Sterling ya koma Feyenoord zuwa karshen kakar bana, Feyenoord

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Tsohon ɗan wasan Chelsea da Manchester City, Raheem Sterling ya koma Feyenoord mai buga babbar gasar tamaula ta Netherlands zuwa karshen kakar bana.
Ɗan wasan tawagar Ingila ya bar Chelsea a bana, bayan da suka amince da soke kwantiragin wata 18 da ta rage da yake karbar albashi fam 300,000 duk mako.
Sterling, mai shekara 31 ya tattauna da ƙungiyoyi da dama kafin ya yanke shawarar buga wa Feyenoord tamaula, wadda take ta biyu a teburin Eredivisie, wadda tsohon ɗan wasan Manchester United da Arsenal, Robin Van Persie ke horar wa.


















