Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/10/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    A nan muka kawo karshen wannan shafin da muke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fata kun ji dadin kasancewa tare da mu.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya nuna mana.

  2. Rikici tsakanin Hamas da mayaƙan Dughmush ya yi ajalin mutum 27 a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    An kashe akalla mutum ashirin da bakwai (27) a mummunan artabu da aka yi tsakanin jami'an tsaro na Hamas da mambobin kungiyar nan mai karfin gaske ta kabilar Dughmush a birnin Gaza.

    Wannan shi ne tashin hankali mafi girma da aka yi a tsakanin Falasdinawa tun bayan da Isra'ila ta dakatar da yakin da take yi a yankin. Dukkanin bangarorin biyu na zargin juna kan wanda ya janyo rikicin.

    Tun da farko Hamas ta kira jami'an tsaronta kusan dubu bakwai (7000), domin tabbatar da ikonta a yankin na Gaza, da Isra'ila ta janye, to amma kuma ana fargabar barkewar rikici tsakanin Falasdinawan.

  3. Ana yunƙurin kifar da gwamnatin Madagascar

    Madagascar

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Bisa ga dukkan alamu an fara yunkurin juyin mulkin soji a Madagascar, inda Shugaban kasar Andry Rajoelina, ya fito fili ya ce yunkurin kwace mulki ta haramtacciyar hanya na kan hanya.

    Rahotanni sun ce an nada janar din sojan da ke jagorantar dakarun kundumbala na kasar wadanda ke mara baya ga masu zanga-zangar neman shugaban ya sauka, a matsayin babban hafsan sojojin kasar.

    Tun da farko Janar Demosthene Pikulas ya ce dukkanin sojojin kasar na karkashin ikonsa. Matasan kasar sun fara zanga-zanga ne a kan karancin ruwa da wutar lantarki tu watan Satumba da ya gabata, lamarin da kuma sannu a hankali ya fi karfin gwamnati.

  4. Ƙasashen Turai sun fara amfani da na'urar daƙile kwararar baƙin haure

    EU

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara amfani da wata sabuwar na'ura a kasashen Tarayyar Turai, yayin da kasashe da dama na kungiyar ta EU, ke daukar matakan dakile matsalar kwararar bakin haure.

    Na'urar wadda ke tattara bayanan mutane - tana bin sawun mutanen da ba 'yan kasashen na Tarayyar Turai ba, wadanda suke shiga da kuma fita daga yankin kasashen na EU da kuma kasashen Turai hudu da ba sa kungiyar - jumulla kasashe 29 da ake kira yankin Shengen, wadanda ba su da shinge a tsakanin iyakokinsu.

    An bullo da amfani da na'urar ne domin gano wadanda suka wuce wa'adin zama da takardar izinin shigarsu - biza - ta kunsa, da kuma hana shigar bakin haure. Gwamnatin Sifaniya ta ce ta yi nasarar fara amfani da sabon tsarin.

    Ana sa ran za a fara amfani da sabon tsarin a fadin yankin kafin karshen watan Afirilu na shekara mai zuwa.

  5. Rikici na ƙara ƙazancewa tsakanin Afghanistan da Pakistan

    Pakistan da Taliban

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Gwamnatin Taliban ta tabbatar da kai hari kan dakarun Pakistan a wasu tsaunuka da ke iyakokin ƙasashen biyu.

    Kakakin gwamnatin Taliban ya ce an kashe sojojin Pakistan guda 58 a abin da ya bayyana da "mayar da martani." Ya ce Pakistan ta yi karan tsaye ga dokokin sararin samaniyar Afghanistan ta hanyar harba bam a wata kasuwa a cikin ƙasarta a ranar Alhamis.

    Sai dai Pakistan ta musanta adadin da Taliban ta bayyana na waɗanda aka kashe, inda ta ce an kashe mata jami'ai 23, sannan ta ce dakarun nata sun nasarar mayar da martani, "inda suka kashe ƴan Taliban da saura ƴan ta'adda masu goya musu baya guda 200."

    Reuters ta ruwaito cewa Pakistan ta sanar da cewa ta rufe bakin iyakarta da Afghanistan.

  6. Afuwar Tinubu za ta ƙarfafa gwiwar masu aikata laifi - Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

    Tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya caccaki afuwar da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ga wasu waɗanda kotu ta yanke wa hukunci, inda ya ce shugaban na yanzu yana ƙarfafa gwiwar masu aikata laifuka ne.

    Atiku ya bayyana haka ne a kafofinsa na sadarwa, inda ya ce asalin afuwar wata dama ce da shugaban ƙasa yake da ita a kundin tsarin mulki, "domin rangwame da tausayi. Kuma idan aka yi amfani da damar yadda ya dace, tana taimakawa wajen ƙarfafa adalci da ƙara aminci da yarda tsakanin mutane da gwamnati."

    "Amma abin ban haushi, wannan afuwar da gwamnatin Tinubu ta yi tamkar mayar da hannun agogo baya ne. Matakin afuwa ko rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai ga waɗanda aka yanke wa hukunci bayan aikata manyan laifuka kamar safarar miyagun ƙwayoyi da garkuwa da mutane da kisa da cin hanci ba ƙaramin mayar da hannun agogo baya ba ne, sannan hakan zai ƙara ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa, "Abin da ya fi ɗaga hankali shi ne abin da ya fito cewa kashi 29.2 na waɗanda suka ci moriyar afuwar waɗanda aka kama ne da laifukan da suka danganci safarar ƙwayoyi, lamarin da ya zo a daidai lokacin da matasanmu ke fama da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi."

  7. An gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasashen Turai

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    An gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a duk fadin Turai. Masu zanga-zangar sun toshe layukan dogo kusa da babbar tashar jiragen ruwa ta Rotterdam a Netherland.

    A babban birnin kasar Switzerland, Bern, an yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi kokarin keta shingen da ke kusa da majalisar dokokin kasar.

    An kuma gudanar da zanga-zanga a birnin Oslo na kasar Norway kafin da kuma lokacin da ake wasan kwallon kafa na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya inda Norway ta lallasa Isra'ila da ci biyar da nema.

    An yi ta yi wa 'yan wasan Isra'ilar ihu kafin a hura tashi. A birnin Landan, dubun dubatar masu zanga-zangar ne suka gudanar da ita cike da shakkun kan yarjejeniyar da aka cimma a Gaza za ta kawo karshen yakin.

    Daya daga cikin masu zanga zangar kenan, ke cewa ina ganin dole gwamnati ta dauki mataki la'akari da yawan masu zanga zangar nan, wannan yarjejeniya da aka cimma ba abar yadda bace dari bisa dari.

  8. Labarai da dumi-dumi, Malaman jami'a a Najeriya za su fara yajin aiki

    Tambarin Jami'ar Ahmadu Bello

    Asalin hoton, Ahmadu Bello University

    Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya Asuu ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aiki daga gobe Litinin na tsawon mako biyu.

    Academic Staff Union of Universities (Asuu) ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa'adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.

    Shugaban Asuu Farfesa Chris Piwuna ya faɗa yayin taron manema labarai a Abuja cewa matakin ya zama dole "saboda gazawar gwamnatin wajen biyan buƙatunmu".

  9. Ɗan'adawa Issa Bakary ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen Kamaru

    Issa Tchiroma Bakary

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗantakarar adawa Issa Tchiroma Bakary ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru.

    Bakary na takara ne a jam'iyyar Cameroon National Salvation Front (FSNC), inda yake fafata wa da sauran 'yantakara tara - ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya.

    Shi da Bello Bouba Maigari ne mafiya shahara daga arewacin ƙasar, kuma ana sa ran masu zaɓe miliyan takwas ne za su kaɗa ƙuri'a a yau ɗin.

    Issa Tchiroma Bakary

    Asalin hoton, Reuters

  10. Taliban ta yi iƙirarin kashe sojojin Pakistan 58

    Dakarun sojin Taliban

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta tabbatar da kai hari kan dakarun maƙwabciyarta Pakistan a wurare da dama da ke iyakarsu ta arewaci.

    Wani mai magana da yawun Taliban ya ce sun kashe dakarun sojin Pakistan ɗin 58 a abin da ta kira "na ramuwa".

    Ta yi iƙirarin cewa Pakistan ta keta alfarmar sararin samaniyarta kuma ta kai hari a wata kasuwa ranar Alhamis.

    Pakistan ta musanta adadin tana mai cewa sojojinta 23 ne suka mutu a gwabzawar da ta jawo kashe mambobn Taliban 200.

    Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan Mohsin Naqvi ya yi iƙirarin cewa harin na Taliban "ba shi da wani dalili" kuma fararen hula suka kai wa hari. Ya sha alwashin ramuwar gayya.

  11. Shugaban Kamaru Paul Biya ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen shugaban ƙasa

    Paul Biya

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Kamaru Paul Biya ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana yau a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

    Biya mai shekara 92 na neman wa'adi na bakwai a mulkin ƙasar, yayin da 'yantakara tara ke neman kawo ƙarshen mulkinsa na shekara 43.

    Ya bayyana yanayin da ake kaɗa ƙuri'ar a matsayin "cikin natsuwa".

    Paul Biya
  12. China ta zargi Amurka da munana mu'amalar kasuwanci

    China ta zargi Amurka da yin amfani da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa ketare bayan da Shugaba Trump ya yi barazanar sanya karin haraji kan kayayyakin da kasar ke shiga da Amurkar.

    Sanarwar da ma'aikatar kasuwancin China ta fitar ta ce barazanar sanya haraji mai yawa a kowane bangare "ba hanya ce da ta dace da mu'amala da China ba".

    Mista Trump ya yi gargadin karin haraji bayan da Beijing ta ba da sanarwar sanya sabbin takunkumai kan albarkatun kasarta da ake fitarwa zuwa Amurka.

    China ce ke sarrafa kashi 90 cikin 100 na albarkatun kasar da ake samawarwa a duniya, inda take amfani da su wajen kera kayayyakin fasaha kamar motoci da wayoyi da na’urorin amfanin soji.

  13. 'Yansanda sun ce sun kama 'yanfashin one-chance huɗu a Abuja

    Kayayyakin 'yanfashi a Abuja

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum huɗu da take zargi da yunƙurin fashi a cikin mota da ake kira one-chance tare da ceto mutum biyu.

    Wata sanarwa ta ce tun a ranar 8 ga watan Oktoba ne wata mace ta kira waya cikin gaggawa cewa wasu sun yi garkuwa da ita a yankin Life Camp, inda suka nemi fansar naira miliyan 1,000,000.

    "Bayan samun rahoton...an kama waɗanda ake zargi ranar 9 ga wata a ƙauyen Dape bayan fafatawa da 'yansanda," in ji sanarwar.

    "An ceto Comfort Habila [mace] da Aliyu Adams [namiji]. Amma an wuce da Aliyu Asibitin Gwarimpa cikin gaggawa saboda raunukan da ya ji bayan caccaka masa wuƙa."

    Sanarwar ta ce bincike ya nuna waɗanda ake zargin sun sha aikata fashin one-chance a yankunan Bannex da Kado ta hanyar amfani da amfani da motoci masu baƙin gilashi.

    "Sun amsa cewa sun ɗauka da kuma yi wa mutum shida fashi, maza da mata, kafin a kama su."

  14. Magoya bayan Norway sun cika filin wasansu da tutocin Falasɗinu kafin lallasa Isra'ila

    Magoya bayan Norway

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Norway sun cika filin wasa da tutar Falasɗinu yayin wasan da ƙasarsu ta lallasa Isra'ila 5-0 ranar Asabar da dare.

    Tauraron ɗanwasa Erling Haaland na Manchester City ne ya ɗura wa Isra'ila uku rigis, sai kuma 'yanwasan Isra'ilar biyu da suka ci gidansu da kansu a wasan na neman gurbi a gasar Kofin Duniya.

    'Yankallo sun yi ife-ife da waƙoƙin "Free Free Palestine" - wato "A 'Yanta Ƙasar Falasɗinu" - yayin wasan.

    Tun kafin fara wasan, ɗaruruwan masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa sun hau titunan Oslo babban birnin ƙasar.

    Magoya bayan Norway

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Norway

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Tinubu zai tafi Italiya yau Lahadi

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tnubu zai kama hanyar zuwa Italiya a yau Lahadi domin halartar taron Aqaba na shugabannin ƙasashe kan tsaro.

    Fadar shugaban ƙasar ta ce taron Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a Afirka ta Yamma.

    "Za a fara taron ranar 14 ga watan Oktoba, wanda zai haɗa shugabannin ƙasa, da shugabannin soji daga Afirka domin tattauna ƙalubalen tsaro a Afirka ta Yamma," in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Asabar da dare.

    Sarkin Jordan Abdullah II ne ya ƙaddamar da taron a 2015 domin yaƙi da ta'addanci, wanda Masarautar Jordan da gwamnatin Italiya ke gudanarwa, a cewar sanarwar.

    "Shugaba Tinubu zai tattauna da wasu shugabanni a gefen taron domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin," kamar yadda fadar ta bayyana.

    Ministan Tsaro Badaru Abubakar, da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje Bianca Ojukwu, da Mai Ba da Shawara Kan Tsaro Nuhu Ribadu, da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA) Mohammed Mohammed, na cikin jami'an da za su yi wa Tinubu rakiya.

  16. Motocin kayan agaji sun fara shiga Gaza

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyon motar agaji a yankin Khan Younis da ke kudancin Gaza

    Hotuna da bidiyo sun fara nuna yadda manyan motoci ke shiga Zirin Gaza ɗauke da kayan agaji.

    Yarjejeniyar tsagaita wutar da Hamas da Isra'ila suka amince da ita a Masar ta ce "kayan agaji za su fara shiga Gaza nan take".

    Tun a ranar Alhamis Cogat, sashen sojin Isra'ila mai kula da shigar da kayan agaji Gaza, ya ce motoci 500 sun shiga zirin, kuma har Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta raba 300 daga cikinsu.

    MDD ta yi ƙiyasin cewa aƙalla motoci 600 ake buƙata a kullum domin daƙile matsalar yunwa da ake ciki a Gaza sakamakon hare-hare da kuma hana shiga da kayan abinci da Isra'ila ta yi.

  17. Masu zaɓe miliyan 8 sun fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen Kamaru

    Zaɓen Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, inda 'yantakara 10 za su fafata a tsakaninsu, waɗanda suka haɗa da Paul Biya mai shekara 92.

    Mista Biya ya kwashe shekara 43 uku a kan karagar mulki kuma yanzu yana neman wa'adin mulki na takwas.

    Akwai kuma wasu 'yantakara kamar Issa Tchiroma Bakary, da Bello Bouba Maigari, da Madame Tomaino Ndam Njoya, da sauransu.

    Sama da mutum miliyan takwas ne za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen, wanda ake yi wa kallon shi ne makomar matasan ƙasar saboda su ne mafiya rinjaye a al'ummar ƙasar.

    Rashin aikin yi tsakanin matasan ƙasar ya zama muhimmin batu a wannan zaɓe, amma kusan duka 'yantakarar sun yi alƙawarin shawo kan matsalar idan aka zaɓe su.

    Zaɓen Kamaru
    Zaɓen Kamaru
  18. Hamas za ta sako Isra'ilawa ranar Litinin

    Hamas

    Asalin hoton, Reuters

    Wani babban jami'in ƙungiyar Hamas Osama Hamdan ya ce za a fara sako mutum 48 da kungiyar ke rike da su ranar Litinin a wani bangare na shirin samar da zaman lafiya a Gaza.

    Yana magana ne bayan da wakilin Amurka na musamman Steve Witkof ya shaida wa wani taron dangin mutanen da ake tsare da su cewa za a saki yan'uwansu ba da jimawa ba.

    Wasu Jami'an diflomasiyyar Qatar uku sun mutu a wani hatsarin mota kusa da Sharm El-Sheikh na Masar, inda za a yi taron ƙasa da ƙasa na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza a ranar Litinin.

    Ana sa ran sama da shugabannin kasashen duniya 20 ne za su halarci taron.

  19. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa na ranar Lahadi.

    Za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Zirin Gaza da kuma zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar Kamaru.

    Sunana Umar Mikail, zan kasance da ku har zuwa ƙarfe 4:00 na rana.