KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga ranar 19 zuwa 24 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 19 zuwa Juma'a 24 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Haaland Ya Soki Arsenal, Ya Ce Sun Sha Gazawa a Lokutan Baya, Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Tauraron ɗan wasan Manchester City, Erling Haaland, ya yi wa Arsenal tuni da irin gazawar da suka yi a kakar wasanni da ta gabata da Liverpool ta lashe Premier League, bayan da ya taimaka wa kungiyarsa wajen samun muhimmiyar nasara a kan abokan hamayyarta na neman kofin Firimiya.

    Dan wasan Norway ya ci kwallon na biyu da Manchester City ta doke Arsenal 2–1 a filin Etihad ranar Lahadi, hakan ya sa saura maki uku tsakanin Arsenal ta daya da kuma City ta biyu a teburin Premier League.

    City na da kwantan wasa, kenan tana da damar hayewa kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila daga nan zai rage wasa biyar-biyar a kammala kakar bana.

    Haaland ya amince cewa Arsenal ce ta fi nuna bajinta a yawancin kakar wasan nan, amma ya kara da cewa Manchester City ba za ta ja da baya ba wajen kalubalantarsu, domin hana su lashe kofin gasar Firimiya da rabon Arsenal da shi 2004.

    “Mun san Arsenal kungiya ce mai karfi, amma mun ga a baya sun taba zuwa kusa ba tare da sun kai ga buri ba,” in ji Haaland bayan wasan.

  2. Giggs: Carrick ya mayar da farin ciki ga magoya bayan Man United, Manchester United

    Carrick

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan Manchester United, Ryan Giggs, ya bayyana cewa magoya bayan ƙungiyar sun sake samun farin ciki da sha’awar kallon wasanni a Old Trafford tun bayan da Michael Carrick ya karɓi ragamar horaswar a kungiyar. .

    Giggs ya ce duk da sallamar da aka yi wa dan kasar Portugal, Ruben Amorim, ya bar ƙungiyar a wani matsayi mai kyau da ya ba Carrick damar ci gaba da gina nasara a kai.

    Manchester United ta samu sauyi sosai cikin mako 15 da suka gabata bayan ficewar Amorim. Matakin da shugabannin kungiyar suka bai Michael Carrick aikin rikon kwarya zuwa karshen kakar nan.

    A ƙarƙashin Carrick, Red Devils ta haura zuwa matsayi na uku a jadawalin gasar Firimiya, inda nasarar da suka samu ta 1–0 a kan Chelsea a ranar Asabar ta ƙara ƙarfafa damar ƙungiyar na samun tikitin shiga gasar Champions Leaguea badi.

    Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyi biyar na farkon teburi a gasar za su wakilci Ingila a manyan wasannin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

    Giggs, wanda shi ma ya taɓa zama kocin riko na Manchester United a ƙarshen kakar 2013/2014 bayan sallamar David Moyes, ya yaba da tasirin da Carrick ke yi cikin ɗan gajeren lokaci.

    Ya bayyana fatan Carrick zai samu cikakkiyar dama a gaba, musamman ta fuskar shirin kakar wasa ta gaba da kuma zaɓen ’yan wasan da suka dace da salon wasansa.

    Tun bayan barin Moyes, Manchester United ta sauya koci biyar. Amma Giggs ya jaddada cewa ko da Amorim ya bar aikin a yayin da ƙungiyar ke matsayi na shida, ya bar tubalin da ya ba sabon koci damar gina ƙungiya mai ƙarfi.

  3. Romania ta naɗa Hagi sabon kociyanta, Romani

    Hagi

    Asalin hoton, Stefean Constantin

    Ƙasar Romania ta naɗa tsohon fitaccen ɗan wasa, Gheorghe Hagi a matsayin sabon kocinta, kamar yadda Hukumar Ƙwallon Ƙafa kasar ta bayyana a ranar Litinin.

    Hagin mai shekaru 61 ya komo kan aikin horaswa tun bayan shekara 25 da ya fara sana'ar.

    Hagi ɗaya ne daga fitattun ƴan wasa a duniya a shekarar 1980s zuwa 1990, kuma ya maye gurbin mai horarwa, Mircea Lucescu, wanda ya bar mukamin tun farkon wannan wata bayan Romania ta sha kashi a wasan neman gurbin shiga Kofin Duniya a hannun Turkiyya. Lucescu mai shekaru 80 ya rasu kwanaki biyar bayan ya ajiye aiki.

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Romania ta ce Hagi ya sanya hannu kan kwangila da za ta shafi kai zuwa neman cancantar shiga manyan gasa guda biyu masu zuwa—Euro 2028 da Kofin Duniya na 2030.

    Romania za ta buga wasannin sada zumunci da Georgia da Wales a watan Yuni, kafin fara gasar Nations League a watan Satumba.

    A lokacin sa ya taka leda a ƙungiyoyi irin su Steaua Bucharest da Real Madrid da Barcelona, kafin ya kammala aikinsa a Galatasaray yana da shekaru 36 a 2001.

  4. An yi rikici a gasar ƙwallon kafa ta Paraguay a karshen mako, Paraguay

    Rikice‑rikicen tashin hankali tsakanin magoya baya da ƴansanda sun tilasta soke wasan gasar Paraguay da aka shirya a ranar Lahadi tsakanin Olimpia da Cerro Porteño a babban birnin ƙasar, Asunción, kamar yadda ƴansanda suka bayyana a wata sanarwa.

    Ƴansanda sun ce tashin hankalin “wani ɓangare na magoya bayan Cerro Porteño ne suka tayar da shi,” lamarin da ya sa aka dakatar da fafatawar na ɗan lokaci saboda dalilan tsaro.

    Hukumomi sun ƙara da cewa an fara bincike domin gano waɗanda ke da alhakin abin da ya faru.

    “Za a miƙa waɗanda suka aikata laifin ga Ofishin Babban Mai Gabatar da Ƙara domin su fuskanci hukunci mai tsauri, kuma za a hana su halartar kallon wasanni idan aka same su da laifi,” in ji ’yan sanda.

    Ƙungiyoyin Olimpia da Cerro Porteño da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Paraguay (APF) ba su ce komai kan wanna lamarin, saboda lokacin da aka nemi jin ta bakinsu a lokutan aiki.

  5. Rosenior ya ce shugabanin Chelsea suna goyon bayansa, Chelsea

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Liam Rosenior ya ce yana da yakinin “kashi 100 cikin 100” masu Chelsea suna goyon bayansa duk da halin da kungiyar ke ciki.

    Kocin ya bayyana cewa har yanzu shugabannin Chelsea suna tare da shi yayin da yake kokarin ganin sun samu gurbin shiga Champions League.

    Chelsea tana da tazarar maki bakwai tsakani da Liverpool ta biyar ɗin teburi a gasar Premier League, bayan rashin nasara huɗu a jere ba tare da cin ƙwallo ba.

    Magoya baya sun nuna rashin jin daɗinsu bayan wasan da suka yi rashin nasara da ci 1-0 a gida a Stamford Bridge a hannun Manchester United ranar Asabar a wasan mako na 33.

    Watakila Chelsea ta kawo karshen wanna mummunan halin da take ciki a wasan Premier da za ta buga da Brifgton ranar Talata.

    Wani abin haɗarin shi ne tazarar maki uku ne tsakanin Chelsea da Fulham, wadda take ta 12 teburi - kenan tana haɗarin kasa samun tikitin shiga gasar zakarun Turai gabaki ɗaya a kaka mai zuwa.

    Rosenior ya bayyana cewa Wesley Fofana ya nemi afuwa kan yadda ya nuna rashin jin daɗda aka cire shi a wasan Manchester United.

    Za a auna koshin lafiyar João Pedro, yayin da Enzo Fernández ke cikin koshin lafiya, amma Estevão Willian ba zai buga fafatawar ba saboda raunin da ya ji a karshen mako.

  6. Konate ya ce ya kusan tsawaita kwantiragi a Liverpool, Liverpool

    Ibrahim Konate

    Asalin hoton, Getty Images

    Ibrahima Konaté ya bayyana cewa ya “kusan cimma yarjejeniya” da Liverpool kan sabunta kwantiraginsa, kuma akwai “babbar dama” da zai ci gaba da zama a Anfield a kakar wasa mai zuwa.

    Ɗan wasan tawagar Faransa, kwantiraginsa zai kare a wannan bazarar, shekara biyar bayan da ya koma Anfield daga RB Leipzig kan kudi fam miliyan 35.

    Tun bayan zuwansa Premier League, Konate ya buga wasa 113 a gasar Premier League, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofin lik a kakar bara, da kuma FA Cup da EFL Cup a shekarar 2022.

    Liverpool za ta kammala wannan kakar ba tare da lashe kofi ba, amma tana da kyakkyawar dama samun gurbin Champions League na kakar wasa mai zuwa. A halin yanzu tana matsayi na biyar da maki bakwai tsakani da Chelsea da ke matsayi na shida.

    A bangaren Konate kansa, kakar ta kasance mai kalubale. Mahaifinsa ya rasu a Faransa a watan Janairu, amma duk da haka ya koma Ingila da wuri daga hutun da ta bashi, saboda matsalolin masu tsaron baya da Liverpool ke fuskanta.

  7. Haaland ya ci Arsenal karo na huɗu a jere a Premier League, Premier League

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Erling Haaland ya zama ɗan wasa na biyu da ya ci Arsenal a wasa huɗu a jere a Premier League, bayan Diogo Jota a Liverpool tsakanin Satumbar 2022 zuwa Maris ɗin 2022.

    Manchester City ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Arsenal ya koma saura uku, bayan da ta yi nasara 2-1 a wasan mako na 33 a Premier League a Etihad ranar lahadi.

    Cherki ne ya fara ci wa City ƙwallo a minti na 16 da take leda, amma minti biyu tsakani Gunners ta farke ta hannun Havert, sakamkon kuskuren da golan City, Gianluigi Donnarumma ya yi.

    Daga baya ne Haalnda ya ci wa City ƙwallon da take bukata da ya rage tazarar maki tsakaninsu.

    Wannan nasarar na nufin ƙungiyar Etihad mai kwantan wasa za ta koma kan teburi da zarar ta ci Burnley a tsakiyar mako musammam da zura ƙwallo biyu a raga.

    Wasannin da suke gaban Arsenal:

    • Za ta karɓi bakuncin Newcastle
    • Za ta buga da Fulham a Emirates
    • Za ta je West Ham United
    • Za ta kara da Burnley a gida
    • Za ta kare wasa a gidan Crystal Palace

    Wasannin da suka rage wa City:

    • Za ta je Burnley
    • Za kuma ta je gidan Everton
    • Za ka karɓi bakuncin Bournemouth
    • Za ka kara da Crystal Palace a gida
    • Za ta fafata da Aston Villa a Etihad
  8. , Daga Jaridu

    Cole Palmer

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid za ta yanke shawara kan makomar kocinta Alvaro Arbeloa a karshen kakar wasani. (Marca - in Spanish), external

    Real Madrid na shirin yin garambawul ga 'yan wasanta a bazara, inda dan wasan Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 23, zai iya barin kungiyar. (Sport - in Spanish), external

    Daukakar da Coventry City ta samu zuwa gasar wasani Firimiya yana nufin cewa dan wasan Najeriya Frank Onyeka mai shekara 28 da aka bada shi aro daga Brentford zai koma na dindindin . (Talksport), external

    Lorient na tunanin daukar tsohon kocin Lens da Southampton Will Still a matsayin kocinta (L'Equipe - in French), external

  9. Nottingham na daf da samun gurbin ci gaba da zama a Premier, Premier League

    Nottingham Forest

    Asalin hoton, Getty Images

    Morgan Gibbs-White ya ci ƙwallo uku rigis da hakan ke daf da tabbatar da Nottingham Forest a gasar Premier League.

    Ranar Lahadi Forest ta dokr Burnley 4-1 a wasan mako na 33 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi.

    Ɗan wasan Ingilan ya ci kwallayen tun kan hutu daga baya Igor Jesus ya ci na huɗu — wanda hakan ya bai wa Forest tazarar maki biyar tsakani da ƴan ukun karshen teburi.

    Burnley, wacce ke matsayi ta biyun kashe tana da tazarar maki 12 daga tsira daga faɗuwa a gasar Premier a kakar nan.

    Nasarar Forest ta kuma ƙara matsa lamba ga Tottenham, bayan ta tashi 2-2 da Brighton ranar Asabar, inda Tottenham ke matsayi na 18, maki ɗaya tsakani da West Ham.

    Wannan nasara ta zo ne bayan da ƙungiyar da Vitor Pereira ke jagoranta ta tsawaita wasanni ba tare da shan kashi ba zuwa bakwai a dukkan fafatawa — ƙwazo mafi ƙyau a kakar bana.

  10. , Daga Jaridu

    Jude Bellingham

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich na zawarcin dan wasan Aston Villa Morgan Rogers mai shekara 23. Kungiyar ta bi sahun Chelsea da Manchester United wadanda ke son dan wasan Ingila. (Football Insider), external

    Dan wasan tsakiyar Ingila Curtis Jones, mai shekara 25 na shirin barin Liverpool a wannan bazara inda Aston Villa ta kara kaimi wajan zawarcinsa (Teamtalk), external

    Manchester City na son ta dauko dan wasan Newcastle United da Ingila Tino Livramento, mai shekara 23, ko da yake suna neman wasu 'yan wasa. (Teamtalk), external

    Real Madrid na tunanin nada tsohon kocinta Jose Mourinho wanda ke jagorantar Benfica.(Record - in Portuguese), external

  11. Caicedo ya ce Chelsea za ta iya samun gurbin Champions League, Premier League

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Moises Caicedo ya jaddada cewa Chelsea tana da damar gurbin Champions League, duk da rashin nasara 1-0 a Stamford Bridge a hannun Manchester United ranar Asabar.

    Matheus Cunha ne ya ci ƙwallon a wasan mako na 33 a Premier League, inda United ta ci gaba da zama ta ukun teburi.

    Wannan na nufin Chelsea ta yi rashin nasara a wasa huɗu a jere a lig ba tare ta zura ƙwallo ba a raga a karon farko cikin shekaru 28, kuma tun daga 1912 ba ta taɓa fuskantar irin wannan mummunan yanayi ba.

    A dukkan fafatawa ta yi rashin nasara shida cikin karawa bakwai, inda aka zura musu ƙwallo 16, yayin da bakwai daga cikin ƙwallo tara da ta ci a kan Port Vale ta zazzaga a FA Cup.

    An gudanar da zanga-zanga kafin fara wasan, domin nuna rashin amincewa da yadda mahukuntan ke gudanar da ƙungiyar.

  12. Liverpool ta ci Everton a wasan hamayya na Merseyside, Premier League

    Van Dijk

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan wasan Liverpool sun yi murna a gaban magoya bayansu, sakamakon doke Everton 2-1 a gasar Premier League mako na 33 ranar Lahadi.

    Virgil van Dijk ne ya zama gwarzo, amma Mohammed Salah ne ya fara cin ƙwallo tun kan hutu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Wannan shi ne wasan farko da Liverpool ta ziyarci sabon filin wasan Everton, Hill Dickinson - da wannan sakamakon Liverpool tana nan a mataki na biyar da maki 55 da tazarar bakwai tsakani da Chelsea ta shida.

  13. Hurzeler ya yaba da ƙwallon da Mitoma ya ci Tottenham, Premier League

    Mitoma

    Asalin hoton, Getty Images

    Fabian Hurzeler ya kwatanta ƙwallon da Kaoru Mitoma ya ci a wasan da Brighton & Hove Albion ta tashi 2-2 da Tottenham Hotspur da bugun tarihin Marco van Basten a gasar UEFA Euro 1988.

    Mitoma, ya zura ƙwallon a wasan da aka yi a arewacin London, irin ƙwallon da shahararriyar ɗan wasa, Van Basten ya ci Tarayyar Soviet.

    Wannan ya taimaka wa Brighton samun maki ɗaya da kuma tsawaita wasanni ba tare da rashin nasara ba a karawa hudu, inda Georginio Rutter — wanda ya maye gurbin Mitoma — ya zura na biyu da ta kai sun raba maki.

    A lokacin da Van Basten ya ci wa Netherlands kwallon a wasan karshe a Euro 88,

    Hurzeler mai shekaru 33 ba a haife shi ba a lokacin da aka ci ƙwallon, amma ya kawo wannan misali lokacin da yake magana kan bajintar Mitoma a fafatawar.

  14. Glasner na fatan lashe Europa League na bana

    Glasner

    Asalin hoton, Getty Images

    Oliver Glasner ya jaddada cewa Crystal Palace ba ta mai da hankali kan jadawalin Premier League ba, duk da cewa har yanzu suna da damar samun gurbin zuwa gasar Turai ta wannan hanya a kaka mai zuwa.

    Hanya mafi sauƙi ga “Eagles” ita ce ta lashe UEFA Europa Conference League, abin da suke fatan yi kenan a kakar nan bayan da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a daren Alhamis.

    Duk da haka, tazarar da ke tsakanin su da gurbin shiga gasar Turai a Premier ba ta da yawa sosai, musamman ganin cewa suna da kwantan wasa ɗaya.

  15. Sociedad tana ta murnar lashe Copa del Rey, Copa del Rey

    Real Sociedad

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Real Sociedad suna ta yin murna a ranar Asabar, sakamakon lashe Copa del Rey, bayan da ƙungiyar ta Basque ta doke Atletico Madrid da ci 4-3 a bugun fenariti, bayan tashi 2-2.

    Mai tsaron raga Unai Marrero ya zama gwarzo, inda ya tare fanareti biyu da ya taimaka wa ƙungiyarsa lashe kofin karo na huɗu jimilla.

    Rabon Sociedad da kofin tun 2021, lokacin da ta buga wasan karshe na 2020 wanda aka yi a La Cartuja a birnin Seville, gasar da aka yi ba magoya baya, sakamakon cutar korona.

    A wannan karon, magoya bayan ƙungiyar Basque sun kalli fafatawar sun kuma samu marawa mata baya da ta kai ta lashe kofin.

    Mai tsaron ragar Atletico, Juan Musso, ya tare fenaritin, Orri Oskarsson, amma daga karshe Pablo Marin ya ci na sa bugun da ya tabbatar da nasarar cin kofin.

    Ƙungiyar Atletico ta Diego Simeone ta zo wasan ne bayan kaiwa daf da karshe a Champions League, amma Sociedad, karkashin jagorancin Pellegrino Matarazzo, ta yi nasara duk da cewa tana ci ana farkewa har karo biyu.

    Ana sa ran ƴan wasan Real Sociedad za ta yi murna bikin lashe kofin a ranar Litinin a San Sebastian domin nuna kofin ga magoya baya da jami'ai.

  16. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.