya nuna cewar:
PDP - 165
APC - 299
SDP - 1
ABP - 1
MPN - 1
Kuri'un da aka soke - 6


Wani jami'in sa ido na jam'iyyar PDP, Omoloye Azeez Ajayi, ya ce shi ya ga 'yan siyasan da suka saka kayan 'yan sanda da na jami'an tsaron Civil Deefence.
Ya ce 'yan siyasan sun lakada masa duka a lokacin da ya ce gane wa idonsa yadda ake zabe a karamar hukumar Ile-Ife South.
An fara shirya kuri'un da aka kada a rumfar zabe ta biyar a Osogbo.

Wasu 'yan jam'iyyar PDP sun ce an hana su zabe a karashen zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Alhamis.
Mutanen sun ce 'yan APC ne suka hana su kada kuri'a a rumfar zaben da suka yi rijista.



Asalin hoton, NIGERIA POLICE
Rundunar 'yan sanda da aka tura aikin ba da kariya a zaben gwamnan jihar Osun ta ce ta kama mutum 16 da kayan zabe na jabu a karashen zaben gwamnan da aka yi a Osun ranar Alhamis.
Sanarwar da kakakin hukumar Folasade Odoro ta fitar, ta ce an kama mutanen ne da kayayyaki masu sa ido a zabe na jabu da kuma katin zama dan jam'iyya na PDP.
Mutanen da aka kama din sun hada da Moshood Adejare, da ke neman takarar kujerar dan majalisar wakilai a mazabar Orolu a karkashin jam'iyyar PDP da Oyelayo Dayo, dan jam'iyyar PDP a karamar hukumar Orolu da Olaoye Asimi, dan jam'iyyar PDP a karamar hukumar Orolu, da kuma Raimi Taofeeq sakataren jam'iyyar PDP a karamar hukumar Orolu.
Hakazalika a cikin muatanen da aka kama din akwai Gbenga Olapade da Charles Amibiogoiu da Ayomide Ayansola da Kayode Dada da Daramola Segun da Tunji Akinroyinmi da Kunle ADEDEJI da Habeeb Bahiru da Yisa Sodiq da Adeolu Bamijoko da Oladipo Samson da kuma Adeolu Bamidele.
Sai dai kuma sanrwar ba ta fadi hanzarin mutanen da ake zargi ba, kuma jam'iyyar adawa ta PDP ba ta ce komai ba game da kama wadannan mutanen da ake zargin ba.

Asalin hoton, NIGERIA POLICE
An kama wani wanda ake zargi da sayen kuri'u a Osogbo.
Wani jami'i mai sa ido a zabe ne ya kama shi kuma ya kai karansa ga 'yan sanda.
Sai dai kuma mutumin da ake zargin ya ce shi ba shi da laifi.

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce an warware matsalolin da aka samu na hana masu zabe da 'yan jarida da kuma masu sa ido a zabe zuwa rumfunar zabe kuma zaben na ci gaba a halin yanzu duk da cewa ana ruwa kamar da bakin kwarya a wasu wuraren.
Dazu ne dai hukumar ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter inda ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an kama 'yan jarida da masu sa ido a zabe.
Sai dai yanzu hukumar ta wallafa wani sako inda ta ce an warware matsalolin
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Duk da cewa ana yada jita-jita a kafafan sada zumunta cewar 'yan sanda sun tare hedikwatar jam'iyyar PDP na jihar, wakilin BBC ya ce shi bai ga motar 'yan sanda a girke a wurin ba.
Sai dai ya ce shi ya ga motocin 'yan sanda suna sintiri a kan tituna domin tabbatar da tsaro.

A rumfar zaben da ke Garaji Ọlọdẹ a kauyen Adereti, cikin karamar hukumar Ìfẹ́ South ne BBC ta ci karo da daya daga cikin kwamishinonin gwamantin Osun, Bola Ilori, da kuma Tope Adejumo wanda mataimaki ne na musamman kan tsaro ga gwamna Aregbesola .


Ga yadda mutane suka fito zabe a rumfar zabe ta takwas a karamar hukumar Orolu>



Wani jigo a jam'iyyar PDP ta jihar Osun, Diran Odeyemi, ya bayyana dalilin da ya sa shi da wasu 'yan jam'iyyar PDP a jihar ba su damu su je su roki dan takarar jam'iyyar SDP a zaben gwamnan, Iyiola Omisore, ba don neman goyon bayansa wajen karasa zaben da ake yi ranar Alhamis.
Da yake zantawa da BBC, Odeyemi ya ce 'yan siyasan da ke cikin jihar Osun sun san cewa Omisore ba shi da karfi a rumfunan zabe ukun da ake karasa zabe a kananan hukumomin Ile-Ife ne ya sa ba su damu su je su roke shi ba don neman ya taimaka musu don samun kuri'u.

Wakilin BBC ya tabbatar da cewar an katse zurga-zurgar motoci a karamar hukumar Ile-Ife South. Duk da cewar tun da safe mutane suka fito, ba a yarda motoci sun shiga karamar hukumar ba.

Duk da cewa ba a fara zabe a kan lokaci ba, masu zabe sun fito da sanyin safiyar ranar Alhamis don duba sunayensu a rijistar zabe a Ile-Ife South.
'Yan sanda sun tsaya tsayin daka don ganin cewa sun ba da kariya ga zaben da ake yi a karamar hukumar.

Mun samu labarin cewar babu wakilin PDP ko daya a rumfar zaben Olode da ke mazaba ta 011 a kauyen Adereti na Ile-Ife har zuwa misalin karfe 9:40 na safen nan.

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce ta samu rahotannin da ke cewa ana kama 'yan jarida da masu saka ido a karashen zaben gwamnan Osun da ake yi a wasu mazabu.
A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, INEC ta ce za ta yi bincike akan rahotannin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar zabe ta INEC ta ce za a hukunta duk wani wanda ya yi abin da ya saba wa doka a lokacin da ake karasa zaben gwamna a jihar Osun.
Kwamishinan hukumar INEC a jihar ta Osun, Segun Agbaje, shi ya shaida wa BBC wannan da safiyar Alhamis.
Agbaje ya ce za a yi zaben ne daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyu na rana, kuma wadanda suke kan layi zuwa karfe biyu za ba su damar kada kuri'a.
