UAE ta sanar da dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Iran

Asalin hoton, Getty Images
Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da hada-hadar kuɗi da Iran har sai baba-ɗa-gani, sakamakon ƙarin tsamin rikicin yankin.
Ma'aikatar Harkokin Wajen UAE ta ce matakin ya biyo bayan ƙara tsananta rikicin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin da kuma duniya.
Sa'o'i kaɗan kafin sanarwar, Ma'aikatar Tsaron UAE ta ce ta gano makamai masu linzami kirar ballistic guda biyu da aka harbo daga Iran zuwa ƙasar. Ta ce ɗaya ya faɗi a wajen ruwanta, yayin da ɗayan ya faɗa cikin ruwanta.
Tun bayan fara hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran, UAE na cikin ƙasashen yankin da suka fuskanci hare-haren Iran, amma tun bayan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Washington da Tehran, ba a kai mata hare-hare ba har zuwa sabon rikicin.


































