Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 24/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 24/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Ka samar da mafita ga 'yan Najeriya ba zargin 'yan adawa ba - Atiku

    ,

    Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi martani ga kalaman Shugaba Bola Tinubu da ke dora alhakin yunwa da talauci kan ‘yan adawa, inda ya bayyana zargin a matsayin kokarin kauce wa alhakin matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

    A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yakin neman zaben ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta kirkiri manufofin da suka janyo tsadar rayuwa sannan ta zargi wasu da bayyana matsalolin da jama’a ke ciki.

    Ya ce jam’iyyar APC ce ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekara takwas kafin Tinubu ya hau mulki, kuma yanzu gwamnatin tasa ta shafe sama da shekara uku tana jagoranci. A cewarsa, ‘yan Najeriya sun san waɗanda ke da alhakin tafiyar da harkokin ƙasar, don haka bai kamata a dora laifin tabarbarewar tattalin arziki kan ‘yan adawa ba.

    Atiku ya kuma soki wasu manufofin gwamnati, ciki har da cire tallafin man fetur da faduwar darajar naira, yana mai cewa wadannan matakai sun kara jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali. Ya yi tambaya kan yadda gwamnati ke tafiyar da wasu kudade da aka ware wa ayyuka daban-daban tare da neman karin bayani kan wasu gibin kudade da ake magana a kai.

    Ya ce babban abin da ‘yan Najeriya ke son ji shi ne matakan da gwamnati ta dauka domin magance yunwa, talauci da rashin tsaro, ba zargin ‘yan adawa ba. Atiku ya kara da cewa zaben shugaban kasa na 2027 zai bai wa masu kada kuri’a damar yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin Tinubu bisa yanayin rayuwar da suke ciki.

  2. Zanga-zanga ta bazu zuwa wasu ƙasashen Turai

    .
    Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun tsaya a gaban hayaki a Dandalin Skanderbeg yayin wata zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin Albania, Tirana

    Baya ga Faransa, an kuma gudanar da zanga-zanga a ƙasashen Belgium, Albania da Italiya ranar Asabar.

    A birnin Brussels, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma feshin barkono yayin da suka yi arangama da masu zanga-zangar adawa da gwamnati, waɗanda ke kiran a inganta yanayin tsarin ilimi.

    A babban birnin Albania, wato Tirana, dubban mutane sun halarci wata zanga-zangar adawa da gwamnati, inda 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

    A birnin Milan na Italiya, jami'an tsaro da sojoji sun tsaurara matakan tsaro kafin zanga-zangar da aka shirya kan hauhawar tsadar rayuwa.

    Gwamnatin Italiya ta amince da ƙarin matakan tsaro, lamarin da ya sa yanayi ya kasance cikin kwanciyar hankali fiye da karshen makon da ya gabata, lokacin da aka fuskanci tarzoma da kuma sace-sacen dukiyoyi a wasu sassan birnin.

    ,
    Bayanan hoto, Mambobin wata ƙungiyar masu adawa da akidar fasikanci (antifascist) suna halartar zanga-zanga a birnin Brussels na ƙasar Belgium.
  3. Houth ta ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin mai da filayen jiragen saman Saudiyya

    ,

    Kungiyar mayakan Houthi ta Yemen ta ce ta kai hare-hare kan bututun man fetur na Gabas maso Yammacin Saudiyya da kuma tashoshin tura mai da ke kan wannan hanya.

    A cikin wata sanarwa da kakakinta na soji, Yahya Yaseer, ya fitar, kungiyar ta ce ta kuma kai hare-hare kan wasu cibiyoyin mai da filayen jiragen sama a cikin Saudiyya.

    A cewar Saree, wuraren da aka kai wa hari sun hada da daya daga cikin cibiyoyin kamfanin Aramco a Yanbu, matatar man fetur ta Rabigh, da kuma Filin Jiragen Sama na Sarki Khalid da ke Riyadh.

    Ya kuma ce an kai hare-hare kan Filin Jiragen Sama na Sarki Fahad a Dammam, Filin Jiragen Sama na Najran, da kuma wani sansanin sojojin sama da ke Khamis Mushait.

    Har zuwa yanzu, Saudi Arabia ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan ikirarin na Houthiyawa ba.

    Sai dai Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta ce ragowar makamai masu linzami guda biyu da aka kakkabo daga Houthiyawa sun fado a yankin Wadi Al-Mughmas da ke kusa da Makka.

    Ma’aikatar ta kuma ce an gano wasu sassan makaman a biranen Jeddah, Taif da Rabigh.

  4. Likitoci sun ce Iran na cikin halin rashin tabbas ne

    Shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya bayyana halin da Iran ke ciki a matsayin yanayi na rashin tabbas, yana mai cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da kasancewa tsakanin zaman lafiya da yaƙi ba.

    Da yake jawabi a birnin Tehran, shugaban ya ce, “Kada mu ci gaba da kasancewa cikin wannan yanayi na rashin zaman lafiya kuma ba yaƙi ba. Ba za a iya yin tsare-tsare cikin yanayin rashin tabbas ba.”

    Pezeshkian ya yi waɗannan kalamai ne a yayin ƙaddamar da aikin ƙidayar jama'a da gidaje, inda ya jaddada cewa wajibi ne a kawo ƙarshen abin da ya kira ruɗani da rashin tabbas da ke tattare da halin da ƙasar ke ciki.

    Ya kuma ce ya sha yin kira da a kawo ƙarshen wannan yanayi, yana mai cewa marigayi jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ali Khamenei, wanda aka ce ya mutu a farkon sa’o’in Yaƙin Kwana Arba’in, ya taɓa bayar da umarnin cewa dole ne a kawo ƙarshen yanayin da ba yaƙi ba ne kuma ba zaman lafiya ba.

    Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar soja daga Amurka da Isra'ila ke ƙaruwa, yayin da jami’an Iran ma ke ƙara tsaurara kalamansu na martani a 'yan kwanakin nan.

  5. Sama da mutum 400,000 sun yi zanga-zanga a faɗin Faransa

    ,

    Kimanin mutane 410,000 ne suka fito zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar Faransa ranar Asabar, bisa alkaluman da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa ta bayar wanda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka wallafa.

    Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta CGT, ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar, ta ce adadin mahalarta ya kai kusan mutane 800,000, adadi da ya kusan ninka abin da gwamnati ta bayyana.

    A birnin Paris, ƙungiyar CGT ta kiyasta cewa mutane 250,000 ne suka halarci zanga-zangar, yayin da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da ‘yan sandan Paris suka ce mahalartan sun kai kusan 110,000.

    .
    ,

    Sau da yawa ana samun bambanci tsakanin alkaluman da masu shirya zanga-zanga da hukumomi ke bayarwa, saboda ƙididdige yawan taron jama’a na iya kasancewa da wahala, musamman idan mahalarta sun bazu a wurare daban-daban. Wannan ne ya sa ake yawan samun saɓani kan ainihin yawan mutanen da suka halarci irin waɗannan taruka.

  6. Houth te ce mutane 11 sun mutu a hare-haren Saudiyya kan Sanaa

    A

    'Yan tawayen Houthi sun ce akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Saudi Arabia ta kai a birnin Sanaa ranar Asabar.

    Tashar talabijin ta Al-Masirah, wadda Houthiyawa ke gudanarwa, ta ruwaito cewa an kai jerin hare-haren sama a sassa daban-daban na Sanaa. A cewar rahoton, ɗaya daga cikin hare-haren ya afka wa wani gida, inda ya kashe akalla mutum huɗu tare da jikkata wasu da dama.

    Rahoton ya kuma ce wani hari daban da aka kai kan wani ginin ma'aikatan masana'antar siminti ya yi sanadiyar mutuwar mata shida da wani yaro, yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka.

    Tun da farko, ƙawancen sojojin da Saudi Arabia ke jagoranta ya sanar da cewa ya kakkabo makamai masu linzami guda biyu da aka harba zuwa wasu biranen ƙasar.

    Yaƙin basasar Yemen, wanda ya lafa bayan tsagaita wuta da aka cimma a shekarar 2022, ya sake ruruwa a watan Yulin bana yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya ƙara faɗaɗa zuwa wasu sassan yankin.

  7. 'Yan sandan Jigawa sun kama mutane uku kan zargin satar wayoyin lantarki

    ,

    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane uku bisa zargin satar wayoyin lantarki da kuma a ƙananan hukumomin Guri da Dutse.

    Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Dutse ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.

    A cewar sanarwar, jami’an ’yan sanda na ofishin Guri sun kama wani matashi mai suna Abdullahi Maina mai shekara 23, mazaunin unguwar Fulatari a ƙaramar hukumar Nguru ta jihar Yobe, da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar 21 ga Oktoba.

    An ce an same shi da wata babbar wayar lantarki mai ƙarfin wuta da ya ɓoye a cikin duhu.

    ’Yan sandan sun ce sun kwace wayar domin ci gaba da bincike, yayin da ake ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

    A wani lamari makamancin haka, jami’an ofishin ’yan sanda na Dutse sun kama wasu mutum biyu, Ahmed Garba mai shekara 20 da Abdullahi Garba mai shekara 25, duk mazauna garin Jigawar Tsada a ƙaramar hukumar Dutse.

  8. Ni ba ɗan siyasa ba ne, ba kuma zan yi wa kowa kamfe ba - Sheikh Daurawa

    ,

    Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, Malam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shi ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zai yi wa wani ɗan takara yaƙin neman zaɓe ba gabanin babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027 mai zuwa.

    A kwanakin baya ne aka sanya sunan Malam Daurawa tare da Tsohon Thugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, Sheikh Abdallahi Pakistan cikin kwamitin ba da shawara kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na jam’iyyar APC a Kano. Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu masu sa ido kan al’amuran siyasa, waɗanda suka soki haɗa malaman addini da harkokin siyasa.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Daurawa ya ce abin da yake fata kawai shi ne "Allah Ya bai wa duk wanda zai yi adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙoƙinsu kuma ya inganta rayuwarsu nasara".

    Ya ce: “Ni ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zan yi wa kowa kamfen ba. Ina roƙon Allah Ya ba mu shugabanni masu gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah, waɗanda za su fifita muradun al’umma a kan maslahohinsu na kashin kansu.” Duk da cewa bai yi magana kai tsaye kan sanya sunansa cikin kwamitin APC ba, kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da malaman addini ke takawa a siyasar jam’iyya gabanin zaɓen 2027

  9. Ba don Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba - Kashin Shettima

    KASHIN SHETTIMA

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashin Shettima ya ce ba don taimakon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ba, da tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari bai samu nasarar shugabancin ƙasar ba.

    Shettima ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron ƙaddamar da yaƙin zaɓen Tinubu domin neman wa'adi na biyu a jihar Kaduna.

    Shettima ya ce Tinubu ya taimakawa ƴan arewa a lokuta daban-daban domin neman takarar shugabancin ƙasar.

    "Ya taimakawa Atiku domin takara a AD, sannan ya taimakawa Nuhu Ribaɗu a AC, sannan kuma ya taimakawa marigayi Muhammadu Buhari a 2015 da 2019."

    Shettima ya ce kasancewar Tinubu ya bayar da gudunmuwa ga ƴan takarar arewa a baya, yanzu lokaci ne da za a mayar da biki.

  10. Mun riga mun kassara arzikin man fetur ɗin Iran - Amurka

    Amurka

    Sakataren Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce shirin ƙasarsa na “lafta takunkumi kan tattalin arzikin Iran” ya yi wa hanyoyin samun kuɗaɗen man fetur na Iran mummunar illa.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X ranar Juma’a, Bessent ya ce: “Ma’aikatar Baitul Malin Amurka ta ƙaddamar da wani shiri na ware tattalin arzikin Iran domin ƙara matsa mata lamba tare da katse duk wata hanyar samun kuɗaɗen shiga ga rundunar juyin-juya-halin Musulunci (IRGC) da gwamnatin Iran. Cikin ƙasa da watanni biyu da fara wannan shiri, mun yi mummunar illa ga dukkan sassan hanyoyin samun kuɗaɗen man fetur na Iran.”

    Ya ƙara da cewa: “An rage yawan jiragen dakon mai da Iran ke amfani da su a ɓoye, babban tashar fitar da man fetur ta ƙasar ta kasance babu aiki sosai, sannan ajiyar man fetur da Iran ke da ita a cikin jiragen ruwa a teku ta ƙare.”

    Da yake magana kan matsalolin tattalin arzikin Iran, Sakataren Baitul Malin na Amurka ya rubuta cewa: “Talakawan Iran na ci gaba da fuskantar matsanancin rikicin tattalin arziki yayin da gwamnatinsu ke kashe albarkatun ƙasar wajen tashe-tashen hankula da abin da Amurka ke kira ta’addanci a ƙasashen waje, maimakon amfani da su wajen inganta rayuwar al’ummar cikin gida.”

    Bessent ya kuma ce Shugaban Amurka, Donald Trump, na ɗaukar matakan da shugabannin Amurka da suka gabace shi suka daɗe suna kauce wa ɗauka.

    A ƙarshe ya jaddada cewa: “Amurka ba wai kawai tana ƙoƙarin shawo kan barazanar Iran ba ne; muna aiki ne domin kawo ƙarshenta.”

  11. Ba za mu sake barin jiragen ruwan Amurka su ratsa Tekun Fasha ba - Iran

    Iran

    Ali Abdollahi, shugaban hafsoshin rundunar sojojin Iran, ya ce ba za a sake barin jiragen ruwan Amurka su shiga Tekun Fasha ba.

    Abdollahi ya ce: "ya kamata shugaban Amurka ya fahimci cewa mafarki kawai yake yi idan ya tunanin cewa sojojinsu za su sake shiga Tekun Fasha. Wannan mafarki ne da ba zai yiwu ba.

    Ya ƙara da cewa: "Ba za mu bari jiragen ruwan sojan Amurka su shiga Tekun Fasha ba a kowane irin yanayi ko kuma a kowane lokaci."

    Wannan na zuwa ne bayan kwamandan rundunar ruwa ta IRGC ya bayyana a jiya cewa: "Amurkawa sun ja da baya zuwa kilomita 600 zuwa 700 daga mashigar Hormuz."

    A wani ɓangaren kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran da ƙoƙarin tayar da farashin mai gabanin zaɓen tsakiyar wa'adin majalisar dokokin Amurka.

    Trump ya yi zargin cewa Iran na yaɗa abin da ya kira "labaran ƙarya" game da fashewar nakiyoyi da hare-hare kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz domin haifar da fargaba a kasuwannin makamashi.

  12. Amurka ta ayyana cibiyoyin al'adun Sin a matsayin barazana ga tsaron ƙasar

    Amurka

    Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ayyana cibiyoyin koyar da harshe da al'adun kasar Sin a matsayin barazana ga tsaron ƙasar.

    Cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya kwatanta cibiyoyin da a matsayin masu yada farfaganda.

    Ya ce irin waɗannan cibiyoyi da dama sun ɓulla a jami'o'in Amurka da sunaye daban-daban, yana mai zarginsu da ƙoƙarin satar fasahohi da bayanan ilimi, tare da abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin yin tasiri a tunanin ɗaliban Amurka.

    Mista Hegseth ya ce ma'aikatarsa ta rushe irin waɗannan cibiyoyi da dama. Har yanzu ofishin jakadancin China da ke Washington bai fitar da wata sanarwa kan batun ba.

  13. Taƙaddama kan yaƙin Iran na jan hankali a shirin zaɓen Isra'ila

    Isra'ila

    Yaƙin neman zaɓe a Isra'ila ya shiga wani gagarumin mataki, inda ake fafatawa mai zafi tsakanin manyan ƴan takara biyu: Firaminista mai ci Benjamin Netanyahu da kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Yashar, Gadi Eisenkot.

    Sauran ƴan siyasa ma na ta ƙoƙarin samun ƙarin kuri'u da kuma tasiri wajen kafa gwamnati ta gaba.

    Yanayin siyasar ya yi zafi matuƙa har wani ɗan jarida na cikin gida ya kwatanta gasar da "wanka da jini". Wato, kowane ɓangaren siyasa ya fito fili yana ƙalubalantar ɗayan a wannan fafatawa.

    Sai dai abin lura shi ne, kusan dukkan ƴan takarar suna da abokin gaba guda ɗaya, wato Iran. Ɗaya daga cikin manyan tambayoyin da ake yi wa dukkan masu neman shugabanci a wannan zaɓe ita ce: me za ku yi game da Iran?

    Amsar da mafi yawansu ke bayarwa kusan iri ɗaya ce: "Za mu ci gaba da fuskantar Iran, amma ta hanyar da muka yi imani ta fi dacewa."

    Sai dai duk da wannan matsaya ta bai ɗaya, hanyoyin da kowane bangare ke son bi wajen mu'amala da Iran suna cike da bambance-bambance da kuma muhawara mai yawa. Wasu na goyon bayan ƙarin matsin lamba ta soja, yayin da wasu ke ganin ya kamata a haɗa hakan da dabarun diflomasiyya da na siyasa.

  14. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami da Houthi ta harba

    Ƙawancen ƙasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta ya sanar da cewa ya lalata makamai masu linzami masu cin dogon zango guda biyu da mayaƙan Houthi suka harba zuwa biranen Taif da Yanbu a ranar Asabar, yayin da rikici ke ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

    Hukumar Kare Fararen Hula ta Saudiyya ta fitar da gargadi a ranar Asabar, tana sanar da yiwuwar barazana a biranen Taif da Yanbu, da kuma Makka da Jidda.

    Sai dai kusan mintuna 10 bayan haka, hukumar ta fitar da wata sanarwa tana cewa an shawo kan barazanar, kuma lamarin ya koma daidai.

  15. Zaɓen shugaban ƙasar Brazil na ƙara ɗaukar zafi

    Sebastião Moreira EPA

    A muhawarar talabijin ta ƙarshe gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Brazil da za a gudanar a ƙarshen wannan makon, shugaban ƙasar Luiz Inácio Lula da Silva da babban abokin hamayyarsa mai ra'ayin ƴan mazan jiya, Sanata Flávio Bolsonaro, sun yi musayar yawu kan manufofinsu.

    Lula, wanda tsohon jagora ne mai sassaucin ra'ayi, ya kare nasarorin gwamnatinsa musamman kan harkokin tattalin arziki.

    Shi kuwa Flávio Bolsonaro, ɗan tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro da ake tsare da shi, ke yakin neman zaɓe kan batutuwan tsaro da tabbatar da doka da oda.

    Zaɓen na wannan karon ya sake haifar da rarrabuwar kawunan siyasa da aka jima ba a a gani ba a cikin shekaru huɗu da suka gabata, wato lokacin da Lula ya yi nasara, lamarin da ya haifar da suka daga magoya bayan Bolsonaro.

  16. Birtaniya za ta kasafta fam miliyan 220 domin ƙarfafa tsaron AI

    Birtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa za ta ware kusan dala miliyan 300, kwatankwacin fam miliyan 220, domin ƙarfafa tsaron ƙirƙirarriyar basira ta AI, a cikin kasafin kuɗinta na shekara da za a gabatar a ranar Laraba mai zuwa.

    Kimanin rabin kuɗin za a yi amfani da su wajen kafa dakin gwaje-gwaje na farko a duniya da zai mayar da hankali kan tsaron halittu ta amfani da AI, domin ƙarfafa kariya daga yiwuwar barazanar da ke da alaƙa da ƙwayoyin halitta.

    Sauran kuɗaɗen kuwa za su tafi ga Cibiyar Tsaron AI ta Birtaniya, wadda ke gwada manyan nau'ikan tsarin AI kafin a fitar da su don amfani.

    A baya-bayan nan an samu karuwar damuwa kan barazanar kutse ta intanet da kuma haɗurran da ci gaban fasahar AI cikin sauri ka iya haifarwa.

  17. Cutar Ebola da aka gano a Najeriya na kama da wadda ta ɓarke a Kenya

    Ebola

    Ministan Lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce binciken ƙwayoyin halittar wadda aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Najeriya ya nuna cewa ƙwayar cutar tana da kamanceceniya sosai da nau’in cutar da aka gano a mutum na farko da ya kamu da ita a Kenya.

    Wannan shi ne karo na farko da aka samu wata hujjar kimiyya da ke nuna alaƙa tsakanin ɓarkewar cutar a ƙasashen biyu.

    Sai dai hukumomin Najeriya sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa mutumin farko da ya kamu da Ebola a Kenya ya taɓa zuwa Najeriya ko kuma yana da wata alaƙa kai tsaye da wanda aka gano da cutar a Najeriya.

    Minista Pate ya ce hukumomi na ci gaba da gano da bibiyar duk waɗanda suka yi hulɗa da wanda ya kamu da cutar, inda ake killace su tare da yi musu gwaji. Ya ce wasu daga cikin sakamakon gwaje-gwajen sun fito babu cutar, yayin da ake jiran sakamakon wasu.

    Najeriya dai ta tabbatar da mutum guda kacal da ya kamu da Ebola, wanda rahotanni suka ce ya yi tafiya zuwa ƙasar Uganda kafin a gano yana ɗauke da cutar.

  18. Faransa na fuskantar wata sabuwar zanga-zangar tsadar rayuwa

    Faransa

    Faransa na fuskantar wata sabuwar zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma taɓarɓarewar ilimi a makarantu, yayin da ake fargabar sake aukuwar tashe-tashen hankula da fashe fashen shaguna irin na karshen makon da ya gabata.

    Gwamnatin kasar ta ce za ta girke jami’an ƴansanda dubu 70 a fadin kasar, tare da alkawarin gaggauta daukar mataki idan aka samu wata alamar tarzoma.

    A birnin Paris, masu shaguna sun rufe ko kuma sun kare wuraren kasuwancinsu domin dakile yiwuwar barna. Garin Orleans, da ke kudancin Paris, na daga cikin wuraren da ake da matukar damuwa akansu.

    Jam’iyyar National Rally mai ra’ayin rikau, na gudanar da taronta na shekara-shekara a garin, inda ake sa ran shugabarta, Marine Le Pen, za ta sanar a hukumance aniyarta ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa. break

  19. Wataƙila mu sake ƙaddamar da hari a Iran - Trump

    Amurka

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Washington na iya sake ɗaukar matakin soja kan Iran, kusan watanni takwas bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, a daidai lokacin da hauhawar farashin mai ke ƙara tayar da hankali gabanin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka.

    A wani gangamin yaƙin neman zaɓe da ya yi a jihar Florida ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, Trump ya ce:

    “Mai yiyuwa ne mu sake gudanar da wani ƙaramin farmaki, ko kuma su amince da yarjejeniya.”

    Ya ƙara da cewa: “Da ace suna da basira, da kawai za su ce, ‘Mu shiga tattaunawa ta gaskiya.’ Amma ina shakka za su yi hakan, domin wataƙila ba su da wannan hikimar.”

    “Operation Epic Fury” shi ne sunan da sojojin Amurka ke amfani da shi wajen kiran yaƙin da suke yi da Iran.

    A cikin jawabin nasa, Trump ya sake kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA a lokacin wa’adinsa na farko. Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta lalata ƙarfin Iran na tace sinadarin uranium ta hanyar farmakin “Operation Midnight Hammer”, sannan ta ci gaba da yi mata ƙarin illa ta hanyar “Operation Epic Fury.”

    Har ila yau, ya ce Amurka ta yi wa Iran mummunar illa, yana mai ikirarin cewa tattalin arzikin ƙasar na cikin mawuyacin hali fiye da kowane lokaci.

    Tun da farko a ranar Juma’a, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa na da ikon kawo ƙarshen yaƙin da Iran cikin sauri, amma ya yi tambaya kan ko ya dace Washington ta nemi kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa ko kuma ta bari ya lafa a hankali.

    Trump, wanda ya sha bayyana manufofi da lokuta daban-daban kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin, ya sanar a farkon watan Oktoba cewa Amurka ba za ta sake kai wani hari kan Iran ba kafin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokoki da za a gudanar a ranar 3 ga Nuwamba.

  20. Farawa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar, inda za mu cigaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta