Iyalan Digo Jota za su halarci wasan Liverpool na farko a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Iyalan tsohon ɗanwasan Liverpool da ya rasu a haɗarin mota, Diogo Jota za su hallara a filin wasan ƙungiyar domin kallon wasanta na farko a gasar premier league ta bana da za a fara a yau Juma,a, 15 ga watan Agusta, wanda ƙungiyar za ta fafata da ƙungiyar Bournemouth a gida.
Iyalan mamacin za su halarci wasan ne domin karramawa ta musamman da za a yi wa tsohon ɗanwasan na gaba kafin fara wasan.
Diogo ya rasu ne yana da shekara 28 a haɗarin mota a Spain tare da ƙaninsa, Andre Silva mai shekara 25.
A game da shirin da suka yi, kocin ƙungiyar Arne Slot ya ce, "mun san tunawa kafin wasan zai ɗaga hankali matuƙa saboda wasan ne zai zama na farko a gasar tun bayan mutuwar Digo Dalot da Andre.
"Ina da yaƙinin cewa matar Diogo da yaransa da sauran ƴanuwansu za su halarci wasan na farko, kuma za mu yi amfani da damar wajen nuna musu ƙauna da goyon baya."



















