Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Sallama

    Masu bin wannan shafi nan muka kwo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin na muke cewa mu kwana lafiya

  2. Majalisar dokokin Amurka ta amince da ƙudirin dokar harajin Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Amurka ta amince da ƙudirin dokar harajin da zai bai wa shugaba Donald Trumph damar ƙara yawan kuɗaɗen da zai dinga kashewa.

    An ɗan samu tsaiko sakamakon dogon jawabi na sa'a takwas da shugaban marasa rinjaye na jam’iyyar Democrats a majalisar, Hakeem Jeffries yayi.

    Jeffries ya ce a shirye jam'iyyarsu take ta kare ƙudirin.

    Shugaba Trump ya kira ƙudirin da mai ɗan karen ƙyau, wanda zai ƙara wa Amurka yawan bashi.

    An amince da ƙudirin duk da turjiyar da wasu daga cikin ‘yan majalisar na ɓangaren Republican suka nuna a daren jiya

  3. Masu zanga-zanga sun cinna wuta a ofishin yansanda a Kenya

    Ɗaruruwan masu zanga-zanga sun kunna wuta a ofishin yansandan kudancin Kenya, bayan wani tattaki da suka yi da gawar, Albert Ojwang, wani Malamin makaranta kuma mawallafi da ya mutu a hannun ƴansanda a watan da ya gabata.

    Rahotanni sun ce an yi amfani da motar ɗaukar Gawa, wajen kai gawar ofishin ƴansanda na Homa Bay, inda aka fara tsare shi.

    Ana zarginsa da laifin sukar babban sifeton ƴansandan ƙasar a shafin yanar gizo.

    Da fari rundunar ƴansandan ta ce malamin makarantar ne ya kashe kansa, amma daga bisani ta ce ta gamsu kashe shi a kai.

    Lamarin dai ya janyo zanga-zangar nuna adawa da cin zali da ƴansanda ke aikatawa a ƙasar.

    Ana dai zargin mutum shida da hannu a kisan malamin ciki har da yansanda uku

  4. Za a gina ɗakin jira na manyan matafiya a filin jirgin Sokoto

    Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festus Keyamo tare da gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State

    Bayanan hoto, Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festus Keyamo tare da gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Ministan sufuri na Najeriya Festus Keyamo ya kaddamar da aikin gida sabon ɗakin jira na manyan baƙi a filin jirgi na Sultan Abubakar III da ke Sokoto.

    Ministan ya kaddamar da aikin ne yau Alhamis a birnin na Sokoto bayan ƙaddamar da titin zuwa filin jirgin saman da gwamnatin jihar ta gyara.

    A lokacin ƙaddamar da aikin, gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ce za a samar da kaya na zamani “waɗanda suka yi daidai da tsari na ƙasa da ƙasa domin walwalar fasinjoji”.

    Gwamnan ya ce aikin zai laƙume kuɗi naira biliyan 1.5

  5. 'Na ga yadda sojojin Isra'ila ke harbin Falasɗinawan da ke layin karbar tallafi'

    Falasɗinawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani tsohon jami'in tsaro a cibiyar rabon kayan agaji ta Amurka da Isra’ila a Gaza, ya ce ya ga yadda sojoji suke harbin Falasɗinawan da suka yi layi a wajen karɓar tallafi.

    Jami'in da ke kwarmata waɗannan bayanai ya ce a lokaci guda sojojin Isra’ilan sun yi amfani da manyan bindigogi wajen buɗe wuta kan taron jama’a da ya haɗa maza da mata, adaidai lokacin da suke layin karɓar abinci.

    Jami’in ya shaida masa cewa lokacin da dakarun Isra’ilan suka buɗe musu wuta, a kan idonsa wani ya mutu nan take.

    Ya kuma ce shugaban tawagar ya ba su umarnin yin harbi da zarar sun ga abin da ba su aminta da shi ba.

  6. Trump da Putin sun tattauna ta wayar tarho

    Shugaba Trump na Amurka da takwaransa na Rasha Vladymir Putin sun yi tattaunawa ta waya, kwana biyu bayan Amurka ta ce ta dakatar da bai wa Ukraine wasu makaman ya ki.

    Wani hadimin Putin ya ce tattaunawar shugabannin biyu ta kai kusan tsawon sa'a guda.

    Ya ƙara da cewa Mista Trump ya yi kiran kawo ƙarshen yaƙin Ukraine nan ba da jimawa ba, amma Mista Putin ya dage cewa dole Rasha ta cimma manufofinta.

    Haka kuma hadimin na Mista Trump ya ce shugabannin biyu sun tattauna batun da ya shafi Iran da yiwuwar alaƙa da tattalin arzikinta.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce yana sa ran zantawa da Putin a gobe Juma'a.

  7. Ƙungiyoyi 12 sun sake neman INEC ta yi musu rajistar zama jam'iyyu

    Shugaban hukumar zaɓen Najeriya

    Asalin hoton, INEC/X

    Bayanan hoto, Shugaban hukumar zaɓen Najeriya

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ce ta sake samun buƙatu daga ƙungiyoyi 12 domin yi musu rajistar zama jam'iyyun siyasa a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X ta ce tuni aka shigar da buƙatun jam'iyyun cikin jerin waɗanda ke jiran layin samun rajistar hukumar.

    A makon da ya gabata ne shugaban hukumar zaɓen ya ce INEC ta samu buƙatu daga ƙungiyoyi 110 da ke son yi musu rajistar zama jam'iyyun siyasa.

    Hukumar ta ce za ta duba waɗannan buƙatu, domin auna ko sun cika ƙa'idojin da hukumar ta gindaya.

    Yanzu dai Najeriya na da jam'iyyun siyasa aƙalla 18, kuma idan duka waɗannan ƙungiyoyi suka samu rajista adadin jam'iyyun siyasar ƙasar ka iya kai wa 140.

  8. Ƴan Majalisar Tarayyar Akwa Ibom bakwai sun koma APC

    Akwa Ibom Governor

    Asalin hoton, Umo Eno/Facebook

    Ƴar majalisar wakilan Najeriya bakwai daga jihar Akwa Ibom sun fice daga jam'iyyunsu na PDP da YPP zuwa jam'iyyar APC.

    Yan majalisar da suka fice sun haɗa da Unyime Idem da Martins Esin da Paul Ekpo da Uduak Odudoh da Okpolu Etteha da Bassey Okon da kuma Emmanuel Ukpong-Udo.

    Komawar yan majalisar zuwa APC ba ya rasa nasaba da ficewar gwamnan jihar daga jam'iyyar PDP a watan da ya gabata.

    Tun da farko Gwamnan jihar ya fice tare da duka kwamishinoninsa da mutanen da ya naɗa muƙamai a gwamnatinsa zuwa jam'iyyar APC.

  9. Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Umar Tsulange

    Asalin hoton, Umar Tsulange/Tiktok

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa wani matashi ɗan Tiktok, mai suna Umar Hashim Tsulange hukuncin ɗaurin shekara guda saboda samunsa da laifin taka doka.

    Shafin Freedom Radio a jihar ya ruwaito cewa kotun ta ba shi zaɓin zaman gidan yari ko biyan tarar naira 80,000.

    Umar Tsulange ya yi fice shafin Tiktok inda a wasu lokutan ake ganinsa yana wanka ko kwanciya ko wani abu da zai ɗauki hankalin jama'a a tsakiyar titi gaban ababen hawa da danja ta tsayar.

    Kazalika kotun ta umarci Tsulangen ya biya Hukumar Tace Fina-finai diyyar Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi na gurfanar da shi.

    A watannin da suka gabata ne rundunar ƴansandan jihar Kano ta ja hankalin matasan da ke tsayawa tsakiyar titi domin ɗaukar bidiyo, tana mai cewa hakan na haifar da hatsura a wasu lokuta.

  10. An ƙara wa shugaban mulkin sojin Mali wa'adin shekara biyar

    Assimi Goita

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A shekarar 2021 ne Assimi Goita ya karɓi mulkin Mali a wani juyin mulki

    Majalisar riƙon ƙwaryar gwamnatin Mali ta bai wa shugaban mulkin sojin ƙasar Assimi Goita wa'adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi ba tare da zaɓe ba.

    A bara ne Kanal Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta samu ba.

    Ƙudirin dokar ya yi tanadin cewa Goita zai ci gaba da mulki har zuwa lokacin da ƙasar za ta daidaita.

    A 2021 ne Kanal Goita ya hau karagar mulkin ƙasar a wani juyin mulkin soji , inda ya alƙawarta magance tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi.

    Sai dai har yanzu mayaƙan na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare, inda a baya-bayan nan ma suka kai hare-hare kan sansanonin sojin ƙasar tare da kashe sojoji masu yawa ciki har da sojojin hayar Rasha.

  11. Mutane na rayuwa cikin uƙuba a Darfur - MSF

    Ƙungiyar Likitoci ta MSF ta ce mutane na cigaba da rayuwa cikin mawuyacin hali a babban birnin Sundan, Dafur.

    MSF ta ce ana cigaba da kai wa mutane hare-hare, yayin da suke fuskantar tsananin yunwa.

    Ana zargin dakarun RSF da halaka mutane, da sata, da cin zarafin mata, da kuma garkuwa da mutane, yayin da suke yunƙurin karbe iko birnin El-Fasher da sojoji ke riƙe da shi.

    Rahotanni sun ce harin ya fi shafar waɗanda ba Larabawa ba.

    MSF ta kuma ce dakarun RSF ne suka kai harin sansanin ‘yan gudun hijrah na Zamzam da ya halaka mutane da dama, da tilasta wa fiye da 400 tserewa daga muhallan su.

  12. Rwanda ta tura sojoji 6,000 zuwa Gabashin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake zargin Rwanda da tsoma baki a harkokin soji a Gabashin DR Congo, inda rahoton da aka fitar ya bayyana cewa Kigali ta tura aƙalla sojoji 6,000 zuwa yankin, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito.

    Rahoton da aka fitar a jiya ya bayyana yadda Rwanda ke bai wa mayaƙan M23 goyon baya a yayin da suka ƙwace biranen Goma da Bukavu a farkon shekarar nan.

    Rahoton ya kuma ce gwamnatin Rwanda ta ɗauko wasu tsoffin mayaƙan FDLR don gudanar da ayyukan leƙen asiri.

    Rahoton ya ambaci wasu manyan jami’an sojan Rwanda da ake zargi da hannu a wannan lamari, ciki har da James Kabarebe wanda Amurka ta riga ta sanya wa takunkumi a watan Fabrairu bisa zargin taimaka wa M23, da kuma Janarori Vincent Nyakarundi da Patrick Karuretwa.

    Majalisar ta ce burin da Rwanda ke ƙoƙarin cimmawa shi ne mamaye ƙasar da mallakar ma’adanai da gonaki da kuma samun fa’ida ta siyasa – matakai da ke iya jawo takunkumi daga ƙasashen duniya.

  13. Mutane da dama sun jikkata yayin da gini mai bene ya rufta a Legas

    ...

    Asalin hoton, Gbenga Omotoso/Facebook

    Wani gini mai bene uku ya rufta a unguwar Legas Island a safiyar Alhamis, lamarin da ya jikkata wasu daga cikin mazauna gidan.

    Ginin da ke kan titin Asesi, kusa da titin Adeniji Adele, ya rufta ne kwatsam ba tare da sanin abun da ya haddasa hakan ba.

    Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Gbenga Omotoso ne ya tabbatar da ruftowar ginin a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    Ya ce “An ceto mutane hudu daga cikin baraguzan ginin kuma an garzaya da su asibiti,” in ji Kwamishinan.

    Jami’an ceto daga hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) da sauran hukumomi sun isa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da ayyukan ceto.

  14. Fararen hula 739 ne suka mutu a Sudan ta Kudu cikin watanni uku - MDD

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Akalla fararen hula 739 ne suka mutu a ƙasar Sudan ta Kudu tsakanin watan Janairu da Maris na shekarar 2025, a cewar wani rahoto da hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar (UNMISS) ta fitar.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa mutum 679 ne suka jikkata a hare-haren da yawanci ƙungiyoyin makamai suka kai faɗin ƙasar a cikin wannan lokaci.

    An ce hare-haren na ƙaruwa musamman bayan da aka tsare mataimakin shugaban ƙasa na farko, Riek Machar, da wasu abokan tafiyarsa a watan Maris, wanda ya haddasa sabon rikici da rashin tsaro.

    Majalisar ta buƙaci a dakatar da tashin hankali da kuma kare rayukan fararen hula, yayin da ake fargabar ƙarin rikice-rikice a ƙasar da har yanzu ke fama da rashin kwanciyar hankali tun bayan samun ‘yancin kai daga Sudan a 2011.

  15. Ɓangaren Abure ya ba Peter Obi Sa'o'i 48 ya bar jam'iyyar Labour

    ..

    Ɓangaren Julius Abure na Jam’iyyar Labour (LP) ya ba Peter Obi wa’adin sa’o’i 48 ya yi murabus daga jam'iyyar saboda alakarsa da jam'iyyar haɗaka ta ADC da David Mark ke jagoranta.

    Mai magana da yawun ɓangaren, Obiora Ifoh, a wata sanarwar da ya fitar ya ce jam’iyyar ba za ta yarda Obi ya haɗe da wata jam'iyya ba yayin da yake memba a Labour Party.

    Sanarwar ta ce jam’iyyar ba ta goyon bayan mutane masu manufofi biyu ko masu yaudara, kuma duk wanda ke son ya goyi bayan jam;iyyar ADC ya yi murabus cikin sa’o’i 48.

    Ɓabgaren Abure ɗin ta ce waɗanda ke cikin jam'iyyar haɗaka ‘yan siyasa ne masu son dawowa mulki ta kowanne hali.

  16. Sojin Uganda sun ce mutum biyar sun mutu a jirgin da ya yi hatsari a Mogadishu

    ...

    Asalin hoton, Munasar Mohamed

    Rundunar sojin kare ƙasar Uganda (UPDF) ta bayyana cewa sojoji biyar sun mutu yayin da jirgin su na Mi-24 da ke kan aikin kai wa sojojin Tarayyar Afrika kariya a Somaliya ya yi hatsari a babban filin jirgin saman Mogadishu jiya.

    Rundunar ta sanar a shafinta na X cewa abubuwan fashewa da ke cikin jirgin sun fashe, wanda hakan ya jikkata wasu fararen hula uku tare da lalata gine-gine a kusa.

    “Sojoji biyar dake cikin jirgin sun mutu a wannan hatsari,” in ji Rundunar.

    Gwamnatin tarayya ta Somalia ta aika da gaisuwar ta’aziyya ga gwamnatin Uganda.

    A ranar 3 ga Yuni ne dai ƙungiyar al-Shabab ta bayyana cewa sun harbo jirgin sojojin ƙungiyar Tarayyar Afirka ɗin a yankin Shabelle ta tsakiya, amma ƙungiyar AU ta musanta wannan iƙirari inda ta ce hatsarin ya faru ne sakamakon matsalar fasaha.

  17. Kotu ta ƙi amincewa da belin shahararren mawaƙi Diddy Combs

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotu ta ƙi amincewa da belin shahararren mawaƙin nan Sean Diddy Combs bayan da aka same shi da aikata laifukan da suka jibanci lalata.

    Hakan dai na nufin cewa zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa ranar da za a yanke masa hukunci -- wanda alƙali ya ce za a yi ranar uku ga watan Oktoba.

    An dai wanke Combs daga tuhume-tuhume masu tsanani da ke da nasaba da safarar mata da nufin lalata da su.

  18. Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Liverpool, Diogo Jota ya mutu a hatsarin mota

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Zamora, ƙasar Spain, kamar yadda hukumar Guardia Civil ta tabbatar wa da BBC.

    A cewar rahoton, ɗan uwansa, Andre Felipe, shima ya rasu a hatsarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare (BST).

    Mota kirar Lamborghini da suke ciki ta fita daga hanya bayan tayar ta fashe yayin da suke ƙoƙarin wuce wata mota a gaba. Bayan haka motar ta kama da wuta, kuma an tabbatar da mutuwarsu a wajen hatsarin.

    Rasuwarsa ya girgiza duniyar wasanni, musamman masoya ƙwallon kafa da magoya bayan Liverpool, inda ake ci gaba da aika saƙon ta'aziyya ga iyalansa da ƙungiyarsa.

  19. Ƙungiyar Lakurawa sun kashe mutum 15 a Sokoto

    ..

    Asalin hoton, Tangaza

    Wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

    Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.

    Ana zargin harin martani ne bayan kashe wasu mutum uku daga cikin kungiyar, ciki har da wanda ake zargin shugabansu ne a wani harin da ya ci tura da suka kai a baya a garin.

    Ɗaya daga cikin shugaba a yakin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun dira ƙauyen ne a daidai lokacin da jama’a ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

    “Muna cikin masallaci lokacin da suka kawo hari da yawansu.

    “Da zuwansu suka fara harbe-harbe.” inji shi.

    Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba don halartar jana’izar waɗanda aka kashe.

    “Wannan shi ne karo na farko da ƴan Lakurawa suka kai hari kai tsaye a garinmu.

    “Amma ina ganin martani ne bayan kashe wasu daga cikin su a wani harin da ya faru a baya,” inji shi.

    Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa ya ce maharan sun ƙone gonaki da gidaje da dama tare da lalata wata ariya ta sadarwa.

    Tangaza

    Asalin hoton, Tangaza

  20. Gobarar daji a Girka ta tilasta kwashe ɗaruruwan mutane

    ...

    Wata gobara mai ƙarfi da ke ƙone tsaunuka da dazuka a tsibirin Crete na Girka ta tilasta kwashe mutane fiye da 1,500.

    Gobarar dajin ta tashi ne kusa da Ierapetra, kuma iska mai ƙarfi na taimakawa wajen yaɗuwarta cikin sauri.

    Gobarar tana barazana ga gidaje da otal-otal da kuma tashar mai.

    An kwashe mutane daga yankin Ferma yayin da hayaki ya mamaye unguwanni har zuwa bakin ruwan Makry Gialos.

    Ana kuma bayar da mafaka ga fiye da mutum 200 a filin motsa jiki na cikin gari yayin da ake ci gaba da aikin kashe gobarar da haɗin gwiwar jami’ai da mazauna yankin.