Sai da safe
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.
Mu hadu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 22/11/2025.
Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.
Mu hadu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.

Asalin hoton, Zamfara Police Command
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta ce ta yi nasarar kuɓutar da mata da 'ya'yansu 25 da 'yanfashin daji suka yi garkuwa da su ranar Juma'a.
Kakakin rundunar a jihar da ke arewa maso yammacin ƙasar, DSP Yazid Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Kuraje da ke Gusau babban birnin jihar, inda 'yanbindigar suka tafi da mata 10 da 'ya'yansu 15.
"Bayan samun kiran gaggawa dakarun haɗin gwiwa na Damba da na Gusau suka ɗunguma zuwa wurin. Tawagar ta bi sawun maharan kuma ta far musu," in ji DSP Abubakar.
Ya ƙara da cewa "hakan ta sa aka yi nasarar kuɓutar da mutanen 25, waɗanda aka kai su Sabon Garin Damba domin tantance su.
Ƙoƙarin jami'an tsaron na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da alhinin sace ɗalibai 25 a jihar Kebbi mai maƙwabtaka, da kuma wasu fiye da 300 a jihar Neja ita ma mai maƙwabtaka da Zamfaran - duka a wannan makon.

Asalin hoton, Reuters
'Yansandan Birtaniya sun kama aƙalla mutum 90 a wajen wata zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na haramta ƙungiyar Palestine Action mai goyon bayan Falasɗinawa.
Zanga-zangar ta birnin Landan na cikin gangamin da ake yi na neman soke haramcin ƙungiyar gabanin hukuncin da kotu za ta yanke a kan batun a mako mai zuwa.
Masu zanga-zangar sun yi iƙirarin cewa ana yi wa ɓangaren shari'a shisshigi a Birtaniya.
An gudanar da irin wannan zanga-zanga a lokuta da dama a bana, kuma ƴansanda sun kama mutane da dama a sassan ƙasar.
Hukumomin soji a Jamhuriyar Dimokuraiyyar Kongo sun ce sun kama hafsoshi, ciki har da masu muƙamin janar a bisa zargin aikata abin da suka kira barazana ga tsaron ƙasa.
Kakakin rundunar sojin ya shaida wa manema labarai cewa ana tsare da jami'an sojin domin gudanar da bincike, amma bai bayar da cikakken bayanin zargin da ake masu ba.
Kama hafsoshin sojin na zuwa ne watanni bayan tsare tsohon babban hafsan sojin ƙasar da wasu ƙananan sojoji kan zargin yunƙurin juyin mulki. Yanzu haka dai an yi wa sojojin ɗaurin talala.

Asalin hoton, Getty Images
An samu zanga-zanga a wajen zauren da ake gudanar da taron G20 a Afirka ta Kudu.
Ƴansandan Afirka ta Kudu sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar, a suka yi yunƙurin tsallaka shingayen da aka sanya.
Mutanen sun ƙi tsayawa a wurin da aka ware musu domin gudanar da ita, kilomita guda daga wurin.
Masu zanga-zangar na kira ne ga shugabannin da ke halartar taron domin mayar da hankali kan ƙwararar baƙi ba bisa ƙa'ida ba da ƙarin laifuka da yafe basuka tare da buƙatar kawo ƙarshen amfani da man fetur.
A nasa ɓangare taron ne jaddada muhimmancin sauyin yanayi.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta rahotonnin da ta ce ana yaɗawa da ke cewa ta umarci a rufe makarantu a faɗin ƙasar daga ranar Litinin mai zuwa.
Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ilimi ta ce rahoton ba gaskiya ba ne.
"Rahoton ba daga gwamnatin tarayya yake ba, ko ma'aikatar ilimi, ko wata ma'aikatar ilimi ta jiha, ko wata hukumar tsaro," in ji sanarwar.
A jiya Juma'a ne gwamnatin Najeriyar ta sanar da rufe makarantun sakandare na kwana 41 mallakarta da ake kira Unity Schools a faɗin ƙasar.
Umarnin na zuwa ne bayan sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi da kuma wasu 315 a jihar Neja a ranakun Litinin da kuma Juma'a.

Asalin hoton, @aonanuga1956
Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Najeriya ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tnubu rahoton halin da ake ciki game da sace-sacen ɗalibai da 'yanbindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu, ya fitar ta ce shugaban DSS, Tosin Adeola Ajayi, ya gana da Tinubu ne a jiya Juma'a da dare.
A ranar Litinin ne 'yanbindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga wata sakandare a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma.
Sai kuma ranar Juma'a wasu 'yanbindiga suka sace ɗalibai fiye da 300 da malamansu a wata sakandaren da ke Papiri a cikin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.
Tuni Tinnubu ya soke balaguronsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu saboda halin matsalar tsaron, kuma ya tura Ministan Tsaro Abubakar Badaru Neja, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tafi Kebbi.

Asalin hoton, Kano State Police Command
Rundunar ƴansandan jhar Kano ta buƙaci jami'anta su tsananta sanya idanu a kan iyakokin jihar.
Kwamishin ƴanandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawagar jami'an rundunar zuwa yankunan ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da ke kan iyakar jihar da Katsina.
CP Bakori ya buƙaci jami'an tsaron da ke sintiri a yankunan su tsananta sanya idanu da matsin lamba kan miyagun da ke harkokinsu a yankunan domin maido da zaman lafiya.
A baya-bayan nan jihar Kano ta riƙa fuskantar hare-haren ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa a yankunan jihar da suka yi iyaka da Katsina mai fama da hare-hare.

Asalin hoton, EPA
Tawagar ƙasashe ƙawayen Ukraine sun ce daftarin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine na buƙatar a sake aiki a kansa.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugabannin ƙasashen Japan da Canada da wasu ƙasashen Turai da dama suka fitar sun ce ba yadda za a yi a sauya iyakoki da ƙarfin tsiya.
Haka kuma shugabannin sun bayyana damuwarsu kan shawarar taƙaita sojojin Ukraine.
Shugaban sun gana ne a taron G20 da ke gudana a Afirka ta Kudu, ton da Donald Trump ya ƙauracewa.

Asalin hoton, Peter Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ƙungiyar OPOB, Nnamdi Kanu gazawa ce ta shugabanci.
Cikin wani saƙo da Obi ya wallafa a shafinsa na X ya ce hukuncin da aka yanke wa jagoran na IPOB zai tilasta wa kowane ɗan ƙasar da ya san me yake yi ya tsaya ya sake nazari a kai.
A ranar Alhamis ne aka yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan kotu ta same shi da laifuka masu alaƙa da ta'addanci.
Peter Obi ya ce hukunci ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar tarin matsaloli da ya ce sun haɗa da na tattalin arziki da matsin rayuwa da rashin tsaro da kuma rashin ingantaccen shugabanci.
''Wannan hukunci ba abin da zai haifar sai ƙara dagula lamura'', in ji shi.
Ƙawayen Ukraine na tattaunawa kan shawarar Amurka a taron G20 da ke gudana a Afirka da Kudu.
Shugaban ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun gana a gefen taron.
Shawarar ta Amurka ta janyo guna-guni tsakanin gwamnatocin Turai.
Shugaba Trump ya ƙaurace wa taron da ke gudana a Johannesburg.
Taron ya amince da muhimmancin sauyin yanayi - batun da gwamnatin Trump ta jima tana adawa da shi.

Asalin hoton, BBC Via Zahradden
Adadin ɗalibai da malaman makarantar sakandiren cocin St. Mary da ƴanbindiga suka sace a ranar Alhamis da daddare ya kai 315 kamar yadda ƙungiyar Kiristocin ƙaar CAN ta bayyana.
Gidan Talbijin na Channels a Najeriya ya ambato, shugaban ƙungiyar CAN reshen jihar Neja, Most. Rev. Bulus Dauwa Yohanna na bayyana haka bayan kammala aikin tantance ɗaliban makarantar.
Yohanna ya ce, “Bayan mun kammala aikin tantance ɗaliban ta hanyar tuntuɓar iyayensu ga waɗanda muke zaton sun gudu sun koma gida, sai muka gano cewa akwai ƙarin ɗalibai 88 da muke kyautata zaton suna hannun maharan''.
“Akwai iyaye da dama da muka yi zaton cewa ƴaƴansu sun koma gida a lokacin da aka tsarwatsa makarantar, amma sai aka shaida mana cewa iyayen sun zo makarantar domin neman ƴaƴansu'', in ji shi.
Yohanna ya ce kawo yanzu akwai ɗalibai 303 da malamansu 12 da ba a gani ba tun bayan harin.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya bayyana cewa akwai ƙyngiyoyin ƴanbindiga kusan 80 a Najeriya.
Shugaban kamfanin, Dokta Kabiru Adamu ne ya bayyana haka ta cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa.
''A binciken da kamfaninmu ya yi, ya gano cewa akwai ƙungioyoyin ƴanbindiga masu riƙe da makamai da ke ayyukansu a Najeriya sukan 80'', in ji shi.
A baya-bayan nan Najeiya na fama da hare-haren ƴanbindiga da ke sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu iyayen ɗaliban makarantar sakandiren ƴanmata ta Maga sun babu wanda ya je musu jaje.
Wasu daga cikin iyayen da BBC ta tattauna da su sun ce duka jami'an gwamnatin tarayya da aka tura jihar suna tsayawa ne a Birnin Kebbi ko shalkwatar ƙaramar hukumar Danko/Wasagu inda makarantar take.
To sai kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Halliru Ali ya musanta iƙirarin iyayen.
Yana mai cewa shi da kansa yana cikin jami'an gwamnatin jihar da suka je garin.
''Kuma gwamna ma da kansa ya je har garin'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa waɗanda ke zuwa daga gwamnatin tarayya gwamnatin Kebbi suke jajantawa.

Asalin hoton, Dikko Umar Radda/X
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe duka makarantun sakandiren faɗin jihar saboda dalilai na tsaro da satar ɗalibai a wasu jihohi.
Kwamishinan ilimi na jihar Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne saboda abubuwan da ke faruwa a maƙwabtan jihohi na satar satar ɗalibai.
''Kan haka ne muka ƙara tsananta matakan tsaron da muke ɗauka a makarantunmu, Bahaushe na cewa idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta shafa wa naka ruwa'', in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, bayan komai ya daidaita za su umarci ɗaliban su koma makarantun domin rubuta jarrabawar ƙarshen zango, wadda ita ce dama yanzu ta rage.
Ya ce matakin ya shafi duka makarantun sakandire da ke faɗin jihar, ban da na furamare, kodayake ya ce su ma idan hali ya yi za su rufe su.
''Mun yi haka ne saboda ɗaukar matakan kariya, bai kamata ba kana jiyo matsala a nesa sannan ka tsaya ta ƙaraso inda kake'', in ji shi.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fasa zuwa taron G20 na ƙasashe masu ƙarfin masana'atu a duniya, sakamakon matsalar satar ɗalibai a ƙasar .
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce shugaban ya ɗauki matakin ne sakamakon halin da ake ciki a ƙasar na satar ɗalibai a makarantu.
A maimakon haka Shugaba Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima domin ya wakilce shi a taron.
Tun da farko fadar shugaban ƙasar ta ce ta ce Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa taron sakamakon sanin halin da ake ciki game da satar ɗalibai a Kebbi da masu ibada a jihar Kwara.
An tsara gudanar da taron ne a yau Asabar 22 ga watan Nuwamban 2025.

Asalin hoton, Caleb Muftwang/X
Ma'aikatar ilimi ta jihar Filato ta bayar da umarnin rufe duka makarantun jihar na furamare da sakandire sakamakon ƙaruwar matsalar satar ɗalibai a ƙasar.
Hukumar Ilimi a matakin farko ta jihar, PSUBEB ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin matakin kariya ga ɗaliban jihar.
Matakin na zuwa ne bayan sace ɗaliban sakandiren Papiri a jihar Neja, kwana biyar bayan sace ɗalibai 25 na makarantar ƴanmata a jihar Kebbi.
Ma'aikatar ilimin jihar ta ce matakin na wucin-gadi ne kuma ya zama dole, la'akari da halin da ake ciki.
Cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta buƙaci duka masu ruwa da tsaki a harkar makarantu su yi biyayya wa umarnin.
Matakin ya shafi duka makarantun sakandire na ƙananan sakandire da na furamare.

Asalin hoton, Nigerian Mknistry of Defence/X
Gwamnatin Najeriya ta tura babban ministan tsaron ƙasar, Muhammad Badaru Abubakar, zuwa jihar Neja inda aka sace ɗalibai 'fiye da 200'.
Ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Muhammed Bello Matawalle ne ya bayyana haka ranar Juma'a da maraice a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa.
''Shi ma Badaru zai je Neja kamar yadda aka turoni Kebbi, domin ƙoƙarin gwamnati na kuɓutar da ɗaliban da aka sace'', in ji shi
Tuni dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura ƙaramin ministan tsaron zuwa jihar Kebbi - inda ƴanbindiga suka sace ɗalibai ƴanmata 25 - domin sanya idanu kan ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.

Asalin hoton, BBC Via Zaharadden
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta ce aƙalla mutum 227, ciki har da ɗalibai 215 da malamai 12 ƴanbindiga suka sace lokacin da suka kai hari makarantar St. Mary da ke garin Papiri a jihar Neja.
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta CAN reshen jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya fitar ya ce harin ya jefa al'ummar yankin cikin ɗimuwa da kaɗuwa.
Da tsakar daren ranar Alhamis ne wasu mahara ɗauke da makamai suka far wa makarantar - wadda ta kwana ce, da ta ƙunshi furamare da sakandire - tare da sace ɗaliban, bayan da suka harbi maigadi.
Gwamnatin jihar Neja ta ce sai da bayar da ba da umarnin rufe duka makarantun yankin sakamakon samun bayanan sirri kan barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen buɗewa tare da ci gaba da karatu ba tare da neman izini ko sanar da gwamnati ba.
To sai dai hukumar makarantar ta musanta ikirarin gwamnatin.
Harin na zuwa ƙasa da mako guda da wasu ƴanbidiga suka sace ɗalibai mata 25 a makarantar sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi mai maƙwabtaka.
Tuni dai gwamnatin ƙasar ta ce ta baza jami'an tsaro domin kuɓutar da duka ɗaliban.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-ytsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wanna lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.
Za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtanta.
Ka da ku manta da tafka muhawra kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.