Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana.

    Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    Mu kwana lafiya.

  2. Najeriya ta kama ƴan Jamhuriyar Benin kan zargin safarar mutane

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta sanar da kama aƙalla mutum goma ƴan asalin jamhuriyar Benin bisa zarginsu da safarar mutane ba a Akure, babban birnin jihar.

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Lawal Adebowale ne ya bayyana hakan a lokacin da yake holen waɗanda ake zargin a ofishin hedkwatar rundunar, inda ya sunayen wadanda ake zargin wanda ya ce dukkans sun ne fito daga Jamhuriyar ta Benin.

    Ya ce yanzun haka dai ana ci gaba da bincikensu kafin gurfanar da su a gaban kotu.

    "Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun shigo Najeriya da wani mai suna Nzaou Yelica Chris-Olse mai shekara 29 ɗan asalin ƙasar Congo ba tare da saninsa ba."

    Kwamishinan ya ce waɗanda ake zargin sun yaudari Nzaou ne da cewa zai samu tallafi domin ya fara kasuwanci ta intanet.

  3. An yi garkuwa da mutum 9 a gidan marayu a Haiti

    Jami'ai a Haiti sun ce an yi garkuwa da mutum tara da suka hada da wani fasto dan kasar Ireland da wani yaro dan shekara uku a wani gidan marayu.

    An kwashe wadanda abin ya shafa daga gidan marayu na Sainte-Hélène da ke kusa da babban birnin kasar, Port-au-Prince, ranar Lahadi.

    Magajin garin birnin Masillon Jean ya ce an tsara harin ne ta yadda maharan suka samu shiga gidan marayun ba tare da sun bude wuta ba.

    Ya zuwa yanzu dai babu wani rahoton samun bukatun kudin fansa daga maharan.

    Haiti dai ta shafe shekaru tana fama da tashe tashen hankula da ke da nasaba da kungiyoyin yan daba.

  4. Trump ya yi barazanar ƙara wa Indiya haraji saboda hulɗa da Rasha

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Amurka Donald Trump ya yi barazanar kara harajin kaso ashirin da biyar cikin 100 na kayayyakin da ake shigowa da su daga Indiya, saboda sayan mai da ta ke yi daga Rasha.

    Mista Trump ya ce Indiya ta ci gaba da sayen man Rasha tare da sake sayar da shi a kasuwannin bayan fage domin samun kazamar riba.

    Wakiliyar BBC ta ce rahotanni na nuna cewa gwamnatin India ta yanke shawarar ci gaba da sayen mai daga Rasha duk da barazanar da Amurka ke yi ma ta.

    Delhi ta mayar da martani, inda ta ce sukar da Amurka ke kai wa Indiya bai dace ba, kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare muradun kasarta.

  5. Ukraine ta ce jiragenta sun kai hari sansanin sojin Rasha a Crimea

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar leken asirin Ukraine ta ce jiragenta marasa matuka sun kai hari a sansanin sojin Rasha da ke yankin Crimea da aka mamaye.

    Ta ce ta kai hari kan jiragen yaki guda biyar tare da lalata guda daya.

    Da take tsokaci game da farmakin da aka kai cikin dare, ma'aikatar tsaron Ukraine ta bayyana yankin Saky da ke yammacin Crimea a matsayin babbar tashar jiragen sama na Rasha wadda ta ke amfani da ita wurin kaddamar da hare-harenta.

    Ta kara da cewa harin ya shafi a wani rumbun ajiye harsasan bindigogin jiragen saman Rasha.

  6. Tsofaffin jami'an tsaro sun buƙaci Trump ya kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Daruruwan tsofoffin manyan jami'an tsaron Isra'ila sun rubutawa shugaba Donald Trump wata wasika suna kira gare shi da a kawo karshen yankin Gaza.

    Tsoffin jami'an sun ce babu wata barazana da ke fuskanta daga bangaren Hamas kuma babu dalilin ci gaba da wannan yakin a halin yanzu.

    Wakiliyar BBC ta ce wannan wasika ce da ke dauke da sa hannun sama da tsoffin manyan jami'an tsaron dari biyar da hamsin wadanda a baya suka taka muhimmiyar rawa wurin yanke hukunci kan wasu muhimman batutuwa.

    Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Firaminista Benjamin Netanyahu na neman fadada yakin domin kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza.

  7. Gwamnatin Ghana ta dakatar da kamfanin tumatirin gwangwani na Tasty Tom

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kula da Abinci da Magunguna FDA ta umurci dakatar da sarrafa tumatirin gwangwani na Tasty Tom Enriched Tomato Mix nan take.

    Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne bayan bincike ya gano kura-kurai a tsarin sarrafa kayan abinci a masana’antar tumatirin ta Nutrifoods Ghana Limited.

    Hukumar ta kuma bayar da umarnin a janye dukkan samfuran tumatirin na gwangwani da wasu na leda masu nauyin 380g da 1.05kg saboda haɗarin yiwuwar gurbacewa.

  8. Iyalan waɗanda Hamas ke garkuwa da su sun zargi Netanyahu da jefa Isra'ila cikin bala'i

    Netanyahu

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar karfafa gwiwar 'yan uwan wadanda Hamas ta yi garkuwa da su, sun zargi firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da jefa kasar cikin musiba.

    Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton shirin fadada yaki a zirin Gaza, wanda firaministan ya bayyana ƙudurinsa.

    Ma'aikatar lafiya da Hamas ke tafiyarwa a Gaza, ta ce matsananciyar yunwa ta yi ajalin karin mutum 5 kwana guda da ya wuce.

    A kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana cewa Hamas ta fitar da bidiyon wasu daga cikin waɗanda take garkuwa da su, lamarin da ya daga hankali a ƙasar ta Isra'ila, inda 'yan ƙasar suka kara zafafa kiraye-kirayen a kara kaimi wajen ceto musu 'yanuwa.

  9. RSF ta miƙa sansanin gudun hijirar Zamzam ga sojojin hayar Columbia

    RSF

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga yammacin Sudan na cewa Dakarun rundunar RSF sun miƙa iko da katafaren sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam ga sojojin haya yan ƙasar Colombia.

    Mai magana da yawun 'yan gudun hijirar ya bayyana cewa yanzu haka sojojin haya masu magana da harshen sifaniyanci ɗauke da makamai sun mamaye sansanin kuma suna yawo cikin walwala.

    RSF dai ta mamaye Zamzam ne a watan Afrilu.

    Birnin da ke kudu da El Fasher shi ne birni daya tilo a yammacin ƙasar da har yanzu ke ƙarƙashin ikon sojojin Sudan, wanda ke zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da ɗaukar hayar ɗaruruwan sojojin haya na ƙasashen waje (- yawancinsu 'yan Colombia -) don taimaka wa ƙungiyar ta RSF.

    Tun da farko dai Ministan harkokin wajen Colombia Luis Gilberto Murillo ya nemi afuwa kan kasancewar sojojin haya ƴan ƙasar a Sudan, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta goyon bayan irin waɗannan ayyuka.

  10. Tinubu ya ba ƴan wasan kwandon Najeriya mata dala 100,000 da lambar girma

    Najeriya

    Asalin hoton, Stanley Kingsley Nkwocha

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba ƴan wasan kwandon Najeriya mata dala 100,000 da lambar girma ta OON saboda nasarar da suka samu ta lashe kofin gasar kofin Afirka ta wato Afrobasket.

    Shugaban ya kuma ba masu horar da ƴanwasan dala 50,000 kowannensu.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ƴanwasan ƙwallon ƙafa mata kyautar dala 100,000 da lambar girma.

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya wakilci Tinubu wajen tarbar ƴanwasan, sannan ya samu rakyar uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Femi Gbajabiamila da sauran su.

    Da yake jawabi a wajen karrama ƴanwasan a fadar shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce, "ina matuƙar farin cikin maraba da ku a madadin shugaban ƙasa. Nasarar da kuka samu wata ƙofa ce ta samun nasara a duniya. Lallai kun zama abin koyi ga ɗimbin ƴanmata masu tasowa."

    Tun da farko, kyaftin ɗin tawagar, Amy Okonkwo wadda kuma ta lashe kyautar ƴarwasa da ta fi hazaƙa ta yi godiya ga gwamnati, musamman uwargidan shugaban ƙasar bisa gudunmuwar da ta ba su, sannan ta ce suna alfaharin damar d suka samu ta wakiltar Najeriya.

  11. WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025

    Wasu daliban sanye da farin tufafi gefensu kuma da tambarin WAEC

    Asalin hoton, WAEC X

    Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025 a Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta saki sakamakon ne a yau Litinin 4 ga watan Agustan 2025.

    Hukumar ta kuma buƙaci ɗaliban da suka rubuta jarrabawar da su shiga shafinta na http://waecdirect.org. domin duba sakamakon jarrabawar tasu.

  12. Tawagar D'Tigress ta Najeriya ta isa gida bayan lashe kofin Afirka

    Kaftin ɗin tawagar Najeriya riƙe da kofi yayin da take fitowa daga jirgi mutane na murna a bakin jirgin

    Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Najeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka.

    Wasu cikin ƴan wasan NAjeriya sanye da tufafi masu launin kore fari kore ,irin na tutar Najeriya

    Tawagar ta D’Tigress ta samu gagarumar tarba daga masoya ƙwallon kwando a Najeriya, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Abuja.

    Ministar matan Najeriya da ta al'adu yayin da suke shirin sauka daga jirgin

    Ministar Mata Iman Sulaiman Ibrahim da takwararta ta al'adu, Hannatu Musawa ne suka yi wa tagawar rakiya tun daga birnin Abidjan zuwa Abuja.

    Iman Sulaiman Ibrahim da Hannatu musawa sanye da tufafi masu launin tutar Najeriya da wasu cikin ƴan wasan

    A ranar Lahadi ne tawagar D’Tigress ta lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, bayan doke Mali da ci 78-64.

    Hannatu Musawa ke zantawa da manema labarai

    Wannan ne karo na bakwai da tawagar Najeriya ta lashe kofin gasar a tarihi, wanda kuma shi ne na biyar a jere da ta ɗauka.

    Tawagar ta samu gagarumar tarba a Abuja
  13. Tsoffin jami'an tsaron Isra'ila sun nemi Trump ya kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    Ɗaruruwan tsoffin manyan jami'an tsaron Isra'ila sun rubuta wa Shugaba Trump wasiƙa, suna masu kiran ya matsa wa gwamnatim Isra'ila lamba don kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Waɗanda suka rubuta wasiƙar sun ce a yanzu Hamas ba barazana ba ce, kuma yaƙin ba shi da wani amfani.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rahotonni ke cewa, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke shirin neman faɗaɗa yaƙin domin kuɓutar da sauran Isra'ilawan da ake garkuwa da su a Gaza.

    Ƙungiyar tallafa wa waɗanda ake garkuwa da su na zargin Netanyahu da jefa ƙasar da masoyansu cikin rugujewa.

  14. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken kwamishinan da ake zargi da belin Danwawu

    Ibrahim Namadi zaune sanye da jar dara da tufafi masu launin ruwan kwai

    Asalin hoton, Facebook

    Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin binciken zargin kwamishinan sufurin jihar Ibrahim Namadi da hannu a belin mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar ya miƙa wa gwamnati rahotonsa.

    A yau Litinin ne kwamitin ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton binciken nasa ga sakataren gwamnatin jihar.

    Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai fayyace abin da kwamitin ya gano a binciken nasa.

    A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin, bayan da aka zargi Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi.

    Batun ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimakawa wajen assasa ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

    Lamarin da ya sa wasu ke ta kiraye-kirayen sauke shi daga muƙaminsa.

  15. Ƴan canji a Abuja sun dakatar da ayyuka don tantance masu sana'ar

    shagunan masu canji a Abuja

    Haɗakar ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta Abuja ta dakatar da ayyukanta domin tantance ma'aikatanta.

    Shugaban ƙungiyar Alhaji Salisu Umar ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne domin tsaftace kasuwar.

    Wasu shagunan masu canji a rufe

    Ya ce dama sukan yi haka lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingancin sana'ar tasu.

    Wakiliyar BBC da ta ziyarci kasuwar da ke unguwar Zone 4 a tsakiyar birnin Abuja, ta ce duka shaguna manya da ƙanana a kasuwar sun kasance a rufe.

    Wani shago a rufe
    Ƙarafunan da ke gefen titi, inda masu canji ke zama a kasuwar ƴan canji ta Abuja
  16. Ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kisan wasu mata zai zama shaida a shari'arsu

    Waɗanda ake zargi a kotu

    Asalin hoton, Nomsa Maseko / BBC

    Ɗaya daga cikin mutane ukun da ke fuskantar shari'a kan zargin kisan wasu mata biyu tare da bai wa aladu gawarwakinsu, zai zama shaidar gwamnati a shari'ar, domin tabbatar da laifin kan wanda ake zarginsu tare.

    Mai kula da gona, Adrian Rudolph de Wet,zai tabbatar wa kotu cewa ubangidansa ne ya tilasta masa kamo matan biyu sannan aka sa shi ya jefa wa aladu gawarwakinsu bayan an kashe su.

    An dai jingine shari'ar zuwa mako mai zuwa domin kammala tattara takardun shaida.

    Idan har kotun ta tabbatar da shaidar Mista de Wet, za a jingine tuhumar da ake yi masa.

    Kisan Maria Makgatho da Kudzai Ndlovu ya haifar da zazzafar muhawara a Afirka ta Kudu tare da haifar da zaman ɗarɗar a faɗin ƙasar.

  17. Gwamnatin Kano za ta mayar da gidan yarin Kurmawa gidan tarihi

    Wasu mutane yayin da suka yi layin shiga gidan yari

    Asalin hoton, Others

    Gwamnatin jihar Kano ta ɓullo da shirin mayar da gidan yarin Kurmawa - da ya kwashe shekara fiye da 100 - gidan tarihi domin adana abubuwan da suka faru lokacin mulkin mallaka.

    Gidan yarin mai shekara 115, an gina shi ne lokacin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar sarkin Kano domin a riƙa ɗaure masu laifi a ciki.

    A bisa ƙa'idar da aka gina gidan yarin Kurmawa zai ɗauki fursunoni 690 ne kawai

    Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin yaɗa labara, Ibrahim Adam ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

    Ibrahim Adam ya ce za a mayar da fursunonin da ke ɗaure a gidan yarin zuwa sabon gidan fursunan Janguza na zamani, da ke kusa da barikin soji a kan babban titin Kano zuwa Gwarzo.

    Mashawarcin gwamnan Kano ya ce za a mayar da Kurmawa gidan tarihi ne domin taskance abubuwan tarihin da suka faru a zamanin mulkin mallaka.

    Sabon gidan yarin Janguza da aka gina a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai iya ɗaukar fusrsunoni kimanin 3,000.

  18. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da dashen bishiya miliyan biyar a jihar

    Gwamnan Kano da wani mutum ke dasa bishiya

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Kano

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi miliyan biyar domin yaƙi da sauyin yanayi da inganta muhalli a jihar.

    An ƙaddamar da gangamin dashen bishiyoyin ne ranar Lahadi a garin Yanbawa da ke yankin ƙaramar hukumar Makoɗa.

    Sauyin yanayi da gusowar hamada wani abu ne da masana suka jima suna gargaɗi a kai tare da buƙatar ɗaukar matakan kariya.

    Wasu bishiyoyin da za a dasa

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Kano

    Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da dashen, Gwamna Abba Gida-gida ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa wajen kare muhalli da nuna muhimmancin dashen bishiyoyi wajen kariya daga gurɓata muhalli.

    “Wannan gangami ba kawai batun dashen bishiya ba ne, abu ne da zai ingantan makomarmu, da kare yara masu tasowa daga illar gurɓacewar yanayi'', in ji shi.

    Gwamnan ya kuma ce za a rabar da bishiyoyin miliyan biyar a faɗin ƙananan hukumomin jihar 44, domin dasawa a wurare muhimmai da suka haɗa da makarantu da masallatai da ma'aikatu da gonaki a birane da ƙauyukan jihar.

    Gwamnan Kano ke dasa bishiya da wani sanye da kayan sarakunan gargajiya

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Kano

  19. Abu uku da suka sa Obi ya samu ƙuri'u masu yawa a 2023 - Keyamo

    Peter Obi tsaye sanye da baƙaƙen tufafi yana murmushi sanye da tubarau

    Asalin hoton, Peter Obi/X

    Bayanan hoto, Peter Obi ne ya zo na uku a zaɓen 2023, inda ya samu ƙuri'a fiye da miliyan shida

    Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Festus Keyamo ya ce da wahala tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya sake samun yawan ƙuri'un da ya samu a zaɓen da ya gabata.

    Peter Obi - wanda yanzu ke cikin haɗakar ADC, kuma ake ganin zai iya tsayawa takara a jam'iyyar - shi ne ya zo na uku a zaɓen 2023, inda ya samu ƙuri'a fiye da miliyan shida.

    To sai dai cikin wata hira da gidan talbijin na Channels, Festus Keyamo ya ce wasu abubuwa uku ne suka sa Obi ya samu ƙuri'un a 2023, wanda kuma a cewarsa ba lallai ne su yi masa a aiki a 2027 ba.

    A cewar Keyamo ''abubuwa ukun da suka sa ya samu ƙuri'u masu yawa a zaɓen 2023 sun haɗa da'':

    • Shi kaɗai ne Kirista cikin manyan ƴan takarar. ''Duka sauran ƴantakarar musulmi ne, don haka ne kiristoci suka mara masa baya''.
    • Yankin kudu maso gabashin Najeriya da al'ummar Igbo na ganin kamar ba a yi da su, don haka suka fito suka ba shi ƙuri'a.
    • Matasa na kallonsa a matsayin ɗan takararsu, kasancewa sauran ƴan takarar tsofaffi ne, don haka suka yi shi.
  20. Fiye da ƴancirani 68 sun nutse bayan hatsarin jirgin ruwa a Yemen

    Wasu ƴanci rani ayayin da ake ƙoƙarin ceto su a cikin teku

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin ruwa da ke ɗauke da ‚yan ci-rani sama da 150 ya nutse a kudancin gaɓar tekun Yemen, inda ya hallaka sama da mutum 68.

    Mutane da dama ne suka ɓace cikin ruwan, yayin da mutum 14 suka tsira.

    Jami'an Yemen sun ce jirgin ya yi hatsarin ne a kusa da lardin Abyna.

    Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya a Yemen Abdusattor Esoev ya ce igiyar ruwa ce ta kaɗa gawarwakin mutum 54 daga cikinsu zuwa gefen teku a gundumar Khanfar.

    Yemen ƙasa ce da ta yi fice da yawanci 'yan ci rani ke bi ta tekunta domin burin samun rayuwa me kyau.

    Hukumar tsaron Abyan ta fitar da sanarwar fara aikin nema da ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.

    Hatsarin jiragen ƴan cirani a teku ba sabon abu ba ne, inda yake laƙume rayukan mutane da dama.

    Ko a watan Maris wasu jiragen ruwa biyu ɗauke da ƴan cirani sama da 180 sun nutse a gaɓar tekun Yemen a gundumar Dhubab saboda mahaukaciyar igiyar teku, inda aka ceto mutum biyu kawai daga cikin, inda dukkanin sauran mutanen ko dai sun mutu ko sun ɓace.