Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/12/2025.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/12/2025.
Rahoto kai-tsaye
Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar
An fara bikin kirsimati a Gaza
Asalin hoton, gett
An fara bikin kirsimati a cocin katolika ɗaya tilo da ke Gaza.
Babban limamin ɗalikar Katolika a Isra'ila da Falasdin, Cardinal Pierbattista Pizzaballa, ya ce mabiya katolika na rayuwa cikin manyan ƙalubalen rayuwa.
A watan Yuli wani harin sra'ila ya kashe mutane uku a cocin.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce ya yi matuƙar nadamar harin, wanda ya ce ya faɗa a cocin ne a bisa kuskure.
Isra'ila za ta kafa sabbin matsugunnai 19 a gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Asalin hoton, Reuters
Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da kafa sabbin matsugunnai 19 a gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Ministan kuɗin Isra'ila mai ra'ayin riƙau, Bezalel Smotrich, ya ce matakin wata hanya ce ta hana kafa ƙasar Falasɗinu mai ƴancin kanta.
Matakin ya ƙara yawan matsugunnan yahudawa da aka kafa a cikin sheakaru uku zuwa kusan 70.
Na baya-bayan nan na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce kafa matsugunnan yahudawa a ƴan shekarun nan ya zarce wanda aka yi cikin shekaru takwas baya.
A bisa dokar ƙasa da ƙasa, dukkan matsugunnan da Isra'ila ke kafawa sun saɓa wa tanadin doka.
Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 347 a bana
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutane aƙalla 347 a bana, alƙaluman da suka zarce na shekarar da ta gabata.
Wani rahoto da ƙungiyoyin Reprieve da kuma ESOHR suka fitar ya ce mafi yawan waɗanda aka zartar wa hukuncin kisan a Saudiyya masu safarar miyagun ƙwayoyi ne, kuma fiye da rabin su ƴan ƙasashen waje ne.
Fursunonin baya bayan nan da aka zartar wa hukuncin kisa ƴan asalin ƙasar Pakistan ne masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Akwai kuma wani ɗanjarida da wasu matasa da suka aikata laifi tun suna ƙananan yara da kuma wasu mata biyar.
Hukumomin Saudiyya dai ba su amsa buƙatar BBC ta yin martani a kan ƙaruwar mutanen da ake zartar wa hukuncin kisa a ƙasar ba.
A jingine sabuwar dokar haraji sai an tantance zargin cushe - ADC
Asalin hoton, X/ADC
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta jinkirta aiwatar da dokokin haraji da aka yi wa gyara saboda zargin an cusa wasu tanade-tanade da a basu cikin dokokin da majalisa ta zartar.
Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya zargi gwamnati da yi wa sassa da dama na dokokin harajin, ciki harda tanadin bai wa shugaban ƙasa ikon kama duk wanda bai yi biyayya ga dokokin harajin ba, da kuma ƙwace ƙaddarorinsa.
“ADC na kiran a gaggauta dakatar da batun aiwatar da dokokin harajin 2025 da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu omin bayar da dama ga ƴan majalisa su gudanar da cikakken nazari a kai,'' in ji Bolaji Abdullahi.
ADC ta ce wannan kira ya zama wajibi saboda tantance zargin da ya biyo bayan bankaɗar da aka yi, da ta gano yadda aka yi cushen wasu ƙa'idoji a cikin dokokin harajin, duk da cewa majalisar dokokin tarayya ta riga ta kammala aiki a kai.
Jam;iyyar adawar ta ce irin wannan mummunar hanya ce aka ɗauka wadda ke barazana ga tanadin rabon ƙarfin iko da bibiyar ayyukan juna tsakanin ɓangaren zartarwa da na dokoki da kuma na shari'a a Najerya.
A cikin watan Yuni shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokokin harajin da aka yi wa gyara, bayan shafe watanni ana muhawara mai zafi a zauren majalisun ƙasar biyu, da kuma a tsakanin jama'ar ƙasar.
Amma a ƴan kwanakin nan, wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya ja hankalin majalisar cewa dokar da ake shirin fara aiwatarwa a ranar ɗaya ga watan Janairun 2026 ta yi hannun riga da wadda majalisar ta zartar ta kuma aikewa shugaban ƙasa.
Dakarun Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP 17
Asalin hoton, gett
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), da haɗin gwiwar ƴan sintirin sa kai sun yi nasarar kashe mayaƙan ISWAP 17 a wani samame da suka kai da sanyi safiyar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025.
Kakakin rundunar, Laftanal kanal Sani Uba, ya ce sun yi nasarar ne bayan tattara bayanan sirri a kan zirga-zirgar mayaƙan.
Ya ce dakarun sun ''tarwatsa maɓoyar ƴan ta'addan ƙungiyar JAS da na ISWAP a ƙauyukan Sojiri da Kayamla na jihar Borno.''
“Da misalin ƙarfe 2:24 na dare mayaƙan suka taru kan babura a wani waje da suke karɓar kayyakin da ake masu safara, lamarin da ya tabbatar da rahoton sirri da muke da shi. Daga nan sai dakarunmu da suke ɓoye suka buɗe masu wuta kuma suka kashe da dama a cikin su,'' in ji Laftanal Kanal Uba.
Ya bayyana cewa a yayin arangamar, dakarun sun kashe mayaƙan 17 kuma wasu da dama sun gudu da munanan raunuka a jikinsu.
Daga cikin kayan da aka ƙwato daga hannun mayaƙan akwai babura da kayan abinci da magunguna da kayan sawa da kuma bindigogi da alburusai kala-kala.
Za a riƙa buga Afcon bayan shekaru huɗu daga 2028
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirika, Patrice Motsepe ya sanar da sabon tsarin buga gasar cin kofin Afirika (Afcon) inda za a koma buga gasar bayan shekaru hudu daga 2028.
Tun daga 1968 ake buga gasar bayan shekaru biyu, bayan jinkirin da ya sa aka buga ta a 2012 da kuma 2013.
Amma daga gasar ta 2028, hukumomi sun ce za a koma ga sabon tsari na shekaru huɗu tsakanin gasar.
Motsepe ya kuma sanar da sabuwar gasa da aka yi wa laƙabi da 'African Nations League' wacce za a riƙa bugawa kowacce shekara a tsakanin ƙasashen Afirika daga 2029.
"Mun ɓullo da sabon tsari na inganta wasan ƙwallo a Afirika," in ji Motsepe.
Ya ƙara da cewa "Ina yin duk wani abu da zai kare muradun Afirika a wasan ƙwallo. Mun ɗauki mataki tsara jaddawalinmu domin ya tafi daidai da abin da ke gudana a duniyar ƙwallon ƙafa."
Sanarwar sabon tsarin buga gasar Afcon na zuwa ne gabanin fara gasar ta 2025 da za a fara yau Lahadi a Morocco.
Australia ta sanar da sabbin matakan tsaro bayan harin Bondi
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya bayar da umarnin duba tsarin aikin rundunar 'yansanda da kuma hukumomin tattara bayanan sirri na kasar bayan kisan jama'a da aka yi a bakin tekun Bondi a makon da ya gabata.
Mista Albanese ya ce nazarin zai duba ya ga ko hukumomin suna da iko da kuma matakan da ya kamata su kare lafiyar jama'ar Australia.
Ana makokin kasa baki daya, bayan cika mako daya da kai harin, wanda aka kai a wajen wani bikin addinin Yahudawa, inda aka kashe mutum 15.
Jami'ai sun yi amanna 'yan bindigan biyu, ɗa da mahaifi sun kai harin ne saboda rungumar akidar kungiyar IS.
Venezuela ta zargin Amurka da fashin jirgin dakon mai
Asalin hoton, X/Sec_Noem
Venezuela ta zargi Amurka da fashi a tekun da kuma satar mutane, bayan da gwamnatin Amurkar ta sake kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a yankin Karebiya.
Wannan shi ne jirgin ruwa na biyu da Amurkar ta kwace a gabar tekun Venezuela a watan nan.
Rahotanni sun ce jami'an Amurka sun ce jirgin na dauke da man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne, wanda ake amfani da kudin wajen daukar nauyin abin da suka kira ta'addancin miyagun kwayoyi, amma kuma ba tare da sun bayar da wata sheda ta tabbatar da hakan ba.
A ranar talata Shugaba Trump ya ce ya bayar da umarnin hana shigarwa da fitar da man da aka sanya wa takunkumi Venezuela.
Ƴanbindiga sun kashe mutane 9 a Afirika ta Kudu
Asalin hoton, AFP via Getty Images
'Yansanda a Afirka ta Kudu sun ce ana shirin fara wani gagarumin aikin farautar wasu mutane bayan mutum tara sun mutu, wasu karin goma kuma sun ji rauni bayan da aka bude wuta a wani wajen shan barasa a yamma da birnin Johannesburg.
Ƴansandan sun ce akwai kusan mutum 12 da ake zargi da harbin wadanda suka je wajen a wasu motoci biyu, suka kuma bude wuta.
A farkon watan nan ma akalla mutum 11, da suka hada da wani yaro aka harbe a wani haramtaccen wajen shan barasa a kusa da birnin Pretoria.
Afirka ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashen da aka fi kisan kai a duniya
Assalamu alaikum
Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.