Ghana ta tashi canjaras da Chadi a wasan neman zuwa Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghana ta tashi canjaras 1-1 a wasan neman gurbin zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka buga da Chadi.
Jordan Ayew ne ya fara ci wa tawagar ta Black Stars ƙwallo a minti na 17 da take wasa, kafin Celestine Ecua ya farke wa masu masauƙin baƙin.
Sakamakon ya sa Ghana ta ci gaba da zama a samen teburin Rukunin I da maki 16 bayan wasa bakwai, yayin da Chadi take a matakin ƙarshe da maki ɗaya.
Comoros ce ta biyu a teburin da maki 12, sai Madagascar ta uku da maki 11, da Mali mai maki 9, da Afirka ta Tsakiya mai maki 6.
A ranar Litinin Ghana za ta buga wasanta na gaba, inda za ta karɓi baƙuncin Mali a birnin Accra.


















