Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 08/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 08/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.

    Ku duba ƙasa domin ganin labaran da muka kawo a yau.

  2. Inec ta wallafa sakamako 5,639 cikin 5,720 na zaɓen gwamnan Anambra

    Sakamakon zaɓen Anambra

    Asalin hoton, Inec

    Hukumar zaɓe ta Inec a Najeriya ta kusa kammala wallafa sakamakon zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke kudancin ƙasar.

    Zuwa yanzu Inec ta wallafa kashi 98.74 cikin 100 na sakamakon - ko kuma 5,639 cikin 5,720 - daga ƙananan hukumomi 21 na jihar.

    Hukumar na wallafa sakamakon ne a shafin intanet na musamman mai suna IReV, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanada.

    Sai dai hakan ba ya nufin sanar da wanda ya yi nasara a yanzu.

    Inec za ta sanar da wanda ya yi nasara ne kawai bayan kammala tattara dukkan sakamako a cibiya ɗaya a matakin jiha, sannan a karanto ƙuri'un da kowace jam'iyya ta samu, inda daga baya a faɗi wanda ya fi yawa da kuma wanda ya yi nasara.

    Za ku iya latsa nan domin ganin sakamakon kai-tsaye.

  3. Zaɓen Anambra: EFCC ta kama mutum uku da zargin sayen ƙuri'a

    Wani da ake zargi da sayen ƙuri'a a zaɓen gwamnan Anambra

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce ta kama mutum uku da zargin sayen ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka yi a yau Asabar.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, EFCC ta ce ta kama duka mutanen ne a ƙaramar hukumar Dukonukofia.

    Ta wallafa hotunan mutanen ɗauke da garin kuɗi, waɗanda ta ce ta kama su ana tsaka da kaɗa ƙuri'a.

    "Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binicke," in ji EFCC.

  4. Faransa ta nemi 'yan ƙasarta su fice daga Mali cikin gaggawa

    Faransa ta shawarci 'yan ƙasarta su fice daga Mali cikin gaggawa yayin da masu iƙirarin jihadi ke ci gaba da yi wa Bamako babban birnin ƙasar ƙawanya.

    Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta neme su da su fita ta hanyar amfani da jiragen haya tun kafin a rufe hanya, da kuma guje wa yin tafiye-tafiye.

    A gefe guda kuma, kamfanin fito mafi girma a duniya na MSC ya dakatar da ayyukansa a Mali saboda toshe hanyoyi da 'yanbindigar suka yi, wanda ya jawo ƙarancin man fetur a ƙasar da ke yammacin Afirka.

  5. Akwai yiwuwar Iraniyawa su yi hijira daga birnin Tehran saboda ƙarancin ruwa

    Ruwan sha a Tehran

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Iran ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar yin hijira daga Tehran babban birnin ƙasar idan ba a samu ruwan sama ba nan gaba kaɗan.

    Masoud Pezeshkian ya siffanta matsalar ƙarancin ruwa a birnin da "mai munin gaske" yana mai cewa za a fara auna ruwan idan ba a yi ruwan sama ba cikin mako biyu.

    Ƙasar mai bin tsarin addinin Musulunci ta shiga shekara ta shida a jere mai cike da fari, kuma wuraren ajiye ruwa na Tehran sun yi ƙasa sosai mafi muni cikin shekara 60.

  6. Inec ta wallafa kashi 86 cikin 100 na sakamakon zaɓen Anambra

    Masu zaɓe a jihar Anambra

    Asalin hoton, CDD

    Tuni aka kammala kaɗa ƙuri'a a kusan dukkan rumfunan zaɓen da ke jihar Anambra yayin da sama da mutum miliyan biyu ke zaɓen sabon gwamnan jihar.

    Abin da ya rage yanzu shi ne warewa da ƙirga ƙuri'un, wanda shi ma an kammla a wurare da dama.

    Hukumar zaɓe Inec na ci gaba da tattara sakamakon a matakin ƙananan hukumomin jihar 21 domin ƙirgawa da sanar da wanda ya yi nasara.

    Zuwa yanzu Inec ta wallafa kashi 86.10 cikin 100 na sakamakon zaɓen a shafinta na intanet IReV. Ma'ana ta wallafa sakamako 4,925 cikin jimillar 5,720 da ake buƙata.

    Za ku iya latsa nan domin ganin sakamakon kai-tsaye.

  7. Rashin kasafin kuɗin gwamnati ya shafi tashin jirage 2,000 a Amurka

    Jiragen sama a Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Zuwa yanzu an samu tsaiko ko kuma soke tashin jirage sama da 2,000 a Amurka sakamakon rashin kasafin kuɗi na gwamnati.

    Lamarin bai shafi jiragen da ke fita ko shiga ƙasar ba zuwa yanzu, amma da yawan ma'aikatan da ke bayar da hannu a filayen jirgi waɗanda ba a biya albashi ba sun kamu da rashin lafiya, kuma ba su je aikin ba.

    Haka nan an soke ayyukan bayar da tallafin abinci.

    Yayin da ake tsammanin rashin kasafin zai shiga sati na bakwai, majalisar dattawa za ta sake kaɗa ƙuri'a kan wani ƙudirin 'yan Republican na neman amincewa da kasafin da gwamnati za ta kashe.

    Amma 'yan jam'iyyar Democrat sun ƙi amincewa su kaɗa ƙuri'ar ba tare da gwamnatin Trump ta dawo da kuɗaɗen inshorar lafiya da ta soke ba.

  8. Abin takaici ne yadda ake sayar da ƙuri'a a Najeriya - Peter Obi

    Obi

    Asalin hoton, Screengrab/BBC

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour, Pater Obi ya yi zargin ana tafka maguɗi a zaɓen gwamnan jihar Anambra.

    Jigon siyasar daga kudancin Najeriya, wanda tsohon gwamnan jihar na Anambra ne, ya bayyana haka ne bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a akwati mai lamba 19 a mazaɓarsa ta 2 na unguwar Umidimakasi Agulu da ke jihar a zaɓen na yau Asabar.

    Ya ce bai ji daɗi ba yadda ya ga waɗanda suke shan wahala a sanadiyar rashin mulki mai kyau ne kuma suke sayar da ƙuri'arsu a kan kuɗi ƙalilan.

    "Da alama dimokuraɗiyya na ci gaba da lalacewa a Najeriya. Abin ban haushi mutanen da suke shan wahala ne suka ƙara jawo taɓarɓarewar lamarin wajen sayar da ƴancinsu. Na yi magana da mutane kan abubuwan da ke faruwa, babu abin da ake sai sayen ƙuri'a.

    "Misali matashin da bai da aikin yi, idan ya sayar da ƙuri'arsa a kan naira 30,000, nawa za a biya shi a watan gobe da babu zaɓe? idan ka sayar da ƙuri'arka, kamar ka sayar da iliminka ne da aikinka da ma komai na rayuwarka," in ji shi.

  9. Manyan hafsoshin tsaron Nijar da Mali da Burkina Faso sun gana a Niamey

    AES

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen ƙungiyar AES wato Nijar da Burkina Faso da Mali sun gana a Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tchiani.

    Taron wanda aka yi a ranar 7 ga watan Nuwamba, ya mayar da hankali kan yunƙurin ƙarfafa haɗakar tsaro a tsakanin ƙasashen na ƙungiyar AES domin tabbatar da tsaronsu, kamar kamfanin dillancin labarai ANP ya ruwaito.

    "Mun yi nisa wajen tattaunawa da duba yanayin tsaron ƙasashenmu da niyyar samar da haɗakar tsaro a tsakaninmu," in ji ministan tsaron Mali Janar Sadio Camara.

    Ya bayyana jin daɗinsa kan yunƙurin da suke yi, inda ya nanata cewa yana da ƙarfin gwiwar cewa za su samu nasara wajen tabbatar da tsaro a ƙasashensu.

    A ranar 29 ga watan Janairu ne ƙasashen uku suka fice daga ƙungiywar Ecowas a hukumance, bayan suka zargi ƙungiyar da alaƙa da Faransa da wasu ƙasashen yamma, inda suka ƙafa ƙungiyar Alliance of Sahel States wato AES.

    Yanzu dai ƙasashen sun fi ma'amala da ƙasar Rasha, sannan wasu sassansu na ci gaba da fama da matsalolin tsaro.

  10. Jam'iyyar Republican ta gaza tabbatar da ƙudurin biyan ma'aikata na musamman haƙƙoƙinsu

    AMURKA

    Sanatocin jam’iyyar Republican a Amurka sun gaza a kokarin da suka yi na karshe wajen tabbatar da an biya ma’aikatan da ke aiki na musamman albashinsu yayin da gwamnatin ke ci gaba da dakatar da ayyukanta.

    Ana ganin matakin zai samar da wata dama ta biyan ma’aikata kusan miliyan biyu da sojoji wadanda ake bukatar aikinsu hakkokinsu da aka jima ba a biya ba.

    Tun da farko ‘yan jam’iyyar Democrats sun yi watsi da matakin suna masu cewa ba daidai ba ne a rika dakatar da ayyukan gwamnati ba tare da an biya bukatun ma’aikatan bangaren lafiya da kuma masu tsaron lafiyar al’umma ba.

    ’Yan jam’iyyar ta Repubican wadanda ke samun goyon bayan shugaba Trump sun bukaci da a rage yawan kudin da za a kashe a cikin kasafin shekara mai zuwa.

  11. Kotun Ƙolin Amurka ta soke hukuncin ciyar da talakawa abinci kyauta

    Kotun koli

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun kolin Amurka ta dakatar da hukuncin wata karamar kotu da ya bayar da umarnin cewa gwamnatin Trump ta samar da abinci ga Amurkawa marassa karfi duk da dakatar da ayyukan gwamnatin da ake yi a kasar.

    Mutane fiye da miliyan 40 ne suka dogara akan abincin da gwamnatin ke rabawa, to amma duk da haka gwamnatin ta ce ba za ta iya samar da abinci ga dukkan mutanen ba sai dai ga wasu kalilan.

    Wannan watan ne karon farko da aka samu koma baya a Aikin rabon abincin a cikin shekaru 60 da aka shafe ana wannan aiki.

    Hukuncin kotun kolin zai yi tasiri ne a cikin kwanaki biyu kawai yayin da ake duba yiwuwar daukaka kara kan wannan batu.

  12. Ana neman fursunoni huɗu da aka saka da kuskure a Birtaniya

    Fursuna

    Asalin hoton, PA Media

    Har yanzu akwai aƙalla fursunoni guda huɗu da ake nema daga waɗanda aka yi kuskuren saka daga gidajen yari a Birtaniya.

    Fursunoni 262 ne aka yi kuskuren sakinsu a ƙasashen Ingila da Wales a watan Maris da ya gabata, wanda ƙari ne a kan kuskuren da aka yi na sakin guda 115 a bara.

    Gwamnatin ƙasashen dai na shan suka kan fursunoni masu manyan laifuka da ake zargin suna cikin waɗanda aka saka.

    An sake kama wani ɗan asalin ƙasar Aljeriya da aka ɗaure bisa zarginsa da aikata laifuka da suka danganci cin zarafi a ranar Juma'a.

    Kakakin ma'aikatar shari'a ta Birtaniya ya ce, "yawancin wadanda aka saka da kuskuren an sake kama su, sannan za mu yi duk mai yiwuwa tare da taimakon ƴansanda domin sake kamo sauran."

  13. Ba za mu halarci taron G20 a Afirka ta Kudu ba "saboda ana kashe fararen fata a ƙasar" - Trump

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce babu wani jami’in kasarsa da zai halarci taron kasashe 20 masu arziki a duniya na G20 da za a yi nan gaba a cikin watan da muke ciki a Afirka ta Kudu.

    A watan Satumbar da ya gabata ya sanar da cewa mataimakinsa JD Vance ne zai wakilici Amurka a taron, to amma yanzu ya tabattar da cewa babu wani jami'in gwamnatin Amurka da zai halarci taron.

    Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Mr Trump ya ce abin kunya ne a ce Afirka ta Kudu ce za ta karbi bakuncin taron.

    Sannan ya kara nanata zargin da ake cewa ana kashewa ko kuma kwacewa turawa fararen fata ‘yan Afirka ta Kudu gonakinsu a kasar.

  14. Al'ummar wasu ƙauyukan Kano na tserewa saboda fargabar hare-haren ƴanbindiga

    Kano

    Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa

    Mazauna garuruwan da ke bakin iyakokin jihar Kano da jihar Katsina a ƙaramar hukumar Shanono sun fara tserewa daga gidajensu saboda farbagar hare-haren ƴanbindiga.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yawancin mutanen yanzu sun koma rayuwa ne a garin Faruruwa da ke cikin Shanono saboda fargabar hare-hare a ƙauyukan.

    Rahotanni sun nuna cewa bayan sulhu da ƴanbindiga a jihar Katsina, ƴanbindiga da dama suna tsallakawa zuwa wasu ƙauyukan Kano da ke bakin iyakar shiga Katsina, inda suke kai hare-hare tare da garkuwa da mutane.

    Wani mazaunin garin Santar Abuja ya ce suna cikin fargaba da tashin hankali, "saboda suna iya zuwa a kowane lokaci. Shi ya sa muke komawa Faruruwa ko cikin Shanono domin samun mafaka."

    Ya ce yanzu ƙauyensu babu mutane, "wasu na kwana a titi, wasu a gonaki ko a gidan wasu. Ni ina da mata huɗu da yara 24, kuma dukkanmu mun tsere daga ƙauyenmu, yanzu muna zama ne tare da wani," in ji shi.

    Ya ce mutanen ƙauyukan Unguwar Kudu da 'Yan Kwada da Malamai da Santar Abuja da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse da Tudun Fulani da Kulki ne lamarin ya fi shafa.

    A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya, sannan ya buƙaci su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar, inda ya yi alƙawarin ba su duk gudunmuwar da suke buƙata.

  15. An ceto aƙalla mutum 28, da gawa ɗaya daga harin Rasha a Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu aikin ceto a birnin Dnipro na Ukraine sun yi aiki cikin dare ba kakkautawa bayan Rasha ta kai hari da jirgi mara matuki inda ya fada kan gidajen jama'a.

    Rahotani sun ce an ceto mutane 28 da ransu to amma an gano gawar wta mata a hawa na biyar na wani gini da harin ya shafa.

    Yanzu haka ana yi wa mutane da dama magani a asibiti. A bangare guda kuma, jami'an Ukraine sun ce Rashan ta kai wasu hare-hare da jirage mara matukan kan tashoshin makamashi da kuma tashar samar da hasken lantarki abin da ya jefa wasu yankuna na kasar zama cikin duhu babu wutar lantarki.

  16. Amurka ta cire wa Hungary takunkumi

    Amurka

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Amurka ta cire wa Hungary takunkuman da ta sanya mata na sayen mai da iskar gas din Rasha a wani mataki na mayar wa da Rasha martini akan mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

    Hakan ya biyo bayan wata ganawa da aka yi a Washington tsakanin Firaiministan Viktor Orban da kuma Shugaba Trump.

    Wakilin BBC ya ce wannan mataki na Donald Trump wata babbar nasara ce ga Victor Urban wanda ya ce takunkuman sun yi tattalin arzikinsa matukar illa.

    Jami’ai a fadar gwamnatin Amurka sun shaidawa BBC cewa dagewar zata dauki tsawon shekara guda ne kawai. Hungary wadda ta ke da alaka ta kut da Rasha duk da yakin da ta ke a Ukraine, za ta ci gaba da samun manta cikin sauki daga Rasha saboda saukin jigilarsa ta bututun man da aka shimfida tun da jimawa.

  17. Sudan ta buƙaci Amurka ta ɗauki mataki kan ƙasashen da ke taimakon mayaƙan RSF

    sUDAN

    Asalin hoton, Avaaz via Getty Images

    Jakadan Sudan a Amurka ya yi kira da a dauki kwararan matakai akan kasashen da ke goyon bayan mayakan RSF a yakin da ake a kasarsa.

    Muhammad Idris, ya yi wannan kiran ne bayan rahotanni da ake yadawa cewa mayakan RSF na aikata kisan kare dangi a birnin El Fasher.

    Wakilin BBC ya ce a kodayaushe gwamatin mulkin sojin Sudan na zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da kasancewa daya daga cikin kasashen da ke baiwa mayakan makamai, zargin da ta musanta duk da shaidar da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kwararru suka gabatar.

    Wannan kira na zuwa ne a matsayin wani ci gaba da aka samu a wani yunkuri da Amurka ke jagoranta na cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta wata uku domin kyale shigar da kayan agaji cikin Sudan din.

    Mayakan RSF sun amince da yarjejeniyar to amma bangaren gwamnatin kasar har yanzu na Nazari akai.

  18. Farawa

    Barkanmu da war haka, barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Da fata za ku kasance tare da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.