Bankwana
Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaye a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Ku ci gaba da kasancewa a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labarai da rahotannin da muka wallafa.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/09/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaye a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Ku ci gaba da kasancewa a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labarai da rahotannin da muka wallafa.

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Zimbabwe sun ce za su zaɓi giwaye 200 da za a yanka domin raba naman su ga mutanen ƙasar da ke shan wahala wajen samun abinci saboda tsananin fari.
Kudancin Afirka na fama da tsananin fari, wanda ƙwararu suka ce shi ne mafi muni a tarihi shekaru masu yawa.
Zimbabwe za ta zamo ƙasa ta biyu a yankin da ta yanka giwaye domin raba wa jama'a naman su a bana, bayan Namibia, wadda ta yanka giwaye fiye da 80 a watan da ya gabata.
Zimbabwe tana da giwaye aƙalla dubu ɗari, kuma ita ce ƙasa ta biyu da ta fi yawan giwaye a duniya, bayan Botswana.
Shekara 35 baya dai ƙasar ta taɓa yanka giwaye domin raba naman su ga mutane.

Asalin hoton, EPA
An gudanar da jana'izar Rebecca Cheptegei, ƴar wasan tseren Uganda wadda tsohon saurayin ta ya kashe ta hanyar cinna mata wuta.
Jagororin al'umma a yankin ta sun buƙaci a nemi ɗaya daga cikin titunan yankin da kuma filin wasa domin sanya sunanta a matsayin karramawa.
An dai riƙa gabatar da jawabai masu sosa rai na karramawa gare ta, daga ƴan wasa, da sauran mutane da suka fito daga sassa daban-daban, har da ƙasar Kenya.
Wasu masu jimamin suna sanye da baƙaƙen riguna ɗauke da saƙon wayar da kai a kan cin zarafin mata.
An dai zargi ƴan sandan Kenya da rashin ɗaukar matakan gaggawa domin ceton rayuwar Rebecca, duk da cewa ta kai masu ƙarar cewa rayuwar ta na cikin haɗari.
Matashiyar mai shekara 33 ita ce ƴar wasan motsa jiki ta uku da aka kashe a Kenya.

Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/Facebook
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana farin ciki a kan nasarar da dakarun sojin ƙasar ke samu a kan ƴan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.
Wata sanarwar da kakakin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Asabar ta ce nasarar da dakarun ke samu wani tabbaci ne cewa za su iya aikin wanzar da tsaro a faɗin ƙasar.
A ranar Alhamis dakarun Operation Hadarin Daji suka kashe riƙaƙƙen ɗan bindiga Halilu Sububu, wanda ya daɗe yana addabar jama'a a jihar Zamfara da Sokoto da kuma wasu sassan arewacin Najeriyta.
Dakarun sun kuma yi nasarar kashe wani ɗan bindigar mai suna Sani Wala Burki a wani samemen haɗin gwiwa da suka kai maɓoyar ƴan bindiga a Katsina da kuma Kaduna, inda suka ceto mutanen 13 da aka yi garkuw ada su.
Fadar shugaban Najeriyar ta ce nasarar da sojojin ƙasar ke samu ta biyo bayan umarnin da shugaba Tinubu ya bai wa manyan hafsoshin ne na su koma yankin Arewa maso Yamma da zama har sai an samu tsaro a yankin.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da tabbacin cewa zai ci gaba da tallafawa jami'an tsaron ƙasar domin cimma nasarar samar da tsaro ga jama'a.

Wani mummunar hatsarin kwale-kwale yayi sanadin nutsewar fiye da mutum 40 a garin Gummi na jihar Zamfara.
Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar, a mashayar 'yan daga da ke gulbin Gummi.
Jami'in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Abubakar Umar ya ce har ya zuwa yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutanen da suka nutse.
''Kawo yanzu sarkin ruwan yankin da sauran masu iyo na ci gaba da aikin ceto, don lalubo mutanen da kwale-kwalen ya kife da su, kuma kawo yanzu ko mutum guda ba a kai ga cetowa ba'', kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa galibi waɗanda ke cikin jirgin manoma ne da ke ƙoƙarin tsallaka kogin domin zuwa gonakinsu.
Kwamishinan yaɗa labarai da bunƙasa al'adu na jihar, Mannir Haidara Kaura ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce kawo yanzu a hukumance ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.
Ya kuma ƙara da cewa an ceto wasu daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su, kuma ana ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo mutanen da suka nutse cikin ruwan
Hatsarin na zuwa ne makonni bayan mummunar ambaliya ruwa da auka wa garin na Gummi, inda ta haddasa asarar dukiya mai ɗimbin yawa.
Batun kifewar kwale-kwale dai ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda a lokuta da dama hatsarin ke zuwa da muni sakamakon irin ƙazamin lokdin da ake yi wa jiragen ruwan.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu na gudanar da ganawar gaggawa sa'o'i bayan sanar da ɗage zaɓen ƙasar zuwa nan da shekara biyu masu zuwa.
A baya an tsara gudanar da zaɓukan cikin watan Disamba mai zuwa.
A shekarar 2018 aka cimma yaryajejeniyar zaman lafiya da ta bai wa shugaban ƙasar, Silva Kiir damar ci gaba da zama shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, yayin da tsohon abokan hamayyarsa, Riek Machar ya zama mataimakinsa.
Ƙasar Sudan ta Kudu ba ta taɓa gudanar da babban zaɓe ba tun bayan ɓallewar ƙasar a 2011.
Matakin jinkirta zaɓen zuwa shekara biyu nan gaba, bai zowa da jama'a da 'yan ƙasar da mamaki ba.
Shugabannin siyasar ƙasar ba su shirya wa gudanar da zaɓukan a ƙasar ba.
Hakan ne ma ke ƙara haifar da shakkun cewa suna ƙoƙarin tabbatar da kansu a ikon ƙasar mai arzikin man fetur.
Ofishin shugaban ƙasar ya ce ya kamata a gudanar da wasu muhimman abubuwa kamar rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar kafin gudanar da zaɓen.
Haka kuma jami'an ƙasar sun bayyana matsalolin tsaro da rashin shiryawa zaɓen a matsayin hujjar ɗage zaɓen.

Asalin hoton, Coordination HQ for PoWs
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta jagoranci musayar fursunonin yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.
Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce kowace ƙasa ta bayar tare da karɓar fursunonin yaƙi 103, kuma wannan shi ne karo na takwas da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke jagorantar musayar fursunoni tsakanin ƙasashen biyu.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta da aka saki a musayar fursunonin, yanzu haka na ƙasar Belarus domin samun kulawar likitoci.
A ranar Juma'a Ukraine ta ce ta karɓi wasu ƙarin fursunonin yaƙinta 49 da Rasha ta sako, ciki har da tsoffin dakarun tsaron birnin Mariupol da a yanzu ke hannun ikon Rasha.

An fara jana'izar 'yar wasan tseren Olympic 'yar asalin Uganda, Rebecca Cheptegei wadda tsohon saurayinta ya kashe a farkon wannan wata.

Ana yi wa matashiyar jana'izar ban girma ta soji - a ƙauyenta na Bukwo - kasancewarta mamba a rundunar sojin ƙasar.

'Yar wasan tserern mai shekara 33 ta mutu ne bayan tsohon saurayinta ya watsa mata fetur, sannan ya cinna mata wuta.

Cikin daren da ya gabata ne aka kai gawarta daga ƙasar Kenya, inda take da zama.

Mutuwar Rebecca Cheptegei ta sake farfaɗo da fargabar da ake da ita kan yawan hare-haren da aka kai wa mata a Kenya.
Shi ma dai tsohon saurayin nata da ake zargi da kasheta ya mutu, sakamakon raunukan ƙunan da ya ji.

Asalin hoton, AFP
Ministan Albarkatun ruwa da tsaftar muhallai na Najeriya, Joseph Utsev ya yi gargaɗin sake samun mummunar ambaliya a kogunan Neja da Benue.
Yayin da yake jawabi ga taron menama labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, Ministan ya ce an samu ƙaruwar ruwan da ke ƙwarara a kogunan biyu zuwa yankin Naija Delta da ke kudancin ƙasar.
'A yayin da muke jajanta wa al'ummomin jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Bauchi da sauran jihohin da suka fuskanci ambaliya, muna ƙara jan hankalin 'yan ƙasar game da yiwuwar sake fuskantar wata ambaliyar daga kogunan Benue da Neja da wasu yankunan yankin'', in ji ministan.
Kan haka ne mista Utsev ya yi kira ga mazauna yankin su ɗauki matakai domin kauce wa bala'in ambaliya a wasu sassan kudancin ƙasar.
Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar birnin Maiduguri ke fuskantar mummunar ambaliya da ta auka wa birnin sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin.
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce lamarin ya shafi kusan mutum miliyan biyu.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, bai nuna alamun amince wa Ukraine ta yi amfani da makamai masu cin dogon zango da suka ba ta, don kai harin cikin Rasha ba, bayan doguwar tattaunawa da Shugaba Biden na Amurka.
Shugabannin biyu ba su sauya matsayinsu na farko ba, na hana Ukraine amfani da makaman da ƙasashen Yamma suka ba ta don kai hari cikin Rasha ba.
Mista Starmer ya ce tattaunawar tasu ta taɓo batutuwa masu muhimmanci ciki har da batun yankin GAbas ta Tsakiya.
A nata ɓangare fadar shugaban Amurka ta bayyana damuwarta kan yiwuwar taimaka wa Rasha da makamai daga ƙasashen Iran da Koriya ta arewa.
Tun da faro shugaban Rasha, Vladimir Putin ya gargaɗi ƙasashen Yamma kada su kuskura su bari Ukraine ta yi amfani da makamansu don kai wa ƙasarsa hari.
Mista Putin ya ce yin hakan tamkar shiga yaƙin ne kai-tsaye ƙasashen Nato suka yi.

Asalin hoton, Dangote
Kwamitin sayar da ɗanyen man fetur da tatacce na shugaban ƙasa ya ce zai fara ɗauko kashin farko na tataccen mai daga kamfanin Dangote a gobe Lahadi 15 ga watan Satumba.
Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin wanda kuma shi ne shugaban hukumar tattara kudaɗen haraji ta ƙasar, (FIRS), Zacch Adedeji, ne ya bayyana haka ranar Juma'a.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban na FIRS ya ce daga ranar 1 ga watan Oktoba, babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL zai fara sayen ganga 385,000 a kowace rana daga matatar man ta Dangote.
Ya kuma ƙara da cewa “Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa an kammala duka yarjejeniyar fara ɗauko kashin farko na man fetur da aka tace daga matatar Dangote daga ranar Lahadi 15 ga watan Satumban da muke ciki'', kamar yadda kafofin yaa labaran ƙasar suka ruwaito.
Ya ci gaba da cewa matatar Dangoten za ta riƙa sayar wa Najeriya man fetur da na dizel da zai wadace ta, kuma za a yi cinikin ne da kuɗin ƙasar wato naira.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an Myanmar sun ce aƙalla mutum 230,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon wata mummunar ambaliya ruwa da ta biyo bayan guguwar Typhoon Yagi.
Shugaban gwamnatin sojin ƙasar, Janar Min Aung Hlaing ya roƙi taimakon ƙasashen duniya domin shawo kan matsalar da ta shafi wasu yankunan ƙasar ciki har da babban birnin ƙasar Naypyidaw.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ambaliyar ta yi ajalin mutuwar mutum 33. To amma rahotanni na cewa mutanen da suka mutu sun kai 160, akasarinsu a yankunan tsakiya da gabashin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce tuni gwamnati ta kafa tantuna domin tsugunar da mutanen da suka rasa muhallan nasu.
Guguwar Typhoon Yagi - da ta fi kowacce ƙarfi a nahiyar Asiya cikin wannan shekara - ta shafi ƙasasehn Vietnam da tsibirin Hainan da China da kuma Philippines

Asalin hoton, SPA
Kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 20 a kan tsohon shugaban harkokin tsaron ƙasar kan laifukan Rashawa.
Haka kuma kotun ta ci tarar Janar Khalid Bin Qarar al-Harbi, dala 250,000 tare da umartarsa ya maido da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 3.5 na rashawa da ya wawushe.
An samu tsohon jami'in - da ya riƙe wannan muƙami a ma'aikatar tsaro na tsawon shekara shida - da laifukan zamba da karɓar kuɗaɗen tsohiya da amfani da muƙaminsa wajen biyan buƙatun kansa.
Hukuncin shi ne na ƙarshe kuma babu damar daukaka kara. Ma'aikatar cikin gida ta ƙasar ta jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na ci gaba da yaƙi da duk wani nau'in cin hanci da rashawa.
Shugaba Biden na Amurka, da Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer sun ce sun yi tattauna mai zurfi kan Ukraine, amma ba su sanar da matsayarsu ba, kan buƙatar gwamnatin Ukraine na ba ta damar amfani da makami mai linzami da ke cin-dogon zango a kan Rasha.
Keir Starmer, ya ce tattaunarsu kusan ta ta'allaka ne kan dabarun da ya kamata a yi amfani da su, maimakon karkata a fanni guda.
A lokacin da yake ganawa da manema labarai, Mista Starmer ya musanta cewa Shugaba Putin na barazana ga shugabanni NATO ta hanyar gargaɗin yaƙi muddin aka ɗage takunkumi kan amfani da irin waɗannan makamai.
Ya kuma nuna cewa dole suna goyon-bayan Ukraine da kuma damarta ta kare kai.
Kafin ganawar manyan shugabannin biyu a birnin Washinton na Amurka, jakadan Rasha a MDD, Vassily Nebenzia ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dikin Duniya cewa idan aka kuskura aka yarje wa Ukraine amfani da irin wannan makami, to kasahen Nato za su faɗa cikin rikicin Nukiliya.
Masu binmu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Asabar.
Abdullah Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiyar.
Ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi, domin sanar da ku halin da duniya ke ciki.