Yadda zaben kasar Ghana ya gudana
Wannan shafin ya kawo muku bayanai da rahotani da hotuna kan yadda aka yi zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a kasar Ghana.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
An rufe rumfunan zaben kasar Ghana
An rufe kada kuri'a a zaben kasar Ghana, wanda aka yi na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa na shekarar 2016.
Ana yin zabe cikin kwanciyar hankali a Tamale,
Ana gudanar da zabe a Tamale da ke Arewacin Ghana cikin kwanciyar hankali.
Ba a dai samu labarin barkewar rikicin siyasa ba.
Watakila saboda jami'an tsaro da ke yin sintiri a ciki da wajen birnin ne.

Yadda ake yin zabe a birnin Kumasi
Bayanan sautiBirnin Kumasi shi ne birnin na biyu mafi girma a kasar ta Ghana bayan Accra, 'Yan takarar shugaban kasa masu amsa Nana sun yi zabe
'Yan takarar shugabancin kasar Ghana masu amsa sunan Nana sun kada kuri'arsu a zaben da ake gudanarwa.
Daya namiji ne mai amsa sunan Nana Akufo-Addo, shugaban jam'iyar New Patriotic Party, wanda ya yi zabe a birnin Accra.
Dayar kuwa mace ce mai suna Nana Konadu Agyeman-Rawlings mai takara a jam'iyar National Democratic Party.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Nana Konadu Rawlings
Ana karfafa tsaro a lokacin da ake yin zabe
Jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da yan sanda na ci gaba da sintiri a birnin Kumasi domin tabbatar da tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Babu mutane da yawa a mazabar Malaga,
A wasu mazabun ba mutane kamar mazabar Malaga.
To amma a wasu wuraren akwai masu zabe da yawa, kamar mazabar Malam Dudu akwai mutane da dama a kan layi.
Kuma babban Jami'in mazabar ya shedawa BBC cewa yana fargabar da wuya za su kammala da masu zabe kafin lokacin da za a kammala kada kuri'a.



Yadda ake zabe da harkar kasuwanci a mazabar Sawaba,
Bayanan bidiyo, Tun da sanyin safiyar Laraba aka fara kada kuri'a a zaben kasar Ghana Fursunoni a Ghana na yin zabe a kasar
Fursunoni suna daga cikin masu kada kuri'a a zaben sugaban kasar Ghana da na 'yan majalissu.
Wannan shi ne karo na biyu da fursunonin ke yin zabe, bayan wanda suka yi a shekarar 2012.
A cewar wata kafar yada labarai da ke Ghana City FM a labarin da ta wallafa a shafinta na Intanet ta ce kimanin fursunoni 2,276 ne aka yi wa rijistar yin zabe a kasar ta Ghana.

Asalin hoton, Seth Kwame Boateng
Bin layi domin kada kuri'a
Jami'an zabe na taimakawa masu kada kuri'a hawa kan layi da bin ka'ida a wata mazaba da wakilin BBC Akweasi Sarpong ya ziyarta a birnin Accra:
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yawan mutanen da za su yi zabe
Ana kada kuri'a ne a mazabu dubu ashirin da takwas da dari tara da casa'in da biyu.
Haka kuma mutum miliyan goma sha biyar da dubu dari bakwai da uku, da dari tara da casain ne za su kada kuria a zaben shugaban kasar Ghana da na 'yan majalissu.

Zaben shugaban kasar Ghana da 'yan majalissu


Abubuwan da aka yi yakin neman zabe
Batun tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa su ne suka mamaye yakin neman zaben.
Tattalin arzikin kasar dai ya samu koma baya a 'yan shekarun nan.
Bayanan bidiyo, Halin da tattalin arzikin Ghana ke ciki Abubuwa biyar kan zaben Ghana da ya kamata ku sani
1. Masu suna John sune ke yawan shugabantar kasar
Tun shekarar 1992 masu suna John ne ke shugabantar kasar.
2. Tun shekarar 1992, jam'iyyu biyu ne kawai suka mamaye siyasar Ghana. Jam'iyyar National Democratic Congress ce ta shugaba mai mulki. Sai jam'iyyar New Patriotic Party ta hamayya.
3. A Duk lokacin da jam'iyyar Democrats ta lashe zaben shugaban kasar Amurka..... To sai ka ga Jam'iyyar NDC ma ta ci zabe a Ghana. Kuma idan Republican suka ci a Amurkan, haka ma jam'iyyar NPP ce ke lashe zaben Ghana.
4. A karon farko a tarihin, an samu mace ta farko Charlotte Osei, wadda ke shugabantar hukumar zaben kasar Ghana.
5. Ba a taba samun sauyin gwamnati a Ghana, ba tare da an yi zabe zagaye na biyu ba.

Bayanan hoto, Charlotte Osei ce ke shugabantar hukumar da ke kula da zabe a Ghana Mata masu ciki ba sa bin layin zabe
Mata masu ciki ba sa bin layi, ana basu dama su kada kuria da zarar sun je rumfar zabe.

An tantance mutane 99 a mazabar Zango B
Kawo yanzu mutane 99 sun kada kuria a mazabar Zango B, daga cikin mutane 639 kamar yadda wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai daga Kumasi a Ghana ya aiko mana da yadda ake tantance masu zabe.
Bayanan bidiyo, Tun da sanyin safiyar Laraba aka fara kada kuri'a An tsaurara matakan tsaro a Tamale
Wakilin BBC Thomas Naadi ya wallafa hoto a Twitter da ke nuna jami'an tsaro suna sa-ido kan yadda al'amura ke tafiya a yankin Tamale.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
, Wasu sun kada kuri'a sun koma gida,
Tuni wasu yan kasar ta Ghana suka kada kuri'un su kuma suka koma wajen sana'o'in su

Yadda ake tantace mutane a mazabar Zango B,
Bayanan bidiyo, Tun da safiyar Laraba aka fara yin zabe a Ghana Wakilin BBC ya kada tasa kuri'ar
Daya daga cikin ma'aikatan BBC, Akwasi Sarpong, wanda dan kasar ta Ghana ne, kuma a yanzu yana can domin aiko da rahotanni kan zaben, shi ma ya kada tasa kur'ar:
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X




