Afcon Morocco: Najeriya ta kai zagaye na biyu da maki tara

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Uganda da Najeriya da na Tanzaniya da Tunisia a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan za ku tara nan gaba don kawo muku sharhi da bayanan gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.

    Za a buga sauran wasannin rukuni na biyar da na shida ranar Laraba.

    Daga nan a faɗa karawar zagaye na biyu daga ranar Asabar.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada nake muku fatan alheri

  2. Wasannin da za a buga ranar Laraba

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Karon farko da Super Eagles ta lashe dukkan wasa uku a rukuni, Uganda 1-3 Nageriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan da Najeriya ta yi nasara a kan Uganda, ta lashe dukkan karawa uku a cikin rukuni a karon farko tun bayan 2021.

  4. An kammala wasan Tanzaniya da Tunisiya, Tanzaniya 1-1 Tunisiya

    Tunisiya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka, bayan da ta tashi 1-1 da Tanzaniya a wasa na uku a rukuni na uku ranar Talata a gasar cin kofin Afirka a Morocco.

    Kenan Tunisiya ta kai bante da maki huɗu, ita kuwa Tanzaniya maki biyu ta haɗa kenan ta yi ban kwana da wasannin kakar nan.

  5. An tashi wasa tsakanin Uganda da Super Eagles, Uganda 1-3 Najeriya

    Najeriya ta samu kai wa zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan da ta doke Uganda 3-1 ranar Talata.

    Kenan Super Eagles ta haɗa maki tara a wasa uku a cikin rukuni, yayin da Uganda mai maki ɗaya ta yi ban kwana da wasannin.

  6. , Uganda 1-3 Najeriya

    Uganda ta samu ƙwana amma ba wani haɗari an fitar da ƙwallon

  7. Super Eagles ta kara yin canji, Uganda 1-3 Najeriya

    Salim Lawal ya canji Samuel Chukwueze.

  8. Katin gargaɗi ga ɗan wasan Najeriya Awaziem, Uganda 1-3 Najeriya

    An bai wa Chidozie Awaziem katin gargaɗi.

  9. Najeriya ta fitar da Victor Osimhen, Uganda 1-3 Najeriya

    Ɗan wasan tawagar Najeriya Akor Adams ya canji Victor Osimhen, wanda ƙwallo ɗaya ya ci a Afcon a Morocco a karawa da Tunisiya.

  10. Uganda ta kara yin canjin ɗan wasa, Uganda 1-3 Najeriya

    Tawagar Uganda ta saka Jude Ssemugabi cikin fili ya kuma maye gurbin Uche Ikpeazu.

  11. Har yanzu wasan Tanzaniya da Tunisia ba a kara cin ƙwallo ba, Tanzaniya 1-1 Tunisiya

    Har yanzu ana 1-1 tsakanin Tanzaniya da Tunisiya, kenan idan aka tashi haka Tunisiya ta kai zagaye na biyu da maki huɗu, ita kuwa Tanzaniya za ta samu maki biyu ta ukun teburi da kuma Uganda mai maki ɗaya.

    Kenan Tanzaniya da Uganda ba za su kai zagayen gaba ba, domin ba su da makin da ake bukata da zaɓi huɗun da za a haɗa da 12 da ci gaba da zagaye na biyu a Afcon da Morocco ke karɓar bakunci.

  12. Super Eagles ta yi canjin ƴan wasa, Uganda 1-3 Najeriya

    Zaidu Sanusi ya canji Bruno Onyemaechi, sannan Tochukwu Nnadi ya maye gurbin Paul Onuachu.

  13. Uganda ta zare ɗaya ta hannun Mato, Uganda 1-3 Najeriya

    Tawagar Uganda ta zare ƙwallo ɗaya ta hannun, Rogers Mato, wasan ya koma Uganda 1-3 Super Eagles

  14. Onyedika ya kara cin ƙwallo na uku na biyu a ragar Uganda, Uganda 0-3 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, ge

    Raphael Onyedika ya kara cin ƙwallo, kuma na biyu da ya zura a ragar Uganda.

  15. An bai wa Magoola na Uganda jan kati, Uganda 0-2 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun kafin Najeriya ta ci ƙwallo an bai wa Salim Magoola na Uganda Uganda jan kati.

  16. Super Eagles ta kara na biyu ta hannun, Uganda 0-2 Najeriya

    Super Eagles ta ci ƙwallo na biyu ta hannun Raphael Onyedika

  17. Osimhen ya nemi ragar Uganda, Uganda 0-1 Najeriya

    Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ya nemi raga amma an tare an kwallon, bayan da ya samu tamaula ta wajen Samuel Chukwueze.

    Ya kamata Super Eagles ta kara ƙwallo kada a farke wadda ta ci.

  18. Tanzaniya ta farke ta hannun Salum

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Tanzaniya ta farke ƙwallo ta hannun Feisal Salum da ya buga ƙwallo daga wajen da'irar Tunisiya, bayan da Novatus Miroshi ya bashi tamaula

  19. Najeriya ta canja Bassey, Uganda 0-1 Najeriya

    Kafin a koma zagaye na biyu Super Eagles ta canja, Chidozie Awaziem da ya maye gurbin mai tsaron baya, Calvin Bassey wanda tun farko aka baiwa katin gargaɗi saboda kada a samu kuskure ya yi ketar da za a yi masa jan kati.

  20. Uganda ta yi canjin ƴan wasa uku kafin a koma zagaye na biyu, Uganda 0-1 Najeriya

    Salim Magoola ya maye gurbin Denis Onyango mai tsaron raga da ya ji rauni.

    Allan Okello ya maye gurbin Travis Mutyaba, sannan Steven Mukwala ya canji Denis Omedi.