An dakatar da babban jami’in gudanarwa na Juventus, Damien Comolli daga shiga sabgogin tamaula har zuwa ranar 31 ga watan Maris, saboda halaye marasa ƙyau ga alkalin wasa a karawar da suka sha kashi a hannun Inter Milan ranar Asabar.
An samu Comolli da laifi sakamakon kalubalantar alkalin wasa, Federico La Penna a lokacin da za su je daɗin hutawa bayan kammala zagayen farko da yi masa barazana.
Shima daraktan Juventus, Giorgio Chiellini an dakatar da shi har zuwa 27 ga Fabrairu, saboda rashin girmama La Penna da yi masa kalaman ɓatanci da mataimakan alkalin wasan.
Wannan matakin ladabtarwa ya biyo bayan jan katin da aka bai wa mai tsaron bayan Juventus, Pierre Kalulu, hakan ne ya fusata ƙungiyar da kalubalantar alkalin wasan.
An kori Kalulu ne jim kaɗan kafin hutun rabin lokaci bayan ya samu katin gargaɗi na biyu, saboda ketar da ya yi wa wasan Inter, Alessandro Bastoni.
Inter ta yi nasara da ci 3-2, kuma tana jagorantar teburin Serie A da maki 61, yayin da Juventus ke matsayi na biyar da maki 46 daga wasa 25.
Mai tsara alkalai da ke busa gasar Serie A, Gianluca Rocchi, ya nemi afuwa ranar Lahadi, yana mai cewa hukuncin da La Penna ya yanke na korar Kalulu kuskurene tare da bayyana takaici cewa VAR ba ta da ikon shiga cikin lamuran kati na biyu.