Tambuwal ya koma PDP, Kakakin APC ya sauya sheka

Labarai da sharhi game da sauya shekar wasu jigajigan 'yan siyasa daga Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Abdulwasiu Hassan

  1. Sai wa?, Tambuwal ya koma PDP

    Wa zai sake sauya sheka daga APC? Kawo yanzu.

    Kusan dai dukkanin 'yan siyasar da ke kiran kansu 'yan sabuwar PDP a jam'iyyar APC mai mulki sun koma inda suka fito. Kuma magoya bayansu a jihohinsu za su bi iyayen gidajensu.

    Babban jigo a yanzu da ya rage a sabuwar PDP da suka rage a APC sun hada da kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara, kuma wasu na ganin shi ma yana kan hanyar ficewa daga jam'iyyar.

    Akwai kuma wasu tsoffin gwamnoni a majalisar dattawa da ke da kusanci da shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki da ake ganin za su iya fita daga APC.

    Kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara

    Asalin hoton, @HouseNGR

  2. Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka zuwa yanzu

    sanatoci
    • Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
    • Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal
    • Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed
    • Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto
    • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
    • 'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su
    • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
    • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
    • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC
    • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
    • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.
  3. PDP ta yi maraba da Tambuwal

    Babbar jam'iyyar adawar Najeriya ta PDP ta yi maraba da komawar gwamnan jihar Sokoto jam'iyyar ta PDP daga APC mai mulkin kasar.

    PDP ta yi hakan ne ta wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Dalilin da ya sa na fice daga APC —Tambuwal

    Tambuwal

    Asalin hoton, TAMBUWAL/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Aminu Waziri Tambuwal

    Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana dalilan da suka sa ya koma jam'iyyar PDP daga APC.

    A wani jawabin da ya yi wa magoya bayansa a gidan gwamnatin jihar Sokoto, Tambuwal ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda Shugaba Buhari bai kai ayyukan cigaba jihar ba.

    Ya kara da cewa ya dauki matakin ne saboda shugaban bai je jihar ya yi wa mutane jaje ba a lokacin da aka kashe wasu mutane a jihar.

    Hakazalika, gwamnan ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi wasu nade-naden a zo a gani ba daga jihar.

    A makon da ya gabata ne dai Tambuwal ya ce yana nazari a kan makomar siyasarsa a jam'iyyar APC din.

    Gwamnan na jihar Sokoto daya ne daga cikin jigajigan 'yan siyasar da suka fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC gabannin zaben shekarar 2015.

  5. Wasu hotunan Gwamna Tambuwal yayin da yake sanar da ficewarsa daga APC

    Tambuwal

    Asalin hoton, Sokoto Govt Twitter

    Bayanan hoto, Jama'ar Sokoto a yayin da suke tururwar sauraron jawabin Gwamna Tambuwal
    Tambuwal

    Asalin hoton, Sokoto Govt twitter

    Tambuwal

    Asalin hoton, Sokoto Govt Twitter

    Tambuwal

    Asalin hoton, Sokoto Govt Twitter

  6. Tambuwal ya koma PDP

    tambuwal

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamanan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bar APC.

    A wani jawabin da ya gabatar ga magoya bayansa a fadar gwamnatin jihar Sokoto, gwamnan ya ce shi ya koma jam'iyyar PDP.

    Kalli yadda ya sauya shekar a cikin wannan bidiyon:

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Me tsarin mulki ya ce kan ci gaba da kasancewar Saraki shugaban majalisa?

    Ko me masana shari'a me suke gani game da wannan mataki?

    Barista Muhammad Abdulhamid ya ce: "Tsarin mulki bai yi nazari kuma bai nuna karara cewa don ya bar jam'iyya zai bar kujerarsa ta shugaban majalisa ba.

    "Abun da tsarin mulki ya tanada shi ne sashe na 67G ya ce idan ka bar jam'iyyar da ka ke zuwa wata, idan akwai baraka, ko hadin gwiwa ko kawance ga waccar jam'iyyar, to za ka ci gaba da zama dan majalisar dattijai ko wakilai.

    "Maganar kasancewarsa shugaban majalisar dattijai kuwa, tsakaninsa da ita majalisar ne, idan ta ga ya dace sai ta kawo hujjoji a kan suna bukatar yin haka. Amma dole hujjojin su kasance kan doka."

  8. APC ta tuhumi Bukola Saraki

    Kwamitin gudanarwar na jam'iyyar APC ya tuhumi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da karya dokar APC jiya da yamma 'yan sa'o'i bayan ya bayyana sauya shekarsa daga jam'iyyar ta shafinsa na Twitter. Takardar tuhumar da aka ba shi ta nemi Saraki ya bayyana dalilin da zai sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba cikin sa'o'i 48 .

  9. Kakakin APC ya sauya sheka

    Babban mai magana da yawun jam'iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bar mukaminsa a jam'iyyar kuma ya sauya sheka daga APC.

    Bolaji ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter dazu.

  10. Kiraye-kiraye kan a tsige Saraki daga shugaban majalisa

    Tuni har wasu 'yan Najeriya sun fara kiraye-kirayen cewa kamata ya yi Abubakar Bukola Saraki ya sauka daga kan mukaminsa.

    Sanata Ali Ndume wanda dan jam'iyyar APC ne, ya ce 'da Saraki bai kasance a jam'iyyar da ta fi rinjaye a majalisar dattawa ba, da bai zama shugaban majalisar ba.'

    "Idan ka ce ka sauya jam'iyya zuwa wata, to ai bai kamata a ce ka ci gaba da rike wannan mukami ba," in ji Sanata Ndume.

    Ndume

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sanata Ali Ndume
  11. Wani tasirin sauya shekar za ta yi?

    Bayanan sautiSharhin Dr Kari kan ficewar Saraki daga APC

    Wani masanin kimiyyar siyasa, Dr Abubakar Kari, ya yi wa BBC bayani game da irin tasirin da sauya shekar da ake yi daga jam'iyyar APC mai mulki zai iya yi kan makomar jam'iyyar da kuma kan irin biyan bukatar da wadanda suka fice daga jam'iyyar za su iya samu.

    Ku latsa alamar lasifikar don sauraron sharhinsa.

  12. Kanwar Saraki ta jaddada goyon bayanta ga Buhari

    Gbemi

    Asalin hoton, Twitter/@Gbemisolasaraki

    Sai dai a yayin da ake wannan sa-toka-sa-katsi, kanwar shugaban majalisar wacce suke ciki daya Gbemisola Ruqayyah Saraki, ta jaddada goyon bayanta ga Shugaba Muhammadu Buhari.

    A wani sako a shafin Twitter, an ambato ta tana bayyana cewa: "Ina nan har yanzu da goyon bayan da nake bai wa Shugaba Muhammadu Buhari, har zuwa zaben 2019, da kuma ganin samun nasarar jam'iyyarmuta APC a jihar Kwara da ma kasa baki daya."

    Hakazalika wasu jaridun Najeriyar sun ruwaito wannan labarin.

  13. 'Maraba da dawowa gida, Saraki'

    Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, ya yi wa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, 'maraba da dawowa gida.'

    Ya wallafa sakon ne a shafinsa na Twitter bayan da Sanata Sarakin ya yi shelar komawarsa jam'iyyar hamayya ta PDP daga jam'iyyar APC mai mulki.

  14. An fara mayar da martani

    'Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani game da sauyin shekar Shugaban Majalisar dattawan kasar, Abubakar Bukola Saraki, mako guda bayan takwarorinsa 14 sun bar jam'iyyar APC mai mulki.

    Hakazalika, gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed da kuma galibin 'yan majalisar dokokin jihar ta Kwara sun bi sawun Saraki.

    Wasu 'yan majalisar dattijan Najeriya na jam'iyyar APCn sun ce ba su yi mamakin fitar Sanata Abubakar Bukola Saraki daga jam'iyyar APC ba.

    Yayin da ita kuwa babbar jamiyyar adawa ta PDP cewa ta yi tana farinciki da ficewar Senata Bukola Saraki.

  15. Barka da shigowa

    Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu rinka kawo muku labarai da sharhi game da guguwar sauya sheka da ake ci gaba da yi daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP.