Karshe
A nan muka kawo muku karshen bayanan abubuwan da ke faruwa a wannan rana ta Laraba 28 ga watan Maris a Najeriya da makwabtanta.
Sai kuma ranar Alhamis da misalin karfe 10.30 idan Allah ya kai mu.
Wannan shafin na kawo muku labarai da sharhi kan abubuwan da ke faruwa a yankuna daban-daban na Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana ranar Laraba 28 ga watan Maris, 2018.
Nasidi Adamu Yahya
A nan muka kawo muku karshen bayanan abubuwan da ke faruwa a wannan rana ta Laraba 28 ga watan Maris a Najeriya da makwabtanta.
Sai kuma ranar Alhamis da misalin karfe 10.30 idan Allah ya kai mu.
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya sauya matsaya kan shiga kasuwancin bai-daya na Afirka kafin lokaci ya kure masa.
Cif Obasanjo ya nuna matukar damuwa kan yadda Najeriya ta ki shiga tsarin kasuwancin bai dayan da kasashen nahiyar 44 na kungiyar Tarayyar Afrika suka cimma yarjejeniya a kai.
Jaridar PremiumTimes ta ruwaito Cif Obasanjo na cewa: "Masar ce ta fara tattaunawa don samar da Kungiyar Hadin kan Afirka amma ba ta karasa ba sai Najeriya ta ci gaba.
"Haka kuma Najeriya na gaba-gaba wajen tattauna wannan kasuwanci na bai-daya amma ga mamakina sai ta janye daga sanya hannu a yarjejeniyar.
A karkashin yarjejeniyar daidkanin kasashen Afirka 54 za su amince su rage harajin shigo da kayayyaki da nufin bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Asalin hoton, Getty Images
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim K. Idris, ya sauke kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi daga kan mukaminsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshhod ya aikewa manema labarai ta ce,an sauke shi ne saboda guduwar da mutum shidan da aka tsare bayan sun ba da shaidar cewa dan majalisar dattawan kasar Dino Melaye yana goyon bayan 'yan fashi da makami suka yi.
Amma a baya-bayan nan Sanata Melaye ya musanta cewa rundunar na nemansa a wata hira da ya yi da BBC.

Asalin hoton, NPF
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wasu barayin shanu sun kai hari kan wani kauye har sau biyu cikin kasa da sa'oi 24 kuma sun kashe mutane da yawa.
Wani mazauni kauyen na Bawardaji ya shaida wa BBC cewa mutane 13 ne aka kashe a farmakin da suka kai ranar Talata da rana, kuma ya ce sun sake koma wa kauyen ranar Laraba da safe inda suka bude wuta kan mutanen da suka taru domin jana'izar wadanda aka kashen.
Nan kuma mutane 12 aka tabbatar da mutuwar wasu kuma da dama sun bata.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kayyade albashin manyan jami'an gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan yawan albashin da kowanne dan majalisar dattawan kasar ke dauka.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Mohammed, ya aikewa manema labarai ta ce kowanne wata sanata yana daukar albashi da alawus da suka kai N1,063,860:00, wadanda suka hada da gundarin albashi N168,866:70, kudin sanyawa abin hawa fetur N126,650:00, kudin mataimaki na musamman N42,216:66, kudin ma'aikacin gida -126,650:00, kudin shakatawa N50,660:00, kudin abubuwan yau da kullum N50,660:00, kudin jaridu da mujallu N25,330:00, kudin tufafi -N42,216,66:00, kudin yi wa gida kwaskwarima -N8,443.33:00 da kuma kudin mazaba -N422,166:66
A kwanakin baya ne daya daga cikin 'yan majalisar dattawan Sanata Shehu Sani ya ce kowannensu na daukar N13m a duk wata
Ranar Laraba ne aka cika shekara uku da zaben shugaban kasar Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya lashe.
An yi zaben shugaban kasar ne ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2015.
Buhari ya lashe zaben ne inda ya samu kuri'a 15,424,921 yayin da Goodluck Jonathan ya samu kuri'a 12,853162.
Mr Buhari ya sha alwashin magance tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.
Shin kun gamsu da ayyukan da ya yi ya zuwa yanzu?

Asalin hoton, Getty Images
Ana can ana zanga-zangar nuna adawa da yarjejeniyar soji tsakanin Ghana da Amurka a birnin Accra.
Karkashin yarjejeniyar sojin amurka za su rinka atisaye da sojin Ghana, kuma Sojin Amurka za su rinka amfani da kayan aikin sojin Ghana.


A yau ne 'yan majalisar dattawan Najeriya suke tafka muhawara kan zargin da tsohon ministan tsaron kasar Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya ya yi kan sojojin kasar.
Janar Danjuma dai ya yi zargin cewa sojojin kasar ne ke mara wa 'yan bindiga baya wajen kawar da al'ummu a jihar Taraba, inda ya ce dole mutane su tashi tsaye don kare kansu.
Sai dai rundunar soji ta musanta wannan batu.
Za mu kawo muku karin bayani kan wannan muhawara da sanatocin ke yi.

Asalin hoton, Senate facebook
Najeriya ta samun kudin shigar da ya kai naira biliyan 557.9 a watan Fabrairun da ya gabata, wato kudin sun karu a kan wanda ta samu a watan Janairu.
Kasar ta samu naira biliyan 538.9 a Janairu.
Akanta Janar na kasar ya ce an samu karin kudin shigar ne saboda danyen man da aka sayar da kuma farashinsa sun karu, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
Tun da farko dai, ministar kudin kasar ta kirawo taron gaggawa da shugaban babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC kan biyan kudin shiga.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce wasu mutum shida da ake tsare da su sun kufce daga wajen ‘yan sanda a Lokoja babban birnin jihar Kogi a yankin tsakiyar Najeriya.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba, ta ce hudu daga cikin mutanen ana tuhumar su ne da aikata laifuka da suka yi zargin Sanata Dino Melaye ne ya sa su.
Rundunar ta ce dama tana neman dukkan wadannnan mutum shidan da kuma Sanata Melaye ruwa a jallo.
Amma a baya-bayan nan Sanata Melaye ya musanta cewa rundunar na nemansa a wata hira da ya yi da BBC.
Rundunar ta ce a yanzu tana binciken wasu jami’anta 13 da ake zarginsu da sakaci wajen tserewar mutanen.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da bayanai idan sun gan su ko sun san inda suke.

Asalin hoton, FACEBOOK/DINO MELAYE
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana can yana jagorantar taron ministoci da manyan jami'an gwamnati da ake yi ko wacce Laraba a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.
Taron na tattaunawa kan manyan batutuwan da suka shafi kasar.
Ku kasance da mu domin jin abubuwan da suka wakana a taron.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Sabon ministan kula da harkokin cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji, wanda dan asalin yankin renon Ingila ne ya fara ganawa da sarakunan gargajiya da limaman addinai na kirista da kuma na musulunci, hadi da wasu daidaikun jama'a na wannan yankin, domin yi musu bayani game da muhimmancin zaman lafiya da kuma rayuwa tare a cikin hadaddiyar kasa guda.
Wannan a hukumance, shi ne dalilin da ya sa ya ke ziyartar wannan yanki.
Sai dai kuma ta wani bangaren ana cewa an aika shi ne domin neman kashe wutar rikicin da take ta jawo asarar rayukan jama'a watanni 16 kenan da suka gabata.

Asalin hoton, AFP
Nan da wasu kwanaki masu zuwa ne jam’iyya mai mulki a Najeriya APC za ta sanar da ranar da za ta gudanar da babban taronta na kasa domin zabar sabbin mutanen da za su shugabancin jam’iyyar, in ji jaridar Daily Trust.
Wannan dai ya zamo wajibi, saboda soke tsawaita wa’adin shugabannin jam’iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar Talatar da ta wuce.
Dangane da haka yanzu jam’iyyar za ta zabi sabbin shugabanninta da za su shirya yadda za a gudanar da zaben fitar da gwani a matakin ‘yan majalisun dokokin tarayya da na jiha da na gwamna da kuma na shugaban kasar.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Jama'a barkanmu da saduwa a shirinmu na labarai da rahotanni kan abubuwan da ke wakana a kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi. Ni ne Nasidi Adamu Yahaya zan gabatar muku da shirin.